“Yanzu shi Kamalun ne ya kore ki a gidan sa tsawon watanni? Kuma har ya sa Halima ta koreki a gidanta itama.” Gwaggo Faɗim ta faɗa cike da faɗa da tashin hankali. Jikinta har rawa yake saboda ɓacin rai, idan akwai abin da gwaggo Faɗim ta tsana a rayuwa bai wuce iyaye masu wofintar da yaransu ba.
“Eh gwaggo.” Hafsa ta yi maganar tana matse hawayen ƙarya, ita dama tasan Gwaggo Faɗim ba zata juri ganin ta yi garari ba, kamar yadda ba zata taɓa bari ta fita daga gidan su ba.
Zata iya cewa a duk duniya bata taɓa ganin mace rigimammiya mai son yara kamarta ba, kamar yadda take da tabbacin babu na biyunta a wajen take gaskiya muddum yaro zai samu sakewa.
“To amma me yasa tun lokacin baki faɗa zo kin faɗa min ba, sai yanzu da abu ya ƙara turawa?” Ta jefa mata maganar cike da faɗa da hayaniya kamar zata banketa.
“Ina so ne ya huce kafin lokacin. Ina tsoron kar na zo zafin ya tafasa da yawa.”
Hannu ta kai ta make bakin Hafsa “Ƙaniyarki da tafasar zafin. Da kin san da zafin zai tafasa kika tada masa husuma a unguwa. Ina ruwanki da matansa da abin da yake musu, da zaki ce baya adalci a cikinsu har ki ce zaki ɗauko masa ƴan sanda.
Anya Hafsa rigimarki baya zarta taaa ba kuwa? Gwaggo Faɗim ta faɗa ciki da jin takaici.
Baki Hafsa ta turo tana yamutsa fuskarta da ƙifta idanuwanta “To Gwaggo ai gani nayi hakkinsu zai iya bin mu, mu yaransa. Idan ya zama baya adalci ga matansa ai muma namu mazan za su iya mana hakan. Duk da cewa ni dai nasan ba zan bari namiji ya tauye ni ba, amma su Khadijatu ai su ne abin tausayi.”
Kai Gwaggo Faɗim ta jinjina da alamu dai ta gamsu da bayanin Hafsa. Musamman tun farko da bata ɓoye mata komai ba, bata kuma yi mata ƙarya ba, wadda ta daɗe da sanin halayyar Hafsa. Koda za a kasheta a kan gaskiyarta ne to zata faɗe ta.
“To yanzu dai dare ya riga ya yi, ki bari gobe in sha Allah mu buga sammako mu samu Kamalun a gida. Babu dalilin da zai sa kina kare-kare a gidan wasu, bayan ga gidan mahaifinki da yake raye.”
“Allah ya kaimu gwaggo. Na gode sosai.”
Ta yi maganar tana jan kwanon gurasar da ta tadda Gwaggo Faɗim ta yi.
*****
Tun bayan tafiyar Hafsa hankalinta ya gaza kwanciya, ta kirata yafi sau a ƙirga amma wayarta bata tafiya, har zuwa yamma.
Hakan yasa ta yi shahada ta kira Umman su duk da cewa ba tambayarta ta yi kai tsaye ba.
“Umma ina jin hayaniya ko baƙi kika yi ne?”
“A’a wanne baƙi a wannan lokacin? Hayaniyar yaran gidan ce da iyayen su.”
“Ayya.” Ta faɗa tana jin ba daɗi a ƙasan ranta.
“Ina fatan lafiya dai kuke zaune ke da Hafsa?” Ta doka mata tambayar da ta haddasa mata bugawar ƙirji.
“Halima kina jina kuwa?” Umma ta faɗa da ƙarfi ko tunaninta maganar ta yanke ne, sai dai rashin sanin amsar da zata bata yasa ta yanke wayar.
Lambar Alhaji Malam ta lalimo ta shiga doka masa kira tana fatan Allah yasa Hafsa can ta je, sai da kiran ya kusa yankewa sannan aka ɗauka.
“Assalama alaikum wa rahmatullah.” Muryarsa mai cike da dattijantaka da kamala ya ratsa kunnuwan Adda Haliman.
“Wa alaikumussalam wa rahmatullah wa bara katuhu.” Ta amsa masa muryarta cike da rawa da fatan jin abin da ta kira dan shi.
“Halimatu ina fatan dai lafiya kuke? Ba wata rigimar bace ta haɗaku ke da Hafsatu?” Daga yadda ya yi mata maganar ta fahimci Hafsa bata je gida ba kenan.
“Lafiya lau muke Alhaji malam. Na kira na gaidaka ne dama.”
“Masha Allah. Na gode sosai, a gaida iyalin. Ki kuma ƙara kula da Hafsatu, Idan yanayinta ya zo da matsala ki hanzarta kirana ko Ado domin warware matsalar nan take.”
“In sha Allah.” Ta faɗa cikin sanyin murya bata kashe wayar ba, kamar yadda shima bai katse ba, yana iya jiyo sautin numfashinta.
“Halimatu ko akwai matsala ne?” Ya jefa mata tambayar.
Kukan data danne ya fito da ƙarfi, a yanzu ta riga data san bata da wani zaɓi wadda ya wuce ta faɗawa Alhaji Malam Halin da ake ciki, wataƙila ta wajensu suna da abin da za su iya yi dan taimakawa Hafsa ta dawo.
Labarin abin da ya faru tun farkon rigimarsu har zuwa mayar da Bunayya ga dangin mahaifinta da abin da ya faru a ranar. Bata ɓoye masa komai sai da ta faɗa masa.
“Ba ni da yadda zan yi ne Alhaji Malam. Ban san su Mu’awuyya sun ɗauko ƴan sanda dan su fitar da Hafsa ba. Wallahi ban aika su, duk wuya Hafsa ƴar uwata ce ba zan iya korarta a gidana ba.
Ƴan sandar basu bani damar dakatar da su ba suka sata a gaba suka fice. Na kira Umma tace min bata je Boɗinga ba, gashi nan jega ma bata zo ba.” Ta gama maganar tana fashewa da kuka.
Shuru Alhaji malam ya yi, yana tattara kalaman nata yana neman wajen da zai ajiye maganar tata.
“Hafsatu ba yarinya ba ce Halimatu. Duk inda take zata kula da kanta, na kuma ji daɗin abin da su Mu’awuyya suka yi. Ki daina wahalar da kanki a kanta, duk inda zata je zata dawo gida.”
“Amma kuma a ina xata tsaya?”
“Idan lokaci ya yi, zata bayyana garemu ta sanar da mu.” Ya bata amsar.
Yana ƙara dannarta da lallashinta, har suka yanke wayar.
Da kallo yabi wayar yana mamakin soyayyar da Halima ke yiwa Hafsa, wadda yana da tabbaci ko su iyayenta sai dai su ce sun haifeta ne amma ba wai su nuna mata so ba.
“Allah kai ka bamu Hafsa a matsayin ƴa, ka kuma sanya mana soyayyarta fiye da sauran yaran mu. Ka jarrabe mu da sakayyayen halayyarta. Ya Allah ka bamu ikon jurewa da amsar ƙaddarar da ka aiko kanmu.” Ya yi maganar yana share guntun hawayen da ya jiƙa idonsa.
Ya san yana da yara da yawa, wadda idan da za a lissafa zasu tada ɗan ƙaramin gari, dukansu nutsattsu ne da suke da kyakkyawar tarbiyya mai kyau, da tausayinsu.
Amma kuma Hafsa sai ta zama zakka a cikinsu, ta samu fiye da abin da suka samu, ta kuma zama wani babban ƙalubale ga rayuwarsu. Ƙalubalen da bai san yaushe ne zai rabu da su ba, amma koyaushe cikin mata addu’a yake da fatan zata zama kamar sauran yara.
*****
Bayan gama wayar tasu ta daɗe tana bin wayar da kallo tana jingina kanta a jikin bangon ɗakin, hawayen da take dannewa suna sauƙowa a idanuwanta. Gidan ya mata tayau babu motsin komai, babu sautin komai. Ji take kamar ita kaɗai ke rayuwa a gidan, ashe kwarmatun Hafsa da surutun ta kaɗai su ke cika gidan.
“Umma! Umma!” Sautin muryar Jiddah ya ratsa kunnenta, wadda hakan yasa ta saurin share hawayenta tana daidaita muryarta.
“Mene ne Jiddah wannan kira haka?” Ta yi maganar da ɗan ƙarfi duk da muryarta akwai rauni.
Da gudu Jiddah ta shigo ɗakin tana miƙawa Adda Halima ɗaurarren ɗankwalinta “Ware kiga Umma?” Da sauri ta karɓi ɗankwalin da mamaki kuɗe suka zubo a cikinsa, damin kuɗi ne guda biyu ƴan 1k daga bisani kuma wata farar takarda ta biyo baya.
“Wannan kuɗin na mene ne Jiddah? A ina kika same su?” Ta jefa mata tambayar.
“Ina shara a ɗakin Anty Hafsa na zo share bayan ƙofa na ga ɗankwalinki, shine ina ɗauka naji nauyi, dana buɗe naga kuɗin dayawa. Amma kuma ga takarda nan ta faɗo.” Jiddah ta gama maganar tana warware takardar.
“Nasan za su ishe ki, ki kama wata sana’ar. Ki ne mi kuɗi da guminki, ki daina zuwa wajen wasu roƙo.”
Hafsat Kamaludden Muhammad
Jiddah ta gama karanta takardar tana kallon Ummanta da ta miƙe tsaye tana riƙe da kuɗin tana juyawa “Hafsa dai?” Ta ƙara yin maganar, kafin wani hawayen ya sauƙe a kan idanuwanta.
Hafsan da take kallo a matsayin rigima da kuma fitina a gareta, ta tafi daga gareta, amma bata tafi ta barta haka ba, ta barta da ƙaton miki da tabo a zuciya.
“Me yasa duk da abin da ya faru, amma take son ki yi sana’a Umma? Me yasa ta bar miki waɗan nan kuɗin masu yawa haka?” Jiddah ta yi maganar tana ƙara juya kuɗin.
Bata da wannan amsar a yanzu domin bata san me zata faɗawa Jiddah ba.
“Duk da tana da fitina tana da abu mai kyau a tare da ita Ummah. Ban taɓa jin ta roƙi wani ya bata wani abu, ko a tarihinta na yarinta tana da zafin nema.
Dan Allah Umma ki gwada yin sana’ar kema, ki ƙyale mutane da yawan zuwa neman taimako a kanmu, ina ji a raina wannan kuɗin za su ishemu yin wata sana’ar mu dogara da kanmu. Tun da gasu yaya nan suma suna kasuwancin su.”
Kallon Jiddah ta yi na ɗan lokaci a ƙasan ranta take tambayar kanta _’Yaranta ma da take nema saboda su, hakan baya gamsar da su, basa son zuwanta neman taimako ashe? Hakan na nufin Hafsa ta ankarar da ita daga makantar zucin da take shirin faɗawa.’
*****
Washe gari Gwoggwa Faɗim ta tisa ƙeyar Hafsa suka tafi jega.
Kamar yadda ta tsara sallah azahar ma a can suka yita.
Bayan doguwar gaisuwa da suka ja ta kalli Alhaji Malam da tsukekkiyar fuskarta, kamar yadda shima yake ƙoƙarin haɗe ran nasa, dan yaga shigowar su tare da Hafsa.
“Matan ka sun kawo min abinci Kamalu, amma ban ci ba saboda ba shi nake buƙata ba a yanzu. Maganar data kawo ni ta girmi cin wani abinci.”
Kai Alhaji Malam ya jinjina yana so taje gundarin maganarta kai tsaye.
“Yanzu Kamalu ashe har zaka iya zartar da hukunci mai girma a gidanka ba tare da sanina ba?”
Ɗago da kai ya yi yana kallonta da son ƙarin bayani “Na ɗauka ko Hafsa ta ɗauko ma Police ba zaka koreta a gidanka ba, saboda zamanka malami. Yo Allah na tuba Hafsatun nawa yake da har zaka ce ta bar maka gidanka, banda ma yarinyar na da tsarkakyakkiyar zuciya ai da tuni ta shiga bariki. Amma saboda dafa’in ayoyi da malintar da ke kanta bata yi sha’awar hakan ba ta, tafi gidan ƴar uwarta. Can ɗinma baka barta ta samu salamammiyar kwanciyar hankali ba sai da ka sa ƴar uwarta ta koreta.
Haba Kamalu yaushe ka zama haka ne nikam? Babban malami masani Alƙur’ani da hadisai. Hafsa fa jininka ce da ta tsago daga jikinka. Yo Allah na tuba ko mutum ta kashe ai ka binne ka rayata.”
Yanzu kam bakinsa a buɗe yake yana kallonta da tsananin mamaki, duk da ba wai mamaki bane ya san wacece Faɗim, zata iya faɗan fiye da haka ma.
*****
Barka mutanen Hafsatu. Ina fatan xuciyarku ta risina a yanzu kam.
Hmmmm hafsy er London
G