Da kallo kowa dake wajen ya bishi, zuciyar su ta riga data gama tsinkewa da tausayin sa.
Wasu da yawa kuma suna jinjina butulci da rashin kirki irin na Hafsa, duk ɗiyar da zata yima mahaifinta haka to babu wanda ba zata yima fiye da haka ba.
Kallonta Ado yayi ya share hawayen dake Zuba akan fuskar sa, wanda babu makawa na tausayin Mahaifin nasu ne “Kiga yanda Alhajin mu yake kuka saboda ke Hafsa! Kiga hawayen takaicinki na sauƙa akan fuskar mahafinki daya zama tsani na kowani farin ciki arayuwar ki! Kinji haushin kanki Hafsa. Kin gayyaci sheɗan zama aboki na kusa agareki, kin kuma ruƙo hannun ruɗun duniya dan suyi ƙawance dake acikin tafiyar ki. Ki shirya tarban munanan ranakun da zasu riskeki, ki kuma tanadi makeken abin goge hawaye atare da ke, ki kuma shirya fuskantar nadamarar da ke ɗago miki hannu alokacin da bata da amfani.”
Kallon sa tayi ta yatsina fuska, duk da kalaman da Alhajinsu ya faɗa agareta sun sauƙar da mummunan rauni da tsoro agare ta. Amma ko kaɗan ba zata bari suga karayar ta ba, ba zata nuna raunin ta akan gaskiyar da take cikin abin da take shirin aikatawa ba, mutanen da suke kewaye da su sun isa bata cikakkiyar gaskiya da jajircewar ta amatsayinta na mace guda ɗaya tilo da zata iya fito-na-fito da ko wani Namiji.
“Uhmm yaya Ado kenan! Ko yaushe maganar maza akan abu ɗaya ne, basa fahimtar ƙunci da raunin dake zuciyar mace. Amma na tabbata wata rana zaku fahimci abin da nake son ganar da ku. Shi kansa Alhajinmu zai san soyayyar da nake masa ta gaskiya ce, zai fahimci kunyar dake cikin duniya aikin banza ce. Nagode Allah da Umman mu bata gidan nan da labarin zai fi haka muni a idonun duniya da ku kanku.” tana gama faɗar haka ta raɓa ta kusa da shi ta shige gidan.
“Ya Allah Allah!” ya faɗa yana runtse ido hawaye na zuba akan idon sa. ‘Lallai duk wanda yayi nisa baya jin kira, idan kuma Allah bai shiryar da kai ba to babu mai iya shiryar da kai’ maganar da yaƙe aƙasan zuciyarsa kenan.
Daga nan sauran mutanen da suka taru awajan kowa ya fashe ya kama gaban sa.
Shiga gidan yaya Ado yayi dan riskar Mahaifinsu ya ƙara tausarsa da bashi baki akan abin da Hafsa ta aikata agareshi.
Dai-dai lokacin da Hafsa ta ɗauko jakar kayanta tana riƙe da hannun Ummi ɗiyarta mai shekara bakwai aduniya, bayanta kuma da goyon Bunayya.
Leƙa kanta tayi falon Alh. Kamaludden tana murmushi “Alhajinmu ni na tafi, Allah ya baka ikon adalci akan matayenka, ya rabaka da tashi da shanyayyan jiki aranar lahira.”
Idonsa ya buɗe ya kalleta sai ya rufe yana girgiza kai ba tare da ya ƙara ce mata komi ba.
Baki buɗe Ado ya tashi yana ƙoƙarin dukan ta “A’a fa Ado! Nace ka ƙyaleta ko?”
Ganin fusatar da Ado yayi yasa ta ja hannun Ummi suka bar gidan ba tare data ƙara bi ta kan sauran mutanen gidan ba, ko sallamar kirki batayi da su ba. Agare su kam murna suke suna kiran asauƙa lafiya, zama da Hafsa yafi zama da Annobar bala’i. Su atakure yaransu atakure.
Harara Ado ya aika mata da rakiyar ta, kana yasa hannu abakin sa yana cizawa na takaicin halayyar ƴar uwar sa da hanashi kilarta da Alhajin yayi “Wallahi Abba da badan agida Umman mu ta haifi Hafsa ba da sai nace musauya mana ita akayi. Da kuma babu kamar da ke gudana tsakanin ta da mu da kai to wallahi da nace haure tayi ta cikin rufa-rufa ta zama ƙarƙashin ahalin ka.”
Ido Alh. Kamaludden ya wara yana kallon Ado, kafin yayi murmushi wanda da ganinsa na ciwo ne da takaicin Hafsa “Ko kaɗan kada ka ƙara wanan tunanin Ado. Acikin ko wani gida akan iya samun mai kyau da kuma gurɓataccan cikin sa. Allah ya sani ban ragi Hafsa da wani abu na jin daɗi kama daga ilimi zuwa tarbiyya ba wanda har ta iya aikata min rashin kirkin ta. Nasan bata da kirki bata da haƙuri amma ban san abin nata ya girmi sani na ba, ban kuma san halin ta ya wuce tunani na ba. Amma babu komi ga duniya nan zata koya mata darrusan rayuwa, taje ko ina take son zuwa amma banda gida na.”
Kai Ado ya jinjina yana goge hawaye akan fuskar sa “Haka ne Alhaji, amma dan Allah kayi haƙuri kada ciwon abin da Hafsa ta aikata maka ya shafi walwala da lafiyar ka. Nasan akwai ciwo sosai samun ƴa irin Hafsa, amma kuma idan ka tuna ita ɗin ta zama kamar Jarrabawa agaremu gaba ɗaya. Haƙuri shine yafi dacewa damu dan mu ci wanan Jarrabawar da Allah ya aiko garemu.”
Kallon sa yayi ya gyaɗa kai saboda gamsuwar da yayi da maganar Ado ɗin “Alhamdulillah! Na gode Allah daya ƙaddara min ba Hafsa kaɗai bace ɗiyata. Na tabbata da ciwo da ƙunan da zanci araina sai yafi haka. Allah yayi muku albarka kai da ƴan uwan ka.”
“Ameen Abba. Itama Allah ya ganar da ita gaskiya.”
Murmushi kawai Abba yayi kafin yace “Kayya dai Ado, ban hango mata wanan shariyar ba.”
Shuru ne ya ratsa falon dan kowanne ransa ajagule yake, haka kowa da saƙar zucin da yake aransa.
******
Tana fita ta tare mai mashin suka hau ita da yaran ta. Tasha tace ya kaita aranta tana mita da godiya ga Allah da yasa tana da inda zata je, tana kuma da wadataccan kuɗi ahannun ta, danma ba kaya gareta anan ba, duka kayanta ta kaisu gidan Adda Halima ta ajiye, saboda tazarar tafiyar dake tsakanin Sokota da Jega.
Da yanzu ta ɗorawa kanta wahalar neman wajan ajiye su, ƙila wasu ma su ɓace ko su lalace.
Tana zuwa tasha ta sallami mai mashin ɗin ta nufi motar da take jin ana kiran Sokoto “Zaku iya sauƙeni a BOƊINGA anan zan tsaya.”
“Ba komi Hajiya ai duk hanya ɗaya ce, akwai mutum biyu da zamu sauƙe acan ɗin ma yanzu.” kondostan motar ya faɗa mata yana ƙarɓan ƙatuwar jakarta.
Shiga tayi ta fara wara ido acikin motar, da yawan su maza ne, sai mata su biyu. Tana shiga wani yazo ya shiga motar ta cika, kwandasta ya karɓi kuɗin motar kowani fasinja, sai suka ɗauki hanya.
Tafiyar awanni biyu ne ta kawosu Boɗinga anan wadda zasu sauƙa suka sauƙa ciki harda Hafsa da ta ƙagara ta sauƙa ganin la’asar sakaliya tayi.
Ba laifin garin yana da ɗan girma kasancewar sa ɗaya daga cikin tsaka-tsakin garurruwan da suke da wayewar mutane da ci gaba.
Mashin ta sake tara ya ƙarasar da ita unguwar da zata je.
Da sallama ta shiga gidan, gidane matsa-kaici da akwai zauren farko acikinsa sai ɗakuna guda uku da suke jere, gefe kuma madafar abincin su ne da kuma banɗakin dake zagaye, sai ɓangaran Maigidan da ɗakuna biyu na yaran. Ataƙaice dai gidan yana da girma sosai ta cikin sa.
Da hanzari sauran mata da yaran suka fara mata oyoyo ga maman Bunayya.
Risinawa tayi ta gaida dattijan matan sanan ta ƙarasa ɗakin dake ƙuryar ƙarshe na gidan.
“Assalama alaikum.” ta faɗa tana yaye labulen dake saƙale acikin ɗakin.
“Wa alaikumussalam.” wata dattijuwar mata ta faɗa.
Sanan ta saki fuskarta da fara’a tana riƙo hannun Ummi “Kishiyar yau harda ke aka zo mana ziyara.”
Kai ta gyaɗa tana murmushi, sanan ta tsuggun ta gaida ita, da fara’a shimfiɗe akan fuskarta ta amsa mata.
Kafin ta juyar da kallon ta ga Hafsa tana sauya yanayin fara’ar dake Fuskar ta “Lafiya dai na ganki yamma sakaliya da uwar jaka haka?”
Kai ta girgiza tana sauƙar da Bunayya daga bayan ta, sanan ta yatsina fuska “Alhajinmu ne ya koreni daga gidan sa, saboda kawai na faɗa masa gaskiya akan rashin adalcin da yakewa matan sa. Amma dake zuciyar sa ta ƙeƙashe shine yace baya buƙatar ya ƙara ganin ƙafata agidan sa.”
Kallon ta Umma tayi cikin mamaki baki a sake “Ba saboda haka ba dai ya koreki Hafsa. Kin san nafi kowa sanin halinki, akwai dai abin da kika masa wanda ya fusata shi har ya koroki daga gidan sa.”
“Da gaske saboda wanan ne Ummah.”
“Uhm minene ruwan ki da matan sa to? Ko kuwa ke ce kika haifeshi ba shi ne ya haifeki ba? Har yanzu mungun halinki na katsalandan yana nan atare da ke?”
Baki ta turo tana ƙara yatsina fuskar ta “Umma kema kin san ai bazan iya gani na ƙyale ba, ba kuma zanyi shiru naga ana aikata ɓarna naƙi magana ba, bayan kuma Allah ya tsaga min baki, ya kuma sanya min zuciya marar tsoro da kuma bin bayan ƙarya.”
Kai Umma ta gyaɗa tana riƙe haɓarta “Ba shakka kam! Amma kuma ai kinyi kasassaɓa dan anan gidanma baki da matsugunni, bazan iya zama atare dake koda na kwana ɗaya bane. Saboda tsaf zaki kashe min aure bayan kin raba ko wata yadda da mutane suke da ita akaina. Ni kawai haifarki nayi, amma bazan iya sauya miki munanan ɗabi’unki ba, ba zaki kuma iya gani ki ƙyale ba. Na tabbata baki baro gidan Mahaifinki ba sai da kika barshi da ƙatoton tabon da mutane zasu na sheda shi da shi. Amma kuma ni bana buƙatar tabo da yanke irin naki, wanda sharri da KAIDI irin naki ke samar da shi. Tun gari da sauran rana ki tashi ki ɗebi ƙafa kisan inda dare ya miki.”
Tana gama faɗar haka ta fice tabarta aɗakin ba tare da ta tsaya ta saurari koda kalma ɗaya daga gareta ba.
“Turƙashi! Tsugunno bai ƙare min ba kenan.” Hafsa ta faɗa tana bin bayan Umman su da kallo, kafin nan ta taɓe baki ta ɗaga kafaɗa wanda yake nuna hakan ko ajikin ta.
Can kuma sai ta tuntsure da dariya “Wato ita Umma har gida ta samu na aure da take iƙirarin zan kashe mata aure. Adai wanan gidan mai cike da ihun yara da tarkace banga amfanin zama ba, dan da alama ko barcin safe ba’a samu ayi balle a rintsa.” ita kaɗai take magana tana jijjiga kai.
Tashi tayi ta gyara zaman hijabinta tana ƙokarin jan jakarta, sai ga ɗaya daga cikin abokan zaman Umma ta kawo musu abinci da abin sha.
“A’a Maman Bunayya ya naga kina shirin tafiya? Kaddai kice min yanzu zaki juya?”
Murmushi ta sauƙar akan fuskarta wanda shike ɓoye ko wani mugun hali da tugunta “Aikuwa dai tafiya Zanyi Mama, dama ahanya nake na raɓo tanan mu gaisa, bana son dare yamin kuma ahanya.”
“Banda abinki dare ai ya riga daya gama yi miki, yanzu zakiga an fara kiran sallahr almuru. Da dai zaki bi shawarata da kinyi haƙuri kin kwana Allah basshi gobe sai ki tafi da safe. Ga abinci da ruwa kuci.”
Kallon abincin tayi ta fara yamutsa fuska, itafa dama ba zuwa garin nan ba, tarkacan abokanan zaman Umman ta da suke da ɗan banzan shisshigi wadda take ganin ta kamar Kissa ce, daɗin daɗawa ba girki suka iya mai ɗan-ɗano ba, duk sanda tazo idan ba Umma keda girki ba to haka take ƙare yininta ta koma gida, su kuma kamar kansu ya toshe da rashin ganin hakan, dan naci kullum sai sun kawo mata.
“Nikam aƙoshe nake Mama, dan ahanya naci abinci, daga Jega nake kinga tazarar babu yawa balle asamu gajiya da yunwa atare dani.” ta ƙarasa maganar cikin fara’a da duba agogon dake wayar ta.
“Duk da haka yaranki zasu buƙaci hakan, musamman Ummi.”
“Ya Allah!” ta faɗa aƙasan maƙoshin ta.
“Ki bar ɓata lokacinki Maman yara akan Hafsa, tunda ta miƙe tsaye ba zata zauna ba.” Umma ta faɗa tana ɗan murmushi akan fuskarta.
“Aifa nasan halin har yanzu yana nan ashe?”
“Ai babu fashi.” Umma ta bata amsa tana murmushin da ganinsa na yaƙe ne.
Daga haka Maman yara ta tattara abincin ta koma da shi.
Sai alokacin Mama ta kalli Hafsa cikin tamke fuska “Kibar Sadiya anan ke sai ki tafi yawon duniyar taki.”
Kallon Umma tayi kana ta kai kallonta ga Ummi wanda ainihin sunanta Sadiya kasancewar sunan Adda Halima gareta shi yasa aka mata alkunya da sunan Ummi kasancewar ta babbar yaya mariƙiyar ta wadda tasu tafi zuwa ɗaya aduk gidansu.
“A ina zan barta Umma?” ta aika tambayar cikin mamaki.
“Anan waje nah mana, ina zaki tafi da yara kina gararamba agari.”
Dariya tayi mai sauti cikin muryar ta ta shaƙiyanci ta fara magana “Haba Umma! Kema da araɓike kike agidan taya zan bar ɗiyata tayi zaman agolanci agidan wani, wanin ma ba da Uwarta ba da kakarta, ai agolanci ya kai ƙololuwa. Indai zan barta anan to na kaita wajan ubanta mana, inda iyaka abata kashi amma baza’a mata gorin agolanci ba. Ke ɗin dai Umma ki zauna abinki cikin gidan auren da bazaki fita ba bazaki koka ba.”
Tana gama faɗar haka ta ja hannun Ummi suka fice aɗakin, rasa abin da Umma zata faɗa mata tayi sai kai data girgiza tana nema mata Addu’ar shariya awajan Allah.
“Halayyarki sai ke Hafsa, kulum sabbin shafika kike buɗewa waɗanda suke marasa alfanu da amfanarwa. Allah ya shiryeki ya ganar dake gaskiya.” maganar da tayi tana share hawayen da yake sauƙa akan fuskar ta.
Wannan itace Jarrabawarsu itace kuma ƙuncinsu arayuwa. Jarrabawa mai wahala akan yara da kuma soyayyarsu ga iyaye.
******
Tana fita bata zarce ko inaba sai tasha kai tsaye motar SOKOTO ta shiga.
‘Gidan Adda Halima kawai zanje, ita kaɗai ce ba zata ƙyamaceni ta kore ni ba, anan kuma zan baja kolina son raina ba tare da wani ya nuna min yatsa ko ya aibata ni ba.’ saƙar zucin da take azuciyar ta.
Tafiyar mintuna talatin ne ta kawo su Sokoto daga Boɗinga. Ana sauƙeta ta ɗauki hayar mashin ya kaita unguwar Arkilla.
Hamdala tayi ta gode Allah lokacin data isah gidan ta tadda Adda Halima na nan.
Da hanzari cikin ɗoki da jin daɗi ita da yaranta suka fara mata “Oyoyo Anty Hafsa, Oyoyo Ummi nah.” fuskar su cike da soyayya agareta.
Daɗi ne ya cikata hakan yasa ta ƙarasa ta rungume yaran tana kiran “Oyoyo yara nah!” sanan ta tsugunna har ƙasa ta gaida Addah Halima.
Ɗago da ita tayi tana shimfiɗa fara’a akan fuskar ta “Ni bazaki min oyoyon ba kika tsugunna har ƙasa?”
Saurin rungumeta tayi tana kiran “Adda nah”
Daga nan suka saka dariya gaba ɗayan su. “Maza mu ƙarasa ciki kiyi sallah dan na tabbata ahanya magrib ta riskeki.”
“Addah mana! Ki bari na huta naci abinci nayi wanka, daga baya sai na jero sallolin da ake bina.” Hafsa ta faɗa tana ƙara narkar da murya ƙasa-ƙasa.
Ido Adda Halima ta wara waje tana girgiza kai “Ba iya Magrib bace ta wuceki ba kenan akwai wasu ma kenan?”
“Umm La’asar ce da zuhur kaɗai.”
Harara Adda Halima ta aika mata “Kaɗai fa kikace?”
Hannun ta tasa ta rufe bakin ta “Suɓutar baki ne Addah!”
Bata ƙara ce mata komiba ta bama Zarah jakar ta ta shige mata da ita ɗakin da yake amatsayin mallakin ta, kasancewar anan dukkanin kayanta suke alode tun bayan mutuwar Auren ta.
Ɗakuna biyu ne ajere sai ƴar baranda wanda aka mata rumfa, gefe kuma madafar abinci ne, sai makewayi daga can gefe, akwai ƙatuwar tsakar gida wadda za’a iya ƙara wani sashin ba tare da an samu matsi ba.
Daga wajen gidan kuma akwai shago da ɗaki wanda ta bawa wani hayar sa, yana saida kayan masarufi acikinsa.
Yaranta guda shida aduniya Allah ya karɓi rayuwar mijinta bayan yayi ƴar taƙaitacciyar rashin lafiya.
Babban malami ne wanda yana ɗaya daga cikin ƴan hisbah agarin. Sunyi kuka sosai na rashin sa, haka da yawa daga cikin mutane suma sun koka akan mutuwar sa. Gidan da suke ciki shine yazo amatsayin gadon yaran ta.
Ɗiyarta ta farko mai suna Hajara anyi auren ta, sai ƙaninta mai bi mata Ma’awuya, sanan Aadamu, Jidda, Zarah, sai auta Khalil.
Ma’awuya da Adamu sukan fita kasuwa neman aiki wasu lokutan har dako sukeyi dan su samo abin da zai tallafi mahaifiyarsu su tsira da abin da zasu ci.
Itama Adda Halima ba’a Zaune take ba tana yin sana’ar tuƙa mai da ƙuli tana ɗorama yaranta su siyar. Wanan kenan.
Abinci ta zuboma Hafsa ita da Ummi sanan ta aika aka siyo mata ruwa mai sanyi.
“Ban san da zuwanki ba da na tanadar miki abincin da kika fi so.”
Kallon Abincin tayi tuwon hatsine na laushi da miyar bushasshiyar kuɓewa da man shanu.
Murmushi tayi tana murza hannun ta “Wanan ɗinma yana daga cikin abin da nake so Adda Halima.” sanan ta ranƙwafar da ƙafafuwan ta, tafara ci.
“Nayi kewar daddaɗan girkin nan naki Adda Halima.” ta faɗa bayan ta kai loma ɗaya bakin ta, tana ƙara lumshe ido.
Hannunta Adda Halima ta kara abayan ta “Ba na miki waigi kada ki faɗi garin santi.”
Dariya duka suka saka atare, sanan suka ci gaba da hirar su, har zuwa lokacin data kammala cin abincin.
Sai da tayi wanka ta rama sallolin da yake kanta sanan suka sake sabuwar gaisuwa ita da Adda Halima.
“Kaina ya kulle ganin kinyi shigowar dare, abin da baki taɓa yiba idan zaki zo waje na.” Adda Halima ta faɗa tana kai kallonta ga Hafsa.
Murmushi tayi wanda da ganinsa na takaici ne, kana ta ciza bakin ta tana jinjina kai “Alhajin mu ya koreni daga gidan sa, ya kuma soke ko wata alaƙa dake tsakani na da shi ayau.”
Azabure Adda Halima ta kalli Hafsa cike da mamakin maganar da ke fitowa abakin hafsan, amma kuma da alamu ita hakan bai dameta ba, asalima jikin ta bai nuna nadamar hakan ba.
“Kamar yaya Alhajinmu ya kore ki? Laifin mi kika masa?”
“Addah Halima awanan rayuwar da ko wani namiji ke fifita soyayyar matan sa da shimfiɗe rayuwarsa saboda su, har akwai sabon abu na mamaki dan uba yaƙi ɗiyarsa saboda Mace.”
“Kai Hafsa! Bana san wanan azancin naki na shaci faɗi da neman kare kai. Awanan duniyar da muke ciki babu wata soyayyar dake daƙusar da ƙaunar iyaye akan yaran su. Haka kawai Alhajinmu bazai koreki ba sai dai idan wani abun kika masa mai girma.”
Rai ta ɓata ta kawar da kanta gefe “Kada kice min kema yanzu kin daina ƙauna ta Adda Halima? Nazo da sa rai da tsammani idan kowa zai ƙini ta hanyar binciko mikin dake gareni ke zaki riƙo hannu na ki zauna dani adaɗi da babu daɗi, kasancewar kece kika maye min gurbin mahaifiyata duk da cewa tana araye.”
Riƙe hannunta Adda Halima tayi, sosai zuciyarta ta karaya ta tsinke da kalaman Hafsa “Ko duniya da mutanen cikinta sun juya miki baya ni bazan juya mikiba Hafsa! Zuciyata ce ta kasa samun nutsuwa da jure jin Uba ya kori ƴar sa saboda wani dalili marar ƙarfi. Hafsa na san halinki sarai, amma duk da haka ina iya zama dake cikin daɗi da rashin sa. Sai dai ina tsoron abin da gobe zata haifar, ban saniba ko atare dani sabuwar Hafsa ce da halayyar ta ta ƙaru ko ta ragu, bani da tabbas Hafsa.”
“Kina shakku akaina kenan Adda Halima?”
Kai ta girgiza mata “Ba shakku bane tabbaci gareni, ayanzu hannu ɗaya gareni wanda yake riƙe da wahala, gajiyawa da kuma rauni atare da shi. Ban saniba ko zaki ƙara min wani mikin ko kuma zaki sauƙaƙa min shi agaba ba.”
Kallon ta tayi suka haɗa ido cikin idon Addarta taga rauni da gajiyawa wanda ko bata faɗa ba tasan inda maaganarta ta dosa. Sai dai bata da amsa bata kuma da tabbacin zata iya tallafa mata wajan shumfuɗuwar sauƙi acikin sauƙaƙawar dake gareta.