Skip to content
Part 19 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Abu ɗaya Zubaidah take fuskanta yanzu, mijinta da mahaifiyarta sun yi fushi da ita ta rasa gane kan ko wannen su, Hajiya kullum cikin kiranta take a waya tana surfa mata zagi duk lokacin da abun ya motsa mata, wani lokacin har gida take zuwa ta yi mata fata-fata,
“Ai baki ga ta zama ba, kin salwantar da yarinyar mutane shi ne za ki zauna ki miƙe ƙafafu mutuniyar banza da iliminta bai amfana mata komai ba.”

Abin da ke matuƙar ɗaure mata kai da bata mamaki har yanzu babu wanda yake magana kan dalilin da ya sa ta zartar da hukuncin, hakan na nufin ko da auren Asma’u Ma’aruf ya ce zai yi Hajiya ba za ta ƙalubalanci hakan ba, ba za ta taya ta kishi ba?

Bauɗaɗɗen halin Ma’aruf ya bayyana, yanzu ko kallo ba ta ishe shi ba, da ya dawo zai ya haye sama ya shige ɗakinsa ya kulle, idan za ta kwana tana knocking ba zai buɗe mata ba, idan ta ajiye abinci haka za ta zo ta ɗauki kayanta, wulaƙancin da ba ta taɓa sanin ya iya ba shi yake mata kuma duk a kan banzar yarinyar can Asma’u, wa ce ce ita, wane matsayi ta taka haka a zuciyar mutanen da suka fi komai muhimmanci a rayuwarta?

Zubaidah ta rasa inda za ta saka rayuwarta ta ji daɗi, duk shawarwarin da su Ruƙayya suka ba ta ta gwada, amma abin ya ƙi aiki, gashi ta gaji da halin ko in kular da suke nuna mata.
Yau ta ci alwashin duk runtsi sai ta san matsayinta gun Ma’aruf, ta san inda yake ajiye safayar makullan gidan kaf don haka sai da ta tabbatar ya fita, gaba ɗaya ta je ta kwaso su ta shiga gwadawa har Allah Ya sa ta samu na ɗakinsa, ta ɗauke shi ta ɓoye.
Kamar kullum ya haye gado ya yi kwanciyarsa, har ya fara barci ya ji sukunrniyar buɗe ƙofa har da makulli, ya san abin da ke faruwa don haka ya runtse idanunshi tamkar barci yake, ta san kuma yana jin ta.

“Ma’aruf yanzu wannan hukuncin da ka yanke a zaman mu kana ganin shi ne daidai? A matsayina na matarka ban isa in nuna kishina a kanka ba kenan?”

Bai tanka mata ba, sai ma juya mata baya da ya yi.

“Dukkanmu fa yarinyar nan haka muka ganta da rana tsaka, babu dangin Iya bare na Baba, sai me don ta tafi? Na sani ban isa in hana ka son wata mace bayan ni ba, amma Asma’u har ta yi canzawar da za ka manta yadda ƘADDARA da tarihinta suka kasance, ina abin so ga macen da wani da baka san ko waye ba ya yi wa fyaɗe har ta yi ciki ta haihu? Me za ka samu wanda ban ba ka shi ba Ma’aruf?”

Ko kaɗan bai son tanka mata amma haka kurum yake jin ba zai bar irin wannan tunanin ya ci gaba da tasiri a zuciyarta ba, don haka ya ture lallausan bargon da ya rufe rabin jikinsa da shi tare da juyowa yana dubanta a tsanaki.

“Me yasa kike tufka kina warwarewa ne? Ke da bakinki kika ce ƙaddara ce tushen lamarin yarinyar nan, ba zuwa ta yi ta bada kanta haka ya faru da ita ba, Zubaidah a wane Hadisi ko Ayar Alƙur’ani aka haramta auren macen da aka yi wa fyaɗe? Ina baki shawara idan za ki ƙi mutum, ki ƙi shi don munin halinsa, ba don wata ƙaddara da ba shi da ikon sauya ta ta same shi ba, don haka bana jin duk wani kushe, aibatawa ko tozarci da za ki yi kan yarinyar nan zai yi tasiri a kaina idan har ina da niyyar yin jihadin auren ta in fasa ba.”

Wani irin baƙin ciki ya tokare zuciyar Zubaidah.

“Da kyau! Ta wannan hanyar ka ɓullo kenan? Me ne ne abin jihadi kuma? Ko da yake ku dama maza ai haka kuke idan kuka so aure, sai ku fake da wasu ayoyi da hadisan ku na cuta, haƙiƙa kuma yau ka nuna min kai ɗa namiji ne, ba Asma’u ba? Ka aure ta mu gani.”

Duk da ya ji haushin maganganunta bai sake tanka mata ba ya runtse idon shi kawai yana fatan ta fita ta bar shi ya ji da abin da ya dame shi, yayin da ita kuma a wannan lokacin ne ma ta samu damar amayar da duk wani abu da ke ƙunshe cikin zuciyarta game da tsananin kishin da ke cin ranta, wanann furuci nata KA AURE TA MU GANI na da alaƙa da mummunan shirin da ta yi.

A rayuwar Zubaidah wannan shi ne karo na farko da ta taɓa kaiwa malamai da bokaye buƙatarta bisa shawarar Ruƙayya. Ko haƙanta zai cimma ruwa?

*****
Zaman Asma’u a ƙauyen kakanninta yana tafiya yadda take so. Ba ta nemi komai ta rasa ba, ko da yake dama ƙauye shi ne asalinta, ba ta ma ji a ranta tana son komawa birni, abu guda ya rage mata, shi ne yadda za ta shafe wasu abubuwa masu wuyar mantawa daga zuciyarta, babban abin takaicin ta kasa daina tuna Ma’aruf bare ta samu ta cire son sa daga ƙoƙon ranta, domin a yanzu ta tabbatar ya riga ya mata nisa.

Kuɗin da Zubaidah ta ba ta ba ƙananan kuɗaɗe ba ne a wajenta, da ta lissafa su har da waɗanda take tarawa a wajenta sun haura naira dubu ɗari biyar, ba ta amfanin komai da su, don a qauyen CEFA ake kashewa.

Kamar ko wace rana, tunda ta cika wata guda a ƙauyen, yau ma yara sun taru a wani ɓangare na yalwataccen gidan kakanninta inda take koyar da su karatu a sauƙaƙe.

Ba tun yau ba Iyayen yaran ke matuƙar murna da hakan, domin ganinta kaɗai ya isa tabbatar musu babu abin da ke gyara rayuwar mutum kamar ilimi, shi ne ma tushen rayuwar ta ɗan’adam, a wasu lokutan ma shi ke bambanta shi da dabba, tuni da dama daga cikin yaran sun fara fahimtar English, Hausa, France har da karatun addini da take koya musu.

Da tafiyar ta yi tafiya sai ga matan aure ma sun shigo ana damawa da su. Sam Asma’u ba ta yi mamaki ba da ta riski mafi yawancinsu ko alwala ba su iya ba bare karatun sallah da wankan tsarki, haka ta ci gaba da yin bakin ƙoƙarin ganin ta taya su yaƙar jahilcin da ba don zuwanta ba da shi za su mutu.

Nan da nan labarinta ya fara zagaya wa ko ina har maƙwabtan ƙauyuka. Somayi ma sun samu labarin dawowarta. Wani yammaci sai ga Muntari ya bayyana a ƙauyen saman dokinsa, lokacin Asma’u na tsakiyar karatu da ɗalibanta. Aka yi masa iso har ƙofar gida.

Bayan sun gaisa da tsofaffin nan ya ce ‘Dama ya samu labarin zuwan Asma’u ne shi ne ya zo ya ganta.’ Da gani ka san har yanzu akwai soyayyar nan mai girma a ran Muntari.
Ko da aka isar wa da Asma’u saqon zuwansa, sai ta ji wani iri, amma kuma a ranta tana so su hadu ko don ya ga yadda Ubangiji Ya yi hukuncin Sa, duk da cewa babu sa hannunsa cikin waɗanda suka zalunce ta a can ƙauyen, sai dai ko laifin mahaifiyarsa ya shafe shi. Ko a baya gaskiyarta take faɗa masa zuciyarta ba shi take so ba.

Bayan ta sallami ɗalibanta, aka yi masa iso, ya shigo har inda ta shimfiɗa masa tabarma, baƙonka aka ce Annabinka.

Tunda Muntari ya ɗora idanu a kan kyakkywar fuskar Asma’u bai ɗauke ba, ta nuna masa gurin zama, ya zauna ita ma ta samu guri gefen tabarmar ta zauna, ta gaida shi cikin girmamawa.

Tsarki ya tabbata ga maƙagin da ya qera wannan kyakkyawar halitta, babu wani abun bauta da gaskiya face Shi. Muntari ya sauke ajiyar zuciya.

“Asma’u yanzu ke ce kika zama haka? Na tabbata kaf a ƙauyukan nan ba za taɓa samun mace kamar ki ba, ko dama can na so ki bare yanzu? Amma sai dai na san a yanzun kin fi ƙarfina, domin da idona na ga mijin da zai aure ki ya je har can Somayi yana nemanki, haƙiƙa da a ce na san inda zan samu wannan bawan Allah da ba kai masa wannan babban albishir, don na san zan samu babban goro daga gare shi, domin mutumin na matuƙar ƙaunarki.

Asma’u wa ya isa ya ja da hukuncin Allah? Tabbas su Waziri sun yi kuskure, ina da yaƙinin a yanzu haka ba su san da idon da za su dube ki ba. Lokacin da na samu labarin abin da Liti ya yi miki nemansa na riƙa yi ruwa a jallo ko ni ko shi, amma ko da na ga halin da yake ciki dole na rabu da shi, ya zama mahaukaci tuburan, yawo yake kan juji, ruwa da iska, zafi, sanyi duk a kansa suke ƙarewa.

Asma’u ki daure ki je Somayi ki nuna matsayin da Allah Ya baki ko wasu sa ɗauki darasi daga rayuwarki, sannan su yi koyi da kyawawan halayenki kuma ki ga yadda wancan bawan Allahn ya mayar da mahaifarki, in taƙaice miki za ki ga yadda albarkarki ta shafi kowa da ke Somayi, bakina ba zai iya faɗa miki komai ba sai dai misali domin an ce gani ya kori ji.”

Iyakar abin da Muntari ya faɗa ma ya sa ta kuka ina ga ta je ta gani? Tabbas wannan ba komai ba ne face sakayyar Ubangiji. Abin da kuma ya ƙara ɗaure mata kai wai Ma’aruf ya je ƙauyensu har ya tabbatar musu shi ne mijin da za ta aura, yaushe hakan ta kasance?

Sun jima suna tattaunawa. Daga qarshe Muntari ya yi mata sallama ya tafi bayan ta masa alƙawarin za ta zo Somayi kamar yadda ya nema.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kaddarar Mutum 18Kaddarar Mutum 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×