Skip to content
Part 28 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSA SADAUKARWA NE GA RAMLAR ABDULRAHMAN MANGA (MAI DAMBU)

Ƙara kallon Hafsa Umma take da baki a buɗe, ganin yadda ta yi fess ta murmure abinta, ya yin da take kallon Haliman da ta fita a kamanninta ta yi zuru-zuru kamar da ta kwana biyu tana ciwo.

“Na ɗauka tun lokacin da nace kada ki bawa Hafsa wajen zama a gidanki, kika koreta Halima.” Mayar da kallonta ta yi ga Hafsa da zuwa lokacin ta cika ta yi taf.

“Ki tashi ki tattaro kayanki ki kama gabanki.” Umma ta faɗa da sauti mai amo wadda yasa Hafsa ɗagowa.

“Kin ji ai abin da na faɗa.”
“Dan Allah Umma ki yi haƙuri. Ki barta a nan, idan ta tafi ban san ina zata je ta zauna ba.”

“Taje ko ina take son zuwa mana. Duniya faɗi gareta ai Halima. Akwai darasi mai yawa a cikinta da idan ka kasa samu a zaune zaka same shi a tafe.”

“Dan Allah Umma ban da ta wannan sigar. Hafsa ta sauya, tun da ta zo lafiya muke zaune da ita, ba abin da ya fito sabo da ke nuni da halinta na baya, wannan sabuwar Hafsa ce a gabanki Umma.” Ta yi maganar tana ƙoƙarin jeranta kalmomin da ta ƙarfafi Umma da ita kanta.

“Kina kallon Madubi kuwa Halima. Kin ga yadda kika rame kika fita a hayyacin ki, kuka har kice min kina zaune lafiya da Hafsa.”

Kafin ta yi magana Hafsa ta miƙe a kan ƙafafuwanta tana ɗan turo baki da haɗe rai “Ki tashi lafiya Umma.” Daga haka ta ɗage labilen ɗakin ta bar su a ciki.

Umma bata bi ta kanta ba ta sake kallon Haliman. “Me ke faruwa Halima? Me ya sameki kika yi haka?”

“Lafiya lau nake Umma. Kawai yanayi ne na rayuwa, kin san yanzu komai ya sauya, nauyin da ke kaina ƙaruwa yake saɓanin a baya da nake da maɗaukin nauyin namu.”

“Amma duk da haka kika ƙara ɗorawa kanki nauyin zama da Hafsa?”

“Ban taɓa kallon Hafsa a matsayin nauyi a wajena ba Umma. Ki yi haƙuri ki daina nuna banbancina da ita, hakan zai sa ta ji ba daɗi, ta yi tunanin ko kema bakya sonta ne kuna nuna fifiko a kanmu da ita.”

“Bamu taɓa ƙin Hafsa ba, halinta muke ƙi Halima, kuma kema kin sani ai.”

“Duk da haka ki barta a tare da ni Umma.”

“Kawai kin dage ne Halima, amma ni na riga dana san zamanku waje ɗaya da Hafsat ba abune mai ɗorewa ba, ko kun zauna na daɗi ɗan lokaci kaɗan ne zata sauya a kalar daɗin, Hafsat butsu ce haka kuma mishan ce mai ɓadda kamarta ta zahiri. Ni na haifeku ni nasan halin ko wacce a cikin ku, ba zaki iya zama da ita ba.”

“Zan iya zama da ita Umma, zan zauna da Hafsat ba tare da hayaniya da hatsaniya ba, za ku sha mamakin sauyuwar hali da ɗabi’ar da take da ita a baya. Wanan sabuwar Hafsa ce a tare da ni, wanda ta samu ban-banci mai yawa daga waccan da kuka sani, zan zauna da ita na sake aurar da ita a karo na uku in sha Allah, ke dai kisa ma zamanmu albarka kawai.”

Kallonta tayi kafin ta girgiza kai da ciza laɓɓan ta “Kun zauna da Hafsa a wan can lokacin cikin kariya da dafawar mijinki, amma kuma yanzu akwai ban-banci Halima, mijinki baya tare da ke, ƙasa ta lulluɓe ganin sa, baki da wani mataimaki sai Allah, sai kuma marayun yaran da ya barki da su. Kada ki gayyato wata matsala a cikin rayuwarki, kada ki janyo Annoba cikin zuri’arki ku zauna ta tarwatsa miki kan ahalinki.”

Kai ta fara girgizawa tana toshewa Umman nata baki “Hafsa ma ahalina ce Umma, ki daina aibata ta wajan kiranta Annoba, har yanzu akwai ƙuruciya atare da ita. Ki mana fatan alkhairi kawai Umma, kada ki fara wargaza zaman da ba’a kai ga farashi ba.”

“Yarinta? Yarinta fa kikace Halima a tare da Hafsa, yarinyar data shekara talatin a duniya kike kirama yarinta, yarinyar da take da matashiyar budurwa ƴar shekara 12 a duniya kike kirama yarinta, Hafsan data yi aure huɗu a rayuwarta kike alaƙanta mata suna da yarinya?”

Kai Halima ta gyaɗa “Koma yaya ne Umma, ni awajena Yarinya ce, tunda har yanzu a ƙasa na take, haka kuma a matsayin babba nake a kanta Umma.”


  Tashi tayi ta gyara lulluɓin mayafin ta “Ba zan musanta hakan ba, bazan kuma shiga cikin wata matsala dazata kunno tsakaninku ba, amma ina jin tausayinki Halima.” tana gama faɗar haka ta fice ta barta, duk kiran da take mata bata tsaya ta saurare taba.

Har ƙofar gida ta biyota amma Umma bata yi a lamun ta ji ba balle ta dawo baya.
Tasan Halima ta ɓoye mata wani abu ne, amma zata zuba musu ido ta kalle su, tun zuwanta unguwar taji labarin komai, amma shine Halima ta rufe mata. Zata barta da Hafsa ta koya mata sabon karatu na rayuwa, wataƙila ta sauyata daga mai sanyi zuwa zafi.

Bayan Mako biyu

A cikin kwanakin da suka shuɗe zaman nasu za a iya cewa da daɗi da kuma rashinsa, sai dai ta ture komai ta kuma ɗauki shawarar Hafsa guda ɗaya ta fara sana’a a gidan.

Tana saida tuwon shinkafa da miyar taushe, wani zubin harda waina, sai dai duk da haka bata tsira da ƙananun maganarta ba, wani lokacin ta tanka mata ta bata amsa, wani lokacin kuma ta shareta.

Kusan dai zuwa yanzun Adda Halima ta fara biyewa Hafsa suna musauyan magana wadda wani lokacin maƙota su zo su basu haƙuri wani lokacin a fara mata faɗa.

Kuma har a lokacin maƙotan na yabon kyawawan halin Hafsa domin ba a taɓa jin maganarta ko faɗanta da maƙotanta ba, asalima alkhairinta ke yawo a bakunansu.

A lokacin kuma ta mayar da hirarta da Nasir da magrib ana sallahr issha kuma sai ya tafi, sai dai su yi ta waya, abin na bawa Adda Halima takaici kuma, ita na yarinya ba amma ta kafa kwarkwasa a waya.

A cikin hakan ne Jiddah ta zo ta sameta tana waya ta kirata “Anty Hafsa Ummi na kuka ta tashi a bacci.” Ta mata magana amma bata kulata ta yi ta faɗa, ƙarshe ta ɗauko Ummi ta direta a gabanta tana runtuma ihun.

Haushi yasa ta kashe wayar ta bata yi sallama da Nasir Nasar ba. Ta ɗauke Jidda da mari wadda yasa ɗaukewar jinta.

Kafin ta fara tamola da ita a ɗakin kamar Allah ne ya aikota, jin ihun Jiddah da kuma na Ummi da ya yi yawa, yasa Adda Halima fitowa a guje tana gyara ɗaurin zaninta.

Sai dai me, Hafsa ta gani tana ta take Jiddah kamar Allah ne ya aikota. Da mamakinta kuma taga Hafsa ta ƙyale Jiddah ta ɗauki ƙaton ice zata rafkawa Ummi a kai. Da mugu gudu Adda Haliman ta kare Iccen ya sauƙa a hannunta wadda ya haddasa fidda wani ƙara hannun nata ya karye.

Ido Adda Haliman ta runtse da zafi tana jin azabar da bata taɓa ji ba a tsawon rayuwarta. Zuciyarta na zafi  kamar wuta, tana jin zafin da ke cikin hannunta bai kai wadda take ji a hannunta ba.

Cikin dauriya ta janyo Ummi da ɗaya hannunta ta Miƙawa Jidda ita da har lokacin take kwance tana kuka “Tashi ku fita.” Ta faɗa da ƙyar hakan yasa Jiddah ɗaukan Ummi ta fice a gidan.

“Ba zaki min kisa a gida ba Hafsa. Ba zaki kashe mu ni da yarana ba Hafsa. Dole ki bar gidan nan ko bakya so. Ko babu wadda zai tsaya min akan ki fita a gidan nawa.”

Daga haka ta juya ta bar ɗakin tana jin wani azaba a hannunta, kanta na ɗauka kamar ƙararrarawar da aka buga.

Wayarta ta lalimo ta kira Ma’awuyya kasancewar ƙarfe tara na dare ne “Ma’awuyya ku kira min mai ɗori hannuna ya karya.” Daga haka ta yanke wayar tana jin salatinsa da yake yi, ba a ɗauki mintuna ashirin ba sai gashi da mai ɗaurin, yana ta faman jero ma abin da ya faru, sai dai babu amsa, tana jin azabar da bata taɓa ji ba, tana so ta yi ihu ko ta samu sassaucin azabar da take ji amma inna.

Yaranta da ke wajen ya hanata yi sai hawaye da ke gangarowa a kan idonta, ta kalli Aadamu da shima idanuwansa suka rine saboda tausayi.

“Ka kai Jiddah Kyamis a dubata.” Haka ta faɗa tana ƙara ciza laɓɓanta da take jin kamar zata taune su.

“Mai ya faru da Jiddah?” Suka tambaya a tare, sai dai babu amsa.

Ganin halin da take ciki ya kaita kyamis ɗin wadda xuwa lokacin zazzaɓi ya rufeta sai da aka mata allurai a ka bata magani.

Dawowarsu an gama ɗaurin, ya buƙaci dubu biyar. An yi sa’a akwai kuɗi a wajen Mu’awiyya ya bada kuɗin, kusan har lokacin suna jero mata tambaya amma babu amsa sai lumshe ido da tayi hawaye na gangarowa a fuskarta.Ganin Hakan suka fice sun san ba lafiya ba, ba kuma ƙalau ba. Sun yanke hukuncin da suke tunanin shine na ƙarshe da za su yi koda ace Umma zata iya tsine musu, za su kawo ƙarshen al’amarin.

Hakan yasa washegari ko gidan basu shigoba suka wuce gidan Anty Hajara.

*****
Ƙofar gidan Adda Halima cike take da mutane, da yawa fuskokinsu ɗauke da alhini da jajjaɓin abin da yake faruwa, wanan ba shine karo na farko da suka saba taruwa a wajan ba, haka ba shine karo na biyu da suka fara yi musu shari’a a tsakanin su ba.

Daga tsakiyar wajan kuma Adda Halima ce tana kuka tana jan majina, hannunta ɗaya naɗe cikin bandeji wanda ya saƙalo har wuyan ta, wajen da aka mata ɗorin karayarta ta jiya.

“Halima kiyi haƙuri ki koma gidan ki, kibar kuka da tarawa kanki mutane. Hafsat ƴar uwarki ce, ko babu komai JINI YA TSAGA FATA KUMA TA CIZA. Ita ɗin dolenki ce, komi zata miki ɗole kiyi haƙuri ki zauna da ita.”

Ɗagowa tayi ta kalli mai maganar idonta na ci gaba da ambaliya da fidda hawaye, muryarta har rawa take saboda zafin da zuciyarta keyi “Tabbas jini ya tsaga a tare dani da Hafsat wanda ya maida mu abu guda, amma hakan ba shi ke nuna cewa zan ci gaba da zama da ita ba, Allah ya sani ban iya rigima ba, ku sheda ne a kaina, Zuwa Hafsa rayuwata ya mayar da ni mafaɗaciya ƙarfi da ya ji. Yanzu an kawo gaɓar da zuciyata bazata ci gaba da jure jin miyagun maganganun da suke fitowa daga bakin Hafsat ba. Ƙanwata ce amma kuma ita ce matsala ta. Ba zan bari ta yi kisa a gabana a gidana ba, ba zan bari ta haramtawa yarana jin daɗin zaman gidan su ba.” ƙarasa maganar tayi tana ci gaba da kuka mai sauti.

‘Ta riga data gama yankewa kanta hukunci, idan har Iyayen su basu shiga cikin wanan batun ba, to babu makawa zata tafi tabar Hafsat a gidan, zata kuma rarraba yaranta zuwa gidajan dangin su, ita kuma ta tafi wani garin, wata duniyar daban tayi rayuwa a tare da su.’

“Kawai kin dage ne Halima, amma ni na riga dana san zamanku waje ɗaya da Hafsat ba abune mai ɗorewa ba, ko kun zauna na daɗi ɗan lokaci kaɗan ne zata sauya akalar daɗin, Hafsat butsu ce haka kuma mishance mai ɓadda kamarta ta zahiri. Ni na haifeku ni nasan halin ko wacce acikin ku, ba zaki iya zama da ita ba.”

Ido ta buɗe tana kai kallonta ga mutanen da suke kewaye da ita, hawaye na ƙara zuba akan idon ta _’Umma ta yi gaskiya, da gaske Hafsat Annoba ce, gashi ta raba tsakanina da makusanta na. Gashi maƙotana su ƙi yarda da ni.’

Kallonta ta kai ga inda Hafsa take, tana marairecewa a gaban mutane, sai matsar hawaye ta ke “Dan Allah Adda Halima ki yi haƙuri ki yafeni ki dawo mu zauna tare, kin san bazan iya rayuwa ki na fushi da ni ba.” ƙasa takai tana riƙe ƙafarta, idan ta faki idon mutane kuma sai ta mintsini ƙagar ta aika mata da gwalo da dariya, amma da an kalleta sai ta koma kalar tausayi da hawayen ƙarya.

“Haba! Wata irin zuciya gareki Halima? Kina ga yanda ta ke baki haƙuri kina aika mata da magana marar daɗi, ai naka naka ne komai zai maka, balle kuma ya roƙeka a kan ka yi haƙuri. Ku wuce mu tafi ku ƙyaleta.” Aa’i ta faɗa, kasancewarta aminiyar Hafsa.
Gaba ɗaya mutanen wajan suka fashe suka barta da yawa suna mita akan halinta na rashin haƙuri, kai da ɗan uwanka ace ka gaza haƙuri da shi har kana tara masa mutane. Yau Maman Walid da Maman Khadija basa nan sun tafi sutura rasuwar da aka yi, ta tabbbata da suna nan ƙila da sun tsaya mata sun kori Hafsa.

Sai da mutanen suka baje gaba ɗaya sanan Hafsa ta miƙe tana karkaɗe jikin ta “Kibar ƙoƙarin bayyanar da gaskiyar da ta ke ɓoye, saboda mutane suna yadda da abin dake zahiri ne Adda Halima. Koda bakya so, ni na zama dolenki haka idan kika ce zaki fidda ni ta ƙarfi tofa nima ina da gado a gidan nan, saboda yaran ki yarana ne.” tana gama faɗar haka ta shige cikin gidan tana rausaya jiki da karkaɗa mata ɗuwawu.

“Ya Allah.” Halima ta faɗa hawaye na zuba a kan idonta.

Wannan kuskurenta ne, laifinta ne da ta bari ta zauna da Hafsa, wataƙila harda taurin kanta da ƙin shawararta ya janyo mata girbar abin da ta shuka.

Dan haka zata bar mata gidan ta zauna ita kuma ta kama gabanta Wannan shawarar data yanke ce, sai dai kafin ta cira ƙafarta ta fara jin jiniyar motar ƴan sanda ta cika ƙofar gidan, wadda hakan yasa mutanen unguwar leƙowa, motar bata tsaya a ko ina ba sai a ƙofar gidan Adda Halima.

Ma’awuyya da Adamu suka fito, sai wasu ƴan sanda mata guda biyu da maza guda biyu a bayan motar.

“Ku zo mu shiga tana ciki.” Ma’awuyya ya faɗa bai kalli inda Adda Haliman take ba kamar yadda shima Aadamun bai kalleta ba.

Suka kutsa cikin gidan da Ƴan sandar a lokacin Hafsa da ke zuba waƙarta tana rangwaɗa a tsakar gidan na tabbacin ta yi nasara ta ji an ce “Gata nan.” Hakan yasa ta juyo ganin polisawa mata ƙarafa masu ƙirar ƴan kokawa yasata ƙamewa tana kallon Mu’awuyya da ke huci kamar kumurcin zaki, cak walwalar da ke fuskarta ta kauce sai ruɗani ya maye wajen..

*****

Mutanen nata takaici a kan Hafsa wasu na tunanin anya za a samu mai hali irin na Hafsa? Wannan tambaya ce da na bawa wasu amsarta wasu kuma ke son su bibiya al’amarin rayuwa. Akwai irin Hafsa da yawa a duniya, wataƙila idanuwa basu fiya maida hankali a kansu ba.

Kaɗan a ciki za a samu masu hakan, Idan rayuwa ta ƙara bamu dama zamu haɗu da Ku a cikin labarin *ƘAWATA CE* Labarin Nabeela da Nabeeha, akwai Yiyuwar Nabeela ta dame Hafsa ta shanye ta tsaf a kan nata mugun halin, duk da suna da banbanci na suna da zamani. Sai dai labarin ba free bane kamar na Hafsa na kuɗi ne a kan N300 kacal, in sha Allah za ku so shi fiye da wanan. Mu dai je tafiya, yawan cmnts naku yawan typing da zan na baku.

Na riga na yanke wani hukunci zan daina typing kullum saboda naga cmnts na ƙasa sosai. Kamar yana baku wahala, nima kuma rubutun na bani wahala, sai mu sauƙaƙawa juna kawai.  

Ina gaida duk masu bibiyar rubutun Hafsa, ina kuma jinjina musu da yadda suke jurar takaicin da take ƙunsa musu, an zo gangare da ƙila ta fara tone abin da ta shuka. Ku dai ku ajiye min kalmar giramamawarku ta hanyar yin comments da share na labarin ga masoyanku.

<< Jini Ya Tsaga 27Jini Ya Tsaga 29 >>

1 thought on “Jini Ya Tsaga 28”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×