Skip to content
Part 22 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSA SADAUKARWA NE GA MAI DAMBU

******

Tun bayan tafiyar Mu’awuya ta ke safa da marwa a gidan nata, tana kama saƙa da warwarar zare, neman mafita guda ɗaya take amma ta gaza samun abin da zata iya yi.
Har zuwa lokacin da Mijinta Marwan ta shigo gidan.

Ya gama duk wasu abubuwan da ya saba yi, amma ganin yanayin da take ciki ta gaza samun kwanciyar hankali “Akwai matsala ne, Hajara?” Ya jefa tambayar a saitin ta.

Wadda hakan ya sa ta sauƙe ajiyar zuciya.

“Hankalina ne yana gida Marwan. Ina jin kamar Ummana bata cikin yanayi mai kyau. Dan Allah ka min izini na je na ganta.” Ta yi maganar tana sauƙe ajiyar zuciya.

“Bata cikin yanayi mai kyau?” Ya yi maganar cikin sigar tambaya.

Kai ta gyaɗa masa tana lumshe idanuwanta “Ina so naje na ganta.” Ta sake maimaita maganar a karo na biyu.

Bata so ta sanar da Marwan halin da suke ciki, domin a ganinta wannan abu ne da ya shafi ahalinta da kuma danginta. Koya ta aibata Hafsa a gabansa kamar ta buɗe wata gurɓatacciyar ƙofa ne a gareta da danginta.

Murmushi ya yi yana shafa kanta “Kice dai kina so kije gida, amma ba wai kiga Umma bata yanayi mai kyau ba.

Ko ɗazu na biya ta gidan da naje duba yaron Asma’u. Na sameta ita da Antynku nan mai fara’a suna hira, baki ji yadda take tambayarki ba, da kuma nanata min na gaida ku. Af! Na tuna ma.”

Hannunsa ya zura a Aljihunsa ya zaro wata baƙar leda ya miƙa mata “Gashi tace na kawowa Aafreen.”

Karɓa ta yi cikin sanyin murya da kunce ledar sarƙa ce mai ɗankunne ta yara da kuma warwaro guda uku masu kyau “Anty Hafsa, ta ce ka kawo wa Aafreen?”

Kai ya jinjina “Da har naki ma ta ke nema to ko ƙarewa ya yi, shi yasa bata bada na kawo miki ba, amma tace na gaidaki sosai.”

Idonta ta lumshe tana murza kanta, da ɗan bubuga shi da hannunta ‘To kodai ba gaskiya Mu’awuyya ya faɗa min ba? Domin na sha zuwa gidan naga Anty Hafsa na hidima da kaiwa da kawowa a kaina da kuma Aafreen, hatta Umman ma.’

“Ya dai Hajara? Akwai matsala ne?” Maganar Marwan ta dawo da ita hankalinta.

Kanta ta girgiza tana ƙoƙarin ƙaƙalo dariya “Ba komai. Amma kace kagansu suna hira da Ummana?”

Kai ya gyaɗa mata “Ya wuce wai. Dan na same su suna ɗura kayan ƙamshi da Umman take siyarwa.”

“Amma, shine bata baka ka kawo min ba?” Ta yi maganar da sigar shagwaɓa tana son kawar da waccan ruɗaɗɗen tunanin da ke son fallasata.

“Tace bata jima da baki ba.”

“Oh! Hakama ta ce. Ai shikenan zan je gidan na ɗauko da kaina.”

Ido Marwan ya buɗe “Ki ɗauko kuma?”

“Ba na Ummana ba ne.” Ta yi maganar tana dariya.

Hakan yasa shi girgiza kai da kuma son yin magana, sai dai kuma tashin Aafreen daga bacci yasa maganarsa datse.

*****

Washe gari bayan sun karya ta gama aikin gida Marwan ya sauƙeta a gidansu ya wuce wajen aikinsa, kasancewarsa malamin makaranta.

Tana zuwa gidan ta yi karo da Anty Hafsa ita kaɗai a tsakar gida tana ƙulle-ƙullen kunun ayarta.

Su Jiddah kuma sun fito da shirin tafiya makaranta sai Bunayya da take wanke jarkoki.

“Ha’an ke Bunayya ba zaki tafi makaranta ba kike wanke jarkoki. Gashi har ana neman kaiwa 9:00am na safe? Wata irin makaranta ce wannan duk baku tafi ba akan lokaci?” Ta yi maganar da zafinta.

Hakan yasa Hafsa ɗago da kai “Ikon Allah! Ke kuma Hajara kamar da aka wurgoki da sassafen nan, kin bayyana ba mu ji sallamarki ba sai banbamin faɗanki?”

Ƙarasowa Hajara ta yi tana yamutsa fuskarta cike da takaici “Ai dole na yi faɗa Anty Hafsa. Unguwar nan tayau babu yaran kowa sai naku ke zaune basu tafi ba. Kuma kuna gani ku kasa tusa ƙeyarsu.”

“Tun da ke kin zo ai sai ki tusa ƙeyar ta su.”

Ta yi maganar tana ci gaba da ƙulla kunun ayarta da yin waƙarta.

Mayar da kallonta Hajara ta yi kan Bunayya har a lokacin tana zaune tana aikinta kamar ba ita ta yiwa magana ba “Ke Bunayya ba zaki tashi ki tafi makarantar ba ne?”

Hawaye ya gangaro a fuskar Bunayya tana girgiza kanta “Bana zuwa Anty.”

Ido Hajara ta zaro waje tana kallon yarinyar da shekarunta ba za su wuce shida ba, ta kuma mayar da kallonta kan Hafsa “Kamar ya bata zuwa makaranta Anty Hafsa?”

Bata ɗago ba ta ci gaba da sha’aninta “Kamar yadda dai ta faɗa miki.”

Mamaki da al’ajabi ya sa Hajara jan kujerar tsugunne ta zauna tana kallon Hafsa “Da gaske ne abin da ake faɗa a kanki dama Anty Hafsa? Da gaske ne cewar kina Bautar da marainiyar ƴarki da hanata zuwa karatu?”

Ɗago kanta Hafsa ta yi ta yi da mamaki take kallon Hajara baki a buɗe, so take ta lallayo ashar ta makawa Hajara, sai dai gani take ko ta zageta ba zata huce ba, ba za kuma ta biya takaicin da ta ƙunsa.

“Me kika rasa a rayuwa Anty Hafsa? Mene ne baki samu ba gwargwadon rufin asirinki da zaki matsawa rayuwar marainiyar yarinyar da ke ce kika haifeta.

Me zaki samu da kuɗin tallar da xata kawo miki wadda baki same shi a duk sana’ar da kika yi ba? Dan Allah ki bar yarinyar nan haka, ki barta ta yi karatu ta samu ilimi kamar sauran yara, ki barta ta cimma burinta mai kyau kamar yadda kema ba a tauye miki naki burin ba.”

Shiru ya biyo bayan maganarta, kafin Hafsa ta murza gashin girararta ta kuma tauna laɓɓanta da kanne idanuwanta “Kin gama Hajara?” Ta jefa mata tambayar da ta sa Hajara ɗagowa tana kallonta.

“Na dai dakata ne, Anty Hafsa.”

Kai ta jinjina “Ina fatan ba Uwar Hajara bace ta min naƙudar haihuwar Bunayya? Ina fatan ba Hajara bace ta tsaya a kaina har na samu cikin Bunayya da ita ba?”

Ido Hajara ta ƙwalalo waje tana rufe bakinta da dukkanin hannayenta guda biyu “Subhanallah! A’uzubillah minasshaiɗanin rajim.”

“Ki fita a cikin lammarina da na ɗiyata Hajara. Bana son shisshigi, bana son sa’ido. Wato ashe har mai kai miki ruhoton halin da nake ciki ake, shi yasa kika ɗebo farar ƙada da sanyin safiyar nan kika zo kamar wata korarriya. To ahir ɗinki da ni, ki fita a lamarina.”

Zuwa yanzu Hajara ta gama fahimtar wacece Hafsa, ta kuma yarda da kowacce magana da Mu’awuyya yake faɗa a kanta.

Hakan yasa ta finciko Bunayya daga jikin famfon gidan, ta kuma riƙo hannun yarinyar tamau ta kalli Hafsa.

“Bani ce na samar da cikin Bunayya ba, kamar yadda ba Ummana ce ta yi naƙudarta ba. Amma ina mai tabbatar miki da cewar Bunayya jini nace da ta kasance cikin Ummana.

Me ma kika ce? Na fita a lamarinki, ba laifi idan kin aikata komai da kike so ga wadda kike so. Amma ki sani akwai hakki mai girma ga wadda ya cutar da maraya. Kullum tunakin akan kuɗi-kuɗi, komai na rayuwarki kina yinsa ne da son zaɓin ranki.

A yanzu ba na zo dan na saurareki ba ne, nazo ne dan ke ki saurare ni.

A wannan gidan da ya kasance mallakinmu da kuma ikonmu, bama buƙatar gurɓatattun mutane irin ki. Bama buƙatar mutanen da basu da ƙawa zuci na tausayawa ga yaran da suka haifa ba irin ki.

Zan kare rayuwar Bunayya, zan kuma tsaya mata da dukkanin ƙarfi da ikona, zan shigar da ke ƙara da nema mata hakkinta. Daga nan ke kuma zaki fice ki bar mana gidan mu. Ki fita daga gidan nan Anty Hafsa!”

Ta yi maganar da sauti mai amo, sai dai kafin ta farga taji sauƙar mari a kan kuncinta marin da ya haddasa mata ganin gilmawar farin abu da kuma tsintsaye masu yawo a kanta.

Sai da ta yi kokawa da buɗe idonta sau uku sannan ta ga hasken sa ya daidaita a idonta.

“Umma!” Ta faɗa tana murza wajen da aka mareta.

“Yaushe kika zama marar hankali Hajara? Yaushe kika yi ƙarfin jahilci da mayar da alkhairi sharri, Hajara? Yaushe ne kika fara biya huɗubar sheɗan na watsar da ƙafar zumunci? Yaushe kika fitsare kika zama marar kunya haka?” Adda Halima ta jero mata tambayar tana kallonta.

Kafin ta bata amsa ta fara jiyo tafi da yasa su jiyowa “Da kyau Adda Halima. Wasa mai kyau! Ke kin kasa korata shine kika sa ɗiyarki ta zo ta ci min mutunci!”

Kanta ta risina tana ɗagowa “Jinjina mai yawa Adda Halima.”

Daga haka ta fice ta bar musu gidan, tana jin zuciyarta na zafi, tana jin ba daɗi sosai, karo na farko yarinya ƙarama ta faɗa mata abu ta kasa ɗaukan mataki a akansa..

<< Jini Ya Tsaga 21Jini Ya Tsaga 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×