Karima ta yi 'yar gajeriyar dariya tana mai gyara zamanta sosai, kafin ta janye mayafinta ta ajiye kan gadon tare da duban Sakinah ta fara magana da faɗin.
"Ka da ki yi min mummunar fahimta, ba fa tashi tsaye na zuwa wajen malamai na ke nufi ba."
"To ina jinki," cewar Sakinah da ta kafe Karima da ma daidaitan idanuwanta.
"Gaskiya ki dage da addu'a sosai Sakinah, duk da na sanki ba baya ba, amma ki ƙara dagewa fiye da yanda na sanki a da, ki kuma dinga janyo Kamal a jiki tare da tausarsa a hankali har. . .