“Ba baki zaka buɗe kana kallona ba Kamalu. Maganar nan ta wuce haka nan, domin naka sai na ka.”
Kai ya jinjina cikin ƙosawa da maganar ta ya yi gyaran murya “Shikenan, Yaya Faɗim. Hafsatu zata zauna a gidana, amma ta tabbatar ta fiddo da mijin aure, dan ba zai iyu ta raba min aure da matana ba. Ko kuma ta raba min kan su da yake haɗe. Lokacin da ta ɗauka bata nan komai lafiya lau, amma na tabbata a gobe komai zai iya sauyawa.”
Hannu Gwaggo Faɗin ta shiga tafawa tana rafka salati “La ilaha illalahu, Muhammadur rasulillahi! Yanzu Kamalu a gabana kake fifita matanka a kan Hafsatu? Matan da koyaushe kaga dama zaka iya sauya su, Amma Hafsatu jininka kake cewa ta yi ta bar ma gidan naka.”
Kansa ya dafe cike da gajiyawa “Ba ina fifita su ba ne a kanta Yaya Faɗim. Ki fahimta kin san wacece Hafsan ai.”
“Ba shakka kam na santa. To dan miji mai sauƙi ne ai a wajenta, yarinyar da har gobe luɗifin farin jininta ke nan, kamar ta sha hatimin Annabi Yusufa. Da miji kam bana jin Hafsatu da shi zata fitar dan ta bani labarin wani ma da yake kiranta a can ko Nasiru kamar dai haka tace min sunansa.”
“Koma waye dai ta gabatar da shi a gabanmu. Yauwa Yaya nikam ina labarin Salisu, ya daɗe bai zo ba, kuma na kira wayarsa bana samunsa.” Ya yi maganar dan ya kawar da hirar Hafsa da kuma mitar Gwaggo Faɗim ɗin.
Ai kuwa ya yi nasara domin tuni ta washe bakinta ta fara dariya kasancewar Salisun shine auta a yaranta “Salisu masu ƙasa, ai yana amsar bugun garin ne, wai fa Niger ya tsallaka neman kuɗi, yace a can ba a rasa aikin yi.”
Da mamaki Alhaji malam ya kalleta “Niger kuma Yaya? Kuma kika bar shi.”
“Iyyi. Yo gani na yi ya matsa da hakan, ni kuwa na ƙyale shi ba bishi da addu’a. Bamu san ina arziƙin nasa yake ba. Allah na tuba ma ai Niger kamar gida ne babu tazara mai yawa.”
Kai ya jinja “To Allah ya taimaka ya bada sa’a.”
“Amin dai. Ai Salisu kam akwai ƙulafuncin neman kuɗi.”
“Allah ya basu masu albarka.” Daga haka dai hirar tasu ta sauya akala wasu duk a kan rayuwar salisu ne da gwagwarmayar da ya sha yi. Wato Gwaggo Faɗim Allah ya yassare mata azababben surutu da idan tana yi kamar an sa mata batiri ne.
Washegari
Gwaggo Faɗim ta yi sallama da matan Alhaji Malam da shi kansa, bayan ta ja doguwar togaciya da sunan nasiha, tana ƙara jaddada musu muhimmancin da Hafsa ke da shi a gidan.
Duk da cewa kafin ta tafi sai da aka gabatar mata da Yaya Ado shima ta ja kunnensa akan babu shi banu Hafsatu, tana kuma ɗorawa da cewar ita matafiya ce ba wai zama ne ya kawota gidan na har abada ba.
Wadda kuma a gabansu ta kira Nasir Nasar tana sheda masa ya turo manyansa gaban iyayenta Jega.
Ya amsa da to za su zo washegari. Wadda hakan ya bawa Alhaji Malam mamaki da buɗaɗɗen baki yake kallon yaya Ado ɗin, da shi kuma ya taɓe baki.
“Allah yasa ba hayo iyayen zai yi ba. Daga cewa ya turo su har zai yanke hukuncin ranar zuwan nasu.” Yaya Ado ya faɗa.
Wadda Gwaggo Faɗim ta maka masa harara “Ba hayo su zai yi ba, sato su zai yi? Kaga Ado ka fita a idona na rufe, wannan abin da kake ha halayyar maxa ba ce.”
“To ai gaskiya na faɗa Gwaggo kina jin yadda yake magana da gadara fa.”
“Oh Ana ga yaƙi kana ƙura. To ina ruwanka da gadararsa, nifa bana son neman sila.”
Shiru ya mata bai bata amsa ba, dan idan ya ci gaba da magana to akwai yiyuwar tace tana faɗa yana mayar mata dan ba babansa ke maganar ba.
Sai da kuwa ta ja maganar ta kuma yi faɗan da yasa ba wadda ya iya tanka mata sai Alhaji Malam da ya bata haƙuri ya zaro dubu ashirin a aljihunsa ya bata da sunan ta yi kuɗin mota. Haka matansa suka shiga lalimen yi mata goma ta arziƙi.
Ado ne ya ɗauketa ya kaita tasha sai da ya biya mata kuɗin motar da zata kaita har Tambuwal, kana yaga tashinsu sannan ya tafi gida.
**
Washe gari kamar yadda Nasir Nasar Zayyar ya shedawa Hafsa zuwansu, sai gashi sun zo shi da Abokanan mahaifinsa biyu da kuma ƙannensa guda biyu.
Hannu bibiyu Alhaji Malam ya karɓe su, sun gaisa cike da mutunta junansu, wadda suka gabatar masa da kansu da kuma matsayinsu ga Nasir Nasar.
Kai Alhaji Malam ya gyaɗa yana kallon Nasir ɗin da nazarin shekarunsa, mamakinsa ya gaza ɓoyewa har sai da ya musu magana “Ko kun san Hafsa Bazawarace mai yara biyar?”
“Da sanin hakan muka zo neman iri muma.” Ɗaya daga cikinsu ya yi maganar yana washe bakinsa.
Hakan yasa Alhaji Malam gyaɗa kai kamar riƙeƙƙen gwada “To madallah. Tun da sun aminta da kansu ba mu da ja a kan hakan.” Alhaji malam ya faɗa.
Anan kuma ƙanin mahaifin Nasir Baba Hayatu ya yi magana “Mun taho da sadakinmu a hannu, idan babu damuwa bama so a ɗauki lokaci wajen yin aure. Kasancewar dukanninsu ba yara ba ne.”
“Mako mai zuwa ku zo sai a ɗaura auren da yardar Allah.” Alhaji malam ya basu amsa. Wadda hakan ya musu daɗi, duk da suna tunanin zai kai har wata ɗaya amma sai gashi ya basu mako guda kacal.
Godiya suka masa, bayan sun cika cikinsu da abinci sannan suka tafi suna yabon halayyar Alhaji Malam da kuma malintar sa data taka rawa wajen fito da kimarsa.
Lokacin da Alhaji Malam ya kira Hafsa ya damƙa mata sadakinta dubu ɗari cif bata yi mamaki ba jin yace mako guda ya basu su dawo a ɗaura aure. Ta daɗe da sanin ƴan gidansu sun gaji da zama da ita, sai dai abin da basu sani ba zama da itan shine yafi alkhairi akan abin da zata je ta yi ta dawo gare su.
Bata sani ba ko da gaske tana son Nasir Nasar, bata sani ba ko ƙaddarar zaman su zata miƙe kamar sauran mazajen aurenta, sai dai abu ɗaya da ta sani ta riƙe a kanta, shine gurɓatacciyar shedar da mutane suka fiya badawa a kan Nasir ɗin, da kuma yadda ya ɗauki mace tamkar rigar sawarsa, ya sa yau ya cire an jima.
Tana jin daga kanta zai san cewa mata suna suka tara, zata nuna masa tazara mai yawa tsakanin macen zamani da kuma wadda aka gadar da ta da ɗabi’ar al’ada da kuma daƙusar da ita.
Tabbas zata yi zaman aure a gidan Nasir za kuma ta sauya akalar rayuwar Zahra Zakar Dabo. Zata ɗaga darajarta ta hanyar farfaɗo mata da matacciyar zuciyar da ke manne a ƙirjinta.
Ta shirya tsaf kamar yadda take da tabbacin shima Nasir ɗin ya shirya.
Lokaci kuma ya tabbatar musu da cewa shima a ƙagauce ya ke, a ya yin da ranar ta zagayo Dubbanin mutane suka sake sheda ɗaurin auren Hafsat Kamaludden Muhammad da angonta Nasir Nasar Zayyar.
Wadda ƴan ɗaurin aure basu juya ba sai da Amaryarsu Hafsat da idanuwanta suke buɗe fess babu alamun kuka. To wanne kuka zata yi na rabuwa da gidan da zata dawo ko kuwa na sabo da ƴan gidan da suke kallonta a matsayin babbar maƙiyar da ke hana su rawar gaban Hantsi?
*****
Yanzu zamu ɗora zaren labari mai kyau! Kuna tunanin Hafsa zata iya juya Nasir Nasar kuwa? Wacece Zahra Zakar Dabo da Hafsa ke son sauya mata rayuwa? Shin ma tsakanin Hafsa da Nasir wa zai iya sauya rayuwar wani?
Ina tunanin labarin ya ƙare anan zamu ɗora wani lokacin idan da rayuwa. Na gode da jimirin bibiyar rubutuna, sai mun haɗu a Book 2 in sha Allah.
Oum-Nass