Abu ɗaya Zubaidah take fuskanta yanzu, mijinta da mahaifiyarta sun yi fushi da ita ta rasa gane kan ko wannen su, Hajiya kullum cikin kiranta take a waya tana surfa mata zagi duk lokacin da abun ya motsa mata, wani lokacin har gida take zuwa ta yi mata fata-fata,"Ai baki ga ta zama ba, kin salwantar da yarinyar mutane shi ne za ki zauna ki miƙe ƙafafu mutuniyar banza da iliminta bai amfana mata komai ba."
Abin da ke matuƙar ɗaure mata kai da bata mamaki har yanzu babu wanda yake magana kan dalilin da ya. . .