Skip to content
Part 24 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

“Allah ya mana tsari da bala’i da kuma maɗaukin fatan masifar a rayuwar mu.”

Hajara ta faɗa tana raɓawa ta gefen Hafsa.

Kamar ta watsa mata garwashin wuta a ƙahon zuciya haka Hafsa ta ji sauƙar maganar Hajara a kunenta.
Hakan yasa ta fizgota ta dawo da ita baya “Ni kike kika kira bala’i Hajara? Ni Hafsa?”

Kai Hajara ta risina ƙasa tana kwantar da murya “Ban yi lalacewar da zan kira ki bala’i ba Anty Hafsatu. Kawai dai ina addu’ar neman tsari da shine.”

Baki Hafsa ta ciza tana jin Hajara na ƙoƙarin tura mata ɗan ƙaramin hauka, idan bata yi da gaske ba zata sa ta rasa kimarta a wajen da ake girmamata.

“Me yasa kika kai Bunayya gidan su Mahaifinta? An faɗa miki ba zan iya riƙeta ba ne?” Ta yi maganar a hankali saɓanin yadda ta zo da masifa a baya.

Ɗagowa Hajara ta yi ta kalli Hafsa, ta riga da ta yi karatu akan ɗabi’un cikin Umman nata, ta kuma laƙanci kowacce kalar fuskar da zata zo mata da ita.

“Akwai rana anan Anty Hafsa, ki zo mu shiga daga ciki sai mu tattauna a ka wannan.”

Shiru Hafsa ta yi, kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta jinjina kanta tana bin takun Hajara.

Bayan sun shiga gidan Hajara ta kawo mata ruwa da lemo ta ajiye a gabanta tana ɗaukan kofi da tsiyaya mata shi.

“Bismillah Anty Hafsa.”

Kai ta girgiza “A ƙoshe nake, amsar tambayata nake so daga gareki Hajara.”

“Na sauƙaƙa miki wahalar mayarta da kanki ne, duba da yadda ba zaki ci gaba da zama a haka ba. Musamman da manema aure suka yi ca a kanki. Bana so kije gidan wani da ita a matsayin agolanci.

Mun riga da mun gama magana a kanta da kuma inganta rayuwarta. Bana yiwa ko maƙiyina fatan yin rayuwar talla balle kuma ƙanwata. Duk da nasan ba ra’ayinki ne hakan ba kema, wani dalili ne yasa kika zaɓi cutar da rayuwar Bunayya.”

Ta yi shiru tana kallon Hafsa kamar tana jiran jin amsa daga bakinta.

Miƙewa tsaye Hafsa ta yi tana kakkaɗe jikinta da kuma shimfiɗa murmushi a kan kyakkyawar fuskarta “Na gode da sauƙaƙa sauƙe nauyin hakki. Amma akwai hakkin da ban gama sauƙewa ba, ina fatan zaki taya ni sauƙe shi a amtsayinki na ƴa a wajena.”

Tashi itama Hajara ta yi tana kallon Hafsa “Wani hakkin ne baki sauƙe ba.”

Murmushi ta yi kafin ta juya a kan ƙafafuwanta tana takawa da nufar ƙofar wajen “Idan lokaci ya yi zaki tabbatar da shi.

Ku daina wahalar da kanku a kaina, domin ina yin abin da nake so ne a lokacin da nake ganin ya dace da ni.”

Daga haka ta fice tabar palon tana rufe ƙofar da bigata da ƙarfi, wadda yasa Hajara lumshe idanuwana tana haɗa kalaman Hafsa da ɗora su a ma’auni mai kyau, amma hakan ya gaza daga gareta.

*****

Lokacin da Hafsa ta dawo gida ko a fiska bata nunawa Adda Halima komai ba. Ta ci gaba da yin sabgarta kamar ba abin da ya faru a lokacin baya.

Tun Adda Halima na kasa kunne da kuma jiran jin abin da Hafsan zata ce amma sai taji bata ce mata komai ba.

Kasa haƙuri ta yi ta shiga ɗaki ta kira  Hajara ta tambayeta ko Hafsa ta zo gidanta.

Tace “Eh.”

“To ina Bunayya?”

“Na kaita wajen dangin mahaifinta.” Ta bata amsar.

Wadda hakan yasa Adda Haliman yin shiru tana jin kamar maganar ta zo mata a baibai ne.

“Hafsa ta sani?” Ta iya tambayarta a karo na biyu.

“Mun yi magana da ita na faɗa mata komai. Ko akwai wani abu da ya faru data dawo.”

“Babu.” Adda Halima ta faɗa tana yanke wayar, tasan mai shirun Hafsa ke nufi. Shirunta na nufin abubuwa da yawa, domin gara ace ta yi magana sau dubu akan ta yi shiru ta ƙyale.

Fitowa ta yi daga ɗakin har a lokacin Hafsa na tsakar gida tana wanke-wanken kayan data ɓata.

“Duk da sanin Hajara ta kai Bunayya wajen dangin mahaifinta, amma baki ɗauki kowanne mataki ba, baki ce komai a kan hakan ba Hafsa.

A yawan lokuta nafi son ki yi magana da ki yi shiru.”

Bata ɗago ba balle tasa ran zata tanka mata, har ta buɗe baki zata yi maganar sai taji sauƙar maganar Hafsan a kan dodon kunnenta.

“Aure zan yi.”

Jin maganar ta yi banbarakwai wadda hakan yasa ta buɗo idanuwanta waje “Aure? Aure da wa kenan?”

“Nasir Nasar.” Ta bata amsar kai tsaye.
Wadda yasa Adda Halima zagayowa tana kallon Hafsan “Nasir Nasar fa kika ce Hafsa? Tukunna ma wani Nasir Nasar ɗin? Ba dai ɗan gidan Alhaji Nasar Zayyar ba?”

“Shi ɗin dai Adda Halima.” Ta yi maganar tana kora ruwa a mugujin famfon.

“Lallai kin yi hauka Hafsa. Tukunna ma kin san ko waye Nasir Nasar ɗin? Yaro ƙarami da duka shekarunsa basu haura Ashirin da Bakwai ba.

Sannan yaron da duniya ta gama sheda muguntar sa da kuma rashin tausayi, wadda gata ya gama jiƙa shi.”

“Shi yasa zan aure shi dan na gwada masa kalar tawa tarbiyyar nima.”

Kai Adda Halima ta girgiza tana jin bata taɓa yin dana sani a kan Hafsa ba irin na yau.

“Wannan ba zai taɓa iyuwa ba, kada ma ki fara sa kanki a cikin rigar silken da ke cike da ƙusosi Hafsa. Nasir ba irin mazan da kika aura ba ne. Ta kowata fuska ya kere matsayinki nesa ba kusa ba. Ba zaki iya da shi ba.” 

Miƙewa Hafsa ta yi tana raɓawa ta gaban Adda Halima da kara wayarta a kunne.

“Shin zan iya ganin Nasir Nasar a gidan mu?”

Tana jin muryarsa mai sanyi da take a buɗe yana magana “Idan yanzu gimbiyar tace tana son ganina zan rugo da gudu.”

Sororo Adda Halima ta yi tana kallon Hafsan da ta yi kamar bata san da wanzuwarta a wajen ba “Ina son ganin ka a yanzun. Zaka gaida Addata.”

Daga haka ta yanke wayar tana shigewa ɗaki da kuma ɗauko abin wanka ta shige ta gaban Adda Halima.

“Hafsa wannan kuskure ne za ki yi a rayuwa? Za ki yi kuskuren jefa kanki a halaka.”

“Babu rayuwa idan babu kasada a cikinta Adda Halima. Hafsa ta daɗe da cin dubu sai ceto.”

Daga haka ta shige toilet ɗin tana doko mata ƙofar da ƙarfi wadda yasata lumshe idanuwanta.

Har zuwa lokacin da Hafsa ta shirya cikin ado da kwalliya mai kyau, gani take abin kamar almara ce, bata tsinke da al’amarin ba har zuwa lokacin da Hafsa ta fita ta sake dawowa ta sanar mata da shigowar Nasir Nasar dan ya gaidata.

Bata da zaɓin da ta wuce ya shigo ɗin, tun shigowarsa take kallonsa da kuma nazarinsa.

Matashin saurayi mai ji da kuɗi da kyau, kyakkyawa ne duk da kalar fatar jikinsa ruwan cakwuleti ne, amma kana ganinsa kasan yana ji da fatar da kuma gyarata, ya haɗu fiye da yadda za a ce ya haɗun a matsayinsa na cikekken bahaushe.

Risinawa ya yi zai gaidata ta bashi kujerar tsugunno “Ka zauna Nasir.”

Zama ya yi yana ɗan kakaɗe jiki da hank da ke hannunsa. Yana yamutsa fuska da kuma matseta.

“Ina yini Adda.” Ya yi maganar yana shafa sumar kansa.

“Lafiya lau Nasir. Ya gidan da mutanen gidan.”

“Lafiya suke.” Ya bata amsar yana daidaita fuskarsa.

“Hafsa ta ce aurenta zaka yi? Kana ganin babu matsala da gidanku akan hakan? Kasancewarka matashin saurayi mai jini a jiki.”

“Bani da matsala da ƴan gidanmu. Ina yin abin da nake so ne ba tare da wani ya ɗaga min murya ba.” Ya bata amsar a gajarce.

Hakan yasa ta ƙara kallonsa “Kai ke iko da komai naka kenan?”

“Ki kalle shi a hakan.” Ya sake bata amsa daga haka ya miƙe tsaye yana zura hannu a aljihunsa.

Ya fiddo damin kuɗi ƴan ɗari biyar-biyar guda biyu ya ajiye mata.

“Ki tashi lafiya.”

“Da ka ɗauki kuɗinka bana buƙatarsu.”

“Ba sai kin buƙace su ba dama. Kina iya ajiye su, kyautatawa ce daga Nasir Nasar Zayyar.”
Ya mayar da kallonsa ga Hafsa “Muje ko My Sweethart.”

Ta bi shi suka jera suna tafe tana rausaya da farfara ido shi kuma sai dariya yake yana kwantar da murya da mata magana kamar raɗa.

Dafe kai Adda Halima ta yi ciki da jimami da alhini “Ban ga ta inda wannan haɗin zai haɗu ba ko kaɗan.”

Sai dai kamar yadda ya ta bi shi suka jera suna tafe tana rausaya da farfara ido shi kuma sai dariya yake yana kwantar da murya da mata magana kamar raɗa.

Dafe kai Adda halima ta yi ciki da jimami da alhini “Ban ga ta inda wannan haɗin zai haɗu ba ko kaɗan.”

Sai dai kamar yadda suka fita suka barta haka Hafsa ta dawo ta tarar da ita. Kamar an dasata, bata jin ko damar tashi yiwa yara shimfiɗa ta yi.

Wucewa ta yi ta ɗauro alola zata shige Adda Halima.

“Da fatan kin yi sallahr Isha’i Adda Halima? Wannan zaman da kika yi kamar mai nazarin ɗinke ƙasa gaba ɗaya.”

“Hafsa kin lura da abin da na gani a tare da Nasir? Ko kuwa idanuwanki ne ya rufe ruff a kansa.

Kina ganin yadda yake magana a tsattsaye kai tsaye ba shakka ko shamaki akan maganarsa anya zamanku zai iyu da ke?”

“Ki jira lokaci sai ki tabbatar da yiyuwar hakan.”

“Wannan kuskurewa ne Hafsa ba zan bari hakan ta faru ba. Ke ba yarinya ba ce, Nasir yaro ne sosai ba zaki aure shi ki lalata mana kimar gidan mu ba.”

Dariya Hafsa ta yi dariya mai yawa tana nuna Adda Halima “Kima! Kimafa kike ce Adda Halima? Mece ce ita? Hafsa bata san ta ba.”

Daga haka ta raɓa ta gefenta ta wuce “Kuɗin da Nasir ya baki dama ce a gareki ki fara sana’a ki tsaya da ƙafafuwanki, ina ga za su ishe ki fara sana’ar gida ta mata. Idan kina buƙatar ƙari ki min magana sai na ƙara miki. Ba cin hanci na baki ba, kyautatawa ce a tsakanin ƙanwa ga yayarta.”

<< Jini Ya Tsaga 23Jini Ya Tsaga 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.