Karon farko da Yan biyu suka tako kafar su garin Lagos wurin mahaifiyarsu sumayya.
Takanas alh Kabir yazo garin katsina wurin kakar su haj nana ya dauke su da sunan zasuyi musu hutu idan an koma makaranta zai maidosu ba tare da sumayya ta San zai dauko su ba .
Alh Kabir Yana matukar son Yan biyu tun Yana jawarcin sumayya Allah ya zuba mishi kaunar su aranshi. Sumayya Bata boye mishi komai ba akan rabuwarta da mahaifin Yan biyu da irin zaman da tayi dashi. Akan haihuwar Yan biyun don sun kasance Mata .
Ya Dade Yana mamakin Uban yan Uban. . .