Ajiyar zuciya Hafsa ta sauƙe a lokacin da suka harba motarsu kan titi, tana jin gina da bayan kujerar motar. Tana kuma kintata adadin rashin kara na danginta, wadda a bayyane yake suna murna ne da tafiyarta.
Domin tana iya ganin shimfiɗaɗɗen murmushi a kan fuskar matan gidansu, kamar yadda take hango Asma’u amarya da take taka rawa tana juyawa.
Ita kanta Hafsa ta sani ta fitini rayuwar Amaryar Mahaifin nasu, wadda a zaman mako ɗayan da ta yi sai da ta hanata watayawa, da kuma kafa mata karan zuƙa akan yin girki da nama a ranar girkinta.
Wadda kuma bata da zaɓin da ya wucewa gujewa hakan, kamar dai yadda take ga tana fifita sauranar matan mahaifin nata.
Murmushi ta yi mai sauti wadda ya haddasa lotsawar kumatunta idanuwanta suka zurma ciki, kafin ta dawo hayyacinta ta ji sauƙar hannu Nasir Nasar a cikin nata.
“Wannan murmushin duk na mene ne Amaryata? Ko duk nawa ne?” Ya yi maganar yana kashe idanuwansa ɗaya da kuma kwantar da kansa zuwa kafaɗarta.
Ƙarya ba ɗabi’arta bace shi yasa bata jin ko a yanzu zata iya yi masa ita “Ina tuna yadda ƴan gidanmu ke murna da tafiyata ne.” Ta bashi amsar tana dariya.
Shima dariyar ya yi “Oh Hafsan Rigima, dama ɗaga hannun da suke miki bana alhini ba ne ashe?”
Kai ta jinjina tana ƙara kwantar da kanta a jikinsa.
“Da na Alhini ne ai da an samu ƴan rakiya. Kasan me ake kira da ‘Allah raka taki gona.’ To irin wannan suka min.” Ta ƙara maganar tana dariya da shaga gajeran hancinta da bai miƙe ziyat ba.
“Kina da kyau sosai. Amma mutane sun gaza gane kyan naki? Kamar yadda nasan zuciyarki na da kyau sosai.”
“Na daɗe da sanin hakan Nasir. Shi yasa bana damuwa wani ya taya ni sanin abin da ya shafi rayuwata.”
Kallonta ya yi na ɗan lokaci kafin ya furzar da iska a bakinsa “Amma kuma ai ba lalai ya zama kin kai yadda kike tunani ba ne. Mugun halin da kike da shi yafi tasiri fiye da na kirkin ki.” Ya yi maganar da murmushi da ƙoƙarin bata haushi kamar yadda ta gwale shi a lokacin da ya ke yabonta.
Duk da cewa ba wai wannan ne karo na farko da ta taɓa gwale shi ba idan ya yabeta ɗin, amma kuma ga mamakinsa sai yaga ta yi murmushi ta ɗora hannunta a kan kyakkyawar fatar bakinsa, ba tare da kunya da kuma tunanin direban da ke tuƙo su ba.
“Na sani Nasir. Amma duk da haka idan aka haɗa halayyata da taka abu ne da suke da tazara mai yawa. Ko ba komai ni za a iya samun mutane biyu da zasu yabe ni. Saɓanin kai da ban taɓa jin koda mutum ɗaya ya faɗi kalmar alkhairinka ba.”
Murmushi ta yi tana zagaya hannunta a kan kyakkyawan sajen da ke fuskarsa tana kashe masa ido guda ɗaya “Amma ni ban damu da hakan ba. A hakan na ke son ka da kuma ganin kyan ka.”
Ta gama maganar tana hura masa iska a bakinsa wadda ta haddasa masa haɗiye maganar da ya yi niya.
Wato a rayuwa yaga matan aure kala-kala wayayyun da suka amsa sunansu na mata. Ya kuma mu’amalance su da kyakkyawar mu’amula daidai da ɗabi’arsa a ƙarshe ya watsar da su kamar gasasshiyar masarar da ta bushe aka gasata.
Sai dai duk da hakan bai ga koda mai rabin rabin halayyar Hafsa ba. Zuciyarta a dake take, kamar yadda idanuwanta suke a bushe da rashin tsoro ko shakka na abin da zata faɗawa mutum. Asalima duk abin da ya zo gareta tana faɗarsa ne kanta tsaye ba tare da ta auna shi a cikin ma’auni mai kyau ba.
“Ina fatan kin shirya zama da Nasir Nasar?” Ya jefa mata tambayar cike da shu’umancinsa.
Sai dai itama da ta amsa sunan uwar sheɗan ta bashi amsar da ta dace da shi ɗin “Fiye da yadda xa a kira shiri da shiryawa.”
Hannunta ya matse a cikin nata da ɗan ƙarfi yana kuma shimfiɗa kyakkyawan murmushi a kan fuskarsa.
Daga bisani ya jingina a jikin kujera yana lumshe idanuwansa, badan ya yi bacci ba, sai dan ya nawa ƙwalƙwalwarsa damar nazartar kalaman Hafsa Kamaludden Muhammad.
Har kuma zuwa lokacin da aka shigar da ita katafaren gidan Nasir Nasar ɗin da ke garin sokoto bata ji ya sake yin magana ba.
Sai da direban ya kashe motar ya fita ya basu waje, hakan ya bawa Hafsa damar ɗora laɓɓanta a kan nasa kamar zata sumbace shi, sai kuma ta hura masa iska a kansu.
Wadda yasa shi buɗe idanuwansa ya ɗorasu a kanta da take daf dashi, har numfashinsu na haɗuwa.
Fuskarta ta ɗan yamutsa ta fara magana “Na so na tasheka da sumbata ne, sai na tuna ashe ban fara da tauna kazar amarcina ba.”
Idanuwansa ya lumshe ya sake buɗe su a kanta, kafin kuma ta matsa ya kusantar da bakinsa zuwa nata, sai da ya tsotse ta son ransa sannan ya saketa ta fara meda numfashi.
“Abin har da ƙwace da kuma nuna ƙarfi?” Ta yi maganar tana harararsa.
“Na riga na biya sadaki an kuma ɗaura. Gaki a harabar gidana, a cikin mota ta. Amma kina min maganar wata kaza?” Ya yi maganar yana yamutsa fuskarsa.
Ƙananun idanuwanta ta nitsar da su ciki, tana kai kallonsa gare shi. “Sadaki daban, kazar amarya daban Nasir. Dan haka a kawo min manyan kaji na kafin a haura ƙasusuwana.”
Ta gama maganar tana kanne idanuwanta, da kuma lasar laɓɓanta, wadda hakan ya haddasa masa wata fitina da bai san yana da ita ba.
Kai anya mata irin Hafsa nada yawa a duniya. Duk da yasan bazawara ce amma ai ya auri zawarawa da yawa kuma sun nuna kunyar su da kawaici a kansu a ranarsu ta farko.
Amma wannan so take ta feƙar da shi.
“Ina ne sashi na?” Maganarsa ta dawo da shi daga dogon tunanin da ya lula, da ido ya mata nuni da ɓangaren nata, wadda hakan yasa ta ɓalle murfin ƙofar ta fita.
Wadda fitar tata ta yi daidai da ƙarasowar Gwaggwo Faɗim.
“Oh gwaggwo dama kin taho ashe?”
“Yo ba dole ba, ina aka taɓa kawo amarya zilligididi babu wani nata, ai sai da na yiwa Kamalu fata-fata da matansa, shine ya haɗo ni da Lubabatu da Abu mu zo mu ga gida mu kuma raka ki.”
“Ayya Gwaggo ai da baki wahalarsu ba, duk da haka dai na gode sosai.” Ta yi maganar tana rungume Gwaggo da kuma kama hannun Anty Lubabatu.
“Matar Yaya barka da zuwa.” Ta yi maganar tana rungume Anty Lubabatun da take murmushi.
“Bayan tare muka zo wani barka kuma za ki mana.” Mu je dai mu take miki baya dan Gwaggo tace amarya ko ta buzuzu ce tana da ayarinta.”
Daga haka ta riƙe hannunta duk da saida ta ƙarasa kusa da Baba Abu matar Alhaji Malam.
“Barka matar malam. Masu cin miya ba nama.”
Kai Abu ta girgiza tana dariya, dan zuwa yanzu abin Hafsa ya daina basu mamaki da takaici, wani lokacin tana faɗar gaskiya ne da idan ba a yi dace ba sai a ɗauka ƙarya ne take faɗa.
Amma a wanan lokacin da kowa ke cewa Hafsa ta auri miji daidai ita tana fatan Allah ya saɓa halayyarsu na zaman tare ya kuma kaɗe fitintinu na zaman taren.
Sai da suka shiga sashenta suka zazzagaya ko ina ya yi sai sam barka, gida ne babban gida na masu kuɗin da suka amsa sunan masu kuɗi. Komai na more rayuwa akwai shi a gidan.
Zamansu ba jimawa ma’aikata suka fara shigo musu da abinci da abin sha suna basu tabbacin daga Uwargidan Nasir ne.
Godiya suka mata su gwaggwo na yaba halinta da kuma sa mata albarka. Har zuwa lokacin da suka gama cin abinci lubabatu ta gyara wajen tsaf.
A lokacin ne kuma Uwargidan ta shigo ita da ƙawayenta guda biyu.
A nitse take tafiya da wani rantsattsen lace ɗin da ya amsa sunansa, ko ina a jikinta a haɗe yake da kayan ado na ƙawa daga kan sarƙa abin hannu ɗankunnaye. Ga kuma wani ni’imataccen ƙamshi da ke tashi a jikinta.
Baƙa ce wadda baƙinta mai kyau ne mai sheƙi, tana da idanuwa matsakaita masu ruwan madara da ɗigon baƙi, sai dogon hancinta da ya taimaka ya ƙawata mulmulalliyar fuskarta da take ɗauke da ƙaramin baki.
Gashin idonta basu da yawa kamar yadda na girarata ma basu da yawa. Sai dai murmushin da take shimfiɗawa a fuskarta ya ƙara ƙawata fuskarta da mata kyau, musamman da jerarun fararen haƙoranta suka bayyana.
Muryarta na da sanyi ƙwarai kamar yadda itama take da sanyi a komai na rayuwarta, wannan ya bawa Nasir damar aza kowata shara a kanta.
Su kansu su Gwaggwo sun yaba da hankalinta suna kuma fatan zaman su zai ɗore da Hafsa.
Har zuwa lokacin da ta tashi da zummar tafiya su gwaggo na jero mata godiya da kuma albarka suna ta ƙara dannarsu a kan hakkin zaman tare.
Daga nan suma suka tattara suka tafi dan sun ce ba za su kwana a nan ba gara su je gidan Adda Halima su kwana.
jin sunan Adda Haliman yasa Hafsa murmushi ko ya take yanzu? Ga su dai a gari ɗaya ko xa su sake haɗuwa?
To gamu dai mun dawo, ina fatan tafiyar ta miƙe ta ɗore, amma hakan ba zai faru ba har sai da tallafawarku.
Ta hanyar yin comments
Oum-Nass