A hankali Adda Halima ta sauƙe ajiyar zuciya, bayan ta dawo daga dogon tunanin da ta lula. Tasan Hafsa ciki da bai, tana kuma tsorace da abin da zata iya aikata mata, a waje irin wannan da yake sabo a gareta.
Wata unguwa ce da bata da alƙibla, mutanen cikinta kuma amana ta yi ƙaranci a garesu, dawowar Hafsa cikin rayuwarta daidai yake da fallatsa kowanne sirri na ta. Tana da tabbacin zata haɗa kai da mutanen da ke nan su cutar da haƙurinta.
Wayarta ce ta yi ƙara, ganin sunan Umman su yasa gabanta ya sake faɗuwa a karo na ba adadi.
Da sallama ta kara wayar a kunnenta, daga can aka amsa mata sannan aka ɗora da mata magana.
“Halimatu, ya gidan ya yaran, ya kuma haƙurin rayuwa?”
“Alhamdulillah, Umma.”
Shuru ya biyo bayan amsawar tata, kafin can dai Umma ta furzar da huci a bakinta.“Kawun yara ya sanar da ni Hafsa na gidan ki, ko?”
“Eh! Jiya ta zo.”
Ajiyar zuciya Umma ta sauƙe cikin sanyin murya ta sake magana “Amma kuma zaki iya zama da ita, duk da cewar kin samu labari akan abin da ta yiwa Mahaifinku?”“In sha Allah Umma.”
“A’a Halima ina jiye miki tsoron zama da Hafsa. Kina da haƙuri, kina da kawaici sosai, saɓanin Hafsa da ta kasance tantiriya. Fitinarta yawa gareta, ina jiye miki tsoron kada ta cutar da haƙurinki, kada ta watsar da kimarki a gaban mutanen da kike da kimar. Halima, yanzu ba da ba ne, Malam baya raye balle ya zama garkuwa a gareki, da kuma zama a matsayin shamakin rayuwarki da Hafsa.”
“Umma, Hafsa jini na ce, duk abin da ake faɗa a kanta da wadda ta aikata, hakan baya sauyata da kasancewarta a matsayin jinina. Zan yi haƙuri na zauna da ita da daɗi da rashin daɗin, ina fatan zaku ci gaba da mata addu’ar shiriya a matsayinku na iyayen da kuka kawota duniya.”
“Addu’a muna yinta Halima, lokacin amsawarta ne bai yi ba. Na gode sosai Allah ya miki albarka, idan akwai matsala ki kirani ki sanar da ni, zan zo na yi maganin abin.”
“In sha Allah ba abin da zaki ji sai alkhairi, Umma.”
“Nima haka nake fata. Ki gaida yaran.” Daga haka ta yanke wayar ta barta da kallon wayar.
“Umma ce?” Maganar Hafsa ta ratsa dodon kunenta wadda ta tilasta mata dakatawa daga kallon wayar da take.
“Eh.” Amsar da ta iya bata kenan ba tare da ta ƙara wata kalma ɗaya ba.
“Itama tana so ki kore ni ne? Kamar yadda ta kore ni daga gidanta.”
Kallonta ta yi tana nazartar maganarta da ajiyeta akan ma’aunin da ya dace “Amsar kenan Hafsa. Kin riga da kin liƙawa kanki baƙin fantin da ba kowa ne yake ganinki a mai kirki ba. Kowa na tsoron alaƙarki da shi, yana tsoron abin da zaki iya yi idan zama ya haɗaku da shi a waje ɗaya.
Amma kuma ni nafi kowa sanin wacece ke. Hakan yasa na zaɓi na zauna da ke cikin daɗi da tsani, ina sa rai wata ƙila na samu sassauci da rangwame daga kaidi irin naki. Wataƙila kuma ki tausaya min kamar yadda na tausaya miki musamman da muka zama abu ɗaya ne.”
Shiru Hafsa ta yi tana shiga da fitar maganar Adda Halima da ajiyeta akan muhallin da ya dace, idan har ta fahimta kamar dai tana roƙonta ne akan kada ta barta da mummunan sheda itama.
Murmushi ta yi tana murza girarta da kuma tauna laɓɓanta “Idan har kina kokonto a kaina ne Adda Halima, kema zaki iya korata kamar dai yadda Umma da Alhaji Malam suka yi.
Idan kin gama sanin halina, kin riga da kinsan abin da zan yi da wadda ba zan yi ba. Bana so kullum muna maimaita abu ɗaya kamar karatu.”
“Ba zan kore ki ba Hafsa. Ba zan iya korarki a gidana ba, sai dai idan har na san halinki, ya kuma tabbata a kaina zan iya ƙoƙarin arar juriya da kuma arar daga cikin abin da ya zama naki.”
Dariya Hafsa ta yi tana juyawa da barin ɗakin “Abincin rana ya kammala. A kawo miki ɗaki ko zaki fito mu ci tare?”
Miƙewa Adda Halima ta yi, tana fitowa barandar gidanta, da bishiyar mainar da ke tsakar gidan ke kaɗawa da iska mai daɗi.
Gidan fess da shi kamar a yanzu a ka share shi, domin su kansu yaran idan Hafsa na nan sukan shiga taitayinsu, ba kasafai suke ɓata gidan da yin ta’adi ba.Tabarmar da aka shimfiɗa mata a barandar ta zauna tana ambatar Bismillah. Zamanta ba jimawa sai ga Hafsa ta fito da faranti, ɗauke da abinci a kansa. Maryam na ɗauke da nasu, yayin da Bunayya ke riƙe da babban kofin ruwa da ƙanana a cikin wani farantin roba.
Sai da ta ajiye ta fahimci jalof ɗin shinkafa da taliya ne ta haɗa waje ɗaya.
Yaran ma suka ja gefe suka fara cin nasu “Ga cokali.” Ta yi maganar tana miƙawa Adda Halima cokalin.
Kai ta girgiza tana miƙewa da wanke hannunta a famfon. Ta dawo ta zauna.
“Nafi son cin abinci da hannuna.”
“Lallai ba zamu gayyace ki tafiya gidan ƴan gayu ba.”
“Nima ba zan so tafiyar ba. Domin a gidan malamai na taso na kuma yi rayuwar aure a gidan su.”Baki Hafsa ta taɓe “Shi yasa kike a duhu, komai naki cikin shuɗaɗɗen zamani yake.”
“Ni kuwa nake a waye. Domin al’adata na tafiya ne daidai da Addinina. Idan na aro al’adun da ba nawa ba, sai na shiga dawa a rasa mai dogayen yatsun da zai fiddo da ni.”
Dariya Hafsa ta yi tana kurɓan ruwa a kofi “Karki damu zan fito da ke gari, zan kuma sauya ki daidai da zamani.”
“Babu buƙata.” Ta faɗa kai tsaye.“Lokaci zai nuna hakan.” Daga haka suka ci gaba da cin abincin babu wadda ya tanka musu.
Har zuwa lokacin da suka gama Maryam ta tattare kayan ta kai su kitchen ta wanke su.
A lokacin kuma aka fara kiran sallahr la’asar wadda ta tilasta musu tashi suka ɗauro alola.Bayan sun idar sallah Adda Halima ta fuskanci Hafsa “Har yanzu ba ki sake waiwayar rayuwar yaranki a gidan Abdul Mannan ba? Bakya tunanin akwai wani hakki nasu da ya ke kanki wadda ya kamata ki sauƙe shi?”
Shafa addu’ar da ta kammala ta yi tana kallon adda Halima kamar yadda itama take kallonta.
“Addu’ata na tare da su a duk inda suke, bayan ita kuma wanne hakki ne nasu ya rage a kaina? Ba zan iya komawa baya na waiwayi rayuwarsu ba, na tabbata a duk inda suke yanzu sun yi girman da za su kula da kansu. Shekaru shida kenan rabona da su, bayan lokacin na rufe kowanne kundi da zai tuno min da su.”
“Kina so ki ce min bakya kewar Abdul Mannan da yaransa? Kina so ki ce min abin da idanuwanki suke nuna wa a kan soyayyarsa ba gaskiya ba ce?”
“Inda ace gaskiya ne ba zan yi rayuwar aure da wasu mazan ba shi ba. Da akwai abu da yawa da rayuwa ta gama tsara mana. Wadda bamu so ba da kuma tsammata ba. Kamar dai shuɗewar rayuwar Sayyadi da yaransa a duniya.”
“Hmm har yanzu da ƙuruciya a kanki Hafsa. Shekara Talatin amma har yanzu kin gaza yin hankali da wayo.”
“Ƙila ba zan yi ba kuma, tunda har na haifi yara biyar ban yin ba.” Daga haka ta fice daga ɗakin ta bar adda Halima da binta da rakiyar ido da kuma nema mata shiriya a wajen Allah.A hankali rayuwarsu ta fara zama suna zaune ne cikin daɗi da kuma walwala har kuma a lokacin da Hafsa ta yi wata guda a gidan bata nuna mata wani mugun hali a gareta ba.
A hankali ta fara sabawa da maƙotan Adda Halima kasancewarta mace mai faram faram da barkwanci.
Ta kuma fara yin sana’ar kayanta da ta saba, sai dai wannan karon hadda leman zaƙi take haɗawa tana ɗorawa Bunayya tana tafiya mata talla, duk lokacin da bata siyar ba ko ta daɗe haka zata kamata ta yi ta lakaɗa mata duka.
Tun Adda Halima na yin shiru har ta kai da ta fara mata magana, da faɗa ‘Tallar dole ce? Me zaki samu akan abin ashirin goman da baki samu ba. Duk uwar sana’ar da kike dan ɗora hakli sai kin ɗorawa marainiyar yarinya tallah.” Faɗan Adda Halima kenan a lokacin da ta sha gaban Hafsa daga dukan Bunayya da take yi.“Kamar kin raina sana’ar biyar goma fa Adda Halima? Ba abin mamaki bane ɗin ke ki raina saboda baki san ya ake sarrafa biyar ta koma ba. Wataƙila saboda zuciyarki ta mutu ne kowatarana kina jiran abokanan miji da ƴan uwan miji su kawo miki tallafi a matsayinki na matar ɗan agajin da ya rasu. Kina jiran a kawo miki sadaka dan ki ciyar da marayun yaranki.”
Ido Adda Halima ta ƙwalalo waje “Hafsaaa!” Ta faɗa da muryarta da ke rawa idanuwanta sun zurma ciki, hawaye na taruwa a cikinsu.
Hannu Hafsa ta ɗaga mata “Ni ce na haifi Bunayya Adda Halima. Ina ƙoƙarin gina sassanta ne akan ta san me ake nufi da neman na kai da kuma dogaro da kai. Bana so ta ji a ranta ita marainiyace dan ta samu hanyar da zata raɓa ta shiga jikin wani da neman rigar alfarma, kamar dai yadda kike yi.
Ina so ta ji a ranta babu maraya sai ragon da ya kwanta.”
Yanzu kam hawayen fuskarta ne ya sauƙo a kan ƙuncinta, tana kallon Hafsa har zuwa lokacin da ta tsinke hannun Bunayya a cikin ruƙonta ta kuma ɗora mata farin bokitin da ke cike da kunun zaƙin.
“Ki siyar ki dawo a kan lokaci, sana’a nace ki ba wai ki na roƙon mutane ba. Duk wadda ya ce zai miki juye kada ki siyar masa idanuwana na kanki a duk wani motsinki.”
Daga haka ta dangwarawa yarinyar kayan ta fice tana matse hawayen fuskarta.
Itama ta zari mayafinta ta shige gidan maƙotan Adda Halima ba tare da ta duba yanayinta ba kuma dan ta damu da son ganin halin da take ciki ba….
End of chapter