Skip to content
Part 20 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Da fari shawarwarin su Ruƙayya na bin Bokaye da Malamai sun samu karɓuwa sosai a wajen Zubaidah. Sai dai kuma abun kamar turi, domin yanzu sam Ma’aruf ba ya iya ɓoye son da yake wa Asma’u, domin kullum ta Allah fafutukar da yake wajen nemanta ƙaruwa take, gidajen rediyo da talabijin shi kansa bai san adadin nawa ya bada cigiyarta ba, hankalinsa ma ya ƙi ya tsaya waje guda, ba ya Kano ba ya ƙauyensu da ya mayar kamar na iyayensa.

A hankali Zubaidah ta zame jikinta, babu abin da zai sa ta yi ta ɓarnatar da kuɗaɗenta a banza babu biyan buƙata. Ita fa tuntuni soyayyar gaskiya ce tsakajinta da Ma’aruf, babu wani boka ko Malami da yake taimaka mata, haka nan Ubangiji Ya ƙaddara musu son junan su, kai a wannan rayuwar da muke ta JARI HUJJA in banda so babu abin da zai sa Ma’aruf ya tsallake ‘ya’yan attajiran ‘yan matan da ke bin sa ya aure ta, domin nesa ba kusa ba ya fi ƙarfinta.

Kawo yanzu dai ta watsar da batun su Ruƙayya, a halin da ake ciki ma neman zaman lafiya take da mijinta, za ta lallaɓa ta rarrashi kayanta su koma kamar yadda suke da, domin ta auna babu wata rayuwa za ta yi mata daɗi muddin babu Ma’aruf cikin ta, za ta ci gaba da haƙuri har ya manta da wata Asma’u da babu wanda ya san inda take, kai ko da ma a ce an ganta ya aure ta, babu yadda za ta yi da hukuncin Ubangiji.

Ta same shi zaune a gefen gado yana ƙoƙarin cire takalminsa sawu ciki, da hanzari ta isa ta kama ƙafar don ta taimaka masa, sam bai yi ƙoƙarin hana ta ba har ta gama, ya cire rigar saman ya rataye saura yar ciki, ya shige toilet.

Tana zaune har ya yi wanka ya fito.
“Na zo in bada haƙuri kan laifukana Ma’aruf.” Ta faɗa bayan ta rausayar da kai irin na wanda ke neman gafara.

Tsayawa kawai ya yi yana kallonta ba wai don bai fahimci abin da take faɗa ba, me yiyuwa ko don mamakin yadda take rikiɗa kamar hawainiya.

“Ka san ina sonka ko? Bana tsammanin zan iya ci gaba da jure wannan halayyar da kake nuna min, Ma’aruf ka kwan da sanin dole in yi kishi a kanka, don me ba za ka tausaya min ba? Babu fa wata ‘ya mace da za a zo wa da batun kishiya hankalinta bai tashi ba.” Ta ƙarasa maganar da raunin zuciya.

“Kina ban mamaki Zubaidah, wa ya zo miki da batun kishiya, na taɓa faɗa miki cewa ina son Asma’u zan aure ta?”

“Look don Allah Ma’aruf! Ba fa ƙaramar yarinya ba ce ni ta yadda zan kasa gane inda hankalin mijina ya karkata, ka san dai ai a baya ba haka muke da kai ba ko? Ko kuwa yanzu kana so ka nuna min duk wannan faɗi tashin da kake kan yarinyar ba sonta kake ba? Ta yaya hankali zai iya ɗauka? Ni dai abin da nake so da kai ko ma meye na san na yi kuskure kan korar Asma’u daga gidan nan da na yi, mu bar batun wata alaƙarku.”

Tabbas Zubaidah ba baƙuwarsa ba ce, ko wane mutum da ƙaddararsa, ya san cewa tarayya da su Ruƙayya kaɗai ke wahalar da rayuwarta, wannan ita ce ƙaddararta.

“Wannan shi ne abin da ya sa ni mamakin ki; yadda kika kasa aiki da hankali da iliminki kika rufe ido lokaci guda kika kori yarinyar nan, bayan ke kika sa muka roƙi Hajiya ta barta ta zauna a gidan nan har da alqawarin riƙe ta amana, yanzu ina alƙawarin, ina amanar taki? Kuma da kika tashi ai sai ki maida ta inda kika ɗauko ta ko? Shin fushin da mahaifiyar ki take yi da ke baya damunki Zubaidah?”

Ta sa masa kuka “Wallahi yana damuna Ma’aruf, kada ka manta idan na je gidan na gaishe ta ko amsa gaisuwata ba ta yi, sannan kaima kana fushi da ni, ina zan sa raina? Da a ce na san inda Asma’un nan take ni da kaina zan je in ba ta haƙuri, duk da haka ina ji a jikina duk inda take ba ta cikin matsala, na ba ta kuɗaɗenta duka har na ƙara mata da wasu, ba za ta samu matsala ba.”

“Kuɗi ba za su isa hujjar kasancewarta cikin aminci ba, addu’a kawai ita za ta amintar da ita, babban abin damuwar shi ne sam ba ta ƙauyensu inda ke kike jin kin tura ta. Har yanzu fa babu wani jami’i da ya tuhume ki kan salwantar da ‘yar mutane ko? Zubaidah yadda kike tutiyar ke ba ƙaramar yarinya ba ce, na raina wayonki, ban sani ba ko nan gaba ki tabbatar min da haka, ina nufin ki san kanki ki fahimci rayuwa da abubuwan da ta ƙunsa, ki gane cewa ƙawayen banza babu abin da za su tsinana miki face su kai ki su baro.”

Hawaye take share wa, ta san inda ya dosa, ba shi kaɗai ba, kowa ma zai iya fahimtar Ruƙayya ce ta ɗora ta wannan hanyar Allah wadai ɗin da ta bi ta kori Asma’u daga gidanta. Ruƙayya dai wacce a iyakar amintar su ba ta taɓa nuna mata cewa akwai zama da wasu mutanen a gidanta bayan mijinta da ‘ya’yan da za su haifa ba, ta fi koya mata yadda za su rayu su kaɗai.

Duk yadda Ma’aruf yake tunanin nadama Zubaidah ta yi nadama, duk ta yi laushi kamar ba ita ba a ‘yan kwanakin. Wani irin ladabi take masa da bai taɓa sanin tana da shi ba, idan ta fita school da an tashi gida take dawowa babu wannan yawace-yawacen da aka santa da shi, ta tsaya kan ayyukan gidanta babu kasala ko ganda. Kamar ba wannan Zuby ɗin da take matuƙar jin kanta ba.

Sai dai babu wani tabbaci kan hakan za ta ɗore, kishiya fa! Wataƙila kuma Asma’u.

*****
Tunda Asma’u ta tunkari hanyar ƙauyensu, mahaifarta zuciyarta ta cika da tsananin mamaki, wai yanzu hanyar Somayi ce ta koma haka? Babu ramummukan nan da ta sani, yanzu an zuba burji tun daga bakin babbar hanya har cikin ƙauyen, gidan su ya tashi daga na kara, an lailaye shi da siminti, ku san ko wane gidan kara a ƙauyen ya koma na bulon ƙasa ginanne, gini kuma a cikin tsari, an kai musu wutar nepa, don burtsatse injin niƙa da markaɗe yanzu babu wanda babu, mata sun huta da bautar daka. Asma’u ba ta ankara ba sai ga hawaye suna bin kumatunta. Wata sabuwar soyayyar Ma’aruf ta ƙaru a zuciyarta.
Ita da Muntari suka yi ta zagayawa a ƙauyen, har bayan gari inda ta ga makarantar boko da aka gina, ake kuma shirye-shiryen buɗe ta. A gidansu ta sauka, inda su Innaro da tsoho Arzuka suke ta zagaye gidan suna mamaki da sa albarkarsu, wannan gida ko a birni sai haka, hatta gidan mai gari ba zai nuna masa kyau ba.

Tabawa ma ta ci arziƙi, domin an gyara mata nata gidan, mijinta Malam Iro ya rasu tuntuni yanzu ita kaɗai ce sai marayun ‘ya’yanta.
Tunda Asma’u ta zo gidan kullum cike yake da jama’a masu zuwa godiya, a cewarsu ta yi silar yaye kaso casa’in cikin ɗari na wahalar rayuwarsu. Da jagorancin Muntari suka tafi gidansu, wato gidan Maigari, shi ma da ya ganta har hawaye ya yi yana ta sa mata albarka da roƙon ta yafe masa laifin da ya mata bisa rashin sani. Ita ma sai zuciyarta ta karye ta fara kuka.

“Baku yi min laifn komai ba, idan ma kun yi na yafe muku. Allah Ya yafe mana baki ɗaya.”
Sai ga Tasallah da sauran matansa sun iso zauren, Tasallah ma ta fashe da kuka ta ce, “Ki yafe min ‘yar malam, ban san cewa ke alkhairi ba ce ga kafatanin mutan Somayi sai yanzu.”
Waziri kuwa kasa haɗa ido ya yi da ita bare ya iya furta mata wata kalma, sai Maigari da sirikinsa Muntari ne suka roƙar masa gafarar ta.

Ubangiji ma da ya halicce mu muna masa laifi Ya yafe mana bare ita? Ta yafe musu, da kowa ma, har LITI, duk da cewa har yanzu idan ta tuna tana ɗan jin ɗacin abin da ya yi mata, sai dai tana iyakar bakin ƙoƙarin ta ga ta manta da komai.

Muntari ya roƙi su je gidansa. Ba ta musa ba, don tana so dama ta haɗu da Ramatu, babu komai a ranta sai alkhairi. Sun iske Ramatun zaune a tsakar gida tana shayar da ƙaramin ɗanta, Asma’u na cike da fargaba don tana tsammanin ganin su tare da mijinta zai sa Ramatun ta gwada mata haukan kishi irin na baya ta wulaƙanta ta, ita yanzu ba ta da lokacin wannan shirmen, sai ta ga fuskar Ramatun ta faɗaɗa da murmushi, ta miƙe tsaye tana faɗin “La! Asma’u ke ce, yanzu nake shirin zuwa gidan Maigari don ance min kina can.” Ɗaki ta shiga ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa musu. Bayan sun gaisa suka shiga tambayar juna bayan rabuwa.

Ramatu, Munari, Asma’u su ukun nan ƙawaye ne tun yarinta, Munari ta yi aure sai dai ba a nan ƙauyen ba, jihar Maraɗi aka kai ta. Sun tuna baya sosai kan yarintar su, Ramatu ta ce “Asma’u ina neman afuwarki kan abubuwan da suka faru a baya ki yafe min don Allah.”
Murmushi Asma’u ta yi, “Haba Ramatu, laifin me kika min? A wancan lokacin ma duka ƙuruciya ke ɗawainiya da mu, ƘADDARAR MUTUM fa ba ta taɓa wuce shi, Ubangiji dama ya rubuta ke ce matar Muntari ba ni ba, ko da ace tawa ƙaddarar ba ta sa na bar Somayi ba babu abin da zai sauya hakan, ki rungumi mijinki ku zauna lafiya, kar ki sake ki yi abin da zai ɓata ransa komai runtsi.”

Fashewa Ramatu ta yi da kuka, “To ai Asma’u ko banyi abin da zai ɓata ranshi ba, kullum shi cikin ɓata min rai yake. Tunda muka yi aure ba zan ce miki mun taɓa cikakken sati guda muna zaman lafiya ba, cusguna min yake har ta kai ina dana sanin aurensa, Amma na san duk Baba ne ya cuce ni, shi ya ja min ko ma meye, Asma’u ban san me zan yi in burge Muntari ba. Na san ke yake so ba ni ba.”

Asma’u ta tari numfashinta.

“Kash! Me ya kawo wannan maganar Ramatu? Ina so ki cire wannan tunanin daga ranki, ki ci gaba da addu’a kan samun daidaituwar zaman ku, na miki alƙawarin ni ma zan taya ku da tawa addu’ar, kuma ga ni ga Muntarin ai yana jin mu.” Muntari ya sunkuyar da kansa ƙasa alamun akwai ƙamshin gaskiya cikin maganganun matarsa, don haka Asma’u ta ƙudiri aniyar taya su da addu’a tare da fahimtar da shi yadda ya kamata. So take su zauna lafiya kuma cikin aminci da ƙaunar junasu har abada.

<< Kaddarar Mutum 19Kaddarar Mutum 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×