Skip to content
Part 41 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Kanta ta girgiza tana sake kallon mutumin a karo na biyu, tana ƙoƙarin ɗauko duk juriyar da ta ke tunanin tana da ita, tana son ta fara yin magana ko da a ce gizo yake mata ɗin.

“Ban san wani adadin lokaci zan ɗauka a nan ina raye ba? Ban san kuma ko ƙaddara zata ƙara bani damar da zan sake ganinka a zahiri ba, Sayyadi. Amma ko a hakan ma ina farin ciki, ina jin ba daɗi a duk lokacin da na tuna ka, ina son na samu dama ɗaya tak, damar da zan ganka na roƙi yafiyarka.

Amma ban san ta ina zan fara ba, ban san ta ina zan fuskanta na shiga kusa da mutane ba. Nan sabuwar duniya ce a gare ni, da ta sauya min rayuwata, ta amshi wasu abubuwa daga gare ni, ta mayar da naƙasar zuciyata zuwa sassan jikina.”

Ta gama maganar hawaye na gangarowa a idanuwanta, tana sa hannu tana sharewa, tana murmushi.

Ji ya yi wani abu na huda zuciyarsa da mamayeta, yana jin ƙunci mai yawa a ƙirjinsa, Idanuwansa ya runtse yana jan numfashi da fesar da iska a bakinsa.

A lokacin da ya buɗe idanuwansa, ya ganta a nesa da shi, tana tafiya da sanda a kafaɗarta, ƙafarta ɗaya a ɗage.

Idanuwansa ya buɗe yana kallonta wani abu ya huda ƙoƙon zuciyarsa ya tsaya tsam a cikinta, yana jin wani abu mai ɗaci da kaifi da ya tankare a maƙoshinsa “Nahna!” Ya sake kiran sunanta a karo na biyu.

Wadda hakan yasa ta ja ta tsaya, tana juyo da kallonta daga inda ta ji sunan.

Ganin Sayyadi ya yi yana takowa gabanta da kakin sojoji a jikinsa, wadda hakan yasa ta buɗe ƙananun idanuwanta da wuya ta ƙara sawa suka zurma ciki.

“Nahna, ke ce kika dawo haka?” Ya sake yin maganar a lokacin da idanuwansa suka yi raurau, tana ganin kallon tausayin da yake mata da kuma ƙaunarta wadda a ganinta bata cancanci hakan daga gare shi ba.

Idanuwanta ta murza da hannunta daga tsayen da take, tana ƙara gyara burgujejen mayafin da ta lulluɓe jikinta da shi.

“Da gaske kai ne, Sayyadi ba gizo idanuwana suke min ba? Da gaske kai ne ka zo nan kana kiran sunana?” Ta sake maganar tana shafa fuskarta da kuma tauna yatsan hannunta, ko ta yi dace da rarrabewa tsakanin sarƙaƙiyar da take ciki.

“Ni ne Nahna, ba gizo nake miki ba. Nine Abdulmannan Ishaƙ a gabanki, Nahna.” Ya ƙare maganar yana ruƙo hannunta da ya yi wani buɗu-buɗu ga uban tauri a jikinsa, wadda hakan yasa ta shiga ƙoƙarin ƙwace hannun da girgiza kanta, hawaye na gangarowa a idanuwanta, ta zame hannun nata ta tsugunna a ƙasar wajen ta yi sujjada shukuri.

“Allah na gode ma da ka nuna min Sayyadi, kafin ka ɗauki rayuwata! Allah na godema da ka cika min burina na ƙarshe.” Ta gama maganar tana fashewa da kuka, da ƙoƙarin tashi, sai dai kafin ta tashin Sayyadi ya tsugunna a kan ƙafafuwansa, yana zuba gwuiwoyinsa a ƙasa.

“Nahna ke ce kika dawo haka? Nahna ke ce kika zama haka anan wajen?” Ya jefa tambayar yana ƙara kallonta, idanuwansa akwai rauni sosai, hawayen da suka taru a kuncinsa ya samu damar gangarowa daga idanuwansa.

“Ba zan bar duk wadda ke da hannu a dawowarki haka ba, Nahna. Duk wadda ya zama silar zuwanki wajen nan sai na hukuntashi da mafi girman hukunci Nahna.”

Ya yi maganar muryarsa na rawa kamar yadda jikinsa ke rawa.

Kai Hafsa ta girgiza tana jin nauyi da kunyar Sayyadin wadda har take fatan inama a ce ƙasa ta buɗe ta afka cikinta.

Wani sabon darasin da ta ɗauka na rayuwa yana ƙara bijirowa a kanta “A’a Sayyadi. Ni ban damu da wadda ya kawo ni nan wajen ba, asalima da zan ganshi zan gode masa a bisa inganta rayuwata da ya yi. Zuwana nan wajen ya zame min kamar sabon shafi ne na rayuwata da ke ɗauke da haske. Wadda da ace na rayu ne a duniyar ku da ba lallai ace na samu abin da na samu a yau ba Sayyadi.

Akwai tazara mai yawa tsakanin duhu da haske, duhun da ya mamaye zuciyata da kuma naƙasun da ke cikinta, ya zama haske ga rayuwata a yau. Naƙasun da ke gareni ya koma naƙasa ga gaɓɓar jikina.

Ba a samun wani abu mai daraja, har sai an rasa wani abun mai girma, Sayyadi. Rayuwata a nan ta zama tubalin gina rayuwar mutanen da ke wajen nan, Ubangiji ya kutso da haske cikin rayuwata na zamowa silar shiga hasken wasu mutanen. Ƙaddarata mai kyau ce Sayyadi, duk da ina tunanin ban cancanta da samun rahama irin wannan ba.” Ta kai ƙarshen maganar tana kuka da shassheƙa, kuka mai yawa mai tsumma zuciyar duk waɗanda suke wajen. Musamman mutanen sahara da suma suke kuka, saboda a iya tsawon rayuwarsu da ita basu taɓa jin sautin kukanta haka ba, suna dai ganin hawaye a fuskarta amma ba wai mai sauti ba.

Rintse idanuwa Sayyadi ya yi, yana jin abin da ya maƙale a wuyansa yana ƙara tokare masa, yana jin tashin hankalinsa na ƙaruwa, a duk wata kalmar da Nahna zata faɗa tana keta zuciyarsa ne da samun wani masauƙi a cikinta.

“Duk da yadda nake ta fata da burin na samu damar haɗuwa da kai dan na nemi yafiyarka, amma a yanzu da kake gabana sai nake jin kalmar ta yi girma da shafe kalmar haƙurina a gareka, ina jin rashin kunyata ta kai maƙura idan har zan iya buɗe baki na ce ka yafe min.

Sai dai zan baka wani kyakkyawan albishir wadda zai iya zama abu guda ɗaya a gare ni na alkhairi da zaka daɗe kana farin ciki a bisa sanina.

Ka kalli mutanen wajen nan, Sayyadi.”

Ɗago da kallonsa ya yi, yana ganinsu wasu mutane ne dai gasu nan da suturar arziƙi bata wadace su ba, amma yana iya ganin yadda matansu ke sanye da manyan mayafai irin na Hafsa, yana ganin hawaye a fuskokinsu da soyayyar Hafsa da ke tsugunne a gabansu.

“Kafin zuwana wajen nan basu san su waye su ba, basu san inda rayuwarsu ta dosa ba, suna rayuwa ne kamar sakakkun dabbobin da babu mai gyara musu rayuwarsu. Ubangiji ya zaɓe ni ya aiko da ƙaddarata cikinsu. Ya kuma sanya linzamin haskaka rayuwarsu a hannuna, Sayyadi. A dalilina dukka suka musulunta.”

Idanuwansa ya wara yana ƙara kallon mutanen yana kallon Hafsa, wani farin ciki na mamaye ƙuncin da ya ziyarci rayuwarsa tsawon shekaru, yana jin babu wani albishir da aka taɓa yi masa a rayuwarsa sama da wannan albishir ɗin.

Har sai da ya yi dariya hawaye na gangarowa a kan fuskarsa, ya sa tafukan hannunsa ya shafa kyakkyawar fuskarsa, daga bisani ya ɗora hannayen nasa a kan gwuiwarsa yana girgiza kai yana dariya, har kuma a lokacin hawaye bai daina gangarowa a kan fuskarsa ba.

Daga ƙarshe ya sake kallon mutanen garin da aƙalla za su tasamma ɗari da hamsin a yawa.

“Allah al-hakim!” Ya faɗa yana ƙara murmushi “Alhmadulillah ala kullu halin.” Ya faɗa yana kai goshinsa ƙasa yana Sujjada.

Da kallon Hafsa da yake ji kamar ya rungumeta dan farin ciki, amma yanzu ba mallakinsa ba ce, ba shi da iko da hakan.

“Wannan ita ce farar igiyar ƙaddarar da ta kawo ni nan, Sayyadi. A duk lokacin da na kalli mutanen nan sai naji duhun da ya gurɓata rayuwata da nake yawo a cikinsa ya zame min farin haske a sabuwar duniyata, duk da ban same shi da sauƙi ba, har sai da na ƙetare sarƙaƙiya da kwazazzabai.”

Hawayen Fuskarsa ya share yana ƙara murmushi a fuskarsa “Ke dama can alkhairi ce Nahna, bakya faɗan abin da ba gaskiya ba ne a komai na rayuwarki. Koda sau ɗaya ban taɓa riƙe ki a raina ba, kowata rana ina uzuri da fatan alkhairi a gareki Nahna. Kin bani alkhairanki da yawa, kin kuma sanar da ni abubuwa da yawa.

Na ɗauka idan na rabu da ke za ki samu farin ciki, na ɗauka idan na rabu da ke za ki cika burukan da kike so, duk da na raunata zuciyata da yawa Nahna. Amma kuma a ganina hakan adalci ne a gare ki.”

Kansa ya girgiza wani hawayen na zuba a idanuwansa kamar yadda itama nata hawayen ke zuba “Ban cimma abubuwa masu yawa ba a lokacin da kika fita daga rayuwata. Sai dai nakan yi murmushi a duk lokacin da na tuna da ke.

Wata ƙaddarar ta zarta ƙarfin tunanin ɗan Adam, Nahna. Kamar yadda wani baya taɓa haifar ɗan wani, ina da labari a komai na rayuwarki, na sani rabon su Bunayya kaɗai ya isa ya raba tsakanina da ke. Haka kuma ƙaddarar da zata kawo ki nan dan sauya rayuwar mutanen nan kaɗai ta isa ta raba ki da ni.”

Kallonsa ta ke a lokacin da wasu samari biyu suka tako zuwa gabansu, matasan da shekarunsu za su yi goma sha shida, masu kama ɗaya sak da sayyadi.

“Abba wace ce wannan? Me yasa kake kuka a gabanta?” Ta ji sautin muryar ɗaya daga cikin yaran da take fita da sanyi, kai kace muryar Sayyadi ne a shekarun baya da ta barshi.

Kallonta ya yi yana kallon yaran “Nahna, ga yaranki nan, ban faɗa musu komai a kanki ba bayan alkhairinki, wadda har gobe Anna ke yawan basu labarinki. A yau duk abin da na zama na zamane ta dalilinki.”

Da mamaki ta ɗago da idanuwanta ta kalle su, kamar yadda suka suke kallonta, ƙafafuwansu duk a ƙasa suna kallonta “Ummin mu, Abba?” suka yi maganar da mamaki.

Kai ya gyaɗa musu, a lokacin da Hafsa ta ƙame kamar wata status dan mamaki. Kafin ta rarrabe har sun rungumeta ba tare da ƙyama ba. Wani hawaye ya gangaro a idanuwanta a lokacin da ta ji bugun zuciyarta na harbawa a ƙirjin yaran nata.

Bayan mintuna goma. Duk an nutsu su Affawio sun ƙosa da son jin labari, anan Hafsa ta musu bayani ta faɗa musu ko su waye da yaren su.

Jikinsu duk sai ya yi sanyi, domin basa son ko kaɗan Moilewa ta bar su.

Duk da itama bata son hakan “Ba zan iya tafiya na bar su ba Sayyadi. Idan ka je gida ka roƙa min yafiya a wajen Alhaji malam da kuma Adda Halima.”

Kai sayyadi ya girgiza, “Ba zamu barki anan ba Hafsa, akwai dubbanin mutanen da suke son ganinki, ki faɗawa mutanen ki idan sun amince su so mu tafi can tare, za mu kula da rayuwarsu da abubuwan buƙatarsu. Za mu gina musu rayuwa kamar sauran mutane da yardar Allah.”

Da mamaki ta ɗago ta kalli Sayyadin, duk dai tana ganin mutane a kewaye da shi da kuma shigarsa, ita kam mamaki take me ya haɗa shi da kayan sojoji ma? Amma tasan zata samu amsar idan sun je gida.

Faɗawa su Affawio abin da sayyadi yace, nan suka hau murna suna cewa sun amince.
  Daga nan aka cika manyan motocin langruzar da su, dama ba komai ne da su ba asalima suna shan wahala kafin su samu abin da suke kaiwa a bakinsu.

Sai da suka ɗauki hanya ne Hafsa ta fahimci ashe ba ma a ƙasar su ke ba, suna can yankin sudan a wata sahara mai girma.

Mamakinta ya ƙara girmama ta yadda su Sayyadi har suka iya gano inda ta ke.

Shatar Jirgi guda Sayyadi ya ɗauka musu, shi da tawagarsu, kasancewar an san shi da matsayinsa shi yasa ba a damu da dole sauran mutanen sai sun kawo passport na su ba, nasa da na tawagar sojojinsa sun wadatar. Su kam su Affawio sai bin duniyar da kallo suke da mutanen cikinta, basu taɓa tunanin akwai wasu halittu a duniya haka bayan su ba.

Daga nan suka ɗunguma sai Nigeria.
A sokoto jirginsu ya sauƙa, anan kuma sai da ya kai su Affawio wani babban gidan da yake mallakinsa ne. Bayan ya basu suturu masu kyau su da matansu, ya sa Hafsa ta gwada musu yadda za su yi wanka. Anan gidan Sayyadi ya sa yaransa suka ɗauko musu mai gyaran farce da kuma aski aka tsaftace su gaba ɗaya.

Da suka yi wanka su kansu har ba su so fitowa a cikin ruwan ba, duba da yadda ruwa ke musu wahala sosai a lardin su. Bayan sun tsaftace jikinsu kuma a ka kawo musu abinci wadda basu taɓa tunanin akwai abinci irin wannan a rayuwarsu ba. Daga nan aka kawo musu likitoci suka duba lafiyarsu da kuma basu maganannuwa, wasu kam sai da suka musu allurai saboda kashe ƙwayoyin cutar da ake tunanin sun zo da ita.

Daga nan itama Hafsa gida na musamman Sayyadi ya kaita ya batta ita da yaranta suka tayata hira. Sai da ta yi wanka ta sauya mahaukacin kayan da ke jikinta, sannan aka kawo mata abincin, da yaranta suka ci abinci suna ta mata hira da bata labarin Yumnah, da yadda take kama da ita.

Murmushi take wani lokacin ta yi hawaye, ganin yadda suke bata labari cikin farin ciki.

Ta so zuwa gidan Adda Halima da kuma gidan Nasir Nasar, amma sayyadi ya hana, yace zai kaita amma sai ta samu dama dama ta dawo kamarta.

A daddafe ta yi mako biyu, wadda ita kanta ta san fatarta ta ɗan gyaru, baƙi da kircin da ke jikin fatarta duk ya fita, haka idanuwanta sun ɗa fito, duk da cewar har a lokacin akwai rama da baƙin. Wai danma su Hassan na kawo mata sabulan gyaran fata da kuma mayuka masu tsada, sai abincin da ke gina jiki.

Lokaci da ta cika sati biyu sayyadi ya zo ya ɗauketa suka tafi jega ita da tawagar mutanenta na Sahara. Wadda tsabar sauyawar da kulawar da suka samu sai da ta so kasa gane su.

Kai tsaye taga sun nufi gidan Alhaji Malam, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa tana harbawa da ƙarfi.

A lokacin da motarsu ta tsaya Sayyadi da kansa ya taho ya buɗe mata mota ta fito, tana dogara sandarta.

Idanuwanta a ƙasa tana jin wani sabon rauni da kunya na mamaye zuciyarta, a lokacin da mutanen da suka zo da ita Sayyadi ya nuna musu wata ƙatuwar rumfa da tabarmi yace su zauna.

Daga nan suka ɗunguma cikin gidan, da mamakin Hafsa taga ƙaton falon Alhaji Malam a cike da mutane, wadda hakan ya so ya tsorata ta kasa shiga.

Sai dai Sayyadi da ke bayanta ya girgiza mata kai, ya na ƙwarara mata gwuiwa, hakan yasa ta shiga da sallama a bakinta, hakan yasa mutanen wajen duk suka miƙe duna kai kallonsu ga mai sallamar.

“Hafsa!” Suka faɗa da tsananin mamaki suna miƙewa tsaye. Bata iya ɗarasawa cikin falon ba ƙafarta ta fara karkarwa nan take ta zube a wajen tana kuka.

So take ta ce su yi haƙuri su yafe mata, amma kuma ta ina zata fara, wa zata fara neman yafiyarsa a cikinsu.

Alhaji malam, ko ummanta ko kuma Adda Halima da ta gasawa aya a a
hannu, ko kuwa dai matan mahaifinta da ta gama raba musu rashin darajarta.

“Hafsatuna ke ce wannan? Ke ce yau a gabana a raye?” Ta ji muryar Alhaji Malam ta dira a kunnuwanta, muryarsa da take ɗauke da rawa da sauti mai amo. 

Hakan ya bata ƙwarin gwuiwar ɗago da kanta ta kalle shi, sai taga ya ƙara mata tsufa, ya kuma rame sosai da sosai, fuskarsa ta zurma furfura ta cika ta.

“Allah na godema da baka ɗauki rayuwata ba har sai da Hafsatu ta dawo gare ni.” Ya yi maganar yana ɗaga hannunsa sama.

Hakan yasa Hafsa yin rarrafe ta ƙarasa kusa da shi tana ɗora kanta a kan cinyarsa “Dan Allah Alhaji Malam ka yi haƙuri ka yafe min a bisa abin da na aikata ma a baya. Dan Allah ka yafe min ba dan halina ba.” Ta yi maganar tana ƙara fashewa da kuka.

Wadda ya ƙara bawa mutanen mamaki “Oh duniya yanzu Hafsatu ce ta dawo haka?” Sautin muryar Gwaggo faɗim ta fito sai kuma ta ƙara fashewa da kuka.

Shafa kanta Alhaji Malam ya yi, yana ƙoƙarin ɗauko duk wata sauran dauriyar da ta rage masa “Na daɗe da yafe miki Hafsatu. Domin ban taɓa riƙe ki a raina ba, duk lokacin da kika min abu ina kawar da kai da nema miki shiriyar Ubangiji.

Na san na yi kuskure a baya, kuskuren da kike ganin ya zama tawaya da rashin adalci a gare ni. Har kika haɗa jimlar maza kika musu kuɗin goro. 

Abin da kika gaza fahimta shine, ni ɗan Adam ne, kuma ajizi mai mantuwa da kuma zuciya a ƙirjinsa. Abin da na aikata ni da kaina nasan ban yi daidai ba, amma kuma ya zama cikin ƙaddarata, musamman idan kika yi duba da yaran da mahaifiyarki ta haifa a bayan rabuwar mu. Wani baya zama mahaifin wani, kamar yadda rabon wani zai iya kashe mutum idan har ya so danne shi. 

Hafsatu kin san mai ake nufi da kaidin mace kuwa? Nasan kin sani saboda ke kanki kin shimfiɗar da kaidin mai yawa, kin kuma ɗaukarwa mahaifiyarki fansa a kan matar da ta raba aurenta.

Amma me yasa duk da hakan da kika yi kika kasa dakatar da kanki da kwantar da hankalinki a kan mijin ki? Amsar saboda hankalinki bai cika mizani ba. Bakya sauraron zuciyarki a lokacin da kike shirin aikata kuskure. Na sani ba son kowanne uba bane ya samu balagurbi a cikin yaransa. Sai dai da yawan lokuta Allah baya haɗawa mutum goma dole sai ya jarrabe shi a kan wani abu da ya ke mafi soyuwa a gare shi. Na so ki fiye da sauran yarana, sai kuma a ka jarrabe ni da fitinarki, shi yasa na ɗauke ki a matsayin jarrabawata na kuma godewa Allah a bisa hakan. Na yafe miki Hafsatu.”

Kuka ne ya ƙara kwace mata a yayin da mutanen falon suke gyaɗa kawunansu, su kansu sun sheda mahaifinsu na son Hafsa, musamman a komai nasa yakan kirata, a lokacin da aka ce ta ɓata kuwa sai da ya yanke jiki ya faɗi, tsawon wata guda ya yi kwance a gadon asibiti. Kafin a sallamo shi, shima yau fari gobe tsumma.

“Na gode Abba, ina roƙon ka nema min yafiyar Umma na da Adda Halima, da yaya ado da matanka da kowa da kowa.”

“Ba ki min komai ba Hafsa, idan ma kin min na daɗe da yafe miki.” Umma ta faɗa tana matse hawayenta.

Yaya Ado ma cewa ya yi “Na yafe miki Hafsa. Allah ya ƙara shiryar da mu.”

Haka sauran matan Alhaji malam da yaran gidan suka ce sun yafe mata.

Adda Halima ce ta taso tana sanye da wani haɗaɗen leshi a jikinta da awarwaraye masu kyau da tsada, ta rungume tsugunna a gaban Hafsa tana haɗe hannayensu waje ɗaya.

“Babu nasara a rayuwa muddum babu ƙalubale. Babu jin daɗi a rayuwa mutuƙar babu dangin da za su rufarwa jin daɗinka baya.

Kin san me yasa ake cewa JINI YA TSAGA? Saboda FATA TA CIZA a tsakanin haɗuwar jininmu akwai tsagawar fatarmu  ta zamowa dangi ɗaya ahali ɗaya. Sai kika zama ZINARE A CIKIN TAGULLA(New book na mai dambu da zai zo muku) a cikin dukka danginmu da ma waɗanda zama ya haɗa ku da shi.

Kina faɗa masa gaskiya koda baya so, daga ƙarshe na fahimci gaskiyar da kike faɗa min, na kuma amsheta na kuma ga amfaninta. A yau mutane suna martaba ni, saboda dogaro da kaina, da kuma amfani da gumin halak ɗina. Na daina tsugunnawa a gaban kowa da ƙaramar murya a kan ya taimaka min. Yanzu ni ke taimakawa wani. Na gode da sadaukarwarki gare ni, na kuma gode da abubuwan da kika min na sauya rayuwata.” Daga haka ta rungume ta tana hawaye.

Gyaran murya ta ji a gabanta, wadda hakan yasa ta ɗago, kafin ta ankare taga an turo wani mutum a kan keken guragu, kansa a langare yawu na zuba a bakinsa.

Sai kuma a bayansa taga Zahra Bukar ita da yaranta. Tsugunnawa ta yi gaban Hafsa tana rungumeta.

“Ashe da rabon zan ƙara ganinki?” Ta yi maganar tana hawaye.

Daga nan ta nuna mata wadda ke kan keken guragun “Kinga yadda rayuwa ke yi da mutum Hafsa. Kinga yadda girman hakki ya mayar da Nasir Nasar. Yau babu kuɗi babu dukiya babu ‘yan matan da yake aura yana saki.”

Ido Hafsa ta ƙwalalo tana ganin Nasir ɗin da tsananin mamaki ya daskarar da ita.

“Tun bayan da ya kai ki ya haɗaki da wasu mutane, ya dawo gida, hankalina yaƙi kwanciya, na ke tambayarsa ina kike, yaƙi faɗa min, daga nan na rufe kaina na daina shiga harkarsa, duk da yana kawo min farauta na son kusantata.

Ganin an ɗauki sati biyu babu labarinki yasa na nemi addireshinki na nan na zo na sanar da halin da ake ciki. Daga nan aka yi sa’a General Abdulmannan yana nan, nan take ya biyo ni yasa yaransa suka kama Nasir, aka fara tuhumarsa, daga nan ya sheda musu yasa a kaiki ƙauyen Niger.

Da aka shiga bincike sai aka gano bakya nan, da ƙyar aka gano yaran da suka kai ki can. wadda kafin a same su Nasir ya jikkata. Ashe dukkan da sojojin suka masa ya illata ƙafafuwansa, sannan kuma dama maganin da yake sha ya riga da ya illata sassan jikinsa. Wadda har ya kai da hantarsa ta raunata.

Daga nan muka shiga neman magani kuma har kuɗaɗenmu ya ƙare duk abin da ya mallaka ya ƙare, sai dai an yi nasara gashi nan, Hafsa. Idan kin so ki yafe masa, idan baki so ba kuma kada ki yafe masa, dama ya riga da ya sake ki tun a lokacin da jami’an sojojin suka kamashi.”

Kai Hafsa ta gyaɗa tana share hawayenta, ashe nata mai sauƙi ne? Ashe rayuwarta akwai haske mai yawa.

Kai ta girgiza tana share hawayenta “Babu rayuwa mutuƙar babu yafiya a cikinta Zahra. Idan har ke da kika ɗauki ƙunci a rayuwar Nasir kika dube shi a yanzu kika yafe masa, to babu abin da zai hana Hafsat Kamaludden yafe masa. 

Wallahi na yafe masa Zahra, domin nima iyayena da ‘yan uwana da mijin dana cuta duk sun yafe min. Na kuma amshi abin da ya faru a gare ni a matsayin sabon haske da ya kutso rayuwata. Tabbas nawa labarin ya yi kyau ya kuma tsarkaka duk da na rasa ƙafata da hannuna…”

Daga nan ta basu labarin abin da ya faru hadda mutanen da ta musuluntar wadda suka dawo tare. Kabbara sosai ake a wajen wadda farin ciki ya mamaye ƙuncinsu.

Daga nan suka tashi suka nufi waje dan ganin mutanen, zuciyar Alhaji Malam ta girgiza da tsananin farin ciki, har sai da ya rungume Hafsa.

Anan AbdulMannan ya nemi a bashi auren Hafsa. Nan take  kuwa aka ɗaura auren nasu.

Murna a wajen Anna ba a magana, domin tana wajen ita tasan Hafsa ce farin cikin ɗanta, wadda tun bayan rabuwarsu ya je ya shiga aikin soja, kuma ya ƙi yarda da maganar kowata mace, ashe rabon Hafsa zata dawo rayuwarsa ne.

Sai da ta yi mako biyu a gida ta ɗara warwarewa daga nan ta tare gidanta, bayan ta kaiwa yaranta su Bunayya ziyara, ta kuma nemi yafiyar dangin mahaifinta, sayyadi ya roƙi alfarmar a basu yaran su dawo da su gida. Ba su musa ba suka basu saboda sun san waye Abdul Mannan ba iya soja ba, shine babban malamin da ake ji da shi a ƙasar.

Sayyadi ya so fita da Hafsa ƙasar waje dan a duba ƙafarta, amma ta ƙi tace ya bar mata ƙafarta domin hakan zai sa ta ƙara tsarkaka da imaninta. Duk da dai bai so ba, sai da ya kaita  ƙasar India, likitoci suka tabbatar masa da ƙafarta ba zata gyaru ba, duba da yadda ƙasusuwanta suka yi rugu-rugu, amma hannunta an yi nasarar yi mata aikinsa. Sai dai za a iya cire ƙafar a mata ta katako. Tace haram a barta da ƙafarta har mutuwa.

Dole Sayyadi ya haƙura suka dawo gida, zuciyoyinsu cike da farin cikin gyaruwar hannunta.

Soyayya mai tsafta yake nuna mata, duk da tana ta ɗari ɗari da shi.

“Nifa Nahna ta nake so ba wannan Salihar Hafsa ba. Ina son Nahnata mai cike da izza da alfahari, ba Sayyada Hafsa ba. Dan Allah ki tafi ki dawo min da Nahna ta.”

Kai Hafsa ta girgiza “Nahna ta daɗe da mutuwa Sayyadi. Kamar yadda ba a ɓari a kwashe duka, haka Nahna ta zube babu birbiɗinta.”

Dariya sosai ya yi yana rungumeta “Alhamdulillah burina ya cika, zan rayu da ke har hayan mutuwa..”

Idanuwanta ta lumshe hawaye na gangarowa a idanuwanta tana godiya ga Allah da ya ƙaddari rayuwarta tare da sayyadi har bayan mutuwa.

*****
Alhamdulillah.
Laifin daɗi ƙarewa, Anan na kawo ƙarshen littafina mai suna JINI YA TSAGA… Ina roƙon Allah yasa kun ƙaru da darrusan da ke cikinsa, kuskuren kuma da na yi ina roƙon Allah ya yafe min.

Na sani akwai wasu abubuwa da yawa a labarin wadda basu muku daidai ba, wataƙila zuciyarku ta ɓaci. Amma ku sani babu wata rayuwa da bata rabuwa da kuskure da ƙalubale. Wani sashe na rayuwar Hafsa a gaske ne ya faru, wani kuma ado ne da kwalliya dan ƙawata labarin.

Ina fatan kun nishaɗantu, ga duk wadda na ɓatawa rai kuma ina bashi haƙuri da neman yafiyarsa.

Sai kun sake jina a sabon littafinmu mai suna *ƘAWATA CE!* Ina fatan za ku bibiyi labarin, za ku so shi fiye da wannan, domin akwai abubuwa masu yawa a cikinsa na faranta rai.

Na gode. Ina jiran gyara gyara da ƙorafi da kuma sharhi ga duk wadda ya ga wani abu wadda bai masa ba. Ƙofata a buɗe take ina maraba kuma da gyaran.

<< Jini Ya Tsaga 40

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×