“Wannan itace godiyar da zaki min? Ko kuma wannnan shine kalar naki santin? Ki dai ci a hankali, kada daɗinsa ya ɗebeki har ki ƙwarai.” Ya gama maganar yana murmushi da lumshe mata idanuwansa.
Ɗago da kanta ta yi, tana kallonsa, ta sha jin ana cewa maza suna da saurin tashi da hassala idan mace ta kushe su, amma bata ga hakan ga Abdul-Mannan ba, domin shi ko alamun jin haushin kalamanta bai yi ba, balle ta samu wata ƙofar da zai nuna mata ta yi nasara akan sa.
“Kana so kace baka ji haushin abin da na maka ba? Ko kuma so kake kace baka gane inda na dosa ba?”
Kafaɗarsa ya ɗaga sannan ya taɓe bakinsa “Kin san ni bana iya rarrabe tsakanin magana mai daɗi da akasinta. Musamman idan a bakin mace ta futo, balle kuma matar da ta yi kwana ɗaya tal a gidan mijinta.
Ko wata maganarki mai daɗi ce da sanyi a gare ni Hafsat. Ba yan haka bana jin kunnuwana sun ji wani abu mai rauni a cikinsa.”
Ya ƙarasa maganar yana lumshe idanuwansa da kuma kai loma bakinsa, yana gyaɗa kai.
“Abun da mamaki ace Malam Abdul-Mannan ne ya girka wannan haɗaɗɗiyar taliyar. To amma idan aka duba cewar girkinsa na farko ga haɗaɗɗiyar amaryarsa ne, wannan abin a jinjina min ne. A kuma yi koyi da ni.” Ya sake maganar yana kurɓar ruwan shayi mai ɗumi kasancewarsa ma’abocin shan baƙin shayi.
“Alhamdulillah ala ni’imatihi ta tumussalihat.”
Ya faɗa yana goge bakinsa da tushin da ke jikin table ɗin, sannan ya miƙe ya risina a dai-dai kunnuwanta.
“Mata rahama ne ga mazajensu Hafsa, su ne kuma babbar kyautar da Allah kan bamu a duk tsawon rayuwar mu.
A yayin da suka kasance uwaye a garemu da mataye, sannan masu hidima ga yaranmu. Su ɗin ne dai ƙashin bayan al’umma gaba ɗayanta. Ba namiji ne yake zama bangon tsayuwa ga mata kaɗa ba, asalin kafuwar katangar tana ga matan da suka tafiya a tare da su.
Ni kawai Abdul ne a tare da ke, ba zan iya zame miki wani abu ba, ba tare da kin ruƙo ƙafafuwana dan na tsayu a kan taku na ba.
Sai dai zan ci gaba da shimfiɗa miki daular farin ciki a rayuwar aurenmu har sai kince ya ishe ki. Zan zama futular da zata haska gabanki, zan baki dukkanin kulawar da ya kamata har sai kinji a ranki cewar ni mijin da ya ke kawo farih ciki ne ga iyalinsa.”
Yana gama faɗar haka ya shige ya barta, yana jin idanuwanta na yawo akansa, yana fatan idanuwan da ke biye da shi su kasance masu aminci a tare da shi.
A kai-a kai yake sauƙar da ajiyar zuciya, dan ya samarwa da zuciyarsa nutsuwa, domin ba kaɗan ba yake jin rashin daɗin kalaman Hafsat da kuma gwale shin da ta ke.
Amma ya danganta hakan da rashin sabo da shaƙuwar da ke tsakaninsu, ya tabbata wata rana zai sauyata.
*****
Kai ta jinjina tana ci gaba da cin abincinta, da ace bata jin yunwa da babu abin da zai sa ta ci abincin, sai dai kuma idan tayi hakan kamar ya ci bulus a kanta, kamar yayi nasara ne a kanta.
Sai da ta cinye cikin filet har da ƙari, sannan ta kora da ruwan lemo. Tana lumshe idanuwanta saboda jin wata shawara da ta zo mata.
A haka ta je ta kunna kallo a Tv da ke falon, abin haushi duk babu wasu toshar da za’a kalli ‘yan zamani masu gwangwajewa, daga Sunna T.V sai Manara da sauran tashoshin wa’azi.
Tashi ta yi ta shiga ɗakin Abdul-Mannan ta tarar da shi yana sa hula akansa, da farin hirami a wuyansa, duka kayan jikinsa farare ne.
Yayi kyau ƙwarai, kamalarsa ta futo rangaɗau, ƙwarjininsa ya haura shekarunsa.
Murmushi ya mata a lokacin da ta ƙaraso ɗakin “Ya aka yi ne Hafsa? Na ga fuskarki da damuwa.”
Idonta ta juya ta shiga yawo da ƙwayar cikinta cikin ƙwarewa irin tata.
“Ina son ganin wani abu na nishaɗin da zai sa na manta da wanda nake zaune ne. Babu komi a gidan nan na farin cikin da mutum zai iya mantawa da abin baƙin cikin da ke damunsa.
Ba zan iya zama a cikin wannan rayuwar ta gidadanci ba Abdul.”
Murmushi ya yi a lokacin da ya gama jin maganarta, sannan ya ɗauko mata Alƙur’anin da ke jikin lokar litattafansa ya ɗaura mata shi akan hannunta.
“Babu wani abin nishaɗin da zaki nema a duniya ba tare da kin same shi anan ba Hafsa.
Komi da kike son sani na rayuwa jin daɗi da zai shagalar da ke ƙuncin da kike ciki zaki same shi anan.”
Sannan ya juya ya ɗauki turarensa ya fesa, da ɗaukan Litattafansa ya shige ya barta.
“Na tafi masallaci, daga nan zan tsaya na yi karatu da ɗalibaina, in sha Allah zuwa yamma zan dawo.”
Shan gabansa ta yi tana kallonsa wanda ya sa shi tsayawa shima yana kallonta.
Idanuwanta ta sake shigar da su ciki “Ranar farkona a gidan naka ne zaka futa tun sha biyu kace ba zaka dawo ba sai Yamma? Idan ka tafi kuma wa zai min abincin ranar, ka dai san bani da lafiya, ƙasusuwana duka basu dawo dai-dai ba balle nace zan yi girki.”
Idonsa ya wara yana kallonta, da mamaki akan fuskarsa “Yanzu har kina maganar wani abincin bayan ko mintu goma baki yi da cin wani ba?”
Idonta ta fiddo waje “Ba dai horon yunwa zaka min a gidanka ba Abdul? Ba dai so kake kace kana rukunin Uztazan da suke haramta cin abinci ba? Ta ya zan iya jure ɗaukan nauyinka a kaina idan har sau biyu zanna cin abinci a rana?
Oh na gane! So kake ka haramta min cin abinci sau uku, saboda kai zaka futa kana ciye-ciyenka a mumbari. Ni ba waliyiya ba ce Abdul. Idan har ba zaka iya ciyar da ni ba, to ba zan iya ci gaba da zama da kai a gidan nan ba.”
Ta ƙarasa maganar tana juyawa da barin ɗakin, kamar soko haka ya tsaya yana binta da kallo bakinsa a buɗe, bai san ta ina zai iya da rikicin Hafsa ba kuma yanzu.
Sai dai kafin ya dawo tunanin da yake, ya hangota janye da jaka tana faman janta.
Da sauri ya ajiye litattafansa a table ya nufeta, ya riƙe jakar.
“Ina zaki da wannan uwar jakar kuma Hafsat?”
“Duniya zan shiga Abdul-mannan. Duniya zan shiga tun kafin ka kashe ni da rai na. Dan nasan ban isa zuwa gida da sunan yaji ba, gara na je inda ba’a san ni ba a amshi baƙunta ta.
Dan wallahi ba zan zauna da ciwo biyu ya kashe ni ba, baƙin cikin aurenka da kuma horon yunwarka.”
“Haba mana Hafsat! Me ya yi zafi abin maganar baki kuma. Shikenan ki yi haƙuri ki maida jakar, idan an idar da sallah zan dawo na miki girkin da kike so kinji.”
Ido ta wurga kamar ba zata juya ba, ganin hakan ya amshi jakarta ya shige da ita ɗakin nata, ya ruƙo hannunta ya zaunar da ita akan kujerar.
“Ki yi haƙuri Noorie, ba zan daɗe ba, ana idar da sallah zan dawo. Zan ba su haƙuri yau ɗaya nasan za su min uzurin basu karatun.
In sha Allah zan zo na girka miki abin da kike so.
Ko kuma na siyo miki wani ne mai kyau a gidan abinci?” Ya ƙarasa maganar yana kwantar da muryarsa.
“Taɓɗijam! Ni Hafsa ce zan ci wani abincin waje? Abincin da ban san su waye suka girka ba? Ai gara na shiga duniya na ga wanda suke yi. Idan ya so na siya da kai na.”
“Shikenan! Abun bai kai haka ba. Zan dawo sai mu shiga tare kina gani ina girka miki ma.”
Idonta ta wurga waje “Yanzu naji batu kam.”
Daga haka ya fuce yabar gidan, yana jin ƙafafuwansa kamar ba za su ci gaba da ɗaukansa ba.
Sai da ta ga fitarsa sannan ta kwashe da dariya.
“Muje dai zuwa! Da kanka zaka gaji ka sake ni, sakarai ko wa ya faɗa masa duk tijarata zan iya shiga duniya? Nasan me zan gani a cikinta.” Ta yi maganar tana bushewa da dariya.
*****
Har ya je sallah ya dawo yana tunanin maganar da suka yi da Hafsa, yana hango ta janye da jaka a matsayin wadda zata bar gidansa.
Kwana ɗaya tal da yin aure ace amaryarsa ta shiga duniya? Wannan magana ce da zata karaɗe duniya ba ma iya garinsu ba.
A haka ya bama ɗalibansa haƙuri da suke jiran ya basu karatu, duk da dama tun farko sun ɗauke masa nauyin karatun nasu har zuwa mako biyu, amma shi ya ce zai iya musu karatu, a cewarsa aure ba zai hana ya musu karatu ba.
Sai gashi Hafsa ta watsa masa ƙasa a ido, wannan abun kunya har ina, kasa jurewa ya yi, sai da ya biya ma manya a cikinsu karatu, sannan yace su ɗaurama wanda suke ƙasa da su.
Ƙirjinsa kuwa na ta luguden bugawa dan bai san me zai je ya tarar a gidan ba. Tun daga ƙofar gida ya fara jiyo sautin kiɗa na tashi a cikin gidan, abun sai ya zame masa wani banbarakwai, da sauri ya ƙarasa cikin gidan tsayawa ya yi cak kamar magijin da baya aiki, domin ganin abun da idanuwansa suke.
Hafsa ya gani cikin ƙananun kaya riga da wando wanda suka ɗameta, tana faman tiƙar rawa da juyawa, gefe guda kuma wasu yara ne maza da mata wanda za su kai su shida suma sai tsalle suke da alama suna ƙoƙarin koyan rawar ne.
“Hasbunallahu wa ni imal wakil!” Ya faɗa yana dafe kansa ‘Kiɗa yau a gidana?’ Ya faɗa a zuciyarsa da neman inda sautin ya ke futa. Ya yi sa’a ya hango wata Sifika da sautin ke tashi a cikinta, ƙarasawa ya yi ya ɗauke ta, bai tsaya duba ta ba ya bugata da ƙasa, nan take ta yi filla-filla da ita sautin kiɗan ya ɗauke.
Tuni yaran suka fara rige-rigen fucewa dan ba su taɓa ganin ɓacin ransa irin na yau ba.
“Taɓɗijam! Mp ɗin nawa ka fasa min? Wallahi sai ka biya ni a bata!” Ta yi maganar da ƙarfi jikinta har rawa yake saboda tsananin futunar da ke cinta.
“Ki yi duk abin da kike son yi Hafsa a gidan nan, zan baki ko wata dama a matsayinki na matar aure da take da cikekken ‘yanci, amma ba zan yarda ki mai da min gida ya koma na ‘yan gala ba. Wannan shine kuskure mafi girma da za ki aikata min.”
Ya ƙarasa maganar da buɗaɗɗiyar muryarsa, idanuwansa duk sun sauya kala zuwa ja, alamun dai ransa ya kai maƙura wajen ɓaci.
“Hehehe! Abun dariya Malam! Wato nishaɗi a gidanka ya zama kuskure, amma kai baka taɓa tunanin aurena da kayi shine mafi girman kuskuren da ka tafka a rayuwarka ba? Bayan rashin cika alƙawalin da ka yi na cewar zaka dawo ka mana abinci, shine ka datse min abin da ya ke ɗebe min kewa ta? Nikam wani laifi na aikata a rayuwata da ƙaddara ta haɗa ni zaman aure da kai?” Ta ƙarasa maganar tana dafe kanta da zama akan kujera.
Jikinsa ne ya yi sanyi ganin hawaye na sauƙa akan kyakkyawan fuskarta, hakan ya sa ya risina a kusa da ita.
“Babu wani abun Nishaɗi a wannan rayuwar Hafsat, face shagala da kuma sawa mu manta abin da ya kawo mu. Duk abun da zaki kira da nishaɗi mutuƙar ba ambaton Allah ba ne a cikinsa to shagala ce da kuma naƙasu a gare mu.
Kina da sani sosai, kin kuma san illar abin da kika aikata, babu buƙatar da zai sa ki zauna da girmanki da iliminki kina ta tiƙar rawa a gaban yara kamar wata ‘yar bori.
Ki kama kanki kafin ki samu a girmamaki.”
Harararsa ta yi daga inda ta ke, tana ji kamar ta kwaɗa masa mari.
“Wato rawar da nake ce ta yi kama da ta ‘yan bori? Indai zan yi rawar ‘yan bori na tabbata kai kanka sai na shigo da kai dandalin rawar.”
Murmushi ya yi sannan ya fara share mata hawayensa “Ni a tunanin duk wanda yake kaɗa jiki da tsalle da sunan rawa yake to inaga rawar bori yake ƙoƙarin kwaikwaya.”
Bige masa hannunsa ta yi daga kan fuskarsa, sannan ta haɗe hannayenta biyu wajen yin tagumi.
“Ina ƙoƙarin korar yunwar da ke tare da ni ne! Ina ƙoƙarin samarwa kaina abin da zai sa na manta da wa nake tare da shi ne! Har yanzu da kake zaune a gabana ban ga alamun zaka bani abincin da zai mantar da hautsinewar da cikina ya ke ba.”
Dafe kansa ya yi sannan ya ruƙo hannunta “Zo mu je a gabanki zan yi girkin ma yau.”
Tirjewa ta yi sannan ta kalli Mp ɗinta shima ya mayar da kallonsa kanta “Nifa na yi rantsuwa akan sai ka biyani.” Ta yi maganar tana ƙara haɗe fuskarta.
Hannunsa ya zura a aljihunsa ya ɗebo kuɗin da bai san nawa ba ne ya bata “Gashi amma bana buƙatar wata irinta.”
Kuɗin ta amsa “Da dama dai! Inaga ka yi girkin ba sai ina gani ba, hakan zai fi birge ni akan ace a gabana ka yi.”
Kai ya gyaɗa mata yana murmushi sannan ya shiga kitchen ɗin, ta bishi da rakiyar harara, tana kwanciya akan doguwar kujerar da ke palon.
Daga kwancen da take ta fara jiyo ƙamshin girkin nasa, ido ta lumshe sannan ta fara haɗiyar yawu.
“Allah dai yasa girkin nan ya yi daɗi kamar yanda yake tashin ƙamshi.”
Tana kwance ta hango shi yana jera kayan abincin a daining sannan ya koma kitchen ɗin, bata san me ya yi ba, sai gani ta yi ya sake futowa ya shige ɗakinsa.
Mintuna goma ta gaji da jiran ya zo ya ce ta taso an gama ta miƙe a lokacin ta ga ya futo sanye da jallabiya a jikinsa, hakan ya ankarar da ita wanka ya yi.
“Masha Allah! Kin tashi ashe? Ina niyar na zo na tada ki.”
“Yunwa dai ta tayar da ni, ace mutum tun abincin safe bai ci komi ba har yanzu wajen ƙarfe uku. Gaskiya ba abu mai wahala da kasada a rayuwa kamar auren riƙeƙƙen ustazu.”
Ta ƙarasa maganar tana ɗingisa ƙafarta “Daɗinta ma dai daga hannun aka futo.”
“Amma kuwa ba irin naka ba Abdu. Domin mu ba’a mana iyaka da abin da za mu ci ko sha.”
Kujera ya ja mata ta zauna sannan ya ɗauko filet ya ajiye a gabanta “Anan ɗinma ba’a miki iyaka da komi ba, kawai lalacinki ne ya sa kika tsaya a sarrafa a baki.”
“Bayan ka farkani kake kirana da malalaciya Abdul? Da tunaninka bayan ɗaukarka da nayi zan amfana wajen cika maka tumbinka na baka damar sake mai-maita mun abin da ka yi? Ashe ma kanwa na kawo garin.”
Dariya ce ta suɓuce masa sai dai bai bari yayi mai yawa ba yayi murmushi ya fara zuba mata farar shinkafa.
Sannan ya ɗauko miyar jajjage da naman kaza ya zuba mata.
“Gaskiya kam, bai ci ace duk wannan abun da ya faru a same ki a gaban tukunya ba. Zai fi dacewa dai ki kasance riƙe da cokali a hannunki.” Ya tura mata abincin gabanta.
“A ido dai ya yi kyau. Farar shinkafa da miyar kaji, Allah yasa babu ƙarninsu.” Ta faɗa tana kaiwa bakinta.
Ido ta lumshe saboda abincin ya mata daɗi sosai, ta tabbata ko ita bata isa ta yi irin miyar ba, amma saboda rigima ta yamutsa fuska.
“Shinkafar ta yi tauri da yawa, kamar tafasa ɗaya aka mata aka tsame, miyar kuma dai babu ɗanɗano mai tashi.” Ta yi maganar har a lokacin tana yamutsa fuska.
Zuba nasa ya yi shima ya zauna yana ci, dan yasan neman magana ne kawai irin na ta.
Ma Sha Allah,