Hassana ta zurawa wayar hannunta ido tare da zabga tagumi takira wayar goga yafi sau goma Amma yaki dauka. Ta Kuma sani Yana gani yaki dauka. Ta sake Danna mishi Kiran tana dab da katsewa ya dauka. Baiyi magana sai itace ta fara magana.
"Fatan kana lafiya masoyi na kwana biyu na bar Jin ka har mafarkin ka nake Allah yasa ba laifi nayi maka ba"?
Yayi murmushi. "Wallahi garin ne yayi zafi masoyiya yau kwana na biyar ban rike dari biyar ba.
Tayi murmushi. "To kazo inganka ina so yau muyi fira ta soyayya ko Zan dawo wannan duniyar. . .