Skip to content
Part 23 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Bai musa ba, domin ya gamsu da kalaman Asma’u, ya kuma yaba da hankalinta, yarinya ce amma tana da hangen nesa, yana matuƙar son zaman lafiya da haɗin kan iyalinsa, sai dai ya san halin Zubaidah sarai, wasu lokutan rikiɗa take, saƙon da ta tura masa bai zama lallai har cikin zuciyarta haka abin yake ba, kamar yadda son sa ke makantar da ita, haka ma kishinsa ke rufe mata idanu. Sai dai ko ma mene zai faru dolenta ta ɗauki dangana da haƙuri.

A daren kuwa ya je gare ta, ga mamakinsa sam ba ta wahalar da shi ba wajen shawo kanta irin yadda ya yi tsammani.

Ko da yake a tafiyar nan da ta yi Maiduguri ta sake ɗaukar wani babban darasin kan rayuwar zaman aurenta, ta gane cewa yanzu ba irin da ba ne, ba ita kaɗai ba ce, gashi dai tun ba a je koina ba Ma’aruf ɗin da take haƙilo kansa ya yi watsi da ita, ya gwada mata a duk lokacin da ta shirya zama da abokiyar zamanta yana maraba da ita, idan kuwa ba ta shirya ba ga hanya nan.

Ta tafi Maiduguri ne a ƙoƙarinta na gwada wa Ma’aruf kuskuren auren Asma’u da ya yi, ta ci alwashin wahalar da shi son ranta, to amma ko sati ba ta yi ba a can ta samu labarin sun bar ƙasar, ta sha kuka kamar ranta zai fita, don ta tabbatar yanzu ba ta ita yake ba a daidai lokacin da babu wanda za ta kaiwa kuka ya saurare ta har ya gane muguwar illar da aka mata. Suma ‘yan Maidugurin haƙuri suka ba ta, zaman kishin nan fa ba wani abu ba ne matuƙar an ɗauki rayuwar duniya sassauƙa.

Ranar da ta cika kwana goma sha uku da dawowa Kano ɗakin mijinta bayan ta yanke shawarar watsar da makamanta sannan suma suka dawo daga honeymoon din su.

A kan idonta suka fito daga mota suna saƙale da hannun juna. Abun ya fi yi mata kama da irin yadda ita ma suka kasance lokacin na su amarcin da shi, wani abu ya tokare mata ƙirji, a hankali ta saki labulen ta koma ta zauna kan kujera, ta dafe kanta da ke sarawa kamar ya faɗi.

Motsin shigowar Nabil ya sa ta saita kanta da nutsuwarta, ya yi mata albishir da dawowar ɗan uwansa. Shi Nabil bai ma san ta je Maiduguri har ta dawo ba, ya suri Khalifa da ke wasa suka yi waje. Fitar sa ta yi dai-dai da zubowar hawayenta.

Babban dalilin da ya zaunar da waɗannan ma’aurata lafiya bai wuce yadda ƙaramar wato Asma’u ke iyakar bakin ƙoƙarinta wajen bin uwargidanta Zubaidah sau da ƙafa tana ba ta girmanta yadda ya kamata ba, ga yawan addu’o’inta kan neman haɗin kan su, bugu da ƙari ƙaunar da ta ke gwada wa Mahmud Khalifa. Wanda ya so naka ko kaima ka so shi matuƙar ɗan halak kake.

Ma’aruf yana ƙoƙarin gwada tattali ga ko waccen su, dukkan su don yana son su ya aure su, don haka babu wacce a dalilin ta zai juya baya ga ‘yar’uwarta. Irin tunanin adalin namiji kenan.

ƘARSHE

Mu haɗu a wasu sababbin littattafan;

Haɗuwar Zuciya

Ranar Kuskure

Girman Alkawari

Kaɗan daga littafin GIRMAN ALƘAWARI

Isowarsa bakin office ɗin ne kuma ya riski wata sabuwar matsalar. ‘Wato su dai mata yadda farkon sunan su ya fara da harafin (M) kamar hakan na nufin Matsala kenan.’ A iyakar tsawon rayuwarsa wannan ita ce fahimtar da ya yi musu. Tunanin da ke zuciyarsa kenan har lokacin da ya iso daf da su, sun kai su biyar tsaye cirko-cirko suna dakon jiransa.

“Me ya faru a nan?” Ya tambaya fuskarsa ɗaure.

Ɗaliban suka fara zubo zance ratata in ka ɗauke ɗaya daga cikinsu da ke ta faman sheshsheƙar kuka da matsar ƙwalla.

Abinda ya iya fahimta a gaba ɗaya zantukan nasu sun kawo masa ƙarar Jawahir Alkassim ne sakamakon rikici da suka yi da wannan mai kuka a kan wajen zama har Jawahir ɗin ta fasa mata baki da hanci suna ta zubar da jini.

Ransa ya ɓaci sosai da fitinar yarinyar, ya buɗe office ɗin ya sa kai ya ce, “Su biyo shi ciki, ɗaya kuma ta je ta kirawo mashi Jawahir ɗin.”

Da kansa ya yi wa yarinyar treatment dai-dai lokacin Jawahir ta shigo tana harare-harare. Ya jefa mata wani mugun kallo da ya sa hantar cikinta kaɗawa amma ta murje saboda taƙamar da take yi a kan aikata abinda ya fi dacewa da abokiyar faɗan ta.
Ya miƙe tsam ya koma mazauninsa ransa na suya, ji yake idan ba farfasa mata jiki ya yi da dorina ba ba zai taɓa hucewa ba.

“Me ya sa ki ka yi hakan Jawahir?” Ya tambaye ta da ɗaurarriyar fuskarsa. Ta fara yi masa bayani, a tashin farko ya fahimci ba ta da wata gaskiya kamar dai yadda ‘yan kawo ƙarar suka faɗa, ya buga mata tsawa! “Tsugunna a nan.”

Ta tsugunna tana kumbura baki har da ƙananan guna-guni.
Wannan ya ƙara tunzira shi ya cire bulala ya yi mata biyar masu kyau, sannan ya sa ta ƙara da kamun kunne.
Duk tsananin dauriya irin ta Jawahir sai da ta fitar da ƙwallar wuya, ga tsananin baƙin ciki musamman kan rashin bata gaskiyar da take ganin ita ce mai ita, kuma ta hukunta Zainab Usman ne bisa yunƙurin ƘWATAR ‘YANCINTA, ita mutum ce da ba ta ɗaukar raini daga kowa, ba ta barin ko ta kwana, ba ta yafiya, ba ta manta ɗaukar fansa, ko shi ɗin ma bai daki banza ba, dole za ta hukunta shi dai-dai da girman laifinsa gare ta.

Yana daf da isowa gare ku.

RANAR KUSKURE.

Tsakure daga Babi Na Biyu.

Ƙwalla ta cika idanun Baffa taf, cikin tsananin takaici da ɓacin rai yake duban yadda nake raɓe a bayan Samuel ina kuka.

“Albasa ba ta yi halin ruwa ba Shatu, ni dai ban bijirewa iyayen da suka haife ba, amma yau na haifi ‘yar da ta zaɓi saurayi fiye da ni, saurayin ma kafuri, in dai haka ne kuwa babu ni babu ke Shatu, ki nemi wani uban ba ni ba.”
“Kayya! Bawuro ai hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar.” In ji Malam Jangudo.

“Tuni ma zan datse shege in jefar.”
Yaya Baɗɗo ya matso daf da ni, “Wai meye a ƙwaƙwalwarki ne Shatu? Ki rabu da mutumin nan ki zo mu tafi gida kin ji ko?”

Yana rufe bakinsa shima yaya Giɗaɗo cike da takaici ya shigo da tasa buƙatar duk dai a kaina, “Shatuwa don Allah ki rufa wa kanki asiri ki rufa mana, ki taho mu koma ruga kafin gari ya waye sauran mutane su farga da abin kunyar da ki ka aikata, wallahi ko a yanzu kin gama zubar da mutuncin ahalinmu baki ɗaya.”

Malam Jangudo ya cafe, “Ai ba ahali kaɗai ba, rugarmu gaba ɗaya ta zubarwa da mutunci, ta tonawa asiri, Shatu ke fa tsatson fulani ce da aka sani da kamun kai, yau an wayi gari kin sa ƙafa kin yi fatali da duk wata tarbiyya da kunyarki ta ɗiya mace wai ke Ahlil Khitabi ki ke so.”

Kukan da nake ya tsananta saboda ba ni da baki ko kalamin da zan iya fahimtar da su Baffa cewa ba ni ke aikata duk waɗannan abubuwan ba, zuciyar da ba ni da iko a kanta ke rabar da saƙonni ga gangar jiki, jini zuwa ƙwaƙwalwata, su kuma suna karɓa, ta yaya zan iya fahimtar kuskure nake aikatawa ko dai-dai?

Duka suna tafe gare ku da izinin Ubangiji.

<< Kaddarar Mutum 22

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×