Skip to content
Part 6 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Hannunsa ya bi da kallo yana tuna adadin ƙonewar da ya yi, da kuma yankewar da ya yi, amma wai duk da haka Hafsat bata ga ba, sai cewa ta yi “Zai kashe ta?”

Dankalin ya ɗauka ya kai bakinsa, bai ji komi a tare da shi ba bayan garɗin da ke gare shi, ƙonewar da yayi bai rage shi da daɗinsa ba sai ma ƙara masa ƙamshi da ya yi.

Haka ya haɗa da yaga ƙwan ya kai bakinsa, shi ne ma dai babu ɗanɗanon komi a cikinsa amma kuma bai ji ƙarnin da zai iya hana mutum cinsa ba kamar yanda Hafsa ta ke iƙirari.

Yanzu kam ya ƙara lura Hafsa ba irin matan da ake musu gwaninta su gode ba ne, ita tana daga sahun matan da suke da gwaliya, da kuma ganin tawayar abu su magantu a kansa.

Duk yanda yake jin yunwa da son cin abincin sai yaji ya fuce masa a rai, hakan ya sa ya ture ya tashi ya nufi ɗakin Hafsa, ya tarar da ita zaune akan kujera ta lumshe idanuwanta, kanta na jikin kujerar a kwance.

“Da kika ƙin abinci na yi tunanin kina shirin girka wani ne?”

Idanuwanta ta buɗe tana kallon sa sai kuma murmushi ya suɓuce mata akan kyakkyawar fuskarta “Wata amarya ka taɓa ganin ta yi girki washe garin kaita gidanta?

Sai ni da aka liƙama malami ne zan shiga saboda gidana yana da ban-banci da nasu?”

“Me ki ke son faɗa Hafsat?” Ya tambayeta da sanyin muryarsa.

Tashi ta yi tsage a kan ƙafafuwanta idanuwanta akansa “Ina nufin abun da na faɗa Abdul. Ni da sauran amaren ba mu da ban-banci, ta iyu ma su fini samun ɗaga ƙafa daga mazansu, amma kai sai da ka kunce min duk wasu notunan da aka ɗaura mun a jikina, ka kuma rugurguza abubuwan da na daɗe ina killace su.

Sannan yanzu ka zo ka ce na shiga madafa na yi girki, dan rashin tausayi irin naka! Ko dan kai daɗin ka ji ba wuya ba shi yasa kake tunanin nima hakan ne?” Ta ƙarasa maganar tana ƙif-ƙifta ƙananun idanuwanta.

Idonsa ya lumshe ya buɗe yana jin zuciyarsa ba daɗi, kalmar rashin adalcin da ta danganta shi da ita su suka fi komi tsaya masa a rai.

“Yanzu ya ki ke so ayi?” Ya faɗa cikin sanyin muryarsa.

Idonta ta wurga sama zuwa gefe tana jin takaicinsa na ƙara lulluɓai shi “Ka je ka girka min wani abincin, ko kuma ka samo min wani. Kai ko maganin ɓarnar da ka min baka nemo min ba! Ko da yake abinci ma baka bani ba ta ya zaka nemo min magani.” Ta yi maganar tana turo baki da zama akan kujerar ta haɗe kanta, da gwuiwa tana kukan da bashi da maraba da na sangarci.

“Yi haƙuri bari naje na girka miki wani abun. Ni ban iya girki ba, ban san ya ake yiba? Umma na bata raye da na tabbata da yanzu an kawo min daga gida.” Ya yi maganar cikin sanyin muryarsa.

“Dan kana maraya shine kake so ka hora ni da yunwa? Naga ko ‘ya ‘yan hawainiya suka futo duniya suna neman abinci dan su rayu.”

Kai ya gyaɗa sannan ya sake futa zuwa kitchen zuciyarsa ba daɗi, shi bai san me zai girka musu ba, asali shi ba mutum ne da ya damu da cin abinci ba, domin ya fi buƙatar shayi da kayan marmari.

Wayansa ya ɗako ya fara tunanin wa zai kira, wannan abun takaici da yawa ya ke. Wai dama haka auren ya ke? Ya tambayi zuciyarsa, da kuma neman wanda zai bashi amsa, a matsayinsa na masani yasan suna ɗaya daga masu yin da’awar maza su kula da mata su tausaya musu.

Shi kullum cikin nuna muhimmancin mata yake ga mazajensu kasancewar su ne ƙashin bayan al’umma.

Kenan hakan na nufin Hafsat bata da laifin duk abin da ta aikata masa, shi kansa ya yi mamakin yanda ya wahalar da ita a daren jiya.

Google ya shiga yayi searching ɗin girki, anan ya ga yanda ake yi da kuma yanda zai yi.

Abu mai sauƙi ya zaɓa ya musu jalof ɗin taliya da makaro ni, ya haɗa da kifi sadin, sai kayan haɗin da ya yi amfani da shi, yanzu kam ya yi a hankali dan bai bari ya yanke jikinsa ba kamar yanda ya yi a farko.

Shi kansa ya gamsu da girkin nasa, tun daga kan yanayin ƙamshinsa da ya cika masa hanci.

“Wannan ma sabon ilmi ne.” Ya faɗa yana murmushi da shafa sajen da ke fuskarsa zuwa gemunsa da bai da tsayi sosai.

Kafin yau bai taɓa tunanin zai iya koyan wani abu wai shi girki ba, domin gani yake ba abu ne da za’a ɓata lokaci wajen koyonsa ba, ashe dai mata na ƙoƙari, ya faɗa yana murmushi.

Sannan ya kashe gas ɗin ya juye abincin a filet ya futo ya jere su akan daining, sannan ya ɗauko musu lemo mai sanyi.

A lokacin ya kalli agogo ya ga sha ɗaya ta yi.

“Ikon Allah duk girkinne yau ya makarar da ni haka?” Ya faɗa yana sake shiga ɗakin Hafsat ya sameta ta yi sabon wanka ya sa riga da siket na kanti, ta zubo da gashinta kanta ɗan kwali sai wani ɗan ƙyalle da ta rufe kan nata da shi.

“Masha Allah! Komi naki mai kyau ne Hafsat. Kayan sun amshe ki sosai!” Ya faɗa yana ɗaga hannunsa da alamun dai ta yi kyau ɗin.

“Abdul har yanzu baka fahimci cewar kyau na ne ya ke amsar ko wani kaya ba? Ka kalla da kyau ƙirar jikin da ke gare ni ce ke tafiyar da kyau ga kayan da ya shige su.”

Dariya ya yi har fararen haƙoransa suka bayyana “Kina da kyau kema, amma ni bani damuwa da kyanki kamar yanda kike zuzuta shi. Nasan ke mai kyau ce, domin duk gidanku babu wanda ba shi da kyau ɗin.

Amma abun da nake buƙata a gareki ilimin da kike da shi. Abincin ya kammala ya kamata ki zo ki ci kada ki sake min ƙorafi akan na barki da yunwa.”

Ya faɗa yana ruƙo hannunta, ta na binsa da kallo  “Kai ne kake cewa baka damu da kyau na ba? Bayan ko wani lokaci kana ambarta sa.

Ni fa a duniya bani son ƙumbiya-ƙumbiya da yima abu kwaskwarima akan faɗarsa, ka futo sak mutum ka yabe ni ba sai kana kauce wa ba.”

Murmushi ya yi, sannan ya ja mata kujera ta zauna, ya miƙa mata filet ɗin abincin, tun a ido jalof ɗin ta burgeta, haka kuma ƙamshinta ya doki hancinta, tuni wata makararriyar yunwarta ta fara hautsinawa sama.

Yamutsa fuska ta yi ta fara juya cokalin kamar ba zata ci ba “Yau ina ga rayuwa ni Hafsat. Ranar farkona a gidan mijina an bani taliya jalof a matsayin abincin kari!” Ta ƙarasa  maganar tana kai abincin bakinta, duk da ya mata daɗi ƙwarai hakan bai sa ta nuna a fuska ba.

“Maza sukan kasance babbar kyauta ga matayensu, bangon da suka jingina dan su tsayu akan ƙafafuwansu. Sai dai ni bana jin nawa bangon yana da ƙarkon da zai iya bari na karu a jikinsa. Daga yanda ya amshe baƙuntata har zuwa abin da ya bani a matsayin kyautarsa a gareni. Ƙonannun dankali da waina mai ƙarni. Ga kuma taliya gama gari. ” Ta faɗa tana kaiwa cokalin bakinta.

Da kallo ya ke binta ya haɗe hannayensa waje ɗaya, yana nazarin amsar da zai bata dan ya mayar mata da raddin maganarta.

Hannunsa ya bi da kallo yana tuna adadin ƙonewar da ya yi, da kuma yankewar da ya yi, amma wai duk da haka Hafsat bata ga ba, sai cewa ta yi “Zai kashe ta?”
Dankalin ya ɗauka ya kai bakinsa, bai ji komi a tare da shi ba bayan garɗin da ke gare shi, ƙonewar da yayi bai rage shi da daɗinsa ba sai ma ƙara masa ƙamshi da ya yi.

Haka ya haɗa da yaga ƙwan ya kai bakinsa, shi ne ma dai babu ɗanɗanon komi a cikinsa amma kuma bai ji ƙarnin da zai iya hana mutum cinsa ba kamar yanda Hafsa ta ke iƙirari.

Yanzu kam ya ƙara lura Hafsa ba irin matan da ake musu gwaninta su gode ba ne, ita tana daga sahun matan da suke da gwaliya, da kuma ganin tawayar abu su magantu a kansa.

Duk yanda yake jin yunwa da son cin abincin sai yaji ya fuce masa a rai, hakan ya sa ya ture ya tashi ya nufi ɗakin Hafsa, ya tarar da ita zaune akan kujera ta lumshe idanuwanta, kanta na jikin kujerar a kwance.

“Da kika ƙin abinci na yi tunanin kina shirin girka wani ne?”

Idanuwanta ta buɗe tana kallon sa sai kuma murmushi ya suɓuce mata akan kyakkyawar fuskarta “Wata amarya ka taɓa ganin ta yi girki washe garin kaita gidanta?

Sai ni da aka liƙama malami ne zan shiga saboda gidana yana da ban-banci da nasu?”

“Me ki ke son faɗa Hafsat?” Ya tambayeta da sanyin muryarsa.

Tashi ta yi tsage a kan ƙafafuwanta idanuwanta akansa “Ina nufin abun da na faɗa Abdul. Ni da sauran amaren ba mu da ban-banci, ta iyu ma su fini samun ɗaga ƙafa daga mazansu, amma kai sai da ka kunce min duk wasu notunan da aka ɗaura mun a jikina, ka kuma rugurguza abubuwan da na daɗe ina killace su.

Sannan yanzu ka zo ka ce na shiga madafa na yi girki, dan rashin tausayi irin naka! Ko dan kai daɗin ka ji ba wuya ba shi yasa kake tunanin nima hakan ne?” Ta ƙarasa maganar tana ƙif-ƙifta ƙananun idanuwanta.

Idonsa ya lumshe ya buɗe yana jin zuciyarsa ba daɗi, kalmar rashin adalcin da ta danganta shi da ita su suka fi komi tsaya masa a rai.

“Yanzu ya ki ke so ayi?” Ya faɗa cikin sanyin muryarsa.

Idonta ta wurga sama zuwa gefe tana jin takaicinsa na ƙara lulluɓai shi “Ka je ka girka min wani abincin, ko kuma ka samo min wani. Kai ko maganin ɓarnar da ka min baka nemo min ba! Ko da yake abinci ma baka bani ba ta ya zaka nemo min magani.” Ta yi maganar tana turo baki da zama akan kujerar ta haɗe kanta, da gwuiwa tana kukan da bashi da maraba da na sangarci.”Yi haƙuri bari naje na girka miki wani abun. Ni ban iya girki ba, ban san ya ake yiba? Umma na bata raye da na tabbata da yanzu an kawo min daga gida.” Ya yi maganar cikin sanyin muryarsa.

“Dan kana maraya shine kake so ka hora ni da yunwa? Naga ko ‘ya ‘yan hawainiya suka futo duniya suna neman abinci dan su rayu.”

Kai ya gyaɗa sannan ya sake futa zuwa kitchen zuciyarsa ba daɗi, shi bai san me zai girka musu ba, asali shi ba mutum ne da ya damu da cin abinci ba, domin ya fi buƙatar shayi da kayan marmari.

Wayansa ya ɗako ya fara tunanin wa zai kira, wannan abun takaici da yawa ya ke. Wai dama haka auren ya ke? Ya tambayi zuciyarsa, da kuma neman wanda zai bashi amsa, a matsayinsa na masani yasan suna ɗaya daga masu yin da’awar maza su kula da mata su tausaya musu.

Shi kullum cikin nuna muhimmancin mata yake ga mazajensu kasancewar su ne ƙashin bayan al’umma.

Kenan hakan na nufin Hafsat bata da laifin duk abin da ta aikata masa, shi kansa ya yi mamakin yanda ya wahalar da ita a daren jiya.

Google ya shiga yayi searching ɗin girki, anan ya ga yanda ake yi da kuma yanda zai yi.

Abu mai sauƙi ya zaɓa ya musu jalof ɗin taliya da makaro ni, ya haɗa da kifi sadin, sai kayan haɗin da ya yi amfani da shi, yanzu kam ya yi a hankali dan bai bari ya yanke jikinsa ba kamar yanda ya yi a farko.

Shi kansa ya gamsu da girkin nasa, tun daga kan yanayin ƙamshinsa da ya cika masa hanci.

“Wannan ma sabon ilmi ne.” Ya faɗa yana murmushi da shafa sajen da ke fuskarsa zuwa gemunsa da bai da tsayi sosai.
Kafin yau bai taɓa tunanin zai iya koyan wani abu wai shi girki ba, domin gani yake ba abu ne da za’a ɓata lokaci wajen koyonsa ba, ashe dai mata na ƙoƙari, ya faɗa yana murmushi.

Sannan ya kashe gas ɗin ya juye abincin a filet ya futo ya jere su akan daining, sannan ya ɗauko musu lemo mai sanyi.

A lokacin ya kalli agogo ya ga sha ɗaya ta yi.

“Ikon Allah duk girkinne yau ya makarar da ni haka?” Ya faɗa yana sake shiga ɗakin Hafsat ya sameta ta yi sabon wanka ya sa riga da siket na kanti, ta zubo da gashinta kanta ɗan kwali sai wani ɗan ƙyalle da ta rufe kan nata da shi.

“Masha Allah! Komi naki mai kyau ne Hafsat. Kayan sun amshe ki sosai!” Ya faɗa yana ɗaga hannunsa da alamun dai ta yi kyau ɗin.

“Abdul har yanzu baka fahimci cewar kyau na ne ya ke amsar ko wani kaya ba? Ka kalla da kyau ƙirar jikin da ke gare ni ce ke tafiyar da kyau ga kayan da ya shige su.”

Dariya ya yi har fararen haƙoransa suka bayyana “Kina da kyau kema, amma ni bani damuwa da kyanki kamar yanda kike zuzuta shi. Nasan ke mai kyau ce, domin duk gidanku babu wanda ba shi da kyau ɗin.

Amma abun da nake buƙata a gareki ilimin da kike da shi. Abincin ya kammala ya kamata ki zo ki ci kada ki sake min ƙorafi akan na barki da yunwa.”

Ya faɗa yana ruƙo hannunta, ta na binsa da kallo  “Kai ne kake cewa baka damu da kyau na ba? Bayan ko wani lokaci kana ambarta sa.

Ni fa a duniya bani son ƙumbiya-ƙumbiya da yima abu kwaskwarima akan faɗarsa, ka futo sak mutum ka yabe ni ba sai kana kauce wa ba.”

Murmushi ya yi, sannan ya ja mata kujera ta zauna, ya miƙa mata filet ɗin abincin, tun a ido jalof ɗin ta burgeta, haka kuma ƙamshinta ya doki hancinta, tuni wata makararriyar yunwarta ta fara hautsinawa sama.

Yamutsa fuska ta yi ta fara juya cokalin kamar ba zata ci ba “Yau ina ga rayuwa ni Hafsat. Ranar farkona a gidan mijina an bani taliya jalof a matsayin abincin kari!” Ta ƙarasa  maganar tana kai abincin bakinta, duk da ya mata daɗi ƙwarai hakan bai sa ta nuna a fuska ba.

“Maza sukan kasance babbar kyauta ga matayensu, bangon da suka jingina dan su tsayu akan ƙafafuwansu. Sai dai ni bana jin nawa bangon yana da ƙarkon da zai iya bari na karu a jikinsa. Daga yanda ya amshe baƙuntata har zuwa abin da ya bani a matsayin kyautarsa a gareni. Ƙonannun dankali da waina mai ƙarni. Ga kuma taliya gama gari. ” Ta faɗa tana kaiwa cokalin bakinta.

Da kallo ya ke binta ya haɗe hannayensa waje ɗaya, yana nazarin amsar da zai bata dan ya mayar mata da raddin maganarta.

<< Jini Ya Tsaga 5Jini Ya Tsaga 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×