Skip to content
Part 37 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

kuka take mai ƙaraji wadda yake fitowa tun daga ƙasan zuciyarta. Bata taɓa jin ƙuna da ciwo a rayuwarta kamar wannan ba, kamar yadda bata yi tsammanin zata samu kanta a hali irin wannan ba.

Nasir ya cuceta ya ci amanarta, ya kuma  yaudareta, mafi girman yaudara a rayuwa. To amma hakan na nufin ya karaya ne ya ji tsoro a kan al’amarinta?

“Tabbas ya ji tsoro, da bai bari sun fafata a inuwa ɗaya ba.” Ta yi maganar tana share hawayen kan fuskarta, tana ganin yanzu ba lokacin kuka ba ne, lokacin fuskantar rayuwar zahiri ne, kuka ba zai dawo mata da abubuwan da ta rasa ba, kamar yadda ba zai mayar da rayuwarta baya ba.

Cikinta ne ya bada sautin Ƙulululu  wadda yake tunasar da ita yunwar da ke tattare da ita. Ba ta san adadin lokacin da ta ɗauka a wajenba, kamar yadda bata san kwanakin da ta shafe kafin ta zo wajen ba.

Salloli nawa ake binta? Wannan tambaya ce da babu wadda zai amsa mata.

Fitowa ta sake yi waje tana kallon rairayin sahara iya ganinta, dama da hagunta, gabanta da bayanta.

Kanta ya juye ƙwarai da gaske, bata san ina ne yamma ba balle gabas. Ƙafarta ta ɗora a kan rairayin saharar, wani zafin rana ya huda fatar ƙafarta, tun daga ƙafar har zuwa tsakiyar kanta.

Hakan yasa ta janye ƙafarta da sauri tana rintse idonta, da kuma dafe ƙafarta da tafukan hannunta tana ambaton sunan Allah, hawaye na gangarowa a kan kuncinta.

Ɗakin ta sake komawa ko zata ga takalmi, sai dai idonta ya jagoranci kalmar babu a gareta, domin bata ga komai ba, bayan mayafin da ta yafa a jikinta, ta tabbata shima Nasir bai ankara da shi ba, da ya yi awun gaba da shi.

Rintse idanuwanta ta sake yi, tana mai zuro ƙafafuwanta waje a karo na biyu. Zafin ranar na ƙara gasa mata ƙafa, kamar yadda ya ke huda tsakiyar kanta.

A ƙafarta zafin ke fita, amma tana jin zafin a cikin kowanne sashe na jikinta “Allah ka bi min hakkina a kan Nasir. Ka saka min fiye da abin da ya aikata min! Allah ban cutar kowa da zafin rana ba, ban yaudari kowa a kan abin da ke ƙasa da tunani na ba! Ya Allah ka kwatanta masa illar da yaudara ke samarwa!” Hafsa ta yi magana a bayyane hawaye na biyowa ta kumatunanta, numfashinta yana sama yana ƙasa.

Juyawa ta yi baya dan ta ta ga tazarar da ta samar tsakanin Bikkarta, sai taga ai kamar bai fi taku biyar ta yi ba.

“Duk wannan azabar da na ci a waje ɗaya na ke?” Ta yi maganar tana ɗora hannu a kanta da runtuma uban ihu. Ihu take da ƙaraji da fatan wani ya jiyota ya kawo mata a gaji, sai dai ga mamakinta iskar da ke kaɗawa a saharar bata wanzar da sautinta ga tsilli-tsillin mutanen da suke kaiwa da kawowa ba.

Tafiya ta ci gaba da yi bayan ta aro dauriya da juriya ta yafa a ranta, tana jin yadda ƙafafuwanta suke ɗaɗewa suna zugin azaba, amma tasan bata da zaɓin da ya wuce taka saharar, domin idan ta zauna zata mutu a wajen da ba a san da wanzuwarta a cikinsa ba.  

Ta yi tafiya mai nisa, duk da tana tunanin a baya a kusa ta ke hango bikkokin, amma da fara tafiyarta sai ta fahimci ashe giji lahira ce. Zuwanta wajen Bikkar ta yi tozali da tarin mutanen da bata san a wata ƙabila zata ajiya su ba. Fuskokinsu a ɗame su ke, kamar yadda suke sarƙo da laɓɓansu su masu wata ƙawanya, ba ka ganewa tsakanin matansu da mazansu, idan a ka ɗauke tudun da ke cikin ƙirjinsu, sumar matan a aske take kamar ta mazan, haka kuma kunnensu babu hudar ɗankunne. Fatarsu baƙiƙƙirin kai ka ce ba su taɓa haɗa hanya da ruwa ba.

Sai dai ba su ne suka zama abin kallo a wajen ba, face ita da suka iyo kanta a zabure kamar za su cinyeta ɗanye. Ido ta rintse da ƙarfi tana nanata kalmar shahada a zuciyarta da fili, tana tunanin wannan ce iska ta ƙarshe da zata shaƙa a doron duniya.

Sai da mamakinta ya tsaya cak a lokacin da ta ji ba su mata komai ba, hakan yasa ta buɗe idonta guda ɗaya a hankali, taga suna zagayeta, wasu na shafa kayan jikinta, wasun su na jan mayafin da ta yafe jikinta.

Idonta ta ware gaba ɗaya, wadda ya yi daidai da lokacin da wani ke rarimo fuskarta yana shafa wa, wadda taji kaushin hannun nasa da kuma taurinsa kamar an ɗora mata rodi mai ƙusosi a hannunta ne.

Ƙoƙarin janye kanta take  sai dai yadda ya riƙe kan nata ko numfashin shaƙa bata samu yi da kyau ba. Ga wani warin da bata taɓa tunanin akwai shi a duniya ba, shi ba ɗoyi ba shi kuma ba wari ba, a tunaninta ko masai a ka buɗe to sai ta fi wannan warin daɗin shaƙa.

Hawaye ne ya gangaro a idanuwanta a lokacin da ta rasa madogarar da zata dafa, tana kiran wayyo Allah sau dubu casa’in da ɗaya a ƙasan zuciyarta.

“Woih Liwio Abbuj buhul ƙyuis ” Wawakekiyar muryarsa ta fito da sautin muryar, tana jin bakinsa kamar an buso da masan duniya  an afka a cikin hancinta.

Sai ta ji mutanen sun sa ihu suna tsalle suna zagaye ta “Wooih Wooih jam jam!” Suka faɗa suna tafawa da ihu.

“Shikenan tawa ta same ni. Ya Allah kar ka ɗauki rayuwata anan ba tare da na gana da Mahaifina ba. Ya Allah karka ɗauki rayuwata ba tare da na nemi yafiyar yarana ba.”

Sai dai kafin ta rufe bakinta ta ji an ɗagata sama an fara hajijiya da ita, idanuwanta suka rufe luuu ta daina ganin komai da jin sautin komai.

Da babu gara ba daɗi. Ku yi malejin wannan, matsalolin wutar lantarkin mu ba zata ƙare ba. A haka dai zan kai zuciya nesa ina guntsoro muku shi.

Ina yabawa ƙwarai da gaske, da yadda kuke yin cmnts, ina kuma godiya ƙwarai da juriyar karatun labarin jini ya tsaga. Nasan zuwa yanzu ranku ya yi fess ganin Hafsa a wata duniya daban.

<< Jini Ya Tsaga 36Jini Ya Tsaga 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×