Skip to content
Part 16 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Da ƙyar babban ya tattaro da ƙarfinsa bayan ya haɗiyi wani yawu mai kauri a bakinsa yana ƙara kallon matar da ke zaune a gabansa.

“Ni da zaki ji shawarata da sai a sasanta zamanku. Amma rabuwa da irin malam Abdul mannan ba ƙaramin asara ba ne ga kowata matar aure.”

Kallonsa ta yi ta ɗan kanne ƙananun idanuwana kafin ta sosa gashin girarta guda ɗaya.

“Shin na faɗa muku na samu matsala da shi ne? Ko da na zo nan ban faɗa muku cewar ya min laifi ba, asalima na sanar da ku cewar na gaji ne da zama da shi. Badan yana da mugun hali ba, ba kuma dan baya kyautata min ba, asalima ni tunda nake a rayuwata ban taɓa ganin mutumin kirkin da ke jure halayyar matarsa kamar shi Sayyadi ba.”

Numfashi ta ja kana ta furzar da iska a bakinta, ta lumshe idanuwanta “Duk inda ake neman mutumin kirki, Sayyadi ya wuce haka. Shi ɗaya ne da babu kamarsa a wannan zamani. Yana da sanyi, yana da tausasawa, yana da haƙuri da juriya, yana da kawaici, yana da yafiya sosai. Amma kuma ba irina ya kamata ace yana zaune da ita ba. Domin saɓanin shi ni ina da kishiyar abubuwan da na lissafa a kansa.

Dan Allah ku raba aurena da shi a yanzu.”

Kamar sun samu hoton magiji haka suke kallonta, suna ƙiyasta adadin hauka da ƙuruciyar da ke ɗawainiya da ita.

“Kin san mene ne saki kuwa? Duk da kin faɗi kyawawan halayyar Malam amma kike son rabuwa da shi. Bakya tunanun wani mijin zaki aura a gaba?”

Miƙewa ta yi tsaye tana daidaita zaman hijabinta a wuyanta “An ya za ku iya adalci kuwa anan? Nifa ba sulhu ne ya kawo ni ba. Idan ba zaku iya raba aurenmu ba zan yanko masa sammaci, hakan zai iya zama wani naƙasu ga rayuwarsa, da kuma watsuwar labarin a kan a nan.”

Ta juya da niyar tafiya, a lokacin idanuwanta suka sarƙe da na Sayyadi da yake tsaye ya harɗe hannunsa a kan ƙirjinsa, idanuwansa sun sauya kala zuwa jajaye, jijiyar kansa ta fito raɗo raɗo, hakan ke nuna yana cike da tsantsar ɓacin rai.

Miƙewa sauran mutanen suka yi ganinsa a tsaye, suna sunkuyar da kansu da jin ba daɗi.

“Saki kike so Nahna?” Ya yi maganar da ƙyar da muryarsa da bata fita da kyau.

Kai ta gyaɗa masa tana lumshe idanuwanta da buɗe su a kanta “Mai kyau ma kuwa AbdulMannan.”

Kallon mutanen da ke ofishin nasu ya yi, da suke kallonsa suma “Me yasa ba ku karɓi karanta ba?”

Shuru ne ya biyo bayan maganarsa wadda duk cikin su babu mai iya bashi amsa.

“Na ɗauka wasa kike lokacin da kika buƙaci na sake ki, ban taɓa tunanin da gaske zaki iya neman saki a wajen mijinki ba Nahna. Duba da yadda kike da ilimi na addini da kuma sanin halakar da hakan ke haifar da ita.”

Huci ya furzar mai zafi yana jin wani abu na tasowa tun daga ƙasan zuciyarsa har zuwa maƙoshinsa, wani abu mai ɗacin da bai san ko mene ne shi ba, amma yana jin ya hana shi shaƙar iska da kyau, kamar yadda ya hana shi haɗiye yawun bakinsa da suka yi kauri.

“Allah yana amfani da abin da ke cikin zuciyar bawansa ne, Sayyadi. Abin da ka gaza ganin kamatarsa na duba cancantarsa. Na baka abin da ka ke da buƙatar samu a tare da ni, na baka yara da kuma lokacina fiye da kowanne namiji da zai shigo rayuwata.

Ina sonka ko bana sonka wannan wasu abubuwa ne da suke tseren farmakar zuciyata. Kai ba mijin da ka cancanta da dacewa da mace kamata ba ne. Ina buƙatar na baka waje, kana buƙatar samun wadda zata shimfiɗa rayuwarta saboda kai.
Amma ba Hafsat Kamaludden Muhammad ba.”

Kai ya jinjina ba tare da ya juyo ba, ga wawuri littafi a gaban tabirin ofishin ya shiga rubutu mai tsayi da kuma sauri.

“Kar ka yanke hukunci da sauri Malam. Kana buƙatar samun lokaci ku zauna kai da ita.” Babban mutumin da ke mata tambayoyi ya faɗa, yana kallonsa.

Bai ɗago ya kalle shi ba har sai da ya gama rubutun sannan ya naɗe takardar ya miƙa mata.

“Ina miki fatan alkhairi a rayuwarki ta gaba, ina fatan zaki samu fiye da abin da kika samu a tare da ni a rayuwarki ta gaba. Na gode da kyawawan ranakun da muka yi a tare.”

Sannan ya mayar da kallonsa ga mutanen da ke wajen.

“Duk wadda ya zo nan da niyar kawo kukansa, hakan na nufin kukan da ya yi a gidansa ya wuce a ƙiyasta shi. Idan akwai lokuta mafi dacewa na gyara, to sune lokutan da suka shuɗe ana tare.”

Daga haka ya raɓa ya wuce ta gabanta.

Juya farar takardar ta shiga yi a hannunta, tana jin harbawar zuciyarta da bugawarta na ninkuwa, wani sabon ƙunci na mamaye duniyarta, tana iya jin zafi da turarin da bata taɓa jin irinta ba a duk tsawon rayuwarta.

<< Jini Ya Tsaga 15Jini Ya Tsaga 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×