Skip to content
Part 16 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Yana tsaye yana kallonta ta gama haɗa fulasan abincin ta zuba cikin babban tire.

“Zan hau muku da shi sama wurin Zubaidah.” Ta faɗi tana kallon kyakkyawar fuskarsa a taƙaice, sannan ta ɗauka za ta fita, sai dai ya tokare ƙofar, dole ta ja ta tsaya tana kallon tsakiyar farantin ba tare da ta yi magana ba. Sai da ya gama karance ta tsaf sannan ya kauce gefe ya ba ta hanya, ya fara taku da sauri ya riga ta fita daga kitchen ɗin.

Da ta hau sama ɗakin Zubaidah ta nufa, ta iske ta kishingiɗe tana amsa waya don ko sallamar da ta yi ma ba ta samu amsa mata ba, ta ajiye mata abincin ta fito, a bakin ƙofa suka kusa karo da juna, kallo ɗaya Ma’aruf yi mata yanzu kuma ya ɗauke kansa.

Asma’u na komawa ɗaki wayarta ta dauka, tana mai kyautata zaton za ta ɗauke mata dukkan damuwarta, duk lokacin da ta ga Ma’aruf musamman a ce wata magana ta shiga tsakaninsu, ta kan ɗauki tsawon lokaci tana jinyar zuciyarta, idan ta samu barci duka shi ne a ci cikin mafarkanta, yanzu haka da ta runtse ido shi take gani yana mata murmushinsa mai narkar da zuciya, hawaye suka sulmiyo daga cikin idanunta, hawayen tabbatar da cewa YA FI ƘARFINTA.

A cikin barci ta yi mafarkin sun yi aure ta zama matarsa, har sun haifi ‘ya’ya Zubaidah ta zama kishiyarta, waɗannan dama kullum sune ire-iren mafarkanta.

Bayan ta dawo duniyar zahiri ta kasa sake komawa barcin, kawai ta tashi ta zauna tana roƙon Allah ya yaye mata son abin da ba za ta samu ba, tabbas Ma’aruf kaɗai zuciyarta take so amma kuma shi ba zai so ta ba.

Ba ta san ko ƙarfe nawa ba ta ɗauko wayarta ta yi ta laluben lambobi har Allah ya sa ta zo kan lambarsa da ya sa mata yayi saving da kansa, haka nan take jin sam ba ta kyauta ba da ba ta taɓa gode masa gaba da gaba kan mallaka mata wayar da ya yi ba, bai kamata a ce Zubaidah ce za ta ari bakinta ta ci mata albasa ba. A wauta ko kuma a ce a mayen so haka take ji, don haka cike da ƙwarin gwiwarta ta tura masa kira, sai dai kafin kiran ya kai ga shiga ta yi sauri ta yanke.

Me zai faru idan har yana tare da Zubaidah a dai-dai lokacin me ma za ta fara faɗa masa?

Ta kasa sarrafa tunani da zuciyarta, a haukanta ma so take ta ji muryarsa, idan kuwa hakan bai samu ba tilas a daren ya san halin da take ciki, don haka ta shiga what’s up kanta tsaye ta nemo shi, ga tarin mamakinta sai ta ganshi Online, hannunta na rawa ta rubuta masa gajeren saƙo kamar haka;
“Na gode da kyautar waya Daddy. Mu kwana lafiya.

Jikinta na rawa ta tura masa saƙon, bayan ya tafi sai ta ƙura wa fuskar wayar ido, ba ta jin cewa zai maido mata amsa, amma kuma tana sa ran zai gani, hakan kuma zai gamsar da ita kan wanke laifinta, a ƙalla ta daina ganin rashin kyautawarta. Me yasa take jin kamar ita mai laifi ce a wajensa?

Abin al’ajabi ba a kai mintuna biyar ba sai ga martanin saƙonta daga Ma’aruf kamar haka;
“Asma’u ba ki yi barci ba, me ya hana ki, ko tunanin saurayinki ki?”

“Tunaninka da sonka ne suka hana ni barci Ma’aruf.” Amsar da ya dace ta bashi kenan, sai dai ba za ta taɓa iyawa ba ko da son zai kashe ta, domin ba ta san makomarta ba, don haka sai ta kasa sake rubuta masa komai.

Mintuna biyu a tsakani wayarta ta fara ringing sai ga sunanshi, wai kuma sai gabanta ya faɗi! Tsoro ya kamata, wataƙila idan ta ɗaga faɗa zai mata, ta raya hakan a ranta, to amma kuma ko zaginta zai yi ba ta jin cewa za ta iya ƙin ɗaga wayar saboda kawai ta ji muryarsa, ta buɗe tare da kara wayar jikin kunnenta.
“Kin san ko ƙarfe nawa ne yanzun Asma’u?” Ma’aruf ya tambaye ta, fayau muryarsa babu alamun barci. Ta kai dubanta ga agogo sha biyu har ta gota ta ce, “Na sani, sha biyu da minti takwas.”

“Amma baki kwanta ba, bayan kin san gobe akwai school, wato kina chatting da samarinki ko?”

“Samari fa ka ce Daddy? Ni bani da wani saurayi, karatu kawai nake da yake gobe muna da test.”

“Good, hakan dai-dai ne, amma ki daina takura kanki, ki yi iyakar yadda za ki iya, sauran ki barwa Allah kin ji ko?”

“Na ji, na gode Daddy Allah Ya jiƙan mahaifa.”
Wannan shi ne mabuɗin da ya buɗe kiran waya kai tsaye tsakanin su. Ma’aruf ya shige rayuwar Asma’u sosai, ta kai ga sun yi matuƙar shaƙuwa, duk da cewa Asma’u na jin tana aikata kuskure, amma ba za ta iya juyar da duk wata kula wa da yake gwada mata ba, ba za iya korar alaƙar su ba, har zuwa lokacin da suka ankare suna cikin tsananin mayen son juna.

Ta Faru Ta Ƙare

Tunda Zubaidah ta kira ta gabanta ke faɗuwa kasancewar suna tare da Ruƙayya a falon ƙasa, ta ɗaura kallabinta ta fito, har ta ƙaraso inda suke Ruƙayya na binta da wani kallo mai cike da zargi, yayin da Zubaidah ta miƙa duniyar tunani, babu wanda ya amsa sallamar da ta yi. Ta saci kallon Zubaidar da ta haɗe girar sama da ƙasa, idanunta sun kaɗa, babu walwala ko kaɗan a fuskarta,

“Asma’u ina kuka fita da Ma’aruf a mota shekaranjiya?”

Haƙiƙa tunda Zubaidah ta yi mata wannan tambayar ta san lallai ta faru ta ƙare, wai anyi wa mai dami ɗaya sata.

“A hanya ya gan ni, ya tsaya ya ɗauke ni ina dawowa daga makaranta.” Muryarta na rawa kaɗan ta faɗa.

Harara Ruƙayya ta watsa mata. “Rufe wa mutane bakinki a nan munafuka, tun yaushe ake ganinku tare?” Ta juya kan Zubaidah “Kema banza kin tsaya kina wani tambayarta inda suka fita, yau suka fara keɓewa tare? Kawai ta yi maki bayanin alaƙar da ke tsakaninsu?”

Zubaidah ta haɗiye wani abu da ba ta san ko mene ne ba.
“Wato Asma’u abin da za ki saka min da shi kenan, wannan shi ne sakamakon mayar da ke mutum da na yi?”

Jikinta ne ya fara kyarma, zuciyarta ta karye, ƙwalla kuma ta cika idanunta taf, wane irin bala’i ne yanzu kuma ya tunkaro rayuwarta? Tabbas da tana da hali da ta cire Ma’aruf daga ƙoƙon ranta, domin a yanzu da take tsaye gaban Zubaidah ji take ko da tunaninsa ta yi tamkar ta ci amanarta ne.

“Ni fa ba kuka na kira ki ki zo ki min ba, ki matso ki faɗa min yadda aka yi komai ya faru kin ji ko?”

Matsawa Asma’u ta yi daf da su ta yi zaman raƙuma a gabanta.

Zubaidah ta ƙura mata ido na ɗan lokaci kafin ta ce, “Abin da nake so in sani shin shi ne ya ce yana sonki ko ke ki ke binsa, wato ke nan har kina jin cewa kin isa ki auri mijina?”

Hawayen da Asma’u ke ta ƙoƙarin dakatarwa suka fara sauka kan kuncinta.

“Ki kwantar da hakalinki Aunty Zubaidah, ni na riga na faɗa masa ba zan iya cin amanarki ba, kuma kan wannan maganar a shirye nake in bar gidan nan Wallahi.” Ruƙayya ta tari numfashinta.

“Cin amana na nawa kuma yarinya, wa ya san irin tsiyar da kuka tsula a gidan nan, ta yaya aka yi ya samu ƙofar yi miki magana, in banda dama can akwai wata a ƙasa? Ke kam Zubaidah nema ake a raina maki wayo bayan an maida ke sakarai, wa ya san iyakar lokacin da suka ɗauka suna wannan haramtacciyar alaƙar? Ko da yake ai tun da fari sai da na miki magana kan zamanta a gidan nan ki ka yi watsi da magana ta.”

Kalaman da Ruƙayya ke amfani da su sun mata tsauri, ita ƙoƙarin ƙaga mata wani laifin daban take. Ta kawo ta iya wuya.

“Dakata Ruƙayya! Gaskiya ba zan juri irin wannan ƙazafi da cin zarafin da ki ke min ba, wallahi babu wani abu makamancin tunaninki da ya taɓa haɗa ni da Ma’aruf, idan kuma kin zaɓi yi min sharri Allah yana kallonki.” Ta rufe furucin da sheshsheƙar kuka.

“Iye! Wato rashin kunya ma za ki min? Yanzun nan sai in tashi in tattaki a wajen nan in ga uban da ya tsaya miki, kin kwan da sanin cewa ni ba sa’ar ki ba ce, kuma uwar da ta haife ki ma ta yi kaɗan Wallahi.”

Wani irin baƙin ciki ya tokare zuciyar Asma’u, ta kasa jure kalmar UWAR DA TA HAIFE KI MA TA YI KAƊAN, ba ta san lokacin da ta buɗe baki cikin kuka ba ta ce da Ruƙayya, “Ki yi duk abin da za ki yi, amma kar ki sake ki ambaci uwata ki zage ta Wallahi.”

“Wace ce uwar taki, idan na zage ta sai me, me za ki iya?”

“Ai ko ba uwata ba sai dai ta ki ki ka zaga, marar mutunci.”

Tashi Ruƙayya ta yi za ta doke ta Zubaidah ta dakatar da ita. “Look Ruƙayya, ki bar ni da ita na faɗa miki ko?” Ta koma ta zauna tana huci kamar ta ci babu.

“Ki rabu da ni in koya wa ‘yar iska hankali Zuby, ina faɗa miki fa yarinyar nan ta wuce tunaninki, Wallahi muddin baki ɗauki wani action a kanta ba za ki yi nadama lokacin da nadamar ba za ta yi miki amfani ba.”

<< Kaddarar Mutum 15Kaddarar Mutum 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×