Skip to content
Part 20 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Ta daɗe a tsaye tana zubar da hawayenta, a ƙarshe dai taga kamar tana ɓatawa kanta lokaci ne, kuka akan halayyar Hafsa wadda take da tabbacin yanzu ne ta fara.
Idan kuma tace zata ci gaba da yi to zata ƙarar da hawayenta ne a zama ɗaya.

Girgiza kanta ta yi ta koma ɗaki ganin zama ba zai mata ba yasa ta fito ta fara tattara tsakar gidan, sai da ta shareta tass sannan ta shiga kitchen ta musu jalof ɗin shinkafa da wake.

Har ta gama ta yi sallahr Azahar babu Hafsa babu dalilinta, tana kuma da tabbacin tana gidan maƙotanta waɗanda suka kasance masu bakin ganga, mutanen da suke maraba da ganinka da zarar kuma ka gusa sai su fara aibata ka.

To amma Hafsa ta gagara fahimtar hakan, kamar dai yadda ta gagare gane wasu irin maƙota ne suke tare da ita. Asalima tun lokacin da ta faɗa mata ko su waye ne su sai ya zamana kamar ta buɗe mata ƙofar ƙara kusancinta da su ne.

Har ta yi alwala ta yi sallah su Jiddah suka dawo a makaranta Hafsa bata dawo ba.
Dole ta aika Jiddah ta kirata su zo su ci abinci.

Zuwan Jiddah gidan Maman Siyama ta same su sun sa Hafsa a tsakiya sai labari take basu suna shewa suna tafawa.

Sallamarta bata sa sun dakata daga hirar da suke ba har sai da ta yi magana da murya mai ƙarfi “Anty Hafsa, ki zo in ji Umma mu ci abinci.” Jidda ta faɗa da muryarta mai ƙarfi.
Wadda tasa Hafsa juyowa da maka mata uwar harara “Ki ce na ƙoshi ni.” Ganin kallon da take mata yasa yarinyar ta juya ta tafi gidan.

Sai da ta tabbatar da ta isa gida sannan ta tashi tana yi musu sallama.

“Bari naje kada a sake aiko wani yaron.”

“Da kin zauna anan mun ci ai, dan nima ina gaf da ƙarasa nawa.” Maman Siyama ta faɗa.
Murmushi Hafsa ta yi tana girgiza kanta “Duk daɗina da sabo bana kwaɗayi a gidan mutane maman siyama.” Daga haka ta fice a gidan tana jin idanuwansu na yawo a kanta.
Da kuma sautin muryar Maman Siyaman da take cewa “Ke yanzu dan kin ci abinci a gidan nan sai ace kin yi kwaɗayi?”

Bata jiyo ba balle ta tsaya daga tafen da take ta bata amsa “Mafaɗi maraɗi Maman Siyama, gudun kada a yi kada a fara.”

Ta wuce tana ƙidaya adadin takunta, a hanya suka yi kiciɓus da Mu’awuyya wadda yana ganinta ya sauƙe ajiyar zuciya.

“Dama kiranki zani Anty Hafsa. Umma ta aika Jiddah kiranki sai gata ta dawo wai kin ce kin ƙoshi.”

Ɗan Yamutsa fuska ta yi kaɗan “Eh da haka nace, amma yanzu kuma ina jin yunwar. Bunayya ta dawo ne?”

“Eh! Gasu can suna cin abinci da su Jiddah.” Ya bata amsa yana juyawa domin shima abincin zai ci Umman ta ce ya je ya tabbatar mata da maganar Jidda.

Bin bayansa ta yi tana haɗa taku kamar ta wuntsula “Dan iskanci Bunayya ta dawo amma ba zata min magana ba sai ta afka kwanon abinci kamar ƴar yunwar ƙaƙuduba.”
Tana shiga gidan ta hango Bunayya na zuba lomar abinci da sauri ta ƙarasa kusa da ita tana bige hannun nata.

“Dan ubanki ki dawo a tallar ba zaki neme ni ba sai ki baje a gaban tiren abinci. Ina cinikin da kika yi?” Ta yi maganar da tsawa, wadda yasa su Jidda suma jikinsu ya ɗauki rawa.

Cikin rawar murya da hannu ta fara magana “Ina wajen Umma.”

“Me?” Ta faɗa da murya mai ihu wadda yasa jikin yaran ƙara fara rawa, hawaye na gangarowa a kan idanuwan Bunayya ɗin.
“Karki ƙara bawa wani kuɗina, bana son salon munafunci da kinibibi, ba zan ɗauki wannan halayyar ba sam-sam.” Ta zuba mata uban dungurin da yasa Bunayya dafe kanta da take jin kamar an kwaɗa mata guduma ne.

Hankaɗeta ta yi ta nufi wajen Adda Haliman da take kallonta kamar ta samu wani sabon magiji.

Hannunta ta miƙa mata tana cuno bakinta gaba “Kuɗin halak ɗina.” Ta yi maganar tana ƙara matse fuskarta da cin kunu.

Gefen tabarmar da take kai ta ɗaga ta ɗebo kuɗin ta miƙa mata.

Sai da ta matse su tsaf a hannunta sannan ta yi murmushi “Ina abincin nawa.” Da hannu ta mata nuni zuwa kitchen.

Yayin da Mu’awuyya da Aadamu ke binta da kallo da kuma Umman nasu, suna jin wani abu mai ɗaci na gangarowa a kan maƙoshinsu.

Dubi kalar wulaƙancin da ta yiwa Umman amma har da tambayar abinci.

Tsuka Mu’awuyya ya buga yana ture kwanon abincinsa gefe da barin gidan, domin idan har ya ci gaba da zama tsaf zuciyarsa zata tarwatse.

Ƙarasowa Hafsa ta yi ta zauna a gaban Adda Halima tana kallonta “Adda Halima mu ci mana.” Ta ajiye kwanan gabanta.

“Ki ci abinci kada ki zauna da damuwa da yunwa. Idan ka ce zaka tattauna da zuciyarka akan matsalolin wani jinika na haurawa da yawa. Tashi ɗaya kiji zuciyarki ta buga.

Wannan rayuwar lallaɓawa ake a karɓeta a yadda ta zo, haka kuma sai ka rikiɗai ne kake iya zama da kowanne irin mutum.”
Ta yi maganar tana kai lomar abinci bakinta da lumshe ido “Wow! ɗanɗanon onga mai aramshi.”

Ta faɗa tana sake kai lomar bakinta “Badab kina zaune a tsahuwar unguwa da kuma ƙauyawan mutane ba da sai nace ki fara saida abinci Adda Halima. Ba ƙaramin kuɗi zaki samu ba.”

Shuru ta yi kamar mai nazartar wani abu.
“Oh ashe Addar tawa da gatan ta, ba kamar Hafsa bace da kowa ke gudunta yana ƙinta.
Sana’ar ni ta kama, za ki taimaka min dai na ƙwarai.”

Kallonta Adda Haliman ta yi tana ƙiyasta adadin abin da zata faɗa mata ya dace da ita..

<< Jini Ya Tsaga 19Jini Ya Tsaga 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×