Saukar Marin na bazata da Kabir yayiwa zalifa yazo dai dai da subucewar farantin tangaran daga hannun sumayya saboda shigar maganar da zaliha ta furtawa Yan biyun Wai shegu ne.
Zaliha ta dafe inda Marin ya ratsata.
"Akan wadan Nan shegun yaran ka wasa hannunka akan fuskata Kabir"?
"Saboda na Fadi abinda yake shine gaskiya ka tozar tani agaban yarana"?,
Ta fada hawaye Yana wanke fuskar ta saboda bak'in ciki. Ba marin ne damuwar ta ba sai Don yadda ya shige cikin lamarin yaran ya kuma tozarta ta a agaban yaran ta.
"Ka Mari aurenka wallahi Kuma in Don. . .