Tsaf Sakinah ta kammala dukkan wani abu da ya da ce ta yi kafin kwanciya baccinta, har ta kwanta Kamal bai shigo ɗakin ba, ita kuma har tsawon wannan lokacin bacci ya gagara sauka a idanun ta.
Sai kusan sha-ɗaya-da-rabi ya shi go, ko sallama babu a tunaninsa ta yi bacci, kai tsaye rage kayan jikinsa ya yi kafin ya nufi ban ɗaki ya watso ruwa, tana jinsa ya kammala dukkan wani shige da fice nasa, ya hawo gefan gadon ya kwanta.
Ko wannensu gefan da ya ke kallo daban sun jima a haka kafin da ga bisani ta ji yo tashin saukar numfashinsa a hankali, hakan ne ya bata tabbacin ya samu damar barci kenan.
Ita kuwa baki ɗayan daren barci ya gagareta har kusan ƙarfe ɗaya na dare ganin lokuta masu daraja suna wanzu agareta a banza ya sanya ta miƙewa a hankali ta nufi ban ɗaki, mintuna kaɗan ta fito jikinta duk ruwa da dukkan alamu alwala ta yi, abin sallah ta shinfiɗa tare da sanya hijab ta dubi gaban ta tayar da kabbarar sallah domin ganawa da Ubangiji a irin wannan lokacin yana da matuƙar falala da lada, kuma Ubangiji na gaggawar amsa addu’ar wanda ya roƙe shi a wannan lokacin.
Bayan ta idar ta jima zaune bisa abin sallar tana addu’o’inta, sai kusan uku da wani abu na dare ta koma ta kwanta, shi kuwa Kamal har lokacin barcinsa kawai ya ke shirga abinsa, bata jima da kwanciya ba wani barci mai wanzar da nishaɗi ya yi a won gaba da ita.
Washe Gari
Kiran sallar farko Sakinah ta farka game da salati ta miƙe tana mai bin inda Kamal ke kwance da kallo, a hankali ta kai hannu da nufin tashinsa sai kuma ta fasa domin gudun masifarsa da baya gajiya da yinta a duk lokacin da ta yi gigin katse masa barcin asararsa, wanda ya gagara ga ne hakan tun kafin yanzu.
Kai tsaye alwala ta yi yo, kafin ta nufi ɗakin Sajidah ta tayar da ita sai da ta tabbatar ta tashi sannan na koma nata ɗakin domin gabatar da rakatul-fijir, ko da ta koma har lokacin bai farka ba duk kuwa da irin karaɗin kiran sallar da ke ta faman ta shi a unguwar sabida kusancinsu da masallaci sosai ake jin kiran sallah a gidan.
Haka nan ta ji ta kasa tausar zuciyarta kamar kullum wajen jure haƙora da tashinsa, a hankali ta taka har zuwa gaban gadon tana kiran sunansa, ta kira ya kai sau biyar kafin ya buɗe ido firgigit yana binta da kallo, ta shi ya yi zaune yana faman tsaki haɗe da jefa mata hararar da ta sanya ta yin kasa da kai, domin ta san ta janyowa kanta jangwam ne.
“Wai ke har tsawon wane lokaci gargaɗina da jan kunnen da na ke yi miki a kullum za su fara shiga kunnenki iyeeh?”
Shiru Sakinah ta yi masa, ba tare kuma da ta kalle shi ba har lokacin kanta na ƙasa tana saƙe-saƙen amsar da zata ba shi mai taushi.
“Au kin ma mai da ni ɗan iska ko?”
“A’a ka yi haƙuri, gani na yi wannan shi ne lokacin da aka fi so mutum ya gai da Ubangijinsa domin samun ladan rakatul-fijir tare da tarin ladan zuwa Masallaci ga kuma ladan jam’i..!”
“Ke da Allah ya isa malama..! Wa’azin za ki yi min yau ma kenan? Tuni na haddace wannan babin kinji ko? Bana buƙatar tashinki ki barni na dinga tashi don kaina domin na fison sai ta nuna sosai na yi ta.”
“A kwai nunar Sallah da ta wuce ka yi ta a cikin lokacin ta?”
Nan ma dai tsaki Kamal ya ja, ba tare da ya bata amsa ba ya miƙe ya nufi ban ɗaki domin ba ya son maganar ta yi tsayi sabida ƙanwar Sakinah na gidan.
Sakinah murmushi ta yi tana mai bin bayansa da kallo, domin tuni ta harbo jirginsa naƙin tanka mata, domin tasan a kullum in dai har zata tashe shi to kuwa sai ya yi banbami da masifa iya iyawarsa, iya kuma ƙarfin muryarsa, kuma hakan nan dole zai je masallacin, hakan ne yasa baki ɗaya ta riga ta saba da wannan hali na shi, bata kuma bi ta kansa ba ta tayar da kabbarar sallarta.
Yanda ya ja ƙofar ɗakin na su ya buga da ƙarfi shi ya bata tabbacin ya fita masallacin Kenan, tasan har mutanan da ke waje a wannan lokacin za su iya jin ƙarar buga ƙofar, wani lokacin idan yana wani abun dariya kawai ya ke bata domin yakan zama tamkar wani yaron goye ne, ko dan ɗan fari ne? Oho.
Gari na fara haske Sakinah ta sallame karatun Alqur’anin da ta ke yi ta shafa addu’a, kafin ta miƙe tsaye tana mai ninke abin sallar ta ajiye a inda ta saba ajiye shi ta fito domin shi ga kitchen, can ta tadda Sajidah tuni ta fara yi mata dukkan abin da ya da ce ta yi a lokacin, hakan ba karamin daɗi ya yiwa Sakinah ba, shi yasa sosai ta ke jin daɗin zama da ƙanwarta ta sabida sanin ya kamata irin nata.
7:00am
Ƙarfe akwai daidai agogon ɗakin ya buga lokacin tuni sun kammala dukkan abin da ya ce, har sun fara kici-kicin haɗe kayayyakin ɗakin waje guda, sai lokacin Kamal ya shigo gidan kai tsaye wajen Hajiya ya nufa ya gaisheta kafin ya dawo na su ɗakin, a falo ya taddasu duk sun haɗe kujerun da komai, Sajidah ta durƙusa ta gaishe da shi ya amsa fuska a sake yana mai wucewa cikin ɗakin barcinsu.
Sakinah ta miƙe ta nufi kicin mintuna kaɗan ta fito hannunta ɗauke da babban tire cike da kulolin abinci ta nufi cikin ɗakin.
Zaune bakin gado ta hangeshi riƙe da waya yana dannawa, a jiye farantin ta yi ƙasa ta russuna tana mai gai da shi ya amsa ba yabo ba fallasa, zama ta yi gaban kayan abincin ta fara ƙoƙarin haɗa masa abin karin kumallonsa, shi kuwa gogan sai wani shan ƙamshi da basarwa ya ke yana wani ƙara hakimcewa.
Sai da ta gama haɗa masa komai sannan ta fito zuwa falo wajen Sajidah domin su cigaba da aikin, tarar da ita ta yi tana waya cike da nishaɗi bama ta lura da fitowar ta ba sai daga baya ta ce.
“Au ga Aunty Sakinan ma.”
Ta ƙarashe maganar tana mai miƙa mata wayar, Sakinah ta amsa tare da kara wayar a kunnenta haɗe da sallama ta ke faɗin.
“Yayanmu kana lafiya, ya karatu? Ka ƙi dai sanarmana yaushe zaka dawo don kar mu tana de ka ko?”
Daga can ɓangaren ya amsa murmushi kwance bisa fuskarsa har ƙasan ransa ya ke jin nishadi ainun, domin daga yanda ya ke furta magana zaka fahimci hakan.
“Duka waɗan nan tambayoyin ni ka ɗai? Zaɓi wacce ki ke so na amsa miki?”
“A’a duka ina buƙatar amsarsu.”
A tare suka yi dariya kafin ya cigaba da faɗin.
“To shi kenan, komai lafiya ƙalau Ƙanwata, batun zuwa kuma cikin satin nan insha Allah, da a ce ma ni wani hamsaƙin mai kuɗi ne visa zan yi muku ku zo ku tafi da ni, ko ya ki ka gani?”
“Wallahi kuwa da munji daɗi sosai, yau a ce gani a cikin jirgi a ƙasar Misra tab..daɗi kashe ni.”
Suka kwashe da dariya har Sajidah da ke zaune gefe tana sauraronsu.
“Dama kira na yi na ji lafiyarku, sannan na gabatar miki da albishir.”
“Albishir ɗin samun budurwa zaka min ko?”
“Allah shirye ki Sakinah, ke damuwarki kenan ko?”
“Amin, E mana, muna buƙatar ganin ka yi aure ne sosai.”
“Zan yi ne insha Allah, lokaci dai Sakinah na nan zuwa, kinga mubar wannan batun, na turowa Zainuddeen kuɗi anjima zai kawo miki furniture, sai ki yi list na kayan kitchen dukkan abin da ki ke buƙata sai a canja miki.”
“Haba dai, da gaske Yayanmu?”
“Na taɓa yi miki irin wannan wasan?”
“A’a Yayanmu, kai masha Allah na ji daɗi sosai wallahi Ubangiji Allah ya ƙara buɗi ya saka da alkhairi nagode sosai.”
“Amin, amma dai ki bar godiyar haka ai nauyi na ne, karki damu da ina da kuɗi ma zan yi miki wanda ya fi haka kin ji?”
“Hakan ma nagode sosai, amma kai da ka ke karatu kuma kana irin wannan hidima haka.”
“Ke..! Karki damu kanki fa, ba fa zaune na ke haka ba, ko kinmanta a kwai shagunan mu da Zainu ke juya mana, kuma a nan ma na samu wani aboki na kirki muna business sosai, sai na dawo za ki sha labari ai.”
“To Allah ya dawo mana da kai lafiya.”
“Amin Amin, babu wata damuwa ko?”
“Komai lafiya ƙalau wallahi.”
“Masha Allah, ku huta lafiya ki gaida mutanan gidan.”
“Za su ji insha Allah.”
A tare suka kashe wayar cikin nishadi da annashuwa Sakinah ta rungume Sajidah tana faɗin.
“Wayyo Sajidah Yayanmu ya canja min kayan ɗaki.”
Tsalle Sajidah ta yi dan murna har da juyi tana faɗin.
“Kai amma na taya ki murna wallahi, to yanzu waɗan nan ina za’a kai su?”
“Mu bari idan ankawo sababbin sai a tafi da waɗan nan a kaiwa Ummah ko?”
“E haka ne, ta shi to muƙarasa aikin, ko mu fara karyawa?”
“Da dai ya fi.”
Sakinah ta yi maganar tana mai ficewa ta nufi kitchen domin haɗo musu abin kari.
Kamal da ke tsaye jikin window yana jin dukkan abin da su ke yi, ya ɗan taɓe baki kaɗan a fili ya furta.
‘Aikin ɓur…! Koma mene za’a canja ba zai taɓa burge ni ba ehee.’
Ya juya tare da komawa gaban kayan abincinsa ya cigaba da ci yana mita.