Skip to content
Part 29 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Ƙarasowa kusa da ita Jibgegiyar ƴar sandar ta yi  fuskarta baƙa ƙirin kamar motar da ta yi karo da bishiya. Babu sassauci da rangwame, a tare da ita, asalima yadda ta haɗe fuskar tata zaka yi tsammanin zata iya fashewa ne a cikin kowanne hali.

“Ki tattaro kayan ki yanzu ki bar gidan nan.” Muryarta mai kama da rugugin aradu da ke barazanar haddasa girgizar ƙasa ta sauƙa a kunnen Hafsa.

Wadda sai da taji kunnune nata ya yi dumm ya ɗauka kafin kuma ta bubbuga kunnenta “Kamar ya na bar gidan nan? Na je ina kuma?” Ta tattaro duk wani ƙwarin gwuiwarta ta yi maganar da matar.

“Ki tafi ko ina ne a duniya. Amma nan gidan marayu ne.” Ɗayar mai rangwamen fuskar birrai ta yi magana.

Hakan yasa Hafsa juyowa tana kallon Mu’awuyya wadda har a lokacin fuskarsa babu alamun sassauci, da alamu ba haka ya so ba, ba haka ya so su yi magana da ita ba. Yasan wace ce Hafsa, ya kuma san me zata iya yi.

“Yaushe Folisawa suka zama dilallan gidan?” Hafsa ta yi magana, sai dai kafin ta ji amsa kamar yadda ta tsammata, ta ji wankekken mari a kan fuskarta.

Marin da ya ɗauke jinta da ganinta, da kuma fashewar gefen bakinta, haka yasa ta yi taga taga kamar zata faɗi, kafin dai ta yi dauriya ta tsaya tsam a kan ƙafafuwanta da ba su da ƙarfi.

“Ki shiga hankalin ki. Ba wasa ya kawo mu nan ba, idan ki ka ce zaki nuna mana taurin kai yanzu za mu iya sauya miki kamanni.” Fusatacciyar ƴar sandar ta faɗa cikin hargitsattsiyar maganarta, wadda bata fita da hausa sak. Muryata  na tashi wadda take ratsawa har waje da sauran gidajen da ke maƙotaka da Adda Haliman.

Sai da ta ɗauki tsawon mintina uku sannan ta dawo hankalinta, a lokacin kuma ta hango Adda Haliman ta shigo gidan da gudu, saboda jin ihun ƴan sandan.

“Me ke faruwa ne?” Ta jefa maganar tana tambayar mutanen wajen.

Mayar da kallonta ta yi ga Ma’awuyya da ya ke zame idonsa yana ƙin haɗa ido da Umman nasa “Ma’awuya me ke faruwa? Waɗannan jami’an tsaron na mene ne?”

“Za su fitar da Anty Hafsa ne. Dan Allah Umma ki yi haƙuri karki ce komai.” Ya yi maganar yana tauna laɓɓansa.

Kalmar magiyar da yace da kuma roƙon Allah da ya haɗata da shi yasa ta yi shiru ta raɓa ta gefen su ta shige ɗakinta, bai san cewa itama ta kai ƙarshe ba, bai san cewa ta gaji da karɓar uƙubar da Hafsa ke basu a ɓoye ba, ta ƙwace kowata kimar da take da ita.

Amma kuma idan Hafsa ta fita a yanzu ya zata yi da maganar mutane? Tana gudun abin da za a ce daga gareta ne ita ta fara yinsa, Kamar dai yadda take da gudun zuciyar mutane.

Tashi ta yi a hanzarce da ƙafafuwanta ta nufi wajen ƴan sandar sai dai basa nan sun tisa ƙeyar Hafsa da murɗaɗɗen kulkinsu a kan ta fito da kayanta ta fice a gidan.

“Ma’awuyya ka ce su bar wannan abin su ƙyaleta.” Muryar Adda Haliman ta fito da amo da kuma rawa.

Wadda hakan yasa Hafsa ɗagowa ta kalli Adda Haliman. Tana jin wani abu na ketowa tsakanin ƙirjinta, tana jin nauyi da girman ƴar uwarta a karo na ba adadi.

‘Shin a duniya za a samu ƴar uwa kamar Adda Halima? Za kuma a samu mutum mai zuciyar sadaukarwa da kawaici kamar ita ɗin?’_ Kai ta girgiza wani hawaye na zuba a idanuwanta, hawayen da take da tabbacin ya shammaceta ya kuma fito mata ne tun daga zuciyarta.

“A’a Adda Halima. Ya kamata na tafi yau. Karki hana su karɓawa kan su ƴanci, kar ki bari su fara kallon ki a matsayin mai son kai da kuma son zuciya. Karki bari su na kallon ki a matsayin marar sanin ciwon kai.” Ta yi maganar tana janyo ƙatuwar jakarta da kuma ɗaukan Ummi a kafaɗarta.

Ta tsaya a gaban Adda Haliman tana share hawayen fuskarta, da kuma yin murmushi “Na san ban cancanci zama da ke ba. Na san ban miki komai na alkhairin da za ki ci gaba da kashe rayuwarki saboda ni ba. Yaranki na da gaskiya, sun fahimci ƙuncin ki tun kafin ki faɗa musu.”

Kai Adda Haliman ta girgiza hawaye na ɓallewa a fuskarta, har yanzu bata ji ko sau ɗaya tana jin haushin Hafsa ba. Bata ji ko alama guda ɗaya na cewar tana jin haushinta ba, koda take cewa ta bar mata gidanta tana faɗa ne dan ta kore takaicinta na lokacin, ba kuma dan hakan ya kai har zuciyarta ba. Kamar yadda bata ɗauka idan zata tafin zata ji ba daɗi ba.

“Idan kin tafi ina zaki je yanzu?” Ta jefa mata tambayar tana ƙara jin wani  abu na taso mata tun daga ƙirjinta har maƙoshinta, wani abu mai ɗacin ɗaɗatawa.

“Zan koma inda na fito.” Daga haka  ta kawar da kanta tana kallon fusatattun jami’an tsaron.

“Mu je ko?”

“Hafsa kar ki tafi. Ku barta dan Allah mu zauna.” Adda Haliman ta faɗa da gunjin kuka, sai dai tuni Mu’awiyya ya bar gidan shi da Aadamu. Allah ya sani ba za su juri jin kukan mahaifiyarsu ba, kamar yadda ba za su juri ganin Hafsa a gidan ba, domin zata iya ɗorawa mahaifiyarsu hawan jini.

Da sassarfa Adda Halima ta sake shan gabansu “Ki bani Ummi na ruƙeta Hafsa. Bana so ki ci gaba da tafiya da ita kina ɗorar da fushin ki a kanta.” Adda Haliman ta faɗa.

Dariya Hafsa ta yi tana bibbiga bayan Ummi sannan ta kalli Adda Haliman “Ummi na tare da kulawar Uwarta Adda. Idan na barta a tare da ke zata sake zama wani nauyin a gare ki.

Gashi har yanzu kin gagara tsayuwa da ƙafarki.” Bakinta ta taɓe a karo na farko.

“Ƙila kuma saboda ita Alhaji malam ya karɓe ni. Da tuba na, so ki ci gaba da kula da yaranki, amma kada ki ci gaba da miƙe ƙafa kina bin dogon layi da takarda mai ɗauke da tambarin gabatar da kai, kina nuna su a matsayin marayun da suka rasa uba.

Ki nemi na kanki ki nunawa duniya babu maraya sai rago, ki zama ke kike badawa ba wai a baki ba Addah.” Daga haka ta ja ƙatuwar jakarta ta yi gaba tana jin idanuwan Adda Haliman na yawo a kanta.

Lokacin da suka isa ƙofar gidan ta tarar da matan unguwar na tsaye sun yi cincirindo kowa ɗauke da fuskar jimami. Ya yin da suka tareta suna tambayarta “Maman Bunayya haka kuma abun da ya faru? Abin har ya kai da ƴan sanda?”

Murmushi ta yi tana yawata idanuwanta a kansu, a zaman da ta yi da su ta fahimci su wasu irin mutane ne masu son jin gulma da kuma yin zancen wani, da alamu yanzu sun so jin ba’asi da ƙarin bayani a gareta.

“Karku damu. Domin na faɗa muku Adda Halima na da motsi a kanta da yake tashi lokaci zuwa lokaci, so ko ban tafi yau ba dama, nasan tun da suka juyo zan tafi. Adda Halima na sona ba zata bari na yi nesa da ita ba, amma idan abin ya motsa to kowa tana ƙinsa ne. Ina fatan zakuna mata uzuri idan irin hakan ya sake zuwa gareku.”

Ciki da alhini mutanen wajen suke jinjina al’amarin “Zan je gida na karɓa mata magani.”

“Allah sarki. Allah ya bata lafiya, haba Halima mai haƙuri da faram-faram da mutane amma tashi ɗaya tabi ta jirkiɗe ta fita a kamarta. Ni nasan ruwa baya taɓa tsami banza.” Usaina ta faɗa cike da jajjaɓin abin.

Anan dai ta yi sallama da mutanen unguwar har a lokacin polusawan na tsaye.

Ganin abin nata bana ƙare bane yasa ɗan sanda namijin wani tsamurarre mai ƙirara kalangu ya mata magana “Malama wannan sallamar taki ba ƙarewa zata yi ba, ki zo ki hau abin hawa kuma ki kama gabanki.”

“Dole ai malam. Zaman mutunci fa muka yi da su ba zaman yaƙi ba, kaga kuwa ai dole na tsaya mu yi sallama da su.”

Kai ya jinjina a lokacin Aadamu ya dawo da adaidaita nan suka tusa kayanta da ita kanta ta shiga, suna gaba polisawan na biye da ita.

“Oh ni Hafsatu wannan ɗaukaka haka jami’an  tsaro na take min baya.” Ta yi maganar tana tuntsirewa da dariya.

Har zuwa lokacin da suka isa tashar garin, anan kuma tunaninta ya kulle na rashin sanin inda zata dosa ganin Jami’an ƴan sanda na biye da su da kuma sauƙowarsu yasa ta nufi motar da ta ji ana kiran *”Tambuwal.* Saura mutum ɗaya.”

Mamakinta na ƙaruwa a kan dagiyar ƴan sandar da kuma hasashen ko nawa su Mu’awuyya suka basu da har suka yi wannan tsayuwar dakar.

Tana shiga motar aka tashi kwandastan ya juyo yana tambayarta “Hajiya ina zaki sauƙa?”
Shiru ta yi tana nazari kafin daga bisani ta buɗe bakinta “Ƙauyen Mai kaɗa.”

Tana lumshe idanuwanta _’Gidan Gaggwo Faɗim zata je. Ita kaɗai ce a yanzu take sa ran zata dawo da komai ya zama daidai. Kamar yadda ita kaɗai ke iya juya al’amuran gidansu kai tsaye.’

“Dubu ɗaya kuɗin ki.”

Bata ja ba ta zaro ta bashi kuɗin, burinta su isa a kan lokaci.

Barkanmu da war haka masoyan Hafsa. Ina fatan yanzu dai ranku ya yi fari. Hafsa ta bar gidan Adda Halima amma akwai abu guda da ta bari a can. Ina fatan zaku yi share dan ya isa ga masoyanku, domin su taya ku jin daɗin yau.

Na gode da bibiyar rubutuna, in sha Allah zamu ɗora posting kullum dan mu kai ga ƙarshen zaren labarin.

<< Jini Ya Tsaga 28Jini Ya Tsaga 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×