Ajiyar zuciya ya sauƙe yana a hankali, yana ƙoƙarin dai-daita zamansa a kan kujerar.
“Na gode Matata!” Ya samu bakinsa da faɗar hakan a hankali, har a lokacin yana jin wani abu na yawo a kansa.
“Baka gajiya da gode min ne?” Ta tambaye shi a lokacin da ta ke zuba masa soyayyan dankali da ƙwai a plate ɗin da ta ajiye a gabansa.
“Kin taɓa ganin mutum ya gaji da da jin sautin bugawar zuciyarsa?”
Murmushi ta yi bayan ta haɗa masa shayin ta kurɓa, ta ji zafin ya yi dai-dai kana ta ajiye masa.
Zama ta yi akan kujerar kusa da shi, sanan ta sa cokali ta ɗauki dankalin da kwai ta kai bakinta, sai da ta haɗiye ta ƙara ɗiban wani.
Sannan ta ajiye masa cokalin “Bismillah Ya sayyadi!”
“Na ɗauka za ki ba ni ne a baki ai!” Ya yi maganar yana lumshe idanuwansa da sauƙe shi a kan fuskarta.
Dariya ta yi mai sauti wanda ta sa ya ƙura mata ido, yana jin sautin zuciyarsa na ƙara bugawa, yana jin wani farin ciki na lulluɓai shi.
Bai san lokacin da ya yi murmushi ba “Kina da kyau a lokacin da kike dariya Nahna!”
Fuskarta ta tsuke, sai dai har a lokacin da murmushi a fuskarta “Ko me nawa yana da kyau a tare da ni Abdul-Mannan. Shi yasa na ke ta musamman.”
Kai ya girgiza sannan ya ɗebi abinci ya kai bakinsa “Wannan fa alfahari ne da yawa, kuma kin san babu kyau.”
Kai ta girgiza tana taɓe bakinta “Ni’imar da aka min dai na ke yabawa, na ke kuma magana a kanta. Kamar dai yanda Allah s.w.a ya ce mu bada labarin ni’imar da ya mana.”
“Ta ki ya wuce labari Nahna! Ji da kai ne.”
Idanuwanta ta wara tana wurga su gefe “To idan ban ji da kai na ba, da wa zan ji?”
“Ki ji da ni kawai!” Ya yi maganar yana ƙoƙarin gimtse dariyarsa.
“Hehehe! Wai almara kenan! Adadin wani lokaci kake so na ji da kai Abdul?”
Ta yi maganar tana ɗora hannunta a kan nasa “Har ƙarshen rayuwa!” Yayi maganar yana ɗora idonsa a kanta, janye idanuwanta ta yi daga nasa, domin tana jin kaifinsu na ƙoƙarin yi mata illa. Akwai abin da ta ke so, akwai abin da ta ke shiryawa.
“Zan baka shekaru huɗu na rayuwata! Zan ƙawata ma ka su da baka ko wata kulawa a cikinsu! Bayan su kuma?”
“Me ya sa ba zai zama har abada ba! Me yasa shekaru huɗu kawai Nahna?”
Ya yi maganar yana ture filet ɗin daga gabansa, yana kafeta da idanuwansa, da ruwa ya taru a cikinsa.
Murmushi ta yi tana sosa girarta da babban yatsanta, daga bisani kuma ta ɗauko hanunta ta ɗora a tafin hannunta sanan ta sake ɗora nata hannun a kansa. Ya zama nasa hannun na tsakiyar ta sa.
“Su ne adadin lokacin da nake da tabbaci akanka. Akwai ƙaddara da kan yi rubutu ga rayuwar kowa, ta iyu ƙaddararka ta zama mai ƙarfi. Ni kuma ina ƙoƙarin rubuta labarina a cikin taka ƙaddarar.
Shekaru huɗu sun min yawa akan tanadin da nake da shi, daga baya kuma na fahimci cikar burinka zai taimakawa alƙalamina wajen yin rubutun da babu gargada.
Ni mallakinka ce da dukkanin abin da kake so a tare da ni. Har zuwa wannan lokacin zan zama magijin da makunnarsa ke riƙe a hannunka. Ba zan ce komi ba, ba zan ƙi komi ba, muddum kai zaka so shi, kamar yanda zaka faɗa.”
Idonsa ya lumshe yana ɗora hannunsa ɗayan akan nata, yana ganin yanda kalar fatarsu ta ban-banta ta samar da kalar madara da furanto.
Dogayen yatsunsu da suka kusa zama kai ɗaya sun taimaka wajen ƙawata kyan hannayen nasu a tare.
“Ina so hannayenmu su ci gaba da kasancewa a haka har abada. Ban san me kike rubutawa ba, ban san me kike son cimmawa a shekaru huɗun da kike magana ba.
Amma ina da tabbacin rayuwarmu duk a haɗe ta ke a waje ɗaya. Duniya ƴar ƙarama ce, da take ɗauke da ƙananun mutane ma su manyan buruka. Kaɗan ne a cikinsu suke dace wannan burukan na su ya cika.
Sai dai ni a gareki kamar idanuwa ne da ke jagoranci ga gani, duk lokacin da kika kakare a cikin tafiyarki, ki kirani zan ɗigawa alƙalaminki ruwa ta yanda zaki yi rubutu mai kyau.”
“Idan hakan ya shafi kimarka fa?” Ta yi saurin tarar maganarsa.
Murmushi ya yi yana gyaɗa mata kansa “Muddum za ki yi dariya, zan bari ta zuba a ƙasa kowa ya taka ya bi ta kanta.”
Yana gama maganar ya zame hannunsa daga cikin nata, yana tashi akan ƙafafuwansa.
Da ido ta samu damar yi masa rakiya “Ba zaka iya ba Abdul!” Ta yi maganar tana girgiza kanta.
“Ki bari lokaci ya tabbatar miki da hakan.” Ya juya ya nufi ƙofar waje yana ɗaga mata hannu da murmushi akan fuskarsa.
Idonta ta lumshe tana jin duniyar na juya mata da sabon ƙunci, tana jin takaici da shirmen da ta ke ƙoƙarin yiwa kanta. Shekaru huɗu zata zauna a jibge a waje ɗaya ba tare da ta yi komi ba.
Kanta ta shiga bibbigawa da tafukan hannunta. “Gaskiya ni zararriyar mahaukaciya ce!” ta yi maganar cikin sarƙewar idanuwanta sun sauya kala zuwa ja.
Can kuma ta yi shuru sai ta saki dariya ita ɗaya.
Daga nan ta ci abinci ta tattare kayan, da suka ɓata ta kai kitchen, ta yi wanke-wanke. Sannan ta ƙara gyara gidan da kunna abin ƙamshi.
Bayan ta gama ta koma kitchen ta ɗora girkin rana, ta jima tana nazarin abin da zata girka.
Daga ƙarshe ta buɗe firji ganin akwai nama da kaji a ciki, ta ɗauko kazar ta gyarata ta ɗorata silacenta, farfesunta za ta yi, duk abin da xata buƙata ta tana de su a gefe.
Gefe ɗaya kuma ta ɗora dambun kus-kus dan ta a yanda ta ke jin jikinta ba zata yi aiki mai wahala ba.
Sai da ta gama komi harda wanke kayan da ta ɓata. sannan ta fito a kitchen ɗin ƙarfe ɗaya da rabi, ta ji ana kiran sallah a babban masallacin da ke unguwarsu.
“Ya Allah lokaci har ya tafi haka?” Ta faɗa cikin sauri ta shiga toilet ta yi wanka sannan ta ɗora alwala ta futo.
Doguwar riga ta sa ta material ja mai ratsin fararen fulawa a jikinsa, bata tsaya kwalliya ba ta yi sallah.
Bayan ta idar ta daɗe zaune a sallaya tana azkar daga bisani ta tashi ta zauna gaban mudubi.
Kwaliya ta yi mai kyau, da murza ɗaurin ɗankwali, ta daɗe tana kallon fuskarta jikin ƙaton mudubin, a hankali ta yi murmushi.
“Wai ma banda son kai ta ya za a yi mace zuƙeƙiya kamata ace ta ƙare rayuwarta a tare da ustazu? Ustaz ɗinma wanda kullum cikin wa’azi ya ke! Kada ki kunna kiɗa, ki bar rawa, ki yi komi banda taɓa kimata.” Ta ƙarasa maganar tana kwaikwayon muryar Abdul-Mannan ɗin da rangwaɗa kai da taɓe baki.
“Kimo ba kima ba!” Ta yi maganar tana tashi tsaye da nufar waje.
Ja ta yi ta tsaya ganinsa harɗe da hannunsa a kan ƙirjinsa yana murmushi.
Idonta ta kanne tana kallonsa “Laɓe dai babu kyau! Balle kutse a gidan mutane babu sallama.”
Murmushi ya yi yana tako da ƙafafuwansa zuwa kusa da ita har sai da ya matso kusa da ita suka fara jiyo hucin numfashin junansu “Kina nan kina gulmata ta ya za ki ji sallamata?” Ya yi maganar yana hura iska a idonfa da kuma matsowa kusa da ita.
“Kyakkyawar mace ɗauke da launin fure mafi kyau da daraja. Uhmmm bayan Ustaz dai bana tunanin akwai wanda zai san darajar wannan furen. Ustaz ɗin dai Nahna! Shi kaɗai ne zai tsaya a gabanki ya yabi kyanki.”
Kanta ta kawar gefe tana murmushi mai sauti har kumatunta ya lotsa.
“Daga baya za mu yi wannan maganar Abdul.”
“Me yasa ba yanzu ba?”
Hannunta ta ɗora a kan laɓɓanta tana hura masa iskar bakinta a idonsa kamar yanda shima ya mata.
“Ina adana lokacina ne a yanzu Abdul. Ina kuma rage zafin da nake ji ne a duk lokacin da na kasance a tare da kai. Dariya na ke so na yi, amma idan na yi ba daga zuciyata ta ke fitowa ba, a baki kawai na ke jinta. Ka san me yasa haka?
Kai ya girgiza mata yana lumshe idanuwansa.
Ƙirjinsa ta ɗan buga da yatsunta guda ɗaya, sai tin hagun ɗinsa “Saboda babu ruwan zuciya da kusanci da sabo, ita tana karɓa ne daga abin da ta so ba tare da ka shirya hakan ba.”
Ido ya sake lumshewa yana kallon hannunta da ke zagaya ƙirjinsa, yana kallon ƙaramin bakinta mai cike da magana a cikinsa, yana kallon kyakkyawar fuskarta da ta ke ɗauke da ƙuruciya.
“Akwai baƙi a palo suna jiranki.” Ya yi maganar yana ruƙo hannunta suka fito falon.
Bata fahimci yanayin fuskarsa ba, hakan na bata mamaki ƙwarai. Kamar dai yanda murmushi bai ɗaukewa a kan kyakkyawar fuskarsa.
Ido ta waro waje ganin falon cike da yayyenta mata da ƙannenta. Har ta yi tsalle tana ƙoƙarin sakin hannun Abdul-Mannan ta tafi da gudu ta ji ya riƙe hannunta gam yana girgiza mata kai.
“Ina so na je na rungumi Adda Halima.”
Ta yi magana tana nuna masa ita da ido, wanda duka su hankalinsu ba ya kansu.
Hannunta ya saki yana murmushi hakaa ya sa ta sa tsalle da ihu. Wanda ya sa shi toshe kunnensa da lumshe idonsa, suma yaran da gudu suka nufeta suna mata oyoyo, duk da sanin halinta.
Sai dai bata basu kunya ba ta rungume sun, tana ƙarasawa tana gaida yayyenta da Anty Lubabatu matar yaya Ado.
“Nifa da fushi na ke yi ma! Saboda baku zo ba har sai da na yi kwana uku.”
“Ki yi haƙuri ƙanwata! Muna ta fama da baƙi ne, kuma mun baku dama akan ku huta ne sosai kada mu dame ku!” Adda Halima ta faɗa tana murmushi da riƙe hannun Hafsan.
“Mun kuwa huta sosai.” Ta faɗa tana kai kallonta ga Adda Halima.
Kafin ta tashi tsaye “Ba na kawo muku abin motsa baki.”
Bata jira maganarsu ba ta shige kitchen ta ɗauko musu lemo da ruwa sai kofuna.
Ta fito da shi a hannunta, da kanta ta zuba musu sannan ta kai kallonta gare su.
“Nan zan kawo muku abinci ko kuwa dai za ku zo mu je daining table?”
“Haba sai kace mu ne rumbu, daga zuwa sai ci?” Adda Halima ta faɗa tana murmushi suma suna tayata.
“Ko da ba rumbu kuke ba, kun dai san ba za ku zo ku tafi baku ci komi ba. Tunda kun zo sai ku sa wa girkina Albarka.”
Ta yi maganar tana tashi da shiga kitchen ɗin, sai da ta ɗibawa Abdul-Mannan nasa daban sannan ta ɗauko musu ƙatuwar kular.
“Aysha na gaji je ki ɗauko faranti da cokala a kitchen.” Ta yi maganar tana ajiye kulolin.
Wadda ta kira da Aysha kuma ta tashi da sauri ta shiga kitchen ɗin.
“Ke Hafsa abincin gidan na ke ga kin ɗauki mana gaba ɗaya. Kuma mijin naki fa?” Adda Halima ta faɗa da mamaki.
“A’a nasa daban ya ke, bari ma naje na bashi ya ci kada na barshi da yunwa. Kafin na zo ku kuma nasan kun gama ci.” Ta faɗa tana tashi da barinsu da sakekken baki.
“Shegiya Hafsa kamar ba ita ke cewa bata son Auren ba.” Anty Lubabatu ta faɗa suna dariya, ita Bilkisu da Khadija yayun Hafsan.
Shuru Adda Halima ta yi tana bin bayan Hafsa da ido har sanda ta wuce da abincin a hannunta “Akwai dai wani abu!” Ta faɗa a hankali.
A lokacin kuma Aysha ta kawo musu tiren, Khadija ta karɓa ta zuzzuba musu, nasu daban na yaran ma daban.
Suna ci suna hira “Oh ashe dai ƙanwar taki ta iya girki Adda Halima.” Anty Lubabatu ta faɗa tana sake kai cokalin bakinta.
“Khadija ki mata waigi kada ta faɗi.” Adda Halima ta faɗa.
Suka yi dariya a tare, har suka gama cin abincin suka share wajen Hafsat bata futo ba.
“Da alama za mu tafi ba mu yi sallama da amarya ba.” Bilkisu ta faɗa tana kai kallonta ga agogon da ke maƙale a hannunta.
“Kaɗan daga halin Hafsa kenan! Ai ta ce dama fushi ta ke.” Anty Lubabatu ta faɗa.
A lokacin kuma Hafsa suka fito da Abdul-Mannan tana riƙe da hannunsa sai magana ta ke shi kuma yana murmushi.
Khadija ce ta ɗauko wayarta ta musu hoto “Shegiya yarinya tana bata so ku ganta ta maƙalƙale shi, wannan hoton har gaban Alhaji Malam zai je.”
Ta sake ɗaukan wani hoton dai-dai lokacin da suka haɗa ido suna kallon juna da yin dariya a tare.
“Ya Allah Anty Lubie kalli kiga haɗuwa.” Khadija ta faɗa tana miƙa mata hoton.
“Na yarda hoton da ba a shirya masa ba mugun kyau ya ke.”
Har rige-rigen karɓan wayar suke tsakanin Anty Lubabatu da Bilkisu, ita dai Adda Halima bata ce musu komi ba.
“Masha Allah!” Shine abin da suke faɗa a tare.
“Ku yi haƙuri na barku ku kaɗai. Na bawa Sayyadina abinci ne, na kuma taya shi shiryawa.” Hafsa da ta zo wajen ta faɗa bayan ta saki hannun Abdul.
Harara Khadija ta maka mata “Ai da kin zo kin tarar mun tafi.”
Risinawa Abdul-Mannan ya yi yana ajiye musu rafar ƴan ɗari biyu.
Sannan ya miƙawa su Aysha rafar ƴan hamsin. “Ku sha alawa da wanan a hanya.
Adda Halima mun gode da ziyara mu isa gida lafiya.” Ya faɗa yana tashi tsaye.
“A’a Malam Abdul ka zo ka amshi kuɗinka, wanda ka bawa yaran ma mun gode Allah ya amfana.”
Murmushi ya yi ba tare da ya juyo ba “Adda ai kin san hukuncin mai dawo da kyauta dai.”
“Ina da ban-banci da wanda kake tunani Malam Abdul. Mun gode sosai.” Ta yi maganar tana kallon Hafsa, sannan ta mayar da kallonta ga sauran ƴan uwan nata, da hankalinsu ke kan wayar Khadija.
“Zo mu je ƙanwata!” Ta faɗa tana tashi akan ƙafarta. Itama Hafsa ta bi bayanta har zuwa ɗakinta.
Zama ta yi akan gadon itama Hafsa ta zauna.
Kallonta Adda Halima ta yi na ɗan lokaci kafin ta yi murmushi ta girgiza kanta “Me kike son shiryawa Hafsa?”
Kallonta Hafsa ta yi da jin tambayar a matsayin bazata “Kamar ya me na ke son shiryawa Adda Halima?”
Kallonta Adda Haliman ta yi “Sauyin da na ke gani a tare da ke, da kuma murmushin da kike akan fuskarki, bai kai har zuciyarki ba. Ina ganin ƙuna a idanuwanki, ina ganin yaƙen da ke tsayawa akan fatar bakinki. Duk waɗan nan abubuwan na me ye ne Hafsa? Me ki ke shirin yi? Me ki ka tanadarwa Abdul-Mannan?”
Idonta ta waro waje tana kallon Adda Haliman da ta ke faman jero mata tambaya.