Skip to content
Part 3 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Shuru ne ya ratsa atsakanin su, ba tare da sun sake magana ba, sai dai har yanzu hannayen Adda Halima na riƙe dana Hafsat tana kuma kallon ta.

Zame hannunta Hafsa tayi ta kalli Adda Halima tana girgiza kai “Bazan iya cewa na sauya ba Adda Halima, kamar yanda bazan iya hararo abin da zai faru dani agobe ba. Tabbaci ɗaya nake dashi akaina shine zan iya miki biyayya kwatan-kwacin yadda ɗiya kema uwar ta.”

Kallonta Adda Halima tayi, ta girgiza kai “Wanan ma bazan sameshi ba atare da ke ba Hafsa. Kawai zan iya kawar da kaina kamar yanda na saba awancan lokacin. Amma alfarma ɗaya nake buƙata agare ki dan Allah.” ta ƙarasa maganar tana haɗe hannayen ta biyu awaje ɗaya.

Kallon ta Hafsa tayi tana faman ɗaga mata kai “Ina jinki Adda Halima. Wata alfarma kike so agare ni?”

“Nan unguwar sabuwar unguwa ce agaremu, haka kuma sabon waje ne da yake ɗauke da mabam-banta muta ne. Ta ko ina akewaye nake da maƙota kaɗan masu sona da yawa kuma masu jiran ganin gazawa da tawaya atare da ni na kasawa.”

Numfashi taja ta fuzgar da iska mai zafi abakin ta sanan ta sauƙe wata ajiyar zuciya ahankali, kana taci gaba da magana “Hafsa ɗabi’arki da halayyarki ba sabon abu bane agare ni, amma bazan iya jure ƙananun maganganun da suke ɗabi’arki bane, koda zama yayi zama atsakanin mu idan wani saɓani yazo ya gifta to dan Allah ya ƙare alokacin, kada ki fiddashi waje wani yaji cikinmu, kada kuma ki fesar da zafin sa ta yanda zai zama abin gori da manuniya akan zumuncin mu.”

“In sha Allah Adda Halima, na faɗa miki atare da ke wanan sabuwar Hafsa ce. Bazan mai-maita abin da nake abaya ba. Koda ace zama yayi zama to na tabbata zan ƙaru ne da kyawawan ɗabi’u daga gareki, wanda zasu sauya nawa ɗabi’un.”

“Allah yasa hakan to.”

“Ameen.”

Daga nan suka shiga hirar su ta yaushe gamo. Kaɗan-kaɗan sukan taɓa abin da ya shafi rayuwar su da kuma gidan su. Wanda ga Adda Halima takanji kewar gida atare da ita, amma ganin Hafsa ayau sai ya cike mata ko wata irin kewa da take tare da ita. Sai da suka kusan raba dare suna hira kafin kowaccen su ta tafi ta kwanta.

*****
Washe gari.
Kafin Adda Halima ta tashi, Hafsa ta tashi tayi aiyukan gidan hatta shirya yara ita tayi suka tafi makaranta. Kana ta sake gyara gidan.
Lokacin da Adda Halima ta fito taga gidan tarwai atsaftacce tasha mamaki “Kaddai kice min yau kin gama komi na gidan?” ta ƙarasa maganar tana riƙe da haɓarta.

Murmushi Hafsa tayi tana gyaɗa kanta “Aikuwa yau kam na hutar da ke komi Adda. Ga ruwan wanka can na haɗa miki yana toilet, idan kin shirya sai muyi karin kumallo.”

“Ikon Allah! Kice yau kin maida ni asalin basarakiya Hafsa. Lallai na ƙara yadda mutum rahama ne babba, yau gashi babu wanda ya tasheni dan wata hidimarsa, kin ɗauke min wanan nauyin. Nagode ƙwarai da gaske.”

Kai Hafsa ta girgiza mata “A’a Adda Halima duk abin da na miki ko nayima yaran ki kaina nayiwa. Duk wani abu aduniya na kirki ko akasin sa idan mutum ya aikata to kansa ya aikatawa. Balle kuma abin da ya fito daga naki tsagin to sai ya cika ko wata ƙauna atare dani.”

Riƙe hannun ta Adda Halima tayi tana kallon ta idonta ya ɗan taru da hawaye, kasancewar ta mace mai rauni da saurin karayar zuciya “Ba iya yau kaɗai ba! Zanso hakan yaci gaba atare da mu muddum ranmu. Ina fatan wanan halayyar itace zahirin da zata ci gaba da shumfuɗuwa acikin kyakkyawar fuskar ki.”

Kallon ta Hafsa tayi ta ɗan turo bakin ta “Har yanzu kina da tan-tama da shakku akaina Adda halima. Sai dai so nake zuciyar ki ta baki tabbaci da gamsuwa akan wanan sabuwa ce, mai tafe da alkhairai masu yawa atare da ita.”

Sakin Hannun ta Adda Halima tayi tana murmushi “Ba’a iya sauyawa tuwo suna Hafsa, ba kuma a iya canja abin da ya zama jiki da ɗabi’a. Amma ana iya hasashen wata rana zai iya sabuntawa ko kuma ya sauƙaƙa wasu daga cikin su.”

Tana gama faɗar haka ta shige banɗakin ta bar Hafsa da mata rakiyar ido.
Hannunta ta haɗa ta danƙwasa yatsunta suka bada sautin ƙash-ƙash sanan ta gyaɗa kanta, cikin sautin da kunnen ta kaɗai yake isa tace “Kin faɗi gaskiya Adda Halima, bazan iya sauyawa ba, ni na sani. Amma zan iya rangwata miki kaɗan daga cikin wasu abubuwan da sukan zama ɗabi’a agare ni, masu ban haushi.”

Sanan ta koma ɗakin Adda Halima ta gyara mata shi tsaff.
Ta kuma shimfiɗa musu tabarma, ta jera musu ɗumamen tuwon data musu, gefe kuma jalof ɗin taliyar hausa ce wadda tayima yara ita suka tafi makaranta da ita aka samu ragowa, ta haɗo musu da ita. Gefe kuma kunun tsamiya ta dama musu, kasancewar Adda Halima bata rabuwa da garin kunun saboda ƙaunar ta da shi.

Dai-dai fitowar Adda Halima, ta kalli wajan tana jinjina wanan sabon salon na Hafsa, Allah ya sani Zuciyar ta bata samu nutsuwa da gamsuwa da sabbin ɗabi’un da take zuwar mata da su ba. Ita kam da zata mata Adalci to kawai ta fito mata a Hafsan data sani, ba wai tana mata Ƙumbiya-ƙumbiya ba.

Kayanta tasa sanan ta zauna suka fara cin abincin, bayan gaisuwar da suka sake yi.
Babu mai magana acikin su har suka kammala ci.

Anan wayar Adda Halima ta ɗauki ƙara da tsiwa, da sauri Hafsa ta ɗauko ta miƙa mata tana murmushi “Yaya Ado ke kiran ki.”

Karɓa tayi tana latsa wayar “Assalama alaikum kawun yara.”
Daga ɗaya ɓangaran ya amsa mata yana faɗaɗa fara’arsa.
“Mun tashi lafiya Halima? Ya yaran da kuma haƙurin rayuwa.”

Murmushi tayi mai sauti “Mun gode Allah Kawu. Ya Anty Lubabatu da yaran?”
“Lafiya lau.” ya faɗa yana taƙaita maganar.

“Umm Hafsa ko ta zo wajanki?”

“Eh gata jiya ta zo, na bata ku gaisa ne?”
Saurin dakatar da ita yayi “A’a bana buƙatar jin muryar ta ko kaɗan. Dan kema na kiraki na miki kashedi akanta, idan da hali ma ki koreta tasan inda dare ya mata.”

Cikin mamaki da furgicin jin maganar sa ta kalli Hafsa wadda ta tashi tabar musu wajan, tana matsar hawaye.
Kai ta fara girgizawa kamar yana gaban ta “Kasan abin da kake faɗa kuwa kawu? Hafsa ƙanwata kake cewa na kora agidana? Hafsa fa kawu? Ko dai kayi suɓutar baki ne.”

“Ko kaɗan Halima! Asalima na faɗa cikin sani da baki zaɓi akan abin da baki sani ba akan halayyar Hafsan, nasan bazata faɗa miki maƙasudin korar da Alhajinmu ya mata ba……” anan ya sanar da ita duk abin daya faru.

“Inna lillahi wa inna ilaihirraji’un.” kalmar da Adda Halima ta faɗa hawaye na zuba a idonta.

“Dan haka nake baki shawara ki tattara ki koreta, tun kafin kema ta zame miki masifa kamar yadda ta zamewa mahaifinmu.”

Cikin sautin kuka ta fara magana “A’a Kawu! Korar Hafsa ba shine mafita agare mu ba, har yanzu Hafsa jinin mu ce, duk abin da zatayi bazamu iya ƙyamatar ta mu koreta daga garemu ba. Na tabbata wata rana zata sauya. Haka kuma ni zan iya zama da ita, saboda nafi kowa sanin halayya da ɗabi’ar ta.”

“Um-Um Halima! Ke kina da haƙuri da yawa, Hafsa kuma rigimammiya ce. Bana so ta zama silar sake jefaki cikin wani ƙunci da damuwar.”

Murmushi tayi “Ba komi Kawu. In sha Allah zamu zauna da ita lafiya, a yanda na lura da ita kamar ta sauya yanzu saɓanin baya.”

“Kayya dai Halima! Ba sauyawa tayiba, tayi dai kwantan ɓauna ne.”

Dariya tayi tana girgiza kai kamar yana ganin ta “Kawu wani irin kwantan ɓauna kuma? Kai dai kawai ka yadda ta sauya.”

Shima dariyar yayi yana girgiza kai “Ina baki tabbacin Bata sauyaba Halima. Kawai dai tayi tuban baƙin muzuru ne, amma nan kaɗan zaki sheda hakan.” daga haka ya kashe wayar ya barta da bin ta da kallo.

Shuru Adda Halima tayi, taci gaba da kallon wayar tana jujjuyata  bayan ya tsinketa daga kiran.

ta ko ina gumi ne yake tsatssafowa ajikin ta. ‘Tabbas ta san wacece Hafsa, zata aikata fiye da abin da Kawu ya faɗa. Amma bata ɗauka lamarin nata yayi juyin uwar ba’u ya koma har kan Alhaji Malam ba, amatsayin sa na babban malami agarin wanda mutane suke bashi girmamawa, suke kambama tsagwaron alkhairin sa agare su. Ta gefe guda kuma ya zama silar wanzuwarta acikin wanan duniyar.’

“Ya ALLAH!” Ta faɗa tana shafo fuskarta da duka tafukan hannun ta.
sanan ta ɗauki tunanin ta ta cillashi can baya, a lokacin da mijin ta yake raye.

Birnin Kebbi, Jega L.G

10 April 2008

“An ɗaura Auren Hafsat Kamaludden Muhammad, da Angonta shugaban Hisbah na jahar Sokoto Sheikh Abdul-mannan Isyaku, akan sadaki Dubu Ashirin lakadan ba ajalanba.”

Wani maɗaukin lasifa ya faɗa yana nanatawa, yayin da mutane da yawa suke hamdala da kuma musayar hannu wajan yin musabaha a tsakaninsu.

Tabbas wanan shine ɗaurin auren da ya tara manyan malamai da kuma ‘yan hisbar dake jahar. Wasu ma ba daga jahar suke ba, amma saboda kasancewar jigon Hisbah agarin yasa suka masa kara suka zo.

Gefe guda kuma shi kansa Mahaifin Amaryar Kamaludden babban malami ne agarin, wanda yake sahun manyan da sukan faɗa aji.

Tabbas Ilimi baiwa ne, akwai kuma tausasawa da taimakon mutane atare da shi, ba kawai ilimin zaka kwasa agareshi ba, idan ka zauna da shi koda sau ɗaya ne, zaka ribata da tarin alkhairansa.

“Alhamdulillah!” Itace kalmar da yake ta nanatawa akan bakinsa.

Wanan shine babban burinsa a rayuwa, duka yaransa su auri malamai masana addini da kuma haƙƙoƙin zaman-takewa ta aure. Wa ɗanda suke da kyakkyawar mu’amula da mutane.

Sai gashi Allah ya cika masa fatansa da burinsa, duk da Hafsa rikitacciya ce acikin yaransa, amma yasan zaman aure zai iya gyara mata rayuwa, musamman da ya kasance mijinta yana da haƙuri masanin addini kuma.

Abinci akayi ta fitowa da shi daga cikin gidan ana ajiyema ‘yan ɗaurin auren.

Kafin wani lokacin wajan ya zama dan-dalin cin abinci, kowa fuskarsa ɗauke da maɗaukakiyar fara’a na samun gamsasshen abinci.

*****
Daga cikin gidan kuma mata ne, suke nasu budurin, da yawa Matan gidan suna murna akan Hafsat zata barsu susha iska, shi yasa komi da hanzarinsu suke yinsa.

“Hafsa! Ina so ki ɗauki wanan auren naki a matsayin ibada. So nake mutane susha mamakinki Hafsa. Kowa cewa yake fitinarki ba zata bari ki zaunaba, amma ni ina da kyakkyawar sheda akan ɗiyata.”

Ɗagowa Hafsa tayi tana kallon Mahaifiyar tasu, yanayinta bai yi kama dana mai damuwa ba, asalima ba zaka ban-bance abin dake damunta ba.

“Umma! Ban san taya zan zauna da mutumin da babu ƙaunarsa ko kaɗan a ƙasan zuciyata ba? Kin sani ba’a sani abun da banyi niyaba, Alhaji Malam yayi kuskure da yake ganin nima zai tilastani ne kamar yanda yakema su Addah Halima.

Allah ya sani babu auren ustazi acikin rayuwata ba, wanda kullum hidimarsa akan mutane ne da warware musu matsalarsu.”

Cikin sigar lallashi Umma take mata magana “Kiyi haƙuri, bawa baya wuce ƙaddararsa. Mahaifinki shike da hakkin zaɓar miki miji na farko, haka ya duba can-cantar wanda ya aurar miki. Samun kamar Abdul-mannan awanan duniyar ba abune mai sauƙiba.

Kamata yayi ki ɗaga hannu ki godema Allah a bisa ni’imar daya sauƙar gareki, ya baki mahaifi masanin Alqur’ani ƙarshe ya baki miji kwatan-kwacin mahaifinki.”

Cire hannun Ummanta tayi daga kan kafaɗunta, tayi murmushi tana cizan laɓɓanta “Wanan shine takaicinah ai Ummah. Samun miji mai irin ɗabi’un Alhaji malam, ni banga alkhairin da kike ta yaɗawa akansu ba.

Har yanzu ban manta dalilin rabuwarku da Alhajinmu ba Ummah. Idan har ya rabu dake saboda ɗan kuskure ƙarami ya kike ga Abdul-mannan zai aikata agareni.”

Hannu Umma ta ɗaga mata cikin ɓacin rai ta fara magana, dan Hafsan nata ba sauƙi akwai murɗaɗɗan hali da taurin kai, ga rashin mantuwa.

“Ƙaddarar zamanmu ce ta ƙare tun awancan lokacin, da kuma rabon su Al’ameen daya raba atsakani.

Hafsa babu wanda baya aikata kuskure a rayuwarsa, ɗan-Adam ajizine. Har gobe bana ganin laifin mahaifinki, tunda gashi har yanzu muna tare ba’a rabu ba, kuma ina alfahari da kasancewarsa mijina awancan lokacin.”

Miƙewa Hafsa tayi tana kaɗe zaninta “Haka kullum kike faɗa dan ki kareshi. Amma ni zuciyata taƙi yafe masa da yi mana katanga da mahaifiyarmu.

Zan gasawa mijin da yayi gigin aurena aya ahannunsa, har sai ya gaji ya rabu dani.

Babu miji atsarin rayuwata Ummah, babu ƙaunar hakan araina.”

Tana gama faɗar haka ta fice tabar mata ɗakin.
Dafe kai Ummah tayi hawaye na bin kuncinta “Ya Allah!”

Ta faɗa akan laɓɓanta.

Wanan kuskurensu ne da suka aikata ita da Alhaji Malam. Ita tayi kuskure a matsayinta na mace mai rauni.

Shi kuma a matsayinsa na namiji masani ya kasa danne ɓacin ransa, har ya aikata abin da Hafsa take ganin laifinsa ne.

Take kuma ganin baikinsa akan hakan.

<< Jini Ya Tsaga 2Jini Ya Tsaga 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×