Skip to content
Part 15 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Bayan Shekara Ɗaya Da Rabi

Asma’u da Zubaidah ne a kitchen yayin da suka shafe tsawon lokaci tare suna shirya abinci kala-kala, girki a ƙalla kala biyar tare da abin sha lemo haɗin hannu masu rai da lafiya, gidan ya ɗonke da ƙamshi nau’i daban-daban kasancewar sun wayi gari cikin tsammanin isowar Ma’aruf daga doguwar tafiyar da ya yi zuwa ƙasar Dubai.

Lokaci zuwa lokaci Zubaidah na gwada kiransa a waya duk da cewa ba ko yaushe wayar ke shiga ba. Daga ƙarshe ne ya tabbatar mata yana airport har ya haɗu da direba da ya je ɗaukarsa.

Asma’u ma dai ta tsinci kanta cikin matsanancin farin cikin dawowarsa. Suna kammala ayyukan ta wuce ɗakinta kai tsaye ta zarce toilet, bayan ta fito ma ta ɓata lokaci tana kwalliyar da ba ta taɓa yin irin ta ba, riga da siket ta saka na atamfar super holland da aka yi mata tsararren ɗinkin zamani, ko ba a faɗa mata ba ta san duk inda ta motsa sai ta ɗauki hankali, kuma dole a kira ta kyakkyawa, ita ba fara ba ce kamar Zubaidah amma ba za a kira ta baƙa ba.

Kusan ƙarfe biyar motar da ta ɗauko Ma’aruf daga airport Jeep BMW ta sako kai harabar gidan, bayan da mai gadi ya buɗe get, direba ya samu guri ya yi parking a rumfar ajiye motoci. Ma’aruf ya fito sanye cikin baƙaƙen suit riga da wando da suka yi matuƙar dacewa da surar jikinsa, kyakkyawar fuskarsa sanye da baƙin glass sidiƙ, cikin taku irin na cikakku kuma isassun maza ya sa kai cikin falon yana kiran honey ɗinsa.

Zubaidah ta fito cikin kwalliya, kai komai fa na manya daban ne, riga da siket ta saka na tsadadden yadin material ruwan sararin samaniya, ga Khalifa na takawa da ƙafafunsa shi ma an zanzare shi da nasa wankan alfarmar na ƙananun kaya, ya kwasa da gudu ya maƙale Daddynsa, bayan Zubaidah ta ƙaraso daf da shi ne ta kai hannu ta saƙalo wuyan sa tare da kissing ɗin sa a kunci. “We are welcome my honey.” Ya shafi fuskarta cikin shauƙi yayin da ta zaunar da shi kan kujera ta ƙara maƙale shi sosai kamar za ta shige cikin jikinsa.

“Mai gida mun yi kewarka sosai.”

Ya saki murmushinsa mai tsada. “Ni ma na yi kewar iyalina too, da fatan na same ku lafiya.” Ta lumshe idanu ta buɗe tare da rausayar da kai, ta yi masa barka da hanya.

Sun ɗan taɓa hira sama-sama ya miƙe “Honey ya kamata in shiga in zuba ruwa a jikina akwai gajiya sosai a tare da ni.”

“Is okey, ka sauko lafiya.”

Ya haye sama yayin da Zubaidah ta wuce ta fara shirya masa table, a dai-dai lokacin da ba ta buƙatar ganin motsin kowa a wajen, daga ita sai Mahmud Khalifa za ta tarbi mijinta.

Asma’u da ke jikin windon ɗakinta a kan idonta Ma’aruf ya fito daga mota ya shige falo, ya yi mata kyau fiye da kullum ko don ta jima ba ta saka shi a idanunta ba? Ta sauke ajiyar zuciya a hankali, anya ba ta ɗaukarwa kanta dala ba gammo ba kuwa? Anya ba ta yi ganganci ba, gangancin da zai jefa rayuwarta cikin garari? Mijin da Zubaidah take aure shi take so, so ba na wasa ba. Shin ya aka yi ma ta bari hakan ke faruwa da ita? Ma’aruf da Zubaidah fa duka ba sa’anninta ba ne, bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne, wasu siraran hawaye suka biyo kan kuncinta.

Bayan Awa Biyar

Tana kwance a kan gado tana aikin tunanin nemawa kanta mafita, mafitar dai guda ɗaya ce, ta tattara nata ya nata ta bar musu gidan tun kafin asirin zuciyarta ya tonu, sam ba ta ji motsin shigowar mutum ba illa kawai ta ganshi tsaye a kanta, tashi ta yi da hanzari ta zauna tana masa sannu da zuwa.

“Sam ba zan karɓi sannu da zuwanki ba Asma’u, saboda sai da na tako har inda kike, ke ba za ki iya zuwa musamman ki same ni ba, ba ki da kirki ko kaɗan.”

Sunkuyar da kai ta yi ƙasa tana murza yatsun hannunta a hankali.

“Ka yi haƙuri.”

Banda wannan ba ta san wani kalami ba da za ta iya furta masa kan qorafinsa. Haƙiƙa Ma’aruf ya jima yana rikita zuciyarta.

“Haka kika iya, bada haƙuri ba, sai dai wannan karon bada haƙurinki ba zai yi aiki ba yarinya, domin laifukanki na da tarin yawan da haƙuri ba zai iya kankare su ba, tunda nake tafiya baki taɓa kira na ko a waya mun gaisa ba Asma’u why?”

Har yanzu kanta na sunkuye a ƙasa.

“Daddyn Khalifa ka san bani da waya kuma ba ni da lambarka, ban ma san yadda ake amfani da ita ba.”

Shiru ya yi yana nazari kan ɗabi’u da halayenta, haƙiƙa Asma’u daban ce, a wannan zamanin da muke ƙarni na ashirin da ɗaya kan a samu mutum irinta sai an tona, wace iri ce ita? Ya numfasa
“Amma ba ki san muna magana da Zubaidah ba? Da sai ki riƙa ba ta saƙo, za ta faɗa min kuma zan ji daɗi.”

Ta fuskanci dai dole so yake ya kama ta da laifi, da alamu ma bai san cewa ko kaɗan Zubaidah ba ta ba ta irin wannan damar ba a gidan.

“Tuba nake a yafe min, insha Allahu zan kiyaye.”

Ma’aruf ya yi murmushi kaɗan.

“Shi kenan ta wuce, daga yau kuma na soke wannan gidadancin, matuƙar kina so mu shirya dole ki riƙa sauke haƙƙin zaman tare, ki riƙa zumunci, ni kamar ɗanuwa ne gare ki.”

Duk da cewa ta ji daɗin kalaminsa, a fuskarta ma ta gwada masa hakan, amma bayan fitarsa daga ɗakin kawai sai Asma’u ta tsinci kanta da fashewa da kuka, kukan da ta rasa gane ko na meye. Sai da ta yi mai isarta ta share hawaye sannan ta koma ta kwanta. A mafarki shi ne wanda take so amma kuma a zahiri ya fi ƙarfinta.

Ba a jima ba ya sake dawowa, wannan karon kwalin sabuwar waya ƙirar kamfanin Samsung ya shigo da ita, ya miƙa mata, ta karɓa bayan ta tashi zaune.

“Akwai sim card da komai a ciki, Zubaidah za ta gwada miki wasu abubuwan, na yi ta jiran ko za ki fito in baki, sai baki fito ba.”

Ya sake ficewa daga ɗakin ya bar ta riƙe da kwalin wayar tana jujjuya wa, ta buɗe tana dubawa a hankali, ba za ta ce tana murna da mallakar wayar ba, ta fi jin daɗin yadda ya kula da ita ya siya mata kamar yadda take ji a duk lokacin da ya yi mata kyauta komai ƙanƙantarta.

Gudun fitina da sassafe kafin su fita Asma’u ta fito da wayar kitchen ta nunawa Aunty Zubaidah, ashe ma ita ce ta sa ya taho mata da ita daga Dubai, don duk wayoyin da suke amfani da su ba a nan ƙasar yake saye ba. Sau tari Zubaidah na makaranta ko wajen wasu sabgoginta tana son yin magana da ita musamman kan ayyukan da suka shafi gida amma babu hali, saboda babu wayar a hannunta. Wannan shi ne babban dalili.

Kasancewar Asma’u tana da saurin fahimtar abu nan da nan cikin wuni guda ta fara gane kan wayar. Zubaidah ta saka mata lambar kowa da ke gidan Hajiya, ɗaya bayan ɗaya kuwa ta kira su har Yaya Nasir don su ga lambarta. Hajiya Yagana ta yi farin ciki sosai ta kuma ƙara tabbatar da cewa Zubaidah da mijinta ba za su wofantar da rayuwar marainiyar Allah ba, har kullum so take ta ga Asma’u ta samu ci gaba a rayuwarta, ga shi kuma ci gaban na ta samuwa.

Bayan sallar magariba Zubaidah suka shigo gidan tare da Ma’aruf, da alama siyayya kawai suka fita, tana cikin ɗaki bayan ta kammala dukkan ayyukanta, shige da fice kawai take cikin wayarta sai ga kiran Zubaidah ya shigo, ta ɗaga.

“Me kika dafa ne?” Zubaidah ta tambaye ta. Ta faɗa mata ta dafa sakwara da agusi sannan akwai abincin ranar da ta ajiye mata ta yi zaton za ta dawo, wato soyayyiyar shinkafa dafaduka da suke kira fried rice.

“Ki kawo min nawa ɗaki, ba zan jira Ma’aruf ba, ya fita masallaci, sai bayan sallar isha’i zai shigo.” Ta yanke wayar, ita ma daga nata ɓangaren ta ajiye tata wayar ta fita zuwa kitchen don cika umarni, tana cikin zuba abincin ne sai ga Ma’aruf har cikin kitchen ɗin, yana sanye da shadda getzner mai launin ruwan ƙasa, ƙamshin turarensa ne ya fara bayyana kafin shi, ya isa daf da ita yana leƙa tukunyar miyar da ta buɗe.

“Wow! Asma’u me kika dafa mana ne haka?” Wata irin kunya ta rufe ta ta ce.

“Aunty Zubaidah zan kaiwa abincinta.”
“Amma ni banda ni, abun son kai ne ko?”
“Ko kaima da ka buƙata da an kawo maka, ai mun yi zaton ma ba za ka shigo ba sai anyi sallar isha’i.” Ya ce, “Ƙwarai ni ma hakan na so, amma yunwa ta hana min sakat.” Asma’u ta ce, “Ayya to bari in sa muku duka.”

“Ki sako har da ke, ki zo dinning mu ci tare mu duka.” Ya faɗa bayan ya tsare ta da idanu.
“Ai ni na riga na ci nawa tuntuni Daddy.”

“Haka kullum kike faɗa, bisa ga dukkan alamu har yanzu baki sauya ba, ina jin sai na siyo bulala saboda ke tunda ba kya jin maganata sai ta Auntyn can taki ko?”

Dariya Asma’u ta yi kaɗan, a zuciyarta kuma ta tafi tunanin ina ma a ce zai samo bulalar ya riƙa zane ta kullum za ta so hakan, wataƙila ya raba ta da wannan jarababben son da take masa, ƙwarai ta cancanci duka daga gare shi, tsayuwarsa a gurin ya saukar mata wata irin kasala, sannan ga tsoron fitowar matarshi ta riske su a hakan, dole za ta zargi wani abu ko da shi bai ɗaukar hakan a bakin komai.

<< Kaddarar Mutum 14Kaddarar Mutum 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×