Skip to content
Part 2 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Bayan Asma’u ta yi nisa da gida ne ta hangi Malam Iro mijin Tabawa zaune shi kaɗai a a bakin hanya, ko da ta iso dai-dai inda yake ya bi ta da kallo, ta duƙa har ƙasa ta gaida shi.
“Ma’u ina aka nufa haka da uwar ranar nan ba kya ko bari ta yi sauƙi?” Ya tambaye ta ba tare da ya amsa gaisuwar da ta yi masa ba.

“Garin gabas za ni Baba, zan kaiwa Innata saƙo.” Ta bashi amsa.

Ya gyara zama yana kallon ledar hannunta.

“Kin ga Ma’u da kin ƙaunaci yaron nan Muntari babu abin da zai hana yanzu in kira shi da doki ya kai ki har inda za ki je, ina ke ina wannan doguwar tafiya har Garin gabas a ƙafa? Ni ban taɓa ganin yarinyar da arziƙi ke kiran ta ta tana guje masa ba kamar ki Ma’u.”

Zantukan Malam Iro suka fara gundurarta, kullum dai ƙoƙarinsa ya ja hankalinta ta yarda ta auri Muntari. Muntarin da ƙawarta Ramatu ke matuƙar haukan so, ko babu wannan ma ba ta taɓa jin tana son Muntari so irin na aure ba, duk da yana ɗan Maigari, ta ce.

“Baba don Allah ka yi haƙuri ka yafe min, ba da son raina nake gudun auren Muntari ko Salele ba, face ban taɓa jin cewa zan iya zaman aure da ɗaya daga cikin su ba.”

“Wa ya ce da ke ki so Salele Ma’u? Muntari ni nake nufi yaron da ya san darajarki, har akwai wani da ya fi shi kaf faɗin ƙauyen nan?”

Ba ta da amsar da za ta ba shi, domin ba zai taɓa fahimtar ta ba, saboda yana hangen irin alherin da shi kansa zai samu idan ta yarda ta auri Muntari, abinda ya kasa ganewa; shi fa so gamon jini ne, har yanzu jininta bai haɗu da na ko wane ɗa namiji a ƙauyen ba.

“Shi kenan Baba ni zan tafi, da yardar Allah zan isa komai dare kuma zan daɗe a can, ka min addu’a don Allah.”

Ya tabe baki haɗi da juya mata ƙeya. “Shi kenan a sauka lafiya, tunda ba a faɗa miki ki ji.”

*****

Duk tafiyar da Asma’u take cikin dokar daji ba ta fasa kukan Zucin da take ba kukan rabuwa da Innarta haka nan ba ta fasa haɗuwa da Mutane jifa-jifa ba, akasari waɗanda suka yi doguwar tafiya suke dawowa sai kuma waɗanda gonakin su suke nesa da gari, duk wanda ya tambaye ta inda za ta je, amsar ɗaya ce garin gabas tunda kowa da ke ƙauyen ya san suna da alaƙa mai ƙarfi da can duk da rashin jituwar da ke tsakanin ƙauyukan biyu. Sai dai a zahirance babu abin da zai kai ta can, domin a tunaninsu ita da Inna duk kanwar ja ce.

Wajejen Sallar magariba ta fara jiyo kugin motoci, wannan ya tabbatar mata ta kusa isowa bakin babbar hanya inda a nan ne za ta samu motar duk inda take son zuwa. Motoci na wucewa jifa-jifa, kuma kala-kala, ko wacce da inda ta nufa.

A rayuwarta wannan ba shi ne karo na farko da ta tava fitowa babban titi mai kwalta daga surƙuƙin ƙauyensu ba, sai dai a wannan karon ta fito ne da zummar barin ƙauyen na tsayin shekara guda in Allah Ya sa tana da rai. Asma’u ta fara tambayar kanta game da makomarta bayan ta haife cikinta, amma ba ta samu amsa ba. Wani tunani ta yi ya sa lokaci guda ta fara goge busassun hawayen fuskarta, ta kuma sa a ranta lallai ta daina kukan da take, don a yanzu duk wanda zai wuce yana kallonta.

“Kano! Kano!

Asma’u ta ɗaga kai tana kallon motar Bus da ke ƙoƙarin taka burki inda take tsaye “Malama Kano za ki je?”

Yadda motar ta tsaya saitinta kana ƙofar ta buɗe fasinjojin da ke ciki suka mata caa da ido duk sai ta sake ruɗewa kawai ta ɗaga kai alamar amsawa duk da cewa ba amsawar ta so yi ba a cikin Zuciyarta, don ba ta shirya ba.

“Zo mu je Malama.” Muryar karen mota a karo na biyu ta zame wa Asma’u tamkar umarni, kawai sai ta taka ta shige ta zauna a wajen zama ɗaya tal da ya rage cikin motar inda karen motar ya nuna mata.

Ko da motar ta fara tafiya sai ta ji jiri na kwasarta kamar ta sa ihu ta ce a tsaya ta sauka, sai dai yadda ta ga motar cike da mutanen da ba ta taɓa gani ba hakan sam ba zai yiwu ba, don za ta zama abin kallo ne a wajensu ita kuma ba mai son yawan kallo da cece-kuce ba ce, a hakan ma ba ta tsira ba, don wasu daga ciki sun yi mata ƙuri da ido ‘Kai Allah wadaran mutanen birni in dai su ma haka suke da shegen kallon ƙurillan tsiya’ Ta faɗi hakan a ranta.

“Malama bamu kuɗinki.” Karen motar ya buƙaci ta bashi kuɗi fuskarsa a murtuke. Ƙarfin hali sosai ta yi kafin ta iya cewa, “Nawa ne kuɗin?”

“Ɗari takwas da hamsin ne.” Lokaci guda yawun bakinta ya ƙafe da ta tuna ko ɗari bakwai kuɗinta gaba ɗaya har guzuri ba su kai ba, ta zira hannu cikin bujenta ta fito da ƙullin tsumma, ta kunce ta kwashi duk kuɗin ta miƙa masa.

Karen motar ya karɓa ya lissafa sai ko ya kada baki ya ce, “Malama saura ɗari da tamanin.” Asma’u ta yi shiru kamar ba ta ji shi ba.

“Ko ba kya ji ne.” Ya sake faɗa cikin ɗaga murya, da alama ta fara ba shi haushi.
Idanunta ne suka yi rau-rau kamar za ta yi kuka.

“Sauke ni, don ba ni da wasu kuɗin.”

Ya miƙa mata kuɗinta yana faɗin “Aikin banza, kin san ba ki da kuɗi za ki hau mana mota, dakata Oga mu sauke ta.”

Ya buga motar da ƙarfi, abin da take gudu ya faru hankalin kowa ya dawo kanta, motar ta tsaya cak!

“Bismillah sauka Allah raka taki gona.”

Asma’u ta yunƙura ta tashi za ta fita sai ga hawaye suna ɓulɓulowa daga cikin idanunta. Wannan mutumi duk shi ya ja mata ba don haka ba tana zamanta a ƙauyensu me zai haɗa ta da wannan ƙasƙancin?

Zuro ƙafarta ɗaya ta yi da niyyar sako ta qasa sai kuwa ƙafar ta goce ta faɗo ƙasa ji kake tim, jakar kayanta ta yi gefe guda, mutanen motar suka haɗa baki suka ce “Bismillahi.” Asma’u ta ji faɗuwar nan sosai, don har gwiwar hannunta sai da ta dauje, ta tashi ta ɗauki jakarta ta matsa daga wajen tana karkaɗe jikinta.

Har motar ta fara tafiya sai kuma ta ga ta tsaya ta fara yin baya a hankali.

“Shigo mu tafi Malama.” Muryar karen motar ta yi amsa-kuwwa cikin kunnuwanta, tsayawa ta yi tana kallonsa ya sake cewa, “Ki shigo aka ce kika tsaya kina kallon Mutane.” Ranta ya sosu, ita ma haushinsa take ji yanzu yadda yake kyararta ta ce, “Malam ka ja motarka ku yi gaba, ina ce kai kace in sauka kuma na sauka, na meye za a dawo ana min ihu a ka?” Ta ƙarasa da murguɗa masa baki.

Daga cikin motar ne wani mutum ya yi magana. “Yarinya shigo mana tunda an cika maki kuɗin ko?” Ta kai dubanta gare shi, dattijo ne, sai ya yi mata nuni da wata mata a cikin motar.

“Wannan baiwar Allahn ita ta cika miki ragowar kuɗin.”

<< Kaddarar Mutum 1Kaddarar Mutum 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×