Skip to content
Part 15 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Bakinsu motsi yake amma kalmar ta gagara fitowa a laɓɓansu, da ƙyar suka haɗa baki suna kiran “Alhamdulillah.” Wani hawaye mai sanyi na gangarowa a kan fuskar Anna, hawayen da take da tabbacin na farin ciki ne.

A da tana musa cewa farin ciki nasa kuka, domin bata ga kalar farin cikin da zai iya sa mutum kuka ba. Sai gashi yanzu da take ɗauke da tagwayen Abdulmannan hawayen ya gaza ɗaukewa daga idanuwanta.

“Anna kuka kike fa?” Abdul mannan ya faɗa cike da sanyin murya.

“Dole na yi kuka Abdul. Wannan hawayen ba na baƙin ciki ba ne, na farin cikin ganin jininka ne ina raye.”

Ta yi maganar tana rungume yaron da ke hannunta da kuma sumbatar goshinsa.

“Anna ku bani naga yaran mana.” Nabila ta faɗa cikin ƙosawa da ganhn yadda duk suna ƙanƙame jariran suka hanata ganin koda fuskarsu ne.

Miƙa mata ɗayan Sayyadi ya yi yana murmushi a kan fuskarsa, da sauri ta karɓe shi tana kallon kyakkyawar fuskarsa da bata da maraba da ta mahaifinsa.

“Ya Allah! Wannan ai copy naka ne Yaya.” Ta yi maganar tana faɗaɗa murmushin fuskarta.

“Wannan ma kamar sa ce da shi.” Anna ta faɗa tana nunawa Nabilan shi  da kuma kai idanuwanta ga wadda ke hannun Nabilan.

“Wow! Masha Allah kamarsu ɗaya ne ai.” Ta yi maganar tana kara ɗayan kusa da ɗayan.

Duk a tare suke kallon yaran idan aka ɗauke Abdul Mannan da Hankalinsa ke kan Hafsa. Yana so ya je ya ganta ya ga halin da take ciki.

Zamewa ya yi yana shiga ɗakin da Nurse ɗin ta nuna masa, ƙafafuwansa na takawa a hankali kamar mai tsoron isa inda yake son isa ɗin.

Har ya murɗa  ƙofar ya turata, idanuwansa ya shiga cikin na Hafsa da suka zurma ciki suka ƙara ƙanƙancewa saboda wahala. Fuskarta ta yi suwal kamar da ta daɗe tana rashin lafiya.

A hankali ya ƙarasa takawa bayan ya motsa bakinsa da yin sallama, bata amsa ba, kamar yadda shima bai damu ta amsa ɗin ba, ya dai samu waje ya zauna a kusa da ita yana kallon fuskarta, da kuma shafa kanta.

“Sannu Norul Khair.” Ya faɗa yana shafa kanta.

Idanuwanta ta lumshe sai da ya ɗauki tsawon lokaci sannan ta buɗe ta ɗora su a kansa “Kalmar sannu ta gaza ƙwarai Sayyadi. Domin a irin wahalar da na fito da kuma kokawar da na yi tsakanin rayuwa da mutuwa bana jin sannunka zata wadatar a gare ni.”

Numfashi ta ja tana furzar da iska a bakinta, tana kuma ƙara jin wani haushi da zafin duk namijin duniyar da ke ɗaga muryarsa a kan matarsa.

Lallai mata ƴan baiwa ne, lallai wahalhalu mata na yawa ne tsakanin maza. Domin kowanne abu ya haɗaka da namiji sai ka tadda wahala mafi girma a tare da kai.

“Me kike son na ce miki? Ni kaina nasan kalmar sannun ta gaza ga duk wata uwar da ta fidda ɗa a jikinta, sai dai bamu da kalmar da ta zarta ta da zamu nuna tausayawarmu a kan ku.”

Maganar Sayyadi ta dawo da ita daga zuzzurfan tunanin da ta lula. Hakan ya sa ta lumshe idonta tana ɗora su a kansa a karo na ba adadi.

“Abin haushina ma talaka na ke aure balle na ce ya biyani kuɗin naƙudar da na sha yi, duk da nasan kuɗi bai isa ya siyu kalar azabar da ake ji ba. Sai dai ina fatan na samu ladan hakan a wajen Allah.”

Sai kuma ta wara idanuwanta tana kallonsa da mamaki “Amma fa ba zan shayarma da yaronka kyauta ba Sayyadi.”

Murmushi Sayyadi ya yi, domin ya tsammaci jin fiye da hakan daga bakinta “Yaro?” Ya yi maganar yana murmushi kafin kuma ya bata amsar aka turo ƙofar aka shigo da sallama.

Hakan ya sa ya matsa daga kusa da itan da ya yi, ya zauna a kan farar kujerar da ke fuskantar ta.

Nabila ce ɗauke da jariri guda ɗaya a hannu, sai Anna da ke biye da ita da ɗaya.

Ido Hafsa ta wara daga kwancen da yake kafin ta samu zarafin magana suka shimfiɗar mata da yaran a gabanta.

“Sannu Uwar biyu. Ga su nan su ni ɗumin jikin ki.” Anna ta faɗa tana matsar da yaran kusa da ita sosai.

Hakan ya sa Hafsa wara ido tana kallon Sayyadi ɗin da yake ƙunshe dariyarta “Biyu kuma?” Ta yi  maganar kamar ruwan hawaye ya ɓalle daga idanuwanta.

“Biyu kyautar Allah kenan Hafsa. Banda Allah wa zai ma wannan kyautar. Kin ga abin da bamu taɓa kawowa a ranmu ba, sai gashi Allah ya sa albarka a zamanku ya kuma baku yara kyawawa kamarku har biyu gasu nan.” Anna ta faɗa tana wangale bakinta kai kace zata yaga bakin ne saboda tsananin murnar da ta kasa ɓoyuwa a gareta.

“Taɓɗijam!” Kalmar ta ƙwace daga bakin Hafsa tana jin gumi na jiƙa kowanne sashe na jikinta, tana jin wani abu mai zafi da ɗaci na huda fatar jikinta. Bata taɓa tunanin zata haifi yara biyu ba, ita bata kawowa kanta ba ma zata haifi tagwayen ba.

Sayyadi kam kasa riƙe dariyarsa ya yi sai da ya dara yana murmusawa, wadda yasa Hafsa wurga masa uwar harara da kallon zamu haɗu ne.

A lokacin kuma Aisha Ƙanwar Sayyadi ta shigo da manyan kuloli a hannunta na abinci, tana ajiyewa ta nufi yaran ta ɗauki wannan ta ajiye wannan ba za a taɓa cewa biyu ba ne yaran.

Zuwanta ba daɗewa sai ga Anty Lubabatu da Khadija da Bilkisu suma sun shigo ɗakin, Yaya Ado na biye da su domin shine ya kawo su.

Kafin wani lokaci ɗakin ya karaɗe da hayaniyar dangi da murnar Haihuwar Hafsa.

Ganin sun fara cika asibitin yasa Dakta Mu’az ya sallame su musamman da ya kasance lafiya lau mai jegon ta ke.

Nan kuma hayaniya ta koma gidan Abdul Mannan, wadda ganin idanuwan mutane da yawansu yasa Hafsa bawa yaran Mama duk, da kalar azabar da take ji na tsotsar.

Adda Halima ma ta zo daga sokoto inda har aka yi suna tana gidan, an yi shagali da walimar suna kam, inda yaran suka ji sunan Muneeb da Muneer. Sayyadi ya gwangwaje su da kaya na alfarma wadda Hafsa nata taɓa tunanin zai musu irin wannan bajintar ba.

Haka kuma ta samu alkhairai masu yawa daga danginsa da nata da kuma abokanansa, wasu ma bata san su ba bata taɓa tunanin su ba.

Haka aka yi taron suna aka watse cike da fara’a hankalin Mahaifanta sun kwanta da duk wani nata  musamman Ummanta da take ganin Hafsa ta ba su mamaki ta kuma zauna a gidanta.

Bayan suna da kwanaki biyu ta samu Sayyadi akan maganar ta gaji da shayar da yaransa masu ɗan karen tsotsar nono. Hakan yasa ya siyo musu madarar jarirai ya kuma ajiye mata kuɗi dubu ɗari biyu, yace ta yi haƙuri ya ƙarar da kuɗinsa a hidimar sunan.

Karɓa ta yi babu kunya tana yamutsa fuska da babu gara ba daɗi dai.

Haka rayuwar aurensu ta ci gaba da gungurawa yau fari gobe tsumma har zuwa lokacin da yaran suka cika shekara biyu a lokacin kuma Hafsa ta farga da cikin da ke jikinta, nan ta tubure akan bata san batun cikin ba, da ƙyar sayyadi ya lallaɓata ya ajiye mata kuɗin dubu ɗari biyar, ya kwashe ƴan biyun ya kai su wajen Anna yana cewa su huta saboda mamansu na da wani cikin.

Shima kamar na Farko haka Anna ta shiga murna har zuwa lokacin da cikin ya shiga watan haihuwa ta fara naƙuda shikam ya zo mata da sauƙi domin a gida ta haifi ɗiyarta mai tsananin kama da ita, wadda ta ci sunan Anna Maimunatu, ake ce mata Yumnah.

Rainon Yumnah ya koma hannun Anna wadda da su Aisha domin sun ɗauki son duniya sun ɗorawa yarinyar, haka ma ƴan uwanta Twins.

A lokacin ne kuma shekaru huɗun da Hafsa ta ɗibawa Sayyadi ya cika, bata ɓata lokaci ba ta same shi akan maganar lokacinsa ya ƙare.

“Kamar ya lokacina ya ƙare?” Ya yi maganar cikin rashin fahimtar inda maganarta ta dosa.

“Shekarun huɗun da na ƙiyasta ma na aurenmu sun cika Sayyadi, dan haka zamana ya ƙare a gidan.”

Idonsa ta buɗe da hanci yana kallonta “Ban taɓa sanin haukan ki ya kai haka ba Hafsa. Dama banzan shirmen da ke kanki na nan har yanzu?”

Dariya ta yi tana kallonsa da sosa girarta guda ɗaya “Hauka ka ce Sayyadi?”

“Ƙwarai kuwa hauka mafi ƙololuwa Nahna.”

“Za ka ga kuwa hauka tuburan Sayyadi.” Daga haka ta fice ta barshi a ɗakin yana jan tsaki da girgiza kansa, oh da alama haƙurinsa ya ƙare bai kuma sake bi ta kanta ba ya yi ficewarsa.

Itama ta zari hijabi ta tafi, bata zame ko ina ba sai ofishin ƴan Hisbar da ke jahar Kebbi.

Bayan zaman jin kora bayani daga bakinta da kuma cewar “Ta zo ne akan a raba aurenta da mijinta, saboda ta gaji da zama da shi.” Hakan ya sa suka mayar da kallonsu kanta.

“Wane ne mijin naki? Me yasa kike son rabuwa da shi?”

“Saboda bana son sa. Na kuma gaji da zama da shi, inaga ko a musulunci ana raba auren da ɗaya ya gaji da ɗaya.” Kai shugaban ofishin ya jinjina yana kallonta.

“Waye mijin naki?”

Sai da ta nisa kafin ta ce “Sheikh Abdul-Mannan Ishaƙ Nasir!”

A zabure mutanen wajen suka juyo suna kallonta “Me? Sheikh Abdulmannan fa kika ce? Ko kin san shine shuganan Hisba na birnin kebbi da kewayenta gaba ɗaya?”

“Da sanin hakan na zo nan ɗin. Dan na tabbatar da adalcinku, shin har a tsakanin ku ne ko kuwa iya jama’ar gari kawai kuke tsayawa.”

Daɓas mutumin ya zauna kamar yadda sauran mutanen suke tsaye su sun kasa motsawar ma.

Kallonta suke suna ganin wautarta kamar suna kallon sabon magijin film ne da ya fito, yayin da ita kuma take hango tashin hankali shimfiɗe a tare da su…

An zo wajen? Kuna tunanin sayyadi zai iya sakin Hafsa. Ku faɗi kalma ɗaya tak aka wannan shafin da kuma alƙalan da ta kawo ƙara gunsu….

<< Jini Ya Tsaga 14Jini Ya Tsaga 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×