Ta daɗe da sanin Nasir Nasar mugu ne, kamar yadda ta ajiye shi a wani bigire mai zurfi da sarƙaƙiya. Bayan jure wahala da tazgado daga gare shi bata ɗauka zata samu iskar numfasawa mai kyau da kuma lafiya a tare da ita ba.
Lallai maza suna suka tara, ta kuma ƙara yarda da illar da maza kan yiwa mata da ƙumajinsu.
Amma tana fatan daga kanta zaluncin Nasir zai dakata, daga kanta zata wanzar da sauyi da 'yanci ga matan da ya zalunta a lokutan baya.
Sake lumewa ta yi a cikin ruwan zafin, tana. . .
Kutssssw gaba da gabanta kenan😳😳😂😂