Skip to content
Part 38 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Hasken ranar da ya gasa fuskarta da idanuwanta, shi ne abin da ya yi sanadiyyar buɗuwar idanuwanta.

A hankali ta buɗe ƙananin idanuwanta da wahala ta ƙara ƙanƙantar da su, tana buɗe su da rufe su saboda ido biyun da suka yi da rana.

So take ta yi ƙasa d kanta sai dai ta ji hakan ya gaza daga gareta, asalima ji ta yi kamar tana tare da wani abu ne da ya ke sarrafata.

Sake buɗe idon nata ta yi a karo na ba adadi, cikin sa’a wannan karon hasken ranar bai huda idanuwanta da tasirintuwa da shi ba.

A hankali ta ke bin jikinta da kallo da inda ta ke, da mamaki sai take jin ko ina na jikinta a ɗaɗɗaure, daga kan hannunta da aka meƙar da su zuwa kanta, har zuwa kan ƙafafuwanta da ta take jinsu suma a haɗe.

Muskutawa ta yi dan juyi da kallon inda take, sai a lokacin ta kula ashe a ɗaure take a kan wani kututturen ice da aka yi sama da shi, a tsakanin wasu itatuwa masu ƙarfi da ke tsaye. Ƙasansa kuma an aza ice wadda ke bata tabbacin za a yi babbakunta ne nama ɗanye.

Ƙananun idanuwanta ta ƙara buɗewa tana waiwaya kanta da kallon gefe da gefenta, sai ta hango tana wata fadama ne dagan, ba wai duniyar saharar da ta ke ciki ba.

Da alamu nan masheƙarsu ne duba da yadda idanuwanta ke ganin tsibi-tsibi na toka, da kuma dirka ta itatuwa kamar wadda take kai.

“Muƙutt!” Ta haɗiye wani yawu mai kauri da ɗaci a bakinta, a lokacin da hawaye mai ɗumi da zafi ke gangarowa a idanuwanta.

_”Shin duk wani zunubi na rayuwa da na aikata anya na ci sakamako irin wannan?’_ Ta yi tambayar a ƙasan zuciyarta, wani sabon hawaye na sake ɓallewa a cikin idanuwanta.

“Nasan na aikata abubuwa da yawa a cikin rayuwaya. Amma ban taɓa cutar da wani ta hanyar yaudararsa ba, ina faɗawa duk wadda zama ya haɗa ni da shi gaskiya koda a ce zan rasa numfashi na ne. Ya Allah kar ka ɗauki rayuwata a wajen da babu kowa nawa! Ya Allah ka gwada ikonka a kan azzalumin bawan da zalincinsa ya zama linzamin kawo ni wajen nan!” Ta yi maganar tana ƙara fashewa da kuka. Kukan da take da tabbacin babu wani mahaluƙin da zai jita balle ya tausaya mata, kamar yadda take da tabbacin babu wani mai ɓurɓushin imani da ƙaddara zata harboshi zuwa gareta a wannan lokacin.

Tuff! Tufff! TUFFF! Haka kunnuwanta suka fara jiyo mata sautin takun su, kai kace sansanin yaƙi ne ya haɗu. Tun daga nesa take kallon yadda ƙura ta turniƙe wajen, tana iya ganin adadin su wadda bata isa lissafa su ba.

Mamaki ne ya kusan kasheta a lokacin da ta ga yawansu, wadda bata taɓa tunanin suna da shi ba, musamman idan ta yi la’akkari da yadda take hango bukkokin su tsilli-tsilli a baya.

Ƙaran ganga sai tashi yake a bayan tahowarsu, tana iya ganin yadda yaran ke ihu suna tsalle-tsalle kamar yaran birrai a lokacin da suke wasan hawa bishiya.

Idanuwa ta lumshe tana runtse su da ƙarfi tana karanto “Hasbinallahu wa ni’imal wakil. Allahumma la sahala illa ma ja’altahu sahala, wa anta taj’alil hazni iza ma shi’ituhus sahala.” Daga nan ta ci gaba da karanto kalmar shahada.

Har zuwa lokacin da suka ja tinga a gabanta, ta ji kiɗan ya dawo saitin kanta, tana kuma jin yadda yaran su da matan cikinsu suke tafi suna waƙar su.

“Walololo Walololo wajuju,
   Mo wai lajuju wajuju.
    Walololo walololo wajuju,
   Mo wai lajuju wajuju.”

Haka dai suka ci gaba da waƙoƙinsu mai buga ganga na yi.

Daga nan ta ga wani mai kafcece cen hancin da bashi da maraba da na botorami ya ɗaga musu hannu. Fuskarsa kwa idan ka kallah kai kace saniyar da ta dawo daga kafu ce saboda tsanani haɗetan da ya yi, da kuma munin da ta ƙara yi.

“Afoi laouji ujalj fawuiiy.” Ya faɗa da ƙatuwar muyarsa. Nan taga yaran suna tsalle suna kiran.

“Fawuiiy! Fawuiiy!” Suna tafawa suna ihu.

Daga nan ta ga ya mayar da kallonsa ga wani kafcecen mutum “Baoi, Fawuiiy bahrju luwio.”

Tana ganin yadda mutumin mai ƙirar samudawan farko ya fara takowa zuwa gabanta, bai wani tsaya bi ta kanta ba ya tsugunna wadda a ganinta da tsugunnon da miƙewarsa duk abu ɗaya ne, domin ba ta inda tsayinsa ya ragu.

Dutse ya ɗauko guda biyu yana gogawa a jikin juna, wuta ta fara feshi da alamu dai da dutsen suke haɗawa su kunna wuta.

Ganin abin da za su yi yasa Hafsa ƙwalolo ido ta fara karanto addu’ar da take zuwa bakinta.

Tana jin yadda zuciyarta ke harbawa sau 360 tana ji a ranta da ace wani mai hankali ne a kusa da ita, da babu abin da zai hana shi jiyo yadda zuciyrta take tsalle kamar zata faɗo a ƙirjinta.

Duk yadda ƙaton mutumin yasa dutsen ya kama da wuta yaƙi ya kama a ƙarshe ya watsar da su ya sake ɗauko wani.

Ganin sun ƙi yi yasa ya juyo ya kalli shugan nasu yana risinar da kansa ƙasa da ɗora hannunsa a kan ƙirjinsa.

“Affawio, Layrion fawuiiyy.”

Tana ganin yadda mutumin ya ƙara tsuke fuskar shanunsa, ya fara takowa zuwa gaban mutumin, ya risina da hannunsa ya ɗauki dutsen ya goga, cikin dace wutar ta yi farfari kamar zata sauƙa a kan iccen sai kuma ta ɓace.

Ƙara jarrabawa ya yi a karo na biyu wadda kuma bata yi alamun farfarin ba, tun yana yi da zuciyarsa har ya gaji ya watsar da dutsinan ya zo gaban Hafsa ya tsaya, yana kallonta da manyan idanuwansa kamar za su zubo ƙasa.

“Waihio laiwowa?” Ya mata maganar da ƙarfinsa, da kuma tsawa mai rangaji.
Wadda hakan yasa ta ambaci kalmar “Allahumma ajirni fi musubita haza, wakallafni khairan min ha.”

Hakan yasa mutumin ya ja da baya a tsorace yana ɗaga hannunsa da nunata “Moilowa! Moilowa!” Ya ke faɗa yana nunata.

Wadda hakan yasa mutanen da ke wajen suka fara matsowa kusa da mutumin.

Shima ƙaton mutumin miƙewa ya yi a kan ƙafarsa yana matsawa daga kusa da ita da nufar shugan nasu.

“Moilowa ne? Affawio.” Ya jefa masa tambayar.

Kai shugaban nasu ya girgiza kafin daga bisani ya ce “Joille Mailowa af.” Tun kafin ya rufe bakinsa ƙaton mutumin ya fara kunce mata hannunta, daga nan ya kunce mata ƙafafuwanta.

Ita dai har a lokacin addu’a take bata daina yi ba, domin ta san Allah ne ya ji ƙanta ya karɓi addu’arta, duk da bata san me suke cewa ba, bata san me suke faɗa a kanta ba.

Tana ganin yadda ƙaton mutumin ya cicciɓeta ya azata a kafaɗarta kamar ƙaramar yarinya, daga nan ɗunguma da ita gaba, sauran suna biye da su a baya.

Wani ƙaton kogo taga an nufa da ita, wadda yasa ‘ya’yan hanjinta kaɗawa, kogon na da zurfi ƙwarai ga kuma duhun da ya mamaye cikinsa. Amma ga mamakinta ƙaton mutumin yana zura ƙafarsa ba tare da duhun ya kawo masa tsaiko daga tafiyarsa.

Sai da suka yi rabin kogon sannan kamar abin rufa ido haske ya gwauraye a idanuwansu, tana ganin wasu gumaka da aka sassaƙa a wajen masu girma, da suke ko wata kusurwa ta kogon. Ruwa na sauƙa a bakinsu da hancinsu, wadda suka taru suka sa wajen ya ɗauki sanyi.

Sai dai cikin mamakinta ruwan bai shafi hanyar da suke takawa ba, duk da cewa ruwan na sauƙa ne a wajen.

Daga can taga an direta a gaban wata ƙatuwar karaga da take ɗauke da sassaƙen mutum wadda ya zama kamar gunki. jikinsa sanye da kaya na alfarma da rawani amma kuma sai dai gangar jikinsa a sanƙare ta ke.

Takowa gabanta shugaban nasu ya yi, ya risinar da kansa zuwa gareta “Moilowa, Jaiyz Afafawo loi agrajo Failowa.” Ya ƙare maganar yana mata nuni da saƙaƙon mutumin da ke kwance a wajen.

Kanta ne ta juya bata san me zata yi ba, kamar yadda bata gane yaren da suke mata ba.

Hannunta ya kama ya fito da wata ‘yar ƙaramar wuƙa sabuwa dal da ita, ya ɗora hannun nata a kan mutum-mutumin. Kafin ta farga ta ji ya ja wuƙar a tafin hannunta zafin da ta ji da ɓallewar da jinin ya yi a hannunta su suka haddasa mata sakin wani ƙara tana kiran “Hasbunallahu wa ni’imal wakil. Inna lillahi wa inna ilaihirraji’un.” Wadda kalmar ta fita ne a lokacin da jininta ke sauƙa a kan mutum mutumin.

Ga tsananin mamakinta sai taga kogon ya fara girgiza hasken wajen yana kawowa yana ɗaukewa, ‘yan tubalan da ke sama suna faɗowa. tsoro ne ya kamata ta fara matse jikinta tana ƙara karanto duk addu’ar da ta zo bakinta. Ayatul kursiyyu kam ta yi ta har ba adadi, dan ta tabbata a wajen rayuwarta zata zo ƙarshe.

Gunkin mutumin ne ta ji ya fara girgiza yana ɓantarewa, daga bisani ta ji wata rugugin tsawar da ta haddasa mata faɗuwa ta sume a wajen..

*****

Hhhhh Hafsatu dai an zama Moilowa! Da alamu za a biya bashin wani al’amari da ya faru a ƙarni na ashirin da da biyu da ya shuɗe a baya.

<< Jini Ya Tsaga 37Jini Ya Tsaga 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×