Skip to content
Part 11 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

“Yaushe kika zama malamar halayyar ɗan Adam Adda Halima? Asanina dai da ke, ke matar Sayyadi Ƙasim ce  ban sani ba ko kin koma …”

“Hafsa ba fa shirme na ke magana a kai ba. Ko ma ya nake kin sani ni ce mace mafi kusanci da ke, da kuma sanin halayyarki.” Adda Halima ta faɗa tana matse fuska da kafe Hafsan da idanuwanta.

Murmushi Hafsa ta yi, sannan ta ɗauki hannun Adda Halima ta haɗe da nata tana matsawa “A cikin ko wata rayuwa ta ɗan Adam akwai sauye-sauye na warwarar zaren da ke cure ga labarinsa.

Wani kan zama sauyi mai kyau da samar da kyakkyawar rayuwa ta har abada ga wannan mutumin. Wata kuma takan warware masa munanan burukan da ke danƙare a cikin duhuwar zuciyarsa.

Gaskiya kan yi kokawa da zama mai nasara a lokacin da take fatattakar ƙarya, gaskiyar da kan sa idanuwa su buɗe, zuciya ta karɓeta a lokacin da ta bata shirya ba.”
Murmushi ta yi tana sauƙe ajiyar zuciya a kare na biyu “Kun daɗe kuna faɗa min Hafsa kin yi sa’a kin auri miji ɗaya da ɗaya. A lokacin ban ji hakan a raina ba, ban yarda cewa Abdul ya kai mijin da zan iya shimfiɗa rayuwata a tare da shi ba, har yanzu ina jin kuma hakan a zuciyata.

Sai dai na sani, babu inda hakan zai kai ni, babu nasarar da zan cimma ga hakan face faɗuwa. Tun ina ƙarama ake karantar da ni akan ƙaddara, hakan ya sa na fara rubutu akan yanda ƙaddarata zata same ni.

Zan zauna da Abdul, zan zauna da shi har sai kun ji a ranku na zauna da shi. Zan wadata fuskata da murmushi koda ace a zuciyata akwai ƙuna. Zan sa shi ya yi dariya har sautin dariyarsa ya ratsa kunnuwan da ke kusa da shi.

Sai dai ban san kuma mai gobe zata haifar ba, ban san ko hakan zai tabbata har ƙarshen rayuwa ba. Amma zan yi abin da zan iya yi Adda Halima.”

Ta ƙarasa maganar tana zame hannunta daga na Adda Haliman, a karo na biyu tana murza gashin girarta da shimfiɗa murmushi akan fuskarta.

Kallonta Adda Halima ta yi, a yayin da take haɗa maganarta tana mai-maita su a zuciyarta, da kuma son ajiye ko wacce a muhallinta da ya dace.

Ta riga da ta san wacece Hafsa, bata buƙatar a faɗa mata ko me a game da ita, ta san me wannan sosa girar ke nufi, duk lokacin da ta taɓa girarta zata yi haƙo mai zurfin da zai zurma wanda ke kusa da ita.

Murmushi ta yi tana girgiza kanta, kafin ta yi magan Khadija suka shigo ɗakin da Anty Lubabatu “Lokaci ya tafi Adda Halima, ya kamata mu tafi gida mu fata haɗa na mu komatsan mu koma tamu nahiyar.” Khadija ta faɗa tana kallon su da yawata idanuwanta a ɗakin.

“Oh ni Khadija, ashe akwai ranar da zan shigo ɗakin Hafcy naji ƙamshi na tashi ta ko ina?”

“Kin dai san dama baki taɓa tarar da  nawa ɗakin da dattiba ko a lokacin da nake gida ne Anty K.” Ta yi maganar tana ƙarfafa K ɗin.

Kanne ido ɗaya Khadija ta yi “Wato ba zaki raba kanki da kirana da wanan sunan ba ko Hafsa? Ni na rasa inda ma aka yi kika raina ni wallahi.”

Kai Hafsa ta risina tana haɗe hannu “Allah ya huci zuciyar babbar yaya, matar Dakta Suraj Sayyid.”

Duka ta kai mata ta yi saurin zamewa suna sa dariya a tare.

“Ba zaki sauya ba sam Hafsa.” Anty Lubabatu ta faɗa tana dariya.

“Zan sauya Anty Lubbie! Har sai da kanku kun ce Anya wannan Hafsan Umma ce.”

“Ban ga wannan ranar ba sam.” Khadija ta faɗa tana taɓe baki da sake kallon agogon hannunta.

“Adda Halima mu tafi ko?” Ta yi maganar tana kwantar da kanta.

Tashi Adda Haliman ta yi tana kallon Hafsa “To ƙanwa mu zamu tafi, za mu tafi da fatan alkhairai masu yawa a gareki, zamu tafi da tabbacin mun barki da kyakkyawan murmushi akan fuskarki.

Za mu bada labarin abin da idanuwanmu suka gane mana, sai dai..”

Ta yi shuru kafin ta tausasa muryarta a hankali yanda ita kaɗai zata ji “Ba zan yi hasashen abin da kike shiryawa ba, domin kina haƙa ne ki binne ba tare da idanuwa sun ankare da hakan ba.

Sai dai akwai ban-banci da tazara mai yawa tsakanin wancan haƙar da kika saba yi. Wannan idan kika yi ƙurar zata bibiyi rayuwarki ne har abada, zata yi ta buɗeki a yayin da hazonta zai gallabi rayuwarki.

Ki yi abin da kike son yi, amma kada ki yi wanda zai zame miki tambarin shahara marar alƙibila.”

Ta yi magana tana shafa gefen fuskarta da kuma rungumeta “Allah ya miki albarka ya kare rayuwarki.”

Tana gama faɗar haka ta zame jikinta ta yi gaba ba tare da ta waiwayo ba. Tana jin taruwar hawaye a idanuwanta, hawayen da bata san ko na me ye ba, sai dai tana jin wani tsoro na huda zuciyarta.

Itama Hafsat da kallo ta bi su, tana jin maganar Adda Halima na mata yawo a rai da zuciyarta ‘Me yasa kowa ya ke cewa ta yi Abin da ta ke so?’ A hankali ta cira ƙafarta zuwa gaban mudubin da ke ɗakin, tana ƙarewa fuskarta kallo, ganin zata ɓata lokaci ta ɗebi kayan kwalliya da turaruka ta fita a ƙofar gida ta samu wasu wasunsu na zauren gidan.

Aysha ta kira ta miƙa mata kayan kwalliyar.

“Na gode sosai. Allah ya ƙara zumunci.” Ta faɗa da shimfiɗaɗɗen murmushi tana ɗaga musu hannu.

Har zuwa lokacin da suka ɓace a kan idanunta.

*****

Tun bayan tafiyar su Adda Halima take zaune a falonta, kanta ta jingine a saman kujera kalaman Adda Halima na dawo mata kamar a lokacin take faɗa mata.

Ta sani a duk duniya babu wanda ke da kusanci da ita da sanin halayyarta sama da Adda Halima, kamar yanda ita kaɗai ce zata bigi ƙirji tace tana mata tsananin so na mutuwa.

‘Ki yi abin da kike so!’ Maganarta ta sake dukan kunnuwanta kamar a lokacin take faɗa mata.

‘_Ba zan yi hasashen abin da kike shiryawa ba, domin kina haƙa ne ki binne ba tare da idanuwa sun ankare da hakan ba._

_Sai dai akwai ban-banci da tazara mai yawa tsakanin wancan haƙar da kika saba yi. Wannan idan kika yi ƙurar zata bibiyi rayuwarki ne har abada, zata yi ta buɗeki a yayin da hazonta zai gallabi rayuwarki._

_Ki yi abin da kike son yi, amma kada ki yi wanda zai zame miki tambarin shahara marar alƙibila.’_

Maganar Adda Haliman ta sake dawowa kunnenta, maganarta ta ƙarshe da ta faɗa mata.

Ƙananun idanuwanta ta sake buɗewa tana yalawata su a falon, kafin ta yi murmushi mai zurfi.

“Babu ƙurar da zata dawo ta buɗeni Adda Halima, zan yi rayuwar da na tsarawa kaina, zan kuma yi nasara a kan hakan.

Bana son Abdul baku saurare ni ba, dan haka zan gasa zuciyarsa cikin sauƙi, ba iya shi kaɗai ba har da duk wanda ke tare da shi.”

Ta ƙarasa maganar tana ƙara yalwata murmushi a kan fuskarta.

Daga bisani ta tashi ta shiga kitchen dan gabatar musu da abincin dare. ta daɗe tana nazarin abin da zata girka, itafa ƴar gargajiyace tana son ta ci tuwo a duk daren duniya, tuwon ma na laushi da miyar bushasshiyar kuɓewa ko kuma kuka.

Sai dai babu garin masara da na gero, gashi lokaci ya tafi. Ganin semovita yasa ta sauƙe ajiyar zuciya.

“Da dama dai, wai a dole sai an mayarka ɗan gayu.” Ta yi maganar tana murmushi sannan ta yi girkin.

Bayan ta yi haɗin lemon kan-kana wadda ta haɗa mata ƙarin madara da sugar a kai, sai lemon tsamin da ta zuba kaɗan.

Ta jefa ƙanƙara sannan ta saka shi a firji. Sai da ta gyara komi da ta ɓata sannan ta share gidan da sa turaren ƙamshi. Ta shige toilet ta yi wanka, yau kam ta ɓata lokaci a gaban madubi tana ƙyale-ƙyalen fuskarta.
Wajen zaɓen kaya ma sai da ta ɗauki lokaci tana neman wanda zata sa, kafin ta ɗauki wani material baƙi mai zanen fulawoyi farare. Kasancewarta fara sai kayan ya amsheta sosai ta daɗe tana juyawa a gaban mudubi sannan ta feshe jikinta da turaruka masu yawa.

A hankali ta lumshe idonta ta sake buɗe su, sai kuma ta jiyo da zummar barin ɗakin idanuwanta suka sauƙa akan na Abdulmannan ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana kallonta da murmushi a kan fuskarsa.

Ƙananun idonta ta shiga wurgawa tana ƙara takunta da ƙawata shi ta hanyar rausaya jikin a ko ina. Ko wani taku da ta yi sai jikinta ya yi rawa.

Ido Abdul ya lumshe yana buɗewa a kanta, hakan ya zama wata ɗabi’a a gareshi, har ta zo kusa da shi yana kallonta.

Juyawa ta shiga yi a gabansa, tana wara hannunta da kuma ɗorasu a ƙugunta, tana karkacewa daga tsaye.

“Ya kaga kwalliyar tawa?”

Murmushi ya yi yana sauƙe hannunsa daga harɗesun da ya yi “Masha Allah ta yi kyau.”

Ya faɗa yana jinjina hannunsa.
ƙananun idonta ta kanne ciki “Ta yi kyau kace fa? Ba ma ni ce na yi kyau ɗin ba?”

“Kwalliyar kika tambaye ni ba ke ba ai!” Ya yi maganar yana lumshe idanuwansa.

“Ina jin yunwa.” Ya yi maganar yana shafa cikinsa da juyawa da zummar barin ɗakin.

Gabansa ta sha tana yamutsa fuskarta da sosa girarta guda, tana murmushi “Faɗa min gaskiya dai Sayyadi Abdul! Idanuwanka na rawa da yawa kamar yanda ƙafafuwanka suke yi. Mafi girman al’amarin jirkicewar idanuwanka daga launinsu.” Ta yi maganar tana kanne idonta ɗaya, daga bisani ta matso da bakinta saitin idonsa ta hura masa iskar bakinta.

Idon ya lumshe a karo na ba adadi, yana murmushi sai dai kafin ya yi magana ya tsinkayi yatsanta ɗaya tana zagaya ƙwayar idon nasa.

‘Ya Allah!’ Ya faɗa a ƙasan zuciyarsa yana jin wani abu na harbawa tun daga kansa har zuwa yatsansa.

Riƙe hannun nata ya yi yana buɗe idonsa a hankali wanda ya sake faɗawa ciki.

“Rigimarki tana da yawa Nahna!” Ya samu bakinsa da faɗar hakan.

“Na sani Sayyadi,  bana so ka na ɓoye zahirinka ne, ka faɗi abin da kake son faɗa kawai.” Ta yi maganar har a lokacin hannunta na zagaye da fuskarsa tana zagaya sajensa.

“Ina son wannan zagayayyen gashin da ke fuskarka.”

Ɗaukanta ya yi ciɗak ya tafi da kan gadon ya ajiyeta.

“Me zaka yi Abdul? Ba dai kwalliyar tawa zaka ɓata min ba?” Ta samu kanta da faɗa.

Bai tanka mata ba, illa zura bakinsa da yayi kan nata, daga haka ya shiga raguzata da yin fatali da kayan jikinsu duka.

Taƙadirancin Hafsat na son kashe shi da ransa, gara ya gwada mata shi namiji ne lafiyaye. Tun tana kokawa har ta haƙura ta sallama masa, ta lura yau zafin kan Abdul ya ninka na ko yaushe, yau abinsa a kusa ya ke da shi, hakan ya sa ta kwantar da kai bori ya hau.

Bayan shuɗewar abubuwa ya kwanta rigingine yana maida numfashi, a hankali kafin ya taro ƴar rigimar tasa ya ɗorata a kan ƙirjinsa.

Zamewa ta yi ta kwanta a gefe tana ƙifi-ƙifi da idonta “Da baka ƙarfafa da yawa ba Sayyadi dolena na sauƙe hakkinka da ke kaina. Duk sa ina jin zafin hakan a ƙasana da zuciyata amma banga laifinka ba.”

Kwanto da kanta ta yi saitin fuskarsa da yake kalonta da lumshasshun idanuwansa “Komi da ke gareni mallakinka ne da yake halaliyarka. Sai dai kuma kwalliyar da na ɓata awanni ina yinta, gashi ka goge min ita a ɗan ƙaramin lokaci. Ita ce dai na ke son a biyani abata.”

Kai ya gyaɗa  yana sake lumshe idanuwansa, shi kam yana kasa gane abubuwan Hafsa, gashi dai magana take tana murmushi da cuno ƙaramin bakinta.

Tashi ya yi yana ɗaukanta suka shige toilet ɗin tare suka yi wankan suka fito duk da tana ƙara damunsa da surutu a can da kiran bayanta ciwo, jikinta zafi ya tumurmusheta.

Haka dai ya gasa mata ruwan ɗumi sannan suka fito. A gaban mudubi ya ajiyeta ya fara shafa mata mai har a lokacin tana kallonsa “Sayyadi yau babu magana ne? Ko ka manta bakinka a can garin kwasar garata?”

Murmushi ya yi mai sauti har fararen haƙoransa na bayyana. Ya shafa mata powder da kuma sa mata jambaki a bakinta. Sai kwallin da ya sa mata kaɗan.

“Sayyadi mana, ka daina danna min kaina da ƙarfi kamar abin yaƙi, ha’an.”

“Masha Allah! Kinga kwalliyar da na miki ma har tafi taki kyau.”

Baki ta taɓe tana kai kallonta kan mudubin ya yi saurin karewa, yana girgiza kansa.

“Sai na sa miki kaya tukunna.” Daga haka ya juyar da fuskarta daga kallon madubin ya zamana bayanta ne ke ganin madubin.

Kayan ya shiga duba kafin ya ɗauko wata atamfa mai launin green da fari a jikinta.

“Ban san me yasa kika fi son duguwar riga da siket ba a duk kayanki.” Ya yi maganar yana ɗaga rigar wadda itama ta kasance doguwace.

“Saboda ina da cikekkiyar ƙirar jiki mai kyau. Ta ko ina a cike nake ban yi ƙibar Allah tsineba, ban kuma yi ramar Allah kyauta ba.”

Ta yi maganar tana jujjuya idanuwanta sama.

Dariya ya yi bayan ya sa mata rigar mama da  kuma zura mata rigar a jikinta  “Ko yaushe na yi magana akan ki sai naga alfaharinki na ƙara yawa, kina jin kanki na yawo a gajimare.

Anya ba zan daina aiko yabon zuzutau gareki ba kuwa Nahna?”

Hannunsa ta riƙe daga ɗaura mata ɗankwalin da ya ke “Kana so kace min duk abin da na ke faɗa a kaina ba gaskiya bane Sayyadi?” Ta yi maganar tana kafe shi da idonta.

“Gaskiya ne mana Nahna! Matsalar kawai ke ɗince kin fiya ji da kai.”

“Tunda ka ce gaskiya ne ai ka gama magana Sayyadi. Ni ban ga aibu ba dan mutum ya yabi kansa.”

Ni gaskiya ma yunwa na ke ji duk ka sassaƙe min abin da ya rage a cikina, kuma kazo sai jujjuya min fuska kake kana ƙarema kyauna kallo. Gashi ba wai biyan kuɗin kwalliyar ka yi ba, yabonma kana yi kamar kana kushewa.”

Ta ƙarasa maganar tana zare kanta daga ruƙonsa, da kuma tashi a kan ƙafafuwanta.

“Ikon Allah! Yaushe kuma na kushe ki?”

Girarta ta shafa tana ɗaukan man da ya gama shafa mata, da lakuta. “Ka fini sani ai Sayyadi. Bari na shafa ma man mu tafi mu ci abincin.” Zama ta yi ta shafa masa man da yake jin kamar tana masa tafiyar tsutsa ne, a ransa yana girmama halayyar Hafsa mai rikiɗa da sauyawa.

Bayan ta gama ta je ɗakinsa ta ɗauko masa kaya marar nauyi wani yadi ne da ya yi kala da kayan jikinta ta ɗauko masa.

“Bari na taimaka ma ka sa sai mu yi anko. Kaga ba zaka ce kai kaɗai ka min kwalliyar ba, nima na ma.” Ta yi maganar da murmushi a fuskarta.

Kai ya gyaɗa cikin yaba mata da yin dariya, komi na Hafsa mai kyau ne idan ta yi, duk abin da ta masa kyanta ya ke gani. Yana kuma jin baya gajiya da kallonta.

A shirirince dai suka gama ta feshesu da turare masu launuka daban-daban waɗanda ƙamshinsu ba shi da ƙarfi na tashin hankali.

A wajen cin abincinma dai abu ɗaya ne lokacin da ya ke gyaɗa kansa da lumshe idonsa a yayin da shigar da lomar farko bakinsa “Masha Allah! Alhamdulillah!” Sune kalaman da ya faɗa a bakinsa.

Hannu ta kai bayansa tan akare shi “Bari na maka waigi kada ka faɗi Sayyadi! Dan na taɓɓata tsawon rayuwarka baka ɗanɗani girki mai ɗan-ɗanon wannan ba.”

“Nahnaaaa!” Ya faɗa yana murmushi da girgiza kansa.

“Gaskiya na faɗa ai Sayyadi. Fatana kada ka ciza hannunka garin watsa loma.”

Kansa ya juya yana kallonta da murmushi a fuskarsa “Ke ko?”

“Ina faɗar gaskiya ne ai. Gwara kayi mubaya’a ka amsa kawai.”

Hannayensa ya wara sama yana ɗagasu “Dole na ai.”

Dariya suka yi a tare suka ci gaba da cin abincin tare, fuskokinsu ɗauke da fara’a mayalwaciya.

*****

A hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya, duk wani makaman da Hafsat ta ke ɗauke da su ta watsar ta zubar su.

Musamman ganin yanda Abdul-Mannan ke nuna mata kulawa da soyayya, da kuma tattali duk kuwa da kalar maganar da zata faɗa masa hakan baya damunsa. Bata taɓa ganin fushinsa ba, bata taɓa ganin gajiyawarsa akan hidimta mata ba.

Ta sani mutane da yawa na cewa maza ba su da tabbas, a cikin mutanen ita ce mutum ta farko da ta ke ɗaga murya ta ce basu da tabbas ɗin.  Sai dai halayyar Abdul na ƙoƙarin sa ta sauƙa daga kan ra’ayinta.

Ko wata rana da kallar alkhairin da yake zuwar mata da shi, kamar dai yanda danginsa duk suka ɗora ƙauna da kulawarta a kansu.

Bata manta lokacin da taje gaida mahaifiyarsa, matar ta nuna mata soyayya kamar zata cinyeta. Sai godiya take mata na yanda ta ke zaune da Abdul lafiya.

“Abdul yana da zurfin ciki Hafsa, ba ya tattauna matsalarsa ga kowa. Babu wanda ke jin damuwarsa, a matsayina na mahaifiyarsa nakan ji babu daɗi a duk lokacin da naga sauyi a tare da fuskarsa, sai dai babu yanda zan yi, ba zai sanar da ni ba.

Shigowarki rayuwar Abdul kin haska masa rayuwarsa, kin ƙawata fuskarsa da kyawawan murmushi. Hakan yasa na ji ina son ki sosai.”

Kama hannunta Mahaifiyar Abdul-Mannan ta yi ta ɗora shi a cikin ruƙonta “Ban san me zai faru a gaba ba, ban kuma san ya rayuwa zata sauya ba, sai dai ina roƙonki alfarma akan ki kula min da rayuwar Abdul-Mannan, ki ci gaba da bashi farin ciki kamar yanda yake a yanzu. A yanzu ke ce farin cikinsa, ta dalilinki ne muke ganin sauyi da walwala a fuskarsa.

Shi yasa nake kyautata tsammanin alkhairai masu yawa a tare da ke, nake kuma da tabbacin zaki ci gaba da kawo haske a rayuwar ɗana ɗaya tilo namiji a duniya.”

Kallonta Hafsa ta yi tana jin maganarta na karya ko wata laka ta jikinta, tana jin ruwa na tsattsafowa daga ko wata huda ta jikinta.

‘Me yasa take roƙonta ta kula da ɗanta? Me zata ce mata?”

“Na san zaki iya Hafsa, tun da har kika iya sauya Abdul-Mannan a ɗan lokaci kika raba shi da tunani da uzuri wa lammuran rayuwarsa.”

Muryar Anna ta sake dokar kunnuwanta.

Murmusin yaƙe ta yi a lokacin tana goge gumin da ke sauƙa a kan goshinta “In sha Allah zan yi abin da zan iya Anna. Sauran kuma zan barwa Allah domin shine mai sassauya zukatan bayinsa, da kuma sauƙaƙa musu rayuwa.

“Na gode.” Anna ta faɗa tana murmushi da ɗora hannunta akan Hafsa “Allah ya miki Albarka.” Ta ƙarasa faɗa tana tashi a falon.

Da rakiyar ido Hafsa ta bita, tana lumshe idanuwanta, bata san me yasa ta ke kasa musawa wannan matar ba, a ko wani abu da ya shafi lamarin Anna da yaranta tana jin girmamawa a garesu, tana jinsu kamar danginta ne da ta yi nisa a garesu.

Kannen Abdul-Mannan duka mata ne guda huɗu. Nabila, Aisha, Jidda, Mami. Duka yaran suna girmamata a matsayinta na matar yayansu, duk abin da ya shafi lamarinta jikinsu na rawa wajen yi mata shi.

Itama tana son yaran, tana tausaya musu a matsayinsu na mata, hakan yasa ko yaushe cikin siya musu kayan ado da kwalliya na mata ta ke. Suna sakewa su yi hira da ita su faɗa mata matsalolinsu ta magance musu.

Hafsa ƴar harƙalla ce tun bayan da ta cika sati ɗaya ta fara kasuwanci, tana da kuɗi a hannunta da ta samu na biki, hakan yasa ta zuba su a jari komi da ya danganci na masarufi na ci tana siyarwa, na ci da na amfanin yau da kullum na jiki da fata.

Hakan yasa Abdul jinjina mata yana yaba hada-hadar matarsa, gidansa ya zama dan-dalin ƙaramar kasuwar da bata yankewa.
Lokacin da ya mata magana akan kasuwancin ta tare shi da magana.

“Sayyadi nifa bana cikin nau’in matan da suke zama suna jira mijinsu ya basu. Balle ni da na auri Ustazin da ya ke rungume da litattafai kullum, wata rana zan iya zama na sari ƙasa na taunata, idan na kwanta na ce zan jira ka min.”

Tunda ta faɗi haka ya gyaɗa mata kai “Lallai kam ba zaki zauna ki sari ƙasa ba Nahna. Allah ya taimaka.”

“Amin.” Ta faɗa tana ci gaba da uzurinta.

To yanzu gashi mahaifiyar Abdul na ɗora mata nauyin kula da ɗanta. Tana so ne ta ƙarar da rayuwarta wajen kula da shi da bashi farin ciki?

Itafa mamaki ta ke kamar ba ita ba, tana jin kamar akwai wani abun da Abdul ya mata ya sauya masifarta.

“Ya Allah ka dawo da ni dai-dai!” Ta faɗa tana furzar da huci a bakinta, da yunƙurin tashi a ƙafafuwanta, sai dai mai ƙafafunta sun ƙi ɗaukanta, wani abu ta ji ya tokare daga bayanta zuwa cinyoyinta. Bata san lokacin da ta ƙwalla ƙara ba mutanen gidan suka iyo kanta da gudu suna tambayarta.

<< Jini Ya Tsaga 10Jini Ya Tsaga 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×