Skip to content
Part 21 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

“Me yasa kike tunanin kuɗi shine komai a rayuwa, Hafsa? Akwai abubuwa da yawa na kima da kuɗi basu isa mallakarwa mai shi ba?” Adda Halima ta faɗa tana kafe Hafsa da ido.

Kamar yadda itama Hafsa ta ɗago kanta da dakatawa da cin abincin da take tana kallon Adda Haliman.

“Yanzu ke a ganinki har akwai wani abu da yafi kuɗi saurin siyawa Mutum Kima, Adda Halima?” Murmushi ta yi tana girgiza kanta da kuma gyara zamanta.

“Kuɗi shine komai na rayuwa da ke siyawa mace kima da martaba a gidan mijinta. Bama gidan miji kawai ba, hatta mutanen da za su kewaya tsakaninki dole sai kina da abin hannu wadda zai kankaro da kimarki. Musamman ke da kike zaune da mutane mabanbanta masu jiran cas suce kule. Mutanen da basu damuwa da matsalolin gidansu, waɗanda kullum suke haba-haban ganin faɗuwar wani na kusa da su.”

Shuru ta yi tana kallon Adda Halima kamar yadda itama take kallonta “Zama haka ba zai iyu a gareki ba Adda Halima. Yau da gobe sai Allah, na san bani da kirki duk inda na zauna sai na bar baƙin miki ga wadda ke zaune da ni, kin san saboda me ya sa haka?”

Bata jira amsarta ba ta ci gaba da maganar “Saboda ina faɗar abin da ke cikin zuciyata ne, bi ban iya ɓoye ɓoye ba.

Daga haka ta ci gaba da cin abincinta tana sake yin magana “Har yanzu kina da zaɓi na korata a gidan ki. Idan kin so, saboda kada na watsar miki da kimar da kike tunanin kina da ita.”Daga haka ta tashi tsaye tana ɗauke kwanon abincin da ya gama ci, ta kai kitchen.

Sannan ta dawo ta zauna kusa da Adda Halima ta fara ƙirga kuɗi “Oh ni Hafsatu, banda sana’a me zai kawo ma wannan kuɗi haka? A haka dai ashirin goma ce amma gasu sun dunƙule sun zama ɗari, jaka.”

Ajiyar zuciya ta sauƙe ta ce “Gaskiyar maimuna coge da tace,
      “Ku kama sana’a mata.
         Macen da bata sana’a aura ce.
         Lale lale maraba da ke zinariya!”
Sai kuma ta bushe da dariya tana tashi da shige ɗaki.

“Oh Allah gwanin daɗi inji ɓarawon taliya.” Maganar da ta yi a lokacin da take shigewa ɗaki.

Shiru Adda Halima ta yi tana kallon yaranta da suka zuba mata ido, tana hango idanuwan Aadamu da ya gama yin ja, yana matse hannunsa, abincin da ke gabansa kuma bai ci koda rabinsa ba.

Kallonsa take kamar yadda shima yake kallonta, kai ta girgiza masa cike da ƙarfin hali “Hafsa ƴar uwata ce. Duk abin da ta min kada ya sauya matsayinta na ƙanwata a zuciyarku. Kada ku mata kallon da ba zaku min shi ba. Ina sonta a hakan.”

Ta yi maganar tana miƙewa tsam da shigewa ɗakinta, tana jin idanuwansu na mata yawo a fiskarta.

Tabbas sai ta dakatar da yaranta,  daga kallon Hafsa, domim idan ba haka ba, za su haƙa rami mai zurfi na ƙiyayyar ƙanwarta a zuciyarsu, wadda ba zata taɓa son hakan ya faru ba.

*****
A hankali rayuwar ta ci gaba da turawa tana gangarawa, kwanaki na ƙaruwa yana turawa. Cikin sanyi da sauƙin rai Hafsa ta fara fito da asalin halinta da ɗabi’arta ga Adda Halima.

A gaban yaranta zata dama kunin zaƙinta ta kuma aike su, su kaiwa maƙotan Adda Halima, amma ba zata ba su ko ɗal a harshensu ba.  Kamar yadda ba zata bawa Adda Haliman ba ita.

Haka zata ƙulle ta tisa ƙeyar Bunayya ta tafi tallar. Bata damu da ganin yadda yara ke tafiya makaranta ba, ba ruwanta akan lallai sai Bunayta ta je makaranta, domin burinta ɗaya ne, taje ta nemo mata kuɗi.

Haƙurin su Jiddah ya gaza ganin yadda take yin hidimarta ba tare da kyautatawa ko rangwanta musu ba, sai ma izayar da take musu da kuma yi musu izgili.

Zata aike su ta kuma hanasu abinta ita da mahaifiyarsu gashi ba su isa su yi magana ba, zata dake su.

“Jiddah, zo ki kaiwa Maman Siyama kunun ayar nan.” Ta yi maganar bayan ta ɗura shi a ƙatuwar jarka ta faro.

“Ni gaskiya ba zan je ba Anty Hafsa. Ba zan je aiken da ba sannu ba balle godiya, kuma muna gani ki yi abin ki hanamu.”

Da tsananin mamaki Hafsa ta miƙe tsaye tana kallon Jiddah da itama take tsaye tana kallonta idonta ƙyam a kanta.

“Jiddah! Ni zan aike ki kice min ba zaki je ba? Ni Hafsa?”

Ido Jiddah ta wayata tana kallon Hafsa da cinno baki da kuma kumbura fuska “Saboda ban iya ƙarya ba Anty Hafsa. Idan na karɓa na zubar a waje ai na yi zalunci.”

Hannu Hafsa ta ɗaga ta kwaɗa Jidda da Mari, kafin ta farga ta ƙara kai mata wani sabon dukan da yasa ta fashewa da kuka, kuka take mai ƙara wadda yasa Adda Halima fitowa a ɗakin da gudu.

“Subhanallah me ya faru?” Ganin Hafsa na dukan Jiddah kamar Allah ne ya aikota yasa ta harɗe hannunta a kan ƙirjinta tana kallonsu.

Jiddah na kuka bakinta bai mutu ba “Wallahi ko zaki kashe ni ba zan je aiken ba.” Jiddah ta faɗa.

“Aikuwa zan yi maganinki.”

Ta fara yunƙurin kai mata wani ice mai ƙarfi, sai dai ga mamakinta taji an riƙe icen da hannu.

Idonta ta buɗe tana bin wadda ya riƙe icen sai dai ganin Mu’awuyya ne idanuwansa sun yi jajir sun zurma ciki, fuskarsa kamar baƙin hadari.

“Sakar min, ko kaima na haɗa da kai.” Ta yi maganar tana zabga masa harara.

Dariya Mu’awuya ya yi, dariya mai nuna takaicin da jin haushi, wadda tasa Hafsa buɗe ido tana kallonsa.

“Haba Anty Hafsa. Abin ai ya yi duka. Ki zauna a gidanmu ki ci daga abin da aka bamu sannan kuma ki dake mu. Wai nikam baki san kunya ba ne? Ko baki san zuru da ido ba?

To abin ya isa haka, idan baki san duk waɗannan ba, muma zamu koya daga abin da kika koyar da mu. Muma ɗin mun sirka daga jininki.”

Ya yi maganar yana fizge icen daga hannunta da kuma yin jifa da shi.

A lokacin ne kuma ya ji sauƙar mari a kuncinsa wadda yasa shi ɗagowa a fusace, ganin Hafsa na sauƙe numfashi da nuna shi da hannu ya fahimci ita ce ta mare shi.

Hannu ya ɗaga zai rama yaji an riƙe masa hannu, da sauri ya juyar da kansa ga mai riƙe masa hannun yaga Adda Halima.

“Umma!”

Kai ta girgiza masa “Ashe zaka iya ɗaga hannu ka mare ni nima, Mu’awuyya?”

Kai ya girgiza yana jin wani abu na taso masa daga ƙasansa har zuwa maƙoshinsa “Allah ya hanen ni daga ganin wannan ranar.” Ya yi maganar yana yamutsa fuskarsa.

Wadda yasa Adda Halima jinjima kanta “Duk lalacewar Hafsa ƙanwata ce. Kuma jinina ce, babu ruwa ku tsakanin alaƙar da ke tsakanina da ita, kamar yadda ban tarbiyyantar da ku a kan raina na gaba da ku ba.

Jiddah ta mata laifi ta hukunta ta daidai da laifinta. Mene ne ruwanka a ciki?” Ta yi maganar tana kallonsa da kuma sauƙe hannunsa ƙasa.

Ta ƙarasa ta ɗaga Jidda daga zaunen da take, ta kakkaɗe mata jikinta  da kuma share mata hawayenta da bayan hannunta.

“Kuskure ni sa rai a kan abin da ba naka ba ne. Kamar yadda ba laifi bane a cikin kyauta da rowa. Mutum yana bada abu ne ga wadda ya so, wataƙila dan neman suna ko kuma dan neman kambama da kuma yabon ƙarya.

Kada ki ɗora idonki a kan abin da ba naki ba ne, ki tsaya ki jira lokaci zai fayyace komai. Amma hakan ba zai sa ki ari rigar kare ki fara mana haushi ba.”

Daga haka ta riƙe hannun Hafsa ta shige da ita ɗakinta, Ma’awuyya na biye da ita.

“To damw ai lokaci baya jira ne Adda Halima. Shi kuwa kare yana haushi ne a inda ake son jin haushin da kuma inda ake buƙatarsa.” Hafsa ta yi magana da ƙarfi wadda a cikinsu babu wadda ya juyo ya kalleta.

Haka ta koma ta ci gaba da ɗaura kunun Ayar tata, takaici na neman kasheta, ganin kamar tana shirme yasa ta tashi ta zari hijabi ta fice a gidan bayan ta rufe kunun Ayar.

*****
“Umma yanzu haka zamu ci gaba da zama da Anty Hafsa a gidan nan? Abin da a baya bata mana shine yanzu ta ke mana, kuma kina gani baki hanata ba, baki tsawarta mata ba, sai ma ƙoƙarin kareta da kike yi?” Ma’awuya ya faɗa cikin sanyin murya da rawa, wadda kana jinta kasan ransa a mutuƙar ɓace ya ke.

“Ki dubi fuskar Jiddah duk hoton yatsunta ne, banda Allah ya kawo ni a kan lokaci da haka zata ci gaba da dukanta da ƙaton icce kina gani kuma ba zaki iya hanata ba.”

Murmushi Adda Halima ta yi tana shafawa Jiddah magani a jikin nata “Ina ƙara sanar daku dai muhimmanci Hafsa a gare ni. Duk abin da zata muku kada ku sake ku tanka mata. Ku ƙyaleta da halinta, ina tabbatar muku da cewar wata rana zata daina.”

“Ba zata daina ba Umma. Saboda bata fara dan ta daina ɗin ba.” Mu’awuyya ya faɗa yana tashi da barin ɗakin yana jin zuciyarsa ba daidai ba ne.

“Dole zan kira Anty Hajara mu koreta, saboda bata da gado a gidan nan.” Maganar da yake faɗa kenan da nufar gidan ƴar uwarsa.

Bai kuma ɓoye mata komai dake faruwa ba hakan yasa zuciyar Hajara motsawa, ɓacin rai ya fara taso mata.

“Yanzu tsawon lokaci duk kuna zaune a haka a rasa wadda ya zo ta faɗa min?

In dai kuwa haka ne ni zan yi maganin abin, da kaina zan haɗawa Anty Hafsa kayanta ta ƙara mai.”

<< Jini Ya Tsaga 20Jini Ya Tsaga 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×