Tana ganinsa ya yi Bismillah ya fara cin abincinsa, ko kaɗan bai tanka mata ba, kamar yanda bai nuna wata alama ta cewar yaji haushin maganar da ta yi ba.
“Ba dan yunwar da nake ji ba, da babu abin da zai sa ni cin wannan tattauran shinkafar da bata da maraba da gari. Ga wata miya mai ɗan banzan ƙarni kai kace albasa ta ƙare a duniya ne.” Ta yi maganar tana yamutsa fuskarta.
Shi dai ruwan lemon da ya haɗa na abarba da lemon zaƙi, ya kurɓa yana murmushi a kan fuskarsa.
Itama lemon ta ɗauka ta kai bakinta, tun da ta kusan ta gare shi ƙamshinsa ke ratsa ƙofofin hancinta, yana kwaɗaita mata son shan sa.
Lokacin da ta kai bakinta taji kunnuwanta har motsawa suke saboda tsananin daɗinsu. Ido ta lumshe tana jin wani abu na yawo a kanta har zuwa ƙafafunta.
Can kuma sai ta ajiye kofin tana jujjuya shi a hannunta “Babu laifi dai a nan gefen, amma ba za a ce ya kai maƙura ba.”
Tashi ya yi saboda ya kammala cin abincin, yana lumshe fararen idonsa da kallon bakinta da baya gajiya da magana.
“Duk wanda ya fiya surutu a lokacin cin abinci, to akwai yiyuwar zai ciza hannunsa saboda daɗin abincin.” Daga haka ya sa kai ya wuce ya barta. Yana jin tana cewa “Allah ya kiyaye na ciji hannuna akan wannan abin. Badan gudun kada yunwa ta hallaka ni ba da ko da wasa ban yi gigin cin abincin ba.”
Sai da ya kai jikin ƙofa sannan ya tsaya yana kallonta “Gaskiya dai kam, yunwa ba Abdul-Mannan ba ce da zata ɗaga miki ƙafa.” Ya yi maganar yana murmushi da shige ɗaki.
Sarai ta gane magana ya faɗa mata, amma sanin idan ta tanka masa kamar ta na ƙara makarar da lokacin ta ne gara, ta ci abincin ta ƙoshi idan ya so ko me za a yi sai a yi daga baya.
Ganin babu idonsa ya sa ta shiga cin abincin da sauri-sauri, tana lumshe idanuwanta “Oh kuma fa ya iya abinci wallahi.” Ta faɗa tana gyaɗa kanta da kurɓan lemon.
Sai da ta cinye tas har da ƙari, jin cikinta na barazanar fashewa ya sa ta tashi ta koma falo ta kunna kallo, sannan ta miƙe a kan kujera tana faman ƙure sautin talabijin ɗin.
So take ta ƙullar da Abdul hakan ya sa ta kai tashar da ake waƙoƙin disko, nan fa gidan ya cika da sauti mai tashi.
Daga can ɗaki kuma Abdul-Mannan yana nazarta wasu litattafain Addini akan shari’a. Sai jin kiɗa na ta shi ya yi kamar zai fasa masa dodon kunnensa.
“Ya Allah!” Ya faɗa yana tashi akan ƙafafuwansa da futa wajen da sautin ke ta shi. A zuciyarsa yana ƙara girmama lamarin mazan da suka shafe shekaru suna tare da matansu, yana ƙidaya adadin wahalar da tasgadon da suka jure kafin su kai wannan lokacin.
Domin ya san ko da magana kaɗai aka bar mutum an barshi da babban aiki.
A hankali ta ke jiyo takunsa tana jin ƙamshin turarensa na mata maraba a hancinta, hakan ya sa ta lumshe idonta tana dai-daita kwanciyarta da ƙara haɗe girarta sama da ƙasa.
“Kada ka kashe min.” Ta faɗa ganin yana ƙoƙarin kashe kayan kallon. Bai saurareta ba ya kashe kayan kallon, sannan ya naɗe ƴar yawon da ke wajen, ya wuce da niyar komawa ɗakin.
Gabansa ta sha tana ƙara shigar da idonta ciki “Me ye hakan zaka kashe min kallo, sannan ka ɗauke min ƴar yawo?”
Raɓawa yayi ta gefenta zai wuce ta sake shan gabansa “Wannan ɗin mallakina ce ai da Babana ya siya min, baka da ikon da zaka sarrafata a duk lokacin da ka so.
Dan haka ka bani abina.” Ta ƙarasa maganar tana miƙa masa hannu.
Hannunta ya bi da kallo yana kallon fuskarta, yi ya yi kamar zai meƙa mata hakan ya sa ta yi murmushin gefen baki. Sai da mamakinta sai ji ta yi an rabata da ƙasa kafin ta yanke magana sai ji ta yi ana tafiya da ita. Ƙananun idanuwanta ta waro ta sauƙe su akan Abdul-Mannan da ya ke ɗauke da ita kamar jaririya.
Bai tsaya ko ina da ita ba sai a kan gado ya wullata.
“Na lura karatun da na miki jiya mai sauƙi ne, saboda na amshi biyan bashin kazata.
Amma kuma zan baki darasi akan duk abin da ya ke naki tuni Abba Malam ya malam ya mallaka min shi. Igiyoyi biyun da suka ratayu tsakaninmu sun bani damar yin kome da abin da yake naki. Idan nace kome ina nufin kome da ya zama na ji da kanki.”
“Taɓɗijam wannan ai abu ne da ba zai taɓa oyu ba, dan an baka aure na ai ba cewa aka yi ka mayar da jikina filin sukuwarka ba. Wai me yasa mafiya yawanku malamai Allahn ku a bakinku ya tsaya, zuciyarku sam babu imanin nan?
Abdul-Mannan kada ka yi gangancin da zai ƙara ruɓanya min tsanarka a zuciyata, kada ka fara ɗaukan wannan abin a matsayin ƙarfin ikon ka a kaina.”
Bai tanka mata ba hakan illa kayan sa da ya cire ganinsa a tsaye yasa ta rintse idanuwanta, tuni jikinta ya shiga rawa tana jin zuciyarta na hautsinewa da ƙoƙarin watso mata da abin da ta ci.
Kafin ta dawo daga lugudan furgicin ta tsinkayi rikitattun hannunsa yana yaga kayan da ke jikinta.
“Abdul Fyaɗe zaka min?” Ta yi maganar da murya mai amo tana matse jikinta har a lokacin idanuwanta a rufe suke.
Bata manta azabar da ta sha ba, wadda bata fatan ta sake shiga irinta. hatta maƙiyinta kuwa tana fatan ya nesanta daga wannan kalar raɗaɗin.
“Naga kamar kin fi son sa ne shi yasa xan miki shi.”
“A’a Abdul kada ka yi haka, sam bai dace da kai ba. Ka tuna kai malami ne, haka kai shugaba ne da kake kare hakkin mata ga mazajen da ke zaluntarsu. Me yasa ba zaka tsaya min ba ka kare ni daga farmakin mugunta irin ta son ɗaukan fansa.”
Murmushi ya yi yana kaiwa hancinsa saitin wuyansa da shaƙar ƙamshin humrar da ta yi amfani da ita “Amma ai kince mu malamai azzalumai ne, kinga kenan babu ta inda zan iya taimaka miki kasancewata Azzalumi a idonki.”
“Ayya mana Abdul kaima kasan ai ba gaskiya ba ne, nasan babu wanda ya kai malamai tausayi da sanin ya kamata.”
“Ban yarda ba.”
“Dan Allah ka yarda Malam Abdul.”
Dariya yayi mai sauti yana girgiza kansa da yaba irin ƙarfin halin Hafsa ɗin. “Buɗe idonki to!” Ya faɗa yana matsayawa da ga kusa da ita.
Kai ta girgiza “Ba zan iya kallonka a haka ba.”
“Idan ba ki buɗe idonki ba zan miki abin da na yi niya.”
Tun kafin ya dire maganarsa ta wara idanuwanta a kansa, da mamakinta sai ganinsa ta yi sanye da wata farar jallabi da hula a kansa irin ta tashi karka dame ni ɗin nan. Kayan ya masa kyau ƙwarai idan ba sani ka yi ba sai kace wani balarabe ne.
Abdul-Mannan kyakkyawa ne na bada misali, domin banda aure da ƙaddara ta san babu ta inda za su haɗa hanya da shi.
Ido ta lumshe tana cuno baki gefe da jin haushin zuciyarta da yake suburbuɗa masa yabo. Domin dai duk kyansa ai a banza tunda ita bata son sa.
“Bana son kiɗa a gidana Hafsat! Ki yi komi da kika ga ya dace da ke, kike kuma so wanda kike son ya ɓata min rai zan ɗauka. Amma kada ki gayyato sheɗan wajen taya kunnuwanki da jin yasasshen sautin da zai ruɗar da ke.
Da kanki zaki iya yin komi da kike so, saboda ke al’umma ce mai kama da kayan ƙarau, duk inda kika motsa sautinsu na fita a kunne, idan kika kuskure kika faɗi kuma sai ya tarwatse.
Ki yi kome da kike son yi amma dan Allah ya tsaya a kaina kada ya shafi kimata.”
Ido ta lumshe tana jin wani abu na yawo a jikinta, tana jin ƙofofin gashinta suna miƙewa. Bata taɓa jin wani namiji ya bata tausayi ba, bata taɓa tunani maganar wani zata yi tasiri haka a zuciyarta ba.
Gashin girarta ta ɗan sosa tana ƙara shigar da idanuwanta a ciki “Idan na fahimci maganarka kana so ka ce min sharrina ya zarta na sheɗan ko Abdul? Na yi kome da nake son yi ba zai dame ka ba amma kada na haɗa abota da wanda na zarta shi sharri?”
Murmushi ta sake yi tana tauna laɓɓanta a karo na biyu tana murza yatsunta “Zan yi komi ɗin kamar yanda ka lamince min. Zan toshe kunnuwana daga gayyatar makaɗan da ke buga gangarsu. Zan yi abin da zaka daɗe kana yaba min da kuma kallona a cikin zuciyarka da idanuwanka.
Ba zan gayyaci sheɗan ba tunda ka sanar da ni sharri na yafi nasa.” Ta ƙarasa maganar yana haɗe hannunta waje ɗaya sannan ta zamo ƙafarta tana sauƙa a kan gadon.
“Ba haka nake nufi ba Hafsat. Ba ina nufin sharrinki ya fi na sheɗan ba, baki fahimce ni ba.”
“Magana zarar bunu ce fa Abdul-Mannan. Idan ta futo bata komawa, ba kuma a mata kwaskwarima wajen mata kwalliya.
Na gode da damar da ka bani.”
Tana gama maganar ta buɗe ƙofar ta fice. Kansa ya dafe yana tuna abin da ya faɗa mata, yana mamakin kaifin basirarta.
“Ya Allah!” Ya faɗa yana rintse idonsa da ƙarfi jin wani abu ya soki zuciyarsa.
Ya daɗe zaune a wajen yana jin bugun zuciyarsa har a lokacin na tsananta. Bai taɓa tsammanin zata iya fassara kalamansa irin haka ba, duk da ya san wace Hafsat da kuma gidan da ya aurota.
Kamar yanda ta zama zaƙwaƙwari ta farko wajen ilimi haka ta zama zakka ga rashin jinta.
“Hasbunallahu wa ni’imal wakil!” Ya shiga mai-maitawa a ƙasan laɓɓansa, kafin ya ji bugun zuciyarsa ya dai-daita.
Hakan ya sa ya janyo litattafan da ya fara dubawa yana nazartar su. Sai dai rabin hankalinsa na kan Hafsat, bai sake jin motsinta ba.
Ganin baya fahimtar komi ya sa ya rufe littafin ya fice a ɗakin ya nufi ɗakin Hafsat.
Bai ji motsinta ba hakan ya sa ya murɗa ƙofar ɗakin ya yi sa’a ƙofar a buɗe ta ke.
Ajiyar zuciya ya sauƙe ganinta zaune akan abin sallah da littafin hisnul muslim a hannunta.
A hankali ya fara ta ko ƙafafuwansa har zuwa kusa da ita, ya zauna a gabanta kana ta tanƙwara ƙafafuwansa kamar mai shirin cin abinci.
Juyo da kanta ta yi ta kalle shi, sai ta yi murmushi sannan ta mayar da kallonta ga littafin.
A hankali ya sauƙe sassanyar ajiyar zuciya sannan ya buɗe bakinsa ya fara magana cikin sanyin muryarsa.
“Na gode Allah da na same ki a haka. Na kuma ji daɗi ƙwarai da naga fuskarki ɗauke da murmushi.
Nagartarki ta futo a cikin shigar kamalarki, hasken fatarki ya haskaka kamar yanda idanuwanki suka rabauta da samun kyakkyawan gani.
Zan so na ci gaba da ganinki a haka, zan so sautin muryarki ya ci gaba da fita da neman kusanci ga ambaton Allah (S.W.A).”
Rufe littafin ta yi tana shafa addu’o’in ba tare da ta yi magana ba ta tashi tana naɗe abin sallar ta ajiye shi a ma’ajiyarsa sannan ta mayar da kallonta ga Abdul-Mannan da har a lokacin idanuwansa na kanta.
“Ka ce wani abu ne Abdul?”
Tashi yayi tsayen shima ya matso kusa da ita har suna jin hucin numfashin juna.
Idanuwansa fes a kanta kamar yanda itama take kallonsa babu ƙiftawa.
Kawar da idonsa yayi yana murmushi da kallon hijabin da ke sanye a jikinta.
“Abubuwa da yawa na ce Malama Hafsat! Da wanne kike so na fara mai-maita miki dan naji hakan ya miki daɗi sosai?”
Ɗora hannunta ta yi akan kafaɗarsa, tana yalwata murmushi akan fuskarta, sannan ta sa ɗaya hannun nata tana zagaye sajen da ke kwance akan luf a kan fuskarsa.
Idanuwansa ya lumshe jin wani abu na yawo a jikinsa, yana jin tsikar jikinsa na zubawa. Yayin da bugun zuciyarsa ke ƙaruwa kamar zata fito daga maɗaukarta.
Jin hucin numfashinta a kusa da kunnensa ya sa shi saurin waro idanuwansa wa je.
“Maganarka mai kyau ce da son a jita, kamar dai yanda ka kasance mai kyau Abdul. Sai dai ni a ko mi na rayuwata ina adawa da abu mai kyan da ya zarta ni. Kamar yanda na tsani shisshigi da tankawa ga duk abin da aka ga a tare da ni.” Ta ƙarasa maganar tana hura masa iskar bakinta a kunnensa.
Hakan ya sa ya sake wara idonsa. Yana jin jikinsa na rawa kamar mazari.
Janye jikinta ta yi daga nasa tana murmushin ganin halin da ya shiga, ta ruƙo hannunsa kamar raƙumi da akala haka ya shiga binta har suka fito falon, ta saki hannunsa.
“Ka tsaya a iya matsayinka na mijina. Ka daina saurin aika yabo a gare ni, domin kada wata rana ka gaza yafewa zuciyarka.” Tana gama faɗa ta koma ɗakinta da rufo masa ƙofa da ƙarfi.
Wanda hakan ya sa shi rufe idonsa.
Zama yayi shirum a kan kujera yana maida numfashi da kallon yanda jikinsa ya jiƙe da gumi.