Ramatu ta share hawaye, “Shi kenan na gode Asma’u, Allah Ya tabbatar da naki auren, Ya sa masa albarka Ya ba ku zaman lafiya da mijinki, Ya jiƙan mahaifanki.”
Har ƙofar gida ta rako su tana mata godiya.
Da za su wuce ƙofar gidan Sarkin noma Muntari ya nuna mata Liti cikin bola yana tsince-tsincensa bai ma san a hayyacin da yake ba. Tausayinsa ya kama ta. A fili ta yi masa addu’a kan Allah Ya sassauta masa Ya bashi lafiya. Muntari ya jinjina kai.
“Haƙiƙa samun mai tawakkali da imaninki a wannan zamanin sai an tona Asma’u, yanzu bayan abin da Liti ya yi miki har kina iya buɗe baki ki yi masa addu’ar samun sassauci? Na ɗauka zai zama mutum na farko kuma na ƙarshe a duniya da zai dauwama cikin ƙiyayyarki, domin a baya shi ne silar faɗawar ki cikin ƙunci.”
Murmushi ta yi kana ta ce, “Baka gani ba kuma hakan shi ya zama silar warwarewar wasu tarin matsalolin nawa, na tashi daga jahila na koma mai ilimi, na tashi daga ƙasƙantacciya wadda ake tsangwama na koma wacce Allah Ya ɗaukaka. Babu wani bawa da ya isa guje wa ƙaddarar sa, kamar yadda babu wani abu da zai samu bawan face da sanin Ubangijin sa. Muntari akwai addu’ar da aka hori bawa a duk lokacin da ya ga wani wanda wata masifa ta afkawa;
Alhamulillahil lazii aafaani mimman talaaka bihi wa faddhalani alaa kasiran mimman khalaka tafdhiilaa.
Ma’ana; Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda Ya amintar da ni daga abin da Ya jarrabe ka da shi na masifa, kuma Ya fifita ni a kan da yawa daga cikin waɗanda Ya halicce su fifitawa.
*****
A hankali cikin nutsuwa yake tuƙin, yayin da tayoyin motar ke gangarawa kan burjin. Babu abin da yake faranta masa rai irin idan ya tuna cewa shi ya yi amfani da dukiya tare da wasu hanyoyi da Allah Ya hore masa ya samar da kaso mai yawa na rangwame da sauƙin rayuwa ga mutanen ƙauyen da mafi yawancin ire-irensu tamkar gwamnati ba ta san da zaman su ba. Idan har zai ji yana sha’awar shiga siyasa to a dalilin irin waɗannan ƙauyukan ne.
Ɗai-ɗaikun mutanen da ke tafe kan ababen hawa irin su Keke, jaki da amalanken shanu, sai wasu da ke cikin gonakinsu da ke gefen hanya duk inda ya gifta hannu suke ɗaga masa, maraba da sannu da zuwa tamkar dai sun ga wani babban shugabansu, a haka ya isa cikin ƙauyen. Bai tsaya ko ina ba sai ƙofar gidan Maigari, ya faka motarsa.
Akwai kyakkyawar alaƙa da fahimtar juna tsakaninsa da dukkan manyan da ke ƙauyen.
Tuni jama’a sun cika zauren Maigari har ƙofar gida, ganinsa kaɗai wata rahama ce gare su, don duk lokacin da ya zo sai ya ɗorar musu da wani abu na ci gaba. Har abada suna masa fatan idan har saboda Asma’u ɗiyar marigayi Malam Tanimu yake cika su da waɗannan tarin ababen alkhairai Allah Ya haɗa shi da ita har ma ta zama matarsa. Wataƙila kuma Ubangiji Ya kawo lokacin, domin kuwa yanzu haka da ya kawo musu wannan ziyarar baya zaton Asma’un na cikin ƙauyen.
Muntari ne ya kasa haƙuri sai da ya sanar da shi wannan albishir mai matuƙar daɗi, wanda kuma tukuicinsa tukuici ne mai kauri. Asma’u na tsugunne a gindin murhu tana kwashe dambun shinkafa da zogale da ta kammala, ta tsinkayi sallamar Ma’aruf da ko cikin dubban muryoyi ba za ta taɓa ɓace mata ba, ta tsinci kanta da tsayawa cak da aikin da take tare da zubawa ƙofar shigowa daga zauren idanu, yadda dai ta san shi ma’abocin tarin kwarjini, cikar zati da kamala, babu abin da idanunshi suke kallo face ita. A zuciyoyinsu kaɗai farin cikin sake saduwa da juna ya tsaya.
Bisa jagorancin tsoho Arzuka da suka shigo tare suka isa har rumfar gaban ɗakuna inda Innaro ke kishingiɗe tana hutawa, ganin su ne ya sa ta tashi zaune tana musu maraba da ganin baƙuwar fuskar da ba ta taɓa gani ba.
Muntari ne kawai ya yi wa Asma’u sannu da aiki ta gaishe su su duka biyu, kuma shi kaɗai ya amsa yayin da Ma’aruf ya wuce inda Innaro ta musu shimfiɗa ya samu guri ya zauna. “Banda abun Ma’aruf meye abun jingina mata laifi? Ita da ba da kanta ta bar gidansa ba.” Bayan ta kammala aikin da take ne ta taso ta zo inda suke ta duƙa har ƙasa ta yi musu sannu da zuwa haɗe da sabunta gaisuwa. Hira ta balle tsakaninsu ukun in ka ɗauke Asma’u gefe zaune kan kujerar tsugunno ita da shi suna ta satar kallon juna, tana ta mamakin yadda Ma’aruf ya saba da mutanen ƙauyen kamar dama can ya san su.
Innaro ta umarci Asma’u ta zuba musu abinci. Bayan ta zubo Muntari ya ce a waje za su ci, don haka ta kai musu can da tabarma ta shimfiɗa musu ƙarƙashin bishiyar da ke ƙofar gidan mai sanyi, sannan ta koma ciki ta haɗa musu zoɓo mai ɗan karen daɗi da sanyi. Daga gidan Muntari ma ya sa an kawo ɗan waken da Ramatu ta yi haɗe da farfesun kaji da ya sa aka yanke tun tuni, nan suka hau ci Ma’aruf na yaba girke-girken duk da shi ba ma’abocin abincin gargajiya ba ne, amma wannan ya masa daɗi.
Bayan sun kammala akwai ganawa ta musamman tsakanin Ma’aruf da Asma’u. Zaune suke a cikin mota tsayin wasu ‘yan mintuna shiru ya ratsa tsakaninsu, babu mai magana. Zuwa can Ma’aruf ya kawar da shirun da faɗin, “Ina kika sa wayarki ne Asma’u?”
Ta ce, “Tana ɗaki cikin jakar kayana, ka san layukan can ba sa aiki a nan.” “Na sani amma me ya hana ki nemi wani sim card ɗin ki sa, ko da yake ta yaya ma za ki yi hakan bayan kina son wahalar da waɗanda suke nemanki ko?”
Sai yanzu ta gane dalilin fushinsa, wato babban laifinta da ba ta neme shi a waya ba bayan Zubaidah ta kore ta, maimakon haka ma sai ta rufe wayarta gaba ɗaya. Duk da haka bai kamata ya zarge ta ba, domin Zubaidah matarsa ce duk abin da ta yi ta yi ne saboda ta nesanta shi da ita, don me ita za ta ci gaba da bibiyarsa bayan duk abin da ya faru?
“Sam bai kamata ka ga laifina ba kan abin da ya faru Daddy. In ba dole ba me zai sa ni irin wannan tafiya babu sallama bare godiya bisa halaccin da kuka min, na san kuma ka san babban dalili na na ƙin dawowa Somayi da….” Kafin ta ƙarasa kuka ya ƙwace mata. Tausayinta ya kama Ma’aruf, ji yake babu abin da zai hana shi aurenta muddin za ta kwantar da bankalinta ta daina zargin kanta da cin amanar Zubaidah da Hajiya ya ce. “Shi kenan ya isa don Allah, bana son wannan yawan koke-koken naki, ke kuwa kin mayar da shi abin yi, yanzu ki amsa min tambayar da na yi miki a baya shin kin amince za ki aure ni, idan na koma in turo magaba ta na ayi magana?”
Asma’u ta share hawaye, “Ni duk yadda ka tsara shi kenan.” “No Asma’u ba haka nake son jin ba, ban son in riƙa jin kamar na tilasta miki, kin san kuma maganar aure ba magana ce ta ɓangare ɗaya ba, dole sai da amincewar ɓangarori biyu muddin ana son inganta tushen sa, don haka yana da muhimmanci ki tabbatar min da amincewar ki don Allah.” “Na amince, amma don Allah bayan abin da ya faru me ka fahimta daga ɓangaren Hajiya? Na san dai Zubaidah har abada ba za ta taɓa son wannan al’amarin ba, Hajiya kuma ‘yar ta ce, ba ka jin kamar ban kyauta musu ba?” Murmushi ya yi sosai, “Wannan tambayar ta ki, ba ni da amsarta yanzu, amma ki jira zuwan Hajiyar gobe.” Ta dafe ƙirji haɗe da zaro idanu, “Yanzu kana nufin Hajiya na tafe gobe? Shin dama ta san ina ƙauyen nan?” ‘Yar gajeriyar dariya Ma’aruf ya yi yana dubanta. “Nine na buga waya na faɗa mata, ba ita kaɗai ba, hatta Hajiyarmu ma na faɗa mata.” “Kai don Allah?”
Sannu a hankali suka yi ta hira mai cike da fahimtar juna suna sake zayyane wa juna asiran zuƙatan su har aka kira sallar la’asar. Sai yamma sosai Ma’aruf ya bar ƙauyen.
Kamar yadda ya faɗa kuwa washegari sai ga Hajiya. Suna yin ido huɗu Asma’u ta faɗa jikinta yayin da kuka ya ƙwace mata, ita ma Hajiyar sai ga ƙwalla na zuba a idonta. Asma’u ta ce, “Hajiya ki yafe min, sam ba da son raina na taho ba, babu yadda banyi da Aunty Zubaidah ta kawo ni gida ba ta ƙi, ta yaya zan tafi in barki Hajiya?”
“Share hawayenki kin ji ɗiyata, duk abin da kika ga ya faru da bawa muƙaddari ne daga Allah, ni dama damuwata ita ce rashin sanin hannun da za ki faɗa, tunda na san zai yi wahala ki dawo ƙauyen nan, don haka duk tsayin kwanakin nan addu’a nake kan Ubangiji Ya kare ki a duk inda kika kasance, sannan tun ranar da Allah Ya haɗa ni da ke nake miki fatan ki samu miji na gari, wanda zai daraja ki, Wallahi har Nasir na sa ya nemi aurenki Allah bai yi ba, ashe Ma’aruf ne rubuce a ƙaddarar ki. Don an miki fyaɗe ba yana nufin rayuwarki da farin cikinki sun zo ƙarshe ba. Sannan ina so ki sani; shi namiji ba ya fin ƙarfin auren ko wace irin mace a duniya, ita macen ce dai take kai wa munzalin da tafi ƙarfin namiji ya aure ta, domin ita ce a ƙasan sa.
“Ma’aruf ya faɗa min duk yadda kuka yi, kuma ya ce cikin satin nan zai turo manyansa, hakan na nufin ya shawo kan duk wani abu da kan iya kawo cikas cikin lamarinku, Hajiyarsa har gida ta zo ta same ni, ta ce min za ta zo ta gan ki, Asma’u ki ƙara gode wa Allah kan baiwar da Ya miki, ba ko wace ‘ya mace da ta haɗu da ƙaddara irin taki ba ce ke samun irin damarki.
Abu na gaba ina so ki manta da batun Zubaidah da duk wani kishi da za ta yi, ki fito ku goga duk wacce ta fi kyautata wa miji ita ce kan gaba. A zaman da na yi da ke na san ke mace ce mai haƙuri, to ki ƙara ruɓanya haƙurinki a kan na da, domin ita rayuwar duniyar dama dukkanta haƙuri ce, Hausawa sun ce zo mu zauna, zo mu saɓa, sai dai mai hankali shi ke ƙoƙarin kaucewa duk abin da zai sa a saɓa.”
Asma’u ta share hawaye, haƙiƙa maganganun sun ratsa ta sosai, Hajiya Yagana mutum ce da ta san dattako, ta cancanci duk wata kyautatawa da mutuntawa daga gare ta, ta ɗaura ɗamarar bin ta sau da ƙafa.
Sati guda a tsakani aka kawo kuɗin aure, lefe da sadaki duka inda aka sa wata guda kacal za a yi bikin. Lokacin bikin ya kama tsakiyar watan Maulidi.