Skip to content
Part 8 of 10 in the Series Jini Ba Ya Maganin Kishirwa by Qurratul Ayn Salees

‘Da Zaki bi shawarata Sakinah ka da ki yarda Kamal ya aure ki akan sharaɗin ba za ki yi aiki ba, sabida ko zuwa gaba ina guje miki ranar da za ki buƙaci hakan ya ce a’a, bana tunanin da ilminki da komai za ki iya dauwama a haka takaddu zube ƙura na cika su tsayin shekaru.’

‘Ya Jaheed kenan, insha Allahu babu wata matsala, ni daman bawai son yin aikin na ke ba, kawai dai karatu yana da matuƙar amfani ne a zamanin da muke ciki a yanzu ko dan gudun wata rana, sabida akwai damar da zata iya zuwa ga mutum kwatsam kaga sai ya fito a dama da shi.’

‘Na dai fahimci soyayyar da kike yiwa Kamal ta kai wani mizani mai wahalar aunuwa ba lallai ne ki fahimci abin da nake son ki fahimta ba, babu matsala Allah ya tabbatar da alkhairi Sakinah.’

Sakinah na zuwa nan a tunanin ta sake fashewa da wani irin matsanancin kuka mai cin rai kasa jura ta yi, hakan ya sata miƙewa daga kan gadon ta fito zuwa falon inda Kamal ya yi gado da doguwar kujerar falon ya sanya filo ya kwanta, idonsa a rufe kamar mai bacci, Sakinah da ke tsaye tana kare masa kallo ta yi nufin juya da nufin barin gurin sai taga ya bude ido a hankali, duba ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai tare da juya mata baya.

Sakinah ta ƙaraso wajen nasa ta durƙusa daidai kansa tana faɗin.

“Dan Allah ka yi haƙuri ka barni na yi aikin nan, ka da ka yi yunƙurin ɗaukan mataki mai tsauri a kaina tun yanzu, na yarda in dai ka ga ina ba daidai ba ka hana ni zuwa aikin, amma yanzu karka ce a’a dan Allah.”

“Kin san dai bana magana biyu ko? Magana ɗaya tak na ke yi bana kuma sake wata ko na canja ta.”

Kamal ya bata amsa ba tare da ya juyo ya dubeta ba, Sakina tsaye ta miƙe tana mai share hawayen ta, tare da naɗe hannunta duka biyu a ƙirjinta ta cije leɓanta da ƙarfi kamar zata huda su da ƙyar ta iya sarrafa bakinta wajen faɗin.

“Ban taɓa tunanin a ɗan wannan taƙaitaccen lokacin zan iya fara da na sanin aurenka ba Kamal, yau ɗaya na ji ka fita a raina Kamal tare da tsanar aurenka da na yi gaggawar yi, ba tare da karantar asalin halinka na ɓoye ba, ka cutar da ni Kam!”

Kuka ne ya ci ƙarfinta sosai, wanda ya yi sanadiyyar sarƙewar harshenta har maganar da take yi ta samu damar sarƙewa ganin hakan ya sanya ta komawa cikin ɗaki da gudu ta faɗa kan gado tana gunjin kuka.

Duk surutun da ta ke yi Kamal ko juyowa ya dubi inda ta ke bai yi ba, sai bayan ya ji shigewarta ɗaki ya miƙe zaune a fusace cikin zafin nama ya damƙo filon da ya kwanta a kai ya yi jifa da shi ƙasa tare da dafe kansa hannu biyu yana huci cike da matsanancin jin ciwo da zafin maganganun da Sakinah ta gaya masa, nan ta ke ya ji kaman ya miƙe ya je ya rufe ta da duka ko ya samu sa’ida cikin ransa.

Sai dai ya yi ƙoƙarin tausar zuciyarsa kasancewar tunawar da ya yi basu ka dai ba ne a gidan, amma ba dan hakan ba yasan babu abin da zai hanashi sasata.

“Dan taga ina kyaleta ne yasata samun talala da yawa haka har da zata tsaya tana gaya min maganganu son ranta.”

Ya ƙarashe maganar yana mai yin kwafa ya koma ya kwanta fuskarsa na kallon ceiling tare da naɗe hannuwansa a ƙirji ya zubawa fankar da ke juyawa a hankali ido tamkar mai lissafin juyawar da ta ke yi.

Dukkan su bacci a wannan daren sai ɓarawo.

Washe gari

(Rana bata ƙarya…)

7:20am

Yau take juma’a kuma rana wacce ta kasance babbar rana ga dukkan al’ummar musulmi, amma ga Kamal farin cikinsa a wannan ranar ya zarce dukkan tunanin mai tunani, ya kuma tsalle tsammanin masu tsammani.

Yauma kamar jiya su Sakinah tun asuba basu koma bacci ba tuni suka hargitse gidan da aikace-aikace har ƙarfe bakwai da mintuna, wasu da ga cikin maƙota suka shigo domin ɗan taya su aiki, ka sancewar Hajiya ta ɗan aikawa waɗanda tasan sun zama dole a gareta, bare kuma tasan ko bata aike ba za suji sabida yanda maganar auren ta karaɗe dangi da unguwa.

Kamal ango tun shida na safe ya fice da nufin za suyi wasu shirye-shirye kafin zuwa lokacin ɗaurin auren, saboda a masallaci za’a daura bayan sallar juma’a kamar yanda aka rubuta a jikin katin.

Haka gidan Hajiya Shema’u tun jiya ya ɗinke da ‘yan uwanta da ƙawaye damƙam, saɓanin kuma wayewar garin juma’ar ƙawayenta tun safe suka fara sallama a gidan kasancewarta mace mai mutane kuma hamshaƙiyar mace da ta yi suna ta kowanne fanni dalilin bazuwar maganar auren kenan.

Hajiya Shema’u ce zaune kan makeken gadonta tare da ƙawayenta su biyar wasu a kwance wasu a zaune, a marya tasha jan lalle da ɓaki gwanin ban sha’awa da ya ke fara ce ita tas sosai zanan ƙunshin ya bayyana raɗau a jikinta, kanta kuwa ya sha kitson attachment har gadon baya baƙi siɗik sai sheƙi ya ke yi.

Ɗaya daga cikin ƙwayenta ta dubeta tare da ɗan da fa hannun Hajiya Shema’u tana faɗin.

“Amarsu ta Alhaji Kamal, kinsha ƙamshi wallahi mutuniyar.”

Wata baƙa siririya da ke zaune gefe ta amshe da faɗin.

“Ai Shema’u ba da ga nan ba, ni kuwa ya labarin kishiyar taki?”

Biyu daga cikin su waɗanda suke farare ne ma’abota zubin manyan mata sosai suka tafa haɗe da shewa tare da yin guɗa ɗaya daga ciki na faɗin.

“Kamilar kishi zaki ce.”

Suka kuma kwashewa da dariya tare da shewa, Hajiya Shema’u ta yi murmushi kafin ta ce.

“Lallai kuwa Kamilar kishi wai ni zata nunawa barikanci, mu da muka ginu cikin barikin, nan ya zo min yana faɗamin wai bata nuna kishi akan auren mu, da alamu kuma haushin hakan ya ke ji, ki ji min wata tsiya.”

Nan ma dariyar suka sanya duka kafin ɗaya ta amsa da faɗin.

“Ai nasan halinki mutuniyar to ya kuka ƙare da shi?”

“Ni kuma zama zan yi ina ɗiban kayan takaici kenan?”

“To yanzu ke me kika yanke nasan dai ba haka nan kike zaune ba, dole zaki ɗau mataki domin ba kisan me ta taka ba.”

Cewar wata mace wadda duk ta fisu jiki sosai a cikin su a girme ma zata iya ɗarasu da wasu shekaru, Hajiya Shema’u ta gyara zama da wani yalwataccen murmushi akan fuskarta kafin ta furta.

“Kamar kin mance da wacece ni Hajiya Turai? Shema’u fa na ke, ka da ki manta da wani abu guda ɗaya, shiru ba ya da wata katara, shintatar shiru abu ne mai matuƙar wahala, amma wanda ya yi shiru ba’a san iya tsaurin tana dinsa ba.”

<< Jini Ba Ya Maganin Kishirwa 7Jini Ba Ya Maganin Kishirwa 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.