Skip to content
Part 36 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Ta daɗe da sanin Nasir Nasar mugu ne, kamar yadda ta ajiye shi a wani bigire mai zurfi da sarƙaƙiya.  Bayan jure wahala da tazgado daga gare shi bata ɗauka zata samu iskar numfasawa mai kyau da kuma lafiya a tare da ita ba.

Lallai maza suna suka tara, ta kuma ƙara yarda da illar da maza kan yiwa mata da ƙumajinsu.

Amma tana fatan daga kanta zaluncin Nasir zai dakata, daga kanta zata wanzar da sauyi da ‘yanci ga matan da ya zalunta a lokutan baya.

Sake lumewa ta yi a cikin ruwan zafin, tana ƙara rintse idanuwanta, saboda zafin da ke ratsa sassan jikinta, ta tabbata ko a darenta na farko a gidan Sayyadi bata wahala haka ba, bata raunata ba.

Tunaninta ya kulle da rashin samun madafar da zata dafa, ta rasa hanyar da zata bi domin hora Nasir.

Tana iya hango idanuwansa da kallon da yake mata a lokacin da ya samu gamsuwa, ya ƙara kwaɓe fuskarsa da tsallaketa ya fice ya bar ɗakin, bayan ya ajiye mata mummunan kalmarsa da zata iya kiran ta godiyar da ya mata.

“Babu laifi dai, kina da ɗanɗano mai gamsarwa, sai dai hakan ba zai sa  ki juya Nasir Nasar Zayyar ba. Ki kula da lafiyarki, kafin ki riski kanki a gadon asibiti.”

Idanuwanta ta buɗe tana murza gashin girarta, tana murmushi ita kaɗai a cikin kwamin ruwan wankan.

Sai da ta sauya ruwa sau huɗu, mai zafi yana hucewa a jikinta, sannan ta ɗauro alwala jin ana gabatar da sallahr La’asar.

Abin da aka fara yinsa tin sha ɗaya na safe ita ba injin sassaƙa ba amma gashi har an kai la’asar.

Tabbas ba zata juri wasa da ibada ba, dan ta lura sheɗancin Nasir baya barinsa ya mayar da hankali a kan addininsa, kamar yadda ta kula bai san mene ne addinin ba.

A gurguje ta fito ta shafa mai ta zura doguwar rigar material a jikinta, sanan ta shimfiɗa abin sallah. Sai da ta yi Azahar sanan ta yi la’asar. Ta daɗe zaune a kan abin sallar tana jero istigfari domin duk iye shegenta tana tsoron haɗa sallah.

A lokacin ne a ka turo ƙofar ɗakin aka shigo, ƙamshin turaren da ta ji ya fahimtar da ita ko waye ya shigo. Sai dai bata juyo ba balle ta kalle shi.

“An gaida Sayyada Hafsatu. Haka dogon lazimi ko magana ba a yi?” Nasir ɗin ya faɗa da sigar izgili.

Hakan yasa ta shafa addu’ar da take yi tana juyo da kallonta gare shi, da kuma shimfiɗa kyakkyawan murmushi a kan fuskarta “Duk yadda na kai ga lalacewa ban bar addinina da kuma tambarin gidanmu ba Nasir. Ina fatan kaima zaka bar buɗaɗɗiyar ƙofa tsakaninka da Ubangijinka. Domin ni ba zan rayu da mutumin da bai san mene ne ibada da kuma hakkin Ubangiji a kansa ba.”

Zama ya yi a bakin gadon yana murmushi da kallonta da kuma ɗage girarsa guda ɗaya “Duk abubuwan da kika aikata a baya har kina da bakin da zaki iya yiwa wani wa’azi dama?”

Dariya ya yi mai sauti, har jerarrun haƙoransa suna bayyana “Abin mamaki, ɗiyar malam a gidan bariki.”

Murmushin itama ta yi tana murza girarta guda ɗaya da miƙar da ƙafafuwanta samɓal “Ni gidan aure na shigo, ban sani ba ashe ka yiwa gidan naka tambari da na bariki. Abin birgewa da sa’a a gareka.” Ta yi maganar tana miƙewa tsaye da naɗe abin sallar.

Gaban Madubi ta zauna tana shafe shafen mai, har a lokacin idanuwan Nasir na kanta, shifa komai da Hafsa ke yi tana birge shi ne, bai kuma taɓa jin haushinta a kan duk wani abin da zata yi ba.

“Mene ne sa’a a gare ni da kike faɗa?” Ya yi maganar yana tasowa da tsayawa a gaban madubin, a lokacin har ta kammala kwalliyar tana murza ɗaurin ɗankwali, wani taƙadarin ɗauri ta yi shi ba cocilan a gaba ba, shi ba igiya ba.

Sannan ta juyo ta fiskance shi bayan ta tsaya a kan ƙafafuwanta “Sa’ar shigowa da ni cikin rayuwar Barikin ka da ka yi. Zan kuma tabbatar da sauyaka kafin na barka.” Ta kai ƙarshen maganar tana bibbiga ƙirjinsa da hannunta.

“Abu ne mai wahala sauya Nasir Nasar, Hafsa.”

“Zai zama mafi sauƙi a gare ni. Ka ci gaba da jira, zaka ga sauyin a lokacin da baka tsammata ba, balle ka yi zato.”

Daga haka ta ratsa ta gefensa tana takawa. Hannunta ya ruƙo yana dawo da ita gabansa “Idan kika kasa fa?”

“Hafsat Kamaluddeen, bata taɓa kasa yin abin da ta yi niyar yi.

Lokacin cin abinci na ƙara wucewa Habeeby. Akwai abubuwan tattaunawa da yawa a can ɗin ma idan mun zauna.”

Kai ya gyaɗa yana damƙe hannunta da bin bayanta, yana faɗaɗa murmushi a kan fuskarsa, ganin yadda take tafiya da alfaharinta tana jujjuyawa.

Har zuwa lokacin da suka zauna a gaban tebirin cin abincin ta ja masa kujera ya zauna, ta buɗe manyan kulolin da ke jere a daining na farko farar shinkafa ce sai miyar jajjagen da aka yi ta da nama. Ɗayan kuma farfesun kaji ne. Sai ɗayan kuma kuskus ne.

“Wanne kake buƙata a ciki?” Ta yi maganar tana kallonsa.

“Wadda amarya zata ci.” Kai ta gyata tana zuba musu farar shinkafar da miyar kajin a flat ɗaya ta haɗa musu suka fara ci, suna fira wadda yawanci ba ta arziƙi bace, asalima kamar suna yiwa junansu ba’a ne.

“Na daɗe banga Uwar gida kamar taka ba Nasir. Tana da kirki, tana da kara da kawaici.” Hafsa ta faɗa a lokacin da ta ke ajiye cokalinta.

Bai mata magana ba, hakan yasa bata tsaya bi ta kansa ba ta ci gaba “A zaman da na yi da ita, na lura tana da haƙuri ƙwarai, wadda irin haƙurinsu kan iya kai mutum wuta idan bai yi da gaske ba.”

Ɗago kai ya yi yana haɗe girarsa waje ɗaya saboda tsananin tsuke fuskar da ya yi “Kina nufin ni zan cuceta har na faɗa wuta.”

“Ta can ƙasa ma kuwa Nasir. Dan ban ga aibu a tare da ita ba, da ka mayar da kanka bunsuru mai biye-biyen mata. Baka nan baka can kamar maroƙin daya ga tsabobi.”

“Da alamu fuskar da na sakar miki ta baki damar faɗa min komai da ke ranki Hafsa. Har kina kuma ƙoƙarin rainani.”

Kanta ta girgiza “Koda ace ka haɗe fuskarka kamar hadari, ba zan ji tsoro  da shayin faɗa ma gaskiya ba Nasir. Gaskiyar da ka rasa samun wadda zai faɗa ma ita a tsawon rayuwarka.”

“Shi yasa naga ke da kika samu masu faɗa miki kina binta, kina kuma tsaftace babu datti ko ɗis a tare da ke.”

Dariya ta yi tana miƙewa da tattara filet ɗin da suka ɓata “Ba zaka fahimta ta haka ba, amma zan fahimtar da kai ta yaren da zaka yi saurin ɗauka.”

Daga haka ta yi kitchen tana jin idanuwansa a buɗe. Yana aika mata da harara da yake ta faman cika yana batsewa.

*****

Wasa-wasa dai haka suka cinye kwanaki ukunsu, wadda a cikinta babu wani sauƙi ga Hafsa, tun tana mamakin abin da Nasir  ke mata na raba dare a kanta, har ta zo ta daina mamaki.

Tana ƙoƙarin jurewa na wasu ɗan lokacin, duk da idan abin ya isheta takan rufe shi ne ta tafi, ba abin da ya fi bata haushi da takaici sai rashin fitarsa, rai da rai yana tare da ita, ga rashin ibada.

Ta ɗauka a lokacin da ya cika kwanaki ukun zai haɗa su da Zahra ya musu nasiha amma sai ta ga ya kaɗa kansa ya mata sallama, zai koma tsohon rumbu.

Kai ta jinjina, daga haka ta fara kaiwa da kawowa a cikin ɗakin, mafita ɗaya take nema da zata illata Nasir, ta kuma dawo da hankalinsa a ƙarshe ta samu mafita guda ɗaya tak.

A cikin mako biyun da ta yi a gidan ta yi ƙoƙarin janyo yaran Zahra guda biyu jikinta, tana koyar da su karatu. Ganin hakan yasa itama Zahra ta nemi ta koyar da ita, kasancewar ba nisa ta yi ba  a ka mata aure, kuma Nasir ya hanata zuwa makaranta.

Anan ta fara koyar da ita, Zahra ta gaza riƙe, mamaki da ɗabi’un Hafsa har wata rana ta tanka mata “Halayyarki na da ban mamaki. Ina ganin saɓanin abin da mutane suke faɗa min a kanki.”

Murmushi Hafsa ta yi tana ajiye littafin karatun da mayar da kallonta ga Hafsa “Mutane ne basu fahimce ni ba, Zahra. Adawata da maza ce ba wai da mata ba, haka duk lokacin da zan yiwa mutum abu ina yinsa ne da gaskiyata. Ba kuma dan na bashi haushi ba.”

“Amma kuma yayarki fa da a kaa ce ta raine ki tun kina ƙarama itama ba ki ƙyaleta ba.”

Hannun Zahra ta ruƙo ta haɗa a cikin nata tana damƙewa, wadda hakan yasa Zahra jin wani iri, tana jin zuciyarta na bugawa da ƙarfi “Ki bar batu a kan ‘yar uwata Zahra. Ko kuma dangina da kika ji labari a kaina. Ki ƙyale lokaci ya sanar da ni abubuwan da suka dace na rayuwa. Ki mayar da hankalinki a kan rayuwar auren da kike tsakaninki da mijinki. Wanne abu kika cimma a tare da Nasir? Wani matsayi ya ɗauke ki a rayuwarsa? Me yasa ko yaushe kike ƙasa da samun farin ciki a gidan auren ki? “

Ɗago da kai ta yi tana kallon Hafsa, tana jin zuciyarta na bugawa da ƙarfi, wani rauni na mamaye zuciyarta, kafin ta farga hawaye na tseren gangarowa a idanuwanta.

Tabbas babu wani mahaluƙi da ya taɓa yi mata tambaya irin wannan, kamar yadda babu wani da ya taɓa zama da ita dan ya ji damuwarta, tana da tabbacin damuwarta na gaf da kashe mata rayuwa, wadda kuma koda ta mutu babu wadda zai yi hasara da kuka kamar yaranta.

Iyayenta sun gaza fahimtarta, a duk lokacin da ta je musu dan ta sanar da su halin da take ciki, sai su koreta su hanata bata damar faɗar komai, saboda Nasir yana da kuɗi, saboda suna kunyar ta kashe aurenta ta zo ta musu zawarci.

Wani hawaye ya gangaro mata, a lokacin da ta tuna hatta mahaifiyar da ta haifeta tana bata umarni a kan kada ta sake ta kashe aurenta, kowacce mace haƙurin zama take da mijinta.

Matse hannunta Hafsa ta sake yi a karo na biyu “Ba na tambayeki ba ne dan ki bani amsa ba, Zahra. Asali na tambayeki ne dan ki samu hanyar da zaki toshe ɓarakar da ke tare da ke.

Babu wata mace a duniya da bata da abin birgewa ko na so. Kamar yadda nake da tabbacin mata da yawa sukan bar ɓula mai girma da namiji zai take su ya wuce.

Duk wadda zai ce ki yi haƙuri a kan zamanki da Nasir, kamar yana ƙara ɗauko wuƙa ne yana daɓa miki, na sani haƙuri na da daɗi, yana kuma da wahala, amma kuma har zuwa wani lokaci zaki ci gaba da yin sa? Wani tabbaci kike da shi a kan Nasir zai sauya ya zama kamar mutumin da kike mafarkin so ya zama?

Amsar babu ranar, domin babu wadda zai iya sauya shi har sai ke da kike bashi damar ya aza miki ko wata shara kin sauya. Ba da faɗa ba, ba kuma da hayaniya ba, ina da tabbacin za ki fini sanin hanyoyin da zaki gyara abinki da kanki. Ki kuma sanar da shi duk yadda ya zo da zafi akwai wuta a tare da ke. Babu yaji babu saki, koda zai yi yunƙurin sakinki, ki toshe ƙofar, kina da yara a gidan, dan haka akwai gadonsu.

Na san iyayenki sun daƙusheki, ba sa so ki bar gidan gudun zaman zawarci. To ki zauna a gidan, ki nuna masa akwai wutar da tafi tasa ƙuna.”

Shiru Zahra ta yi yana nazarin kalaman Hafsa, wadda take da tabbacin gaskiya ce take faɗa mata.

Zare hannunta Hafsa ta yi daga ruƙonta “Kina da lokaci a yanzu, tun kafin zuciyarki ta buga saboda baƙin cikin ɗa namiji.”

Daga haka ta tashi ta shige sashenta, saboda dama a farfajiyar gidan suke zama su yi karatu har yaran Zahra.

Da ido Zahra ta bita tana nazarin maganar, Hafsa tana ajiye su a muhalli da ya dace, tana tunanin abin da zata yi.

Tabbas tana buƙatar dawo da martabarta, za kuma ta gwada ɗaukan shawarar da Hafsa ta bata, ba zata ci gaba da kashe kanta saboda ɗa namiji ba. Ta yarda duk abin da Nasir ya zama a yanzu tana da kaso mai girma na zamowarsa haka, tana kuma da yaƙini a kan kalmar nan ta sai bango ya tsage ƙadangare ke samun ɓular shiga.

Ta daɗe tana kaiwa tana kawowa da nazari a kan abin da zata yi ta nunawa Nasir itama mace ce, mai ‘yanci.

Kasancewar yau ranar girkinta ne, hakan yasa ta shirya tsaf cikin kwalliyarta, ta sa atamfa riga da siket mai kalar sararin samaniya. ta yi ɗauri daidai da zamani.

Bayan ta ƙawata ko wanne lungu da saƙo da ƙamshi a gidan, daga ƙarshe ta jere abincin da ta girka, wadda bata da tabbaci a kan gwanin nata ko zai ci.

Tun tana zuba idon ganinsa har dare ya yi zuwa ƙarfe goma da rabi na dare, ta ji buɗe get ɗin gidan da kuma tsayuwar motarsa.

Ajiyar zuciya ta sauƙe, tana furzar da iska a bakinta, ba zata ɗauki nauyin zunubansa a kanta ba a yau.

Hakan yasa ta miƙe da zummar shigewa ɗaki, ta ji ya doko ƙofar ya shigo, kai tsaye kanta ya iyo yana rarumarta, da sauri ta daka tsalle ta koma gefe.

“Mene ne hakan?” Ta jefa masa tambaya da aika masa da mummunan kallo. Abu ne wadda bai taɓa gani a tare da Zahra ba, shi yasa ya tsaya kamar kafafen gunkin da aka sassaƙa.

Idanuwansa sun ƙanƙance, kana ganinsa kasan yana tare da fitina, wadda shi ya kwasowa kansa.

“Kamar ya mene ne, yau na saba zuwar miki a haka?” Ya jefa tambayar yana ƙara rarumota.

Hakan yasa ta sake matsawa baya, tana hankaɗa shi baya “Ba yau ka saba zuwar min a haka ba, amma ina tabbatar ma yau ne karo na ƙarshe da zan karɓe ka a haka.” Ta yi maganar tana buɗe ƙofar ɗakin.

Ya yi sauri kamar zai kamota, ta banko masa ƙofar ya bige goshinsa, hakan yasa ya dafe wajen yana kiran “Auwshh!” Saboda tsananin zafin da ya ji.

Ya daɗe yana murza goshinsa kafin yaji ya dawo daidai, hakan yasa ya murɗa ƙofar ɗakin, da mamakinsa ya jita a rufe gam.

Ya fara buga ƙofar “Zahra ki buɗe min ƙofa. Karki sake ki bari na ɗauko mukulli na buɗe.” Ya yi maganar yana sake buga ƙofar.

“Malam karka tasar min yara, yanzu dare ne, ka je inda ka ci abinci ka ci wannan ɗin ma.”
  Ido ya fiddo waje da tsananin mamaki ‘Anya Zahran sa ce kuwa?’ Ya jefawa kansa tambayar.

“Zahra ni Nasir nake magana kina bani amsa?”

“Saboda kai ba Allah ba ne. Ba zaka min abin da Allah bai min ba, ba zaka kashe min rayuwa da ƙaryar da kake haɗawa kanka ba.”

Kai ya jinjina yana huci “Wallahi idan baki buɗe ba sai na ɓaɓallaki. Naga shegen da ya tsaya miki har kike faɗa min maganar nan.”

“Za kuwa mu ɓalla junna.” Ta yi maganar tana kashe hasken ɗakin da kwanciya a kan gado.

“Taɓɗijam!” Nasir ya faɗa yana ciza yatsa, da jin murɗawar mararsa, shifa mamaki ne ya kashe shi, yasan dai babu wadda zai shigo masa gida har ya ziga Zahra. Domin tuntuni ya fatattaki ƙawayenta, bata fita babu kuma wadda zai zo wajenta.

Juyawa ya yi yana tafiya yana buɗewa kamar ɗan shayi, ya nufi ɗakin Hafsa “Sauƙin abin ma mata biyu gare ni.” Ya je sashen nata, sai dai tun ƙofar palo a rufe take, ya san kuma idan ya buga zai iya janyo hankalin mai gadi da maƙotansa.

Hakan yasa ya fara kiranta ta hanyar wayarta, wayar sai da ta katse ba a ɗauka ba, ya sake kira, shima tana gaf da katsewa ta ɗauka.

“Ya dai?” Ta faɗa muryarta da bacci a cikinta.

“Ki zo ki buɗe min ƙofa.” Ya faɗa da faɗa.

“Hauka kenan Nasir. Na yi baccin zan ta so na buɗe ma ƙofa. Ka tafi tsohon rumbunka da kake iyo a cikinsa.” Daga haka ta yanke wayar, tana kasheta gaba ɗaya.

“Kan Uba!” Ya faɗa yana hargitsa gashin kansa da yake tare.

Ya nufi sashensa, yana jin duniyar na juya masa, mararsa da take cike taf tama gaf da fashewa.

Ya riga da ya yi rantsuwa ya kuma yi alƙawari ga mahaifinsa ya daina kula karuwai. Shi yasa ya yarde masa auren mata, duk lokacin da ya so, musamman a yanzu da cuta suka yi yawa.

To amma koba komai a yanzu da yake jin tsantsanin karuwai ba zai taɓa zurma kansa a cikinsu.

Kwanciya ya fara yi yana birgima a kan gadon, har ya faɗo ƙasa, hawaye na zuba a idanuwansa, bai taɓa danasanin a kan abin da yake sha ba, sai yanzu.

Ganin idan ya ci gaba da kwanciya zai mutu yasa ya rarumi wayarsa ya kira abokinsa Dakta Fahat, wadda sai da ya kira shi har sau huɗu kafin ya ɗauka.

“Nasir lafiya kuwa?”
“Fahat zan mutu dan Allah ka zo ka min allura, nasha maganin motsa sha’awa ne.”

“Ina matanka?”

“Babu wanan lokacin Fahat.” Ya yi maganar yana gunji wayar na faɗuwa daga hannunsa.

Agogo Fahat ya kalla yaga ƙarge goma sha biyu na dare. Yanayin yadda ya ji muryar Nasir hankalinsa a tashe yake dole ya je ya taimaki rayuwarsa.

Hakan yasa ya miƙe yana harhaɗa kayan da zai buƙata, ya fita, Aisa matarsa na tambayarsa yace kiran gaggawa ne daga asibiti, sanin aikinsa na irin hakan yasa ta koma ta kwanta.

12:30am ta kawo shi gidan Nasir, mai gadi a tsorace ya fito, ganin Fahat ne ya sheda shi, hakan yasa ya buɗe masa get ya zura motarsa. A gurguje ya shiga gidan ya same shi a kwance ba yadda yake, allura ya fara masa, ya ɗaura masa ruwa. Yana maida numfashi.

“Haba zuwa yanzu ya kamata ka daina wannan shirmen Nasir. Kana biya su Mukhtar kuna cutar da rayuwar matanku. Ku gane akwai cutarwa a halittarku da Allah ya muku ma ya suka ƙare balle kun haɗa wasu abubuwan zaburarwa. Yanzu gashi nan a banza ka kusa mutuwa. Wai da matan naka basa nan ka je ka sha magani?”

Ƙwafa Nasir ya yi yana tauna liɓs ɗinsa “Wallahi zan koyawa Hafsa Hankali, zan bata babban darasi na rayuwa da ba zata taɓa sanin ya yake ba.

Ni Hafsa zata gurɓatawa mata.” Ya yi maganar yana ƙwafa.


   “Mai ya faru?” Fahat ya sake faɗa.

Kai ya jinjina sannan ya kwashe komai ya faɗa masa, dariya fahat ya kwashe da ita har yana riƙe ciki, yana kuma nuna Nasir ɗin.

“To kai ya za a yi kace Hafsa ce ta gurɓata ma mata. Kawai dai ta gaji ne itama, abu kullum ɗaya ba sauyi, kai kuma ba wani faranta mata kake da daɗin rai ba.”

“Fahat, tashi ka tafi ka bani waje. Zan yi maganin abin da kaina.”

Baki Fahat ya taɓe yana ƙara tuntsirewa da dariya “Allah bada sa’a. Dama ba sai ka kore ni ba, ni mata ta tana jirana. Kai da kake da biyu gashi duk sun rufe ma ƙofa.” Ya ƙara tuntsirewa da dariya yana ficewa a ɗakin.

Ido Nasir ya lumshe yana jin wani ɗaci a maƙoshinsa, yana ƙara yin saƙa da warwara, har bacci ya ɗauke shi.

Washegari ya shiga ɗakunan matan ya gaida su, bai nuna musu komai ba, wadda hakan kuma ya bawa Zahra mamaki, domin Nasir bai taɓa dubata da yaranta ba, balle ya tambayeta ya ta kwana. Yo mutumin da zai biya buƙatarsa ya tsallaka ya barka ba zaka ƙara ganinsa ba sai wani abin ya kawo shi.
Lallai ta yarda da zancen Hafsa, za kuma ta ƙara dagewa har ta fanshe takaicin da yake ƙunsa mata.

Tsawon kwana biyu da faruwar hakan, ya samu Hafsa ya ce ta haɗa kayanta kala uku za su yi tafiyar buɗa ido.

“Zahra fa?” Ta jefa masa tambayar.
“Karki damu itama idan mun dawo xa mu je. Yanzu zamu tafi cin amarci ne.”  Ya ƙare maganar yana kanne mata ido.

Murmushi ta yi ta gyaɗa masa kai, daga nan ta fara haɗa kayan da na buƙatarta. Sai kuɗaɗen da ta zura a ƙasan jakarta.

Nasir ya zo ya zo ɗauke da madaidaiciyar jaka a hannunsa, ganinta da ƙatuwar jaka  bai hanata ba, suka je suka yiwa Zahra sallama a kan za su yi mako ɗaya ne su dawo. Fatan alkhairi ta musu tana rungume Hafsa da kiran zata yi kewarta sosai.

Daga haka suka faɗa bayan mota, Rabe direba ya shiga ya ja su.

Kai tsaye tasha suka je, suka hau jirgi. Ita dai tunaninta za su ce ƙasashen waje ne dan anan tasan ana yin honeymoon. Taga tashin Nasir ya ce za shi toilet bayan tafiyarsa ne kuma aka gabatar musu da abin sha.

Ta ɗauka ta sha ganin kowa na sha, daga nan bata san inda kanta ya ke ba.

Har zuwa lokacin da ta buɗe idanuwanta ta ga dishi-dishi, tana iya ganin faɗin sahara da kuma zafin ranar da ke hudawa a saman fuskarta, sai kuma rangajin da take a saman wani abu da bata san ko mene ne ba. Daga nan idanuwanta suka sake rufewa.  

Lokacin da ta buɗesu kuma sai taga kanta a cikin wani ɗaki da bashi da maraba da akurkin kaji. Idonta ta buɗe tarwai, tana shafa hannunta, ta ganta kwance a kan tabarmar kaba tsurarta.

Zabura ta yi ta fito waje, ga mamakinta sai ta hango tarin bukkoki irin nata, wadda suka kasance tsilli tsilli, mutane suna wuce jifa jifa, tana iya ganin shigarsu da suka rufe iya gabansu, matanse ke ɗaure gabansu da ganye, kansu kuma da wasu irin manyan kitso, mazan kuma sumarsu ta ɗaga butu-butu dai d su.

“Na shiga uku! Ina ne nan?” Ta jefawa kanta tambayar tana komawa ɗakin da ta fito, wayam babu jakar kayanta babu kuɗaɗe. Sai wata farar takarda. Da sauri ta fara warware takardar ta ga rubutun Nasir a jiki.

Nasan zuwa yanzu kinga maza da yawa, kin kuma wahalar da mutane da yawa. Mutane masu uzuri da haƙuri da kuma yafiya a gareki, sai dai abin da baki sani ba Nasir baya yafiya, ba ya mantuwa. Ba zan ci gaba da barinki a gidana ki gurɓata min rayuwar salahar matata ba. Saboda haka ki rayu a wata duniyar da mutanen da basu san kara da kawaici ba, waɗanda basu san zo kashe ni da Hausa ba  balle ki cuce su.

Ki ji daɗin duniyarki. Hafsat Kamaludden Muhammad

Wani ihu tasa da ƙara tana hargitsa gashin kanta, tana fashewa da kuka, kuka mai yawan gaske.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jini Ya Tsaga 35Jini Ya Tsaga 37 >>

1 thought on “Jini Ya Tsaga 36”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×