Tafiya mai tsananin nisa a gare ta, dazuzzuka da garuruwa kawai ake cimma ana wucewa, har yanzu kuma ba a zo Kano ba, wasu tuni sun yi barci abinsu a cikin motar, amma ita damuwar Zuciyarta ba za ta taɓa barinta ta runtsa ba…kai a tsammaninta ma barci tuni ya ƙare a cikin rayuwarta tunda an raba ta da Inna, hawaye suka biyo kuncinta, a hankali ta sa hannunta ta share.
Lallai Kano na da nisa da ƙauyensu, har sai da zaman motar ya gundire ta. Tuntuni amai ke yunƙurin taso mata sakamakon wani turare marar daɗin ƙamshi da ya haɗe motar, dauriya kawai Asma’u take tana addu’ar Allah Ya tsayar da shi, ko ba komai tana gudun wulaƙancin karen motar nan da ya tsane ta babu gaira ba dalili.
Duk yadda ta so ta riƙe aman nan sai abun ya ci tura, ya ƙwace mata ba tare da ta shiryawa zuwansa ba, duk ta feshe kan malejin motar, inda kuma a nan ne karen motar nan ke zaune daga gefe, kaɗan ya rage ta yi masa a jikinsa, mutanen da ke kusa da ita duk suka kame jikinsu gudun kar ta ɓata su, amma duk da haka sai da ta ɓata wasu, ita ma abun sam bai mata daɗi ba, nan fa mutumin ya fara bala’i ta inda ya shiga ba nan yake fita ba.
“Billahillazi tunda na ga wannan yarinyar na san matsala ce, sai da fa na sauke ta aka samu wani gabin ya dawo mana da ita, gashi nan ta ɓatawa mutane sit, aikin banza kawai.”
Cikin Asma’u na da matsanancin laulayin da duk lokacin da ya motsa mata sai ta nemi ficewa daga hayyacinta, don haka tana iya sauraren yadda kowa a cikin motar yake tofa albarkacin bakinsa kan aman da ta yi, amma kuma babu abin da yake tasiri a jinin jikinta face larurarta da damuwar da take ciki.
“Ku yi haƙuri don Allah ku yi haƙuri.” Shi ne kawai abin da take iya faɗa cikin karyayyiyar muryarta mai cike da sarewa
Dole direba ya faka motar, aka saka ta ta wanke wurin da ruwa sannan aka ci gaba da tafiya. Ta kasa ɗaga ido ta dubi kowa sai sharar ƙwalla da kukan zuci kawai take. A haka suka iso Kano.
“Har anzo Kano ko?” Wani ya tambaya yayin da wani daban ya bashi amsa “Anzo kam, yanzu haka muna kasuwar Dawanau.” Asma’u ta ɗaga kanta ta kalli waje, sai ta ga kamar guguwa ce ta turniƙe a sararin samaniya, ga motoci manya da ƙanana da babura sun cika titi taf ko wanne na neman hanyar wucewa, wannan ƙurar kuwa ba komai ba ne face hayaƙin motocin da babura.
Tunda Asma’u take a rayuwarta ba ta taɓa ganin gari mai cikowar gine-gine, ababen hawa da jama’a kamar Kano ba, a yadda ta ji mutumin nan yana faɗa ma nan gefen garin ne ba a shiga cikin ƙwaryar birnin na Kano ba. Idanunta kawai take ba haƙƙinsu ba ta ankara ba har aka shigo tasha, sam ta manta da batun Malam Yahuza Mai Dhala’ilu.
Karen motar nan ta ji ya ce, “Malama sauko mana ko ba za ki sauko ba?” Ta juyo ta watsa masa harara da dara-daran idanunta da suka kaɗa saboda kuka, ta sungumi jakar kayanta ta dirgo daga motar.
Cikin ƙanƙanin lokaci kowa ya watse daga jikin motar, ya rage sai ita da ba ta san inda za ta nufa ba, ta ja gefe guda ta tsaya tana raba idanu cikin tashar da kowa sabgar gabansa yake yi babu wanda yake ta ita, dama haka ta yi tsammani, wa za ta dosa a yanayin da ta fuskanci wasu na mata kallon almajira wasu kuma mahaukaciya, gashi yamma ta yi sosai dare ya fara yi, hasken fitilun lantarki na masu saye da sayarwa ya fara tasiri a ko ina cikin tashar, a karon da babu adadi ta ji hawaye sun fara bin kuncinta.
Kafin rana ta faɗi ta tambayi mutane sun fi ashirin, amma babu wanda ya ko taɓa sanin labarin Malam Yahuza Mai Dhala’ilul Khairati. Kusan duk wanda ta tambaya shi ma sai ya kwararo mata tasa tambayar, wato WACE UNGUWA? Nan ake yin ta domin ba ta ma san akwai wasu unguwanni a garin Kano ba. Daga ƙarshe sai mutanen suka daina sauraron ta.
Asma’u ta ci gaba da yawata wa a cikin tashar nan tana aikin neman wanda ya san Malam Yahuza Mai Dhala’ilu, duk da cewa babu mai kula ta, ita ma ta daina kula kowa, domin yanzu yunwa da ƙishirwar da su ke addabatar ta tun a cikin mota sun fara cin ƙarfinta.
Bayan ta gaji da yawo ne ta samu wani guri ta zauna, daga inda take tana iya hangen wata rumfar masu sayar da abinci tana ganin abinci kala-kala suna kai kawo har da wanda ba ta sani ba, ƙamshi na ta tashi irin wanda ba ta taɓa ji ba a rayuwarta, sai dai ba ta da ko sisi.
Sannu a hankali jama’ar da ke cikin tashar nan suka fara watsewa ya rage sai ɗai-ɗaiku da ire-iren masu saye da sayarwa, kawo yanzu dai Asma’u ta kasa jure yunwar da ke neman kifar da ita a wurin, don haka ta fara taku cikin sassarfa zuwa rumfar masu abincin, niyyarta ta roƙe su su sam mata don ba ta jin za ta iya ci gaba da riƙe kanta, amma ko da ta zo daf da wajen sai ta kasa aiwatar da abin da ta zo yi.
Tsananin rashi bai taɓa saka Asma’u roƙo ba, tana da matuƙar juriya, waje ta samu gefe guda ta rakuɓe tana kallon yadda wasu ‘yammata suke gudanar da kasuwancin abincin su, suma suna ganinta amma babu wanda ya damu da ita bare zamanta, bisa ga dukkan alamu ma ba yau suka saba ganin ire-irenta a wajen ba.
Ba za ta iya gane yadda lokutan agogo suke tafiya ba sai dai tana zaune a nan inda take masu zuwa sayen abincin nan wanda galibinsu maza ne suka ɗauke ƙafa tsaf ma’ana kasuwa ta tashi aka rufe shagon kuma ‘yammatan nan da za su tafi ko kallon inda take ba su yi ba, lallai rayuwar birni ta wuce duk tunaninta, sai kuma gurin ya koma tsit duk da cewa akwai gilmawar mutane jifa-jifa.
Miƙewa ta yi tsam ta isa ga rumfar dai-dai ƙofar shagon nan ta zauna, a iyakar lisaafin da kwanyarta ta lissafa mata nan ne inda za ta kwana, don haka ta shimfiɗa gyalenta a ƙasa ta yi matashin kai da ledar kayanta ta yi kwance a wurin, sai dai kwanciyarta ke da wuya cikinta ya yi wata irin murɗawar da dolenta babu shiri ta tashi zaune dafe da cikin, ba ta san lokacin da ta rushe da kuka ba.
Sai da ta yi kukan nan mai isarta sannan ta koma ta kwanta tana faman murƙususu.
Duk daren daɗewa dama Asma’u ta san wannan ranar za ta zo, ranar da za ta yi dana sanin baro ƙauyensu ta zo inda babu wanda ta sani babu kuma wanda ya santa, to amma sam ba ta so ta yi dana sanin, don wannan shi ne kaɗai zai kuɓutar da ita da Innarta, sunan abin da ta yi gudun abin kunya, don haka ba za ta bari ta karaya ba, dole ta koyi jure duk wata wahala. Tun tana iya buɗe baki ta yi kuka har ta kai ƙarfinta ya qare gaba ɗaya, don haka ta yi lamo a wajen tsakanin rayuwa da mutuwa.
inda ɗan’adam yake ba zai iya rayuwa babu ci ba sha ba. Cikin daren nan Asma’u ta farka daga ɓarawon barcin da ya iya yi mata kutse a halin da take ciki. Har yanzu dai yunwa ce da ƙishi suke ɗawainiya da ita, kawai ta tsinci kanta tana fagamniya a cikin tashar nan, har sa’ar da Allah Ya kawo ta wani ƙaramin masallaci da aka tanadi mazuban ruwa a kusa da shi, ta sani an yi tanadin randar ne kawai don al’ummar Annabi su amfana, a ko ina ana yin wannan.
Tana leƙa randar nan sai ga ragowar ruwa, don haka ta duƙa ta ɗauki moɗa ta kwalfo ta kai bakinta, ba ita ta ajiye moɗar ba sai da ta ji ruwan nan ya cika mata ciki taf! sai me? Kanta ne ya fara juyawa lokaci guda jiri ya fara kwasarta ta zube a gurin.
Wani irin wahalallen amai ta fara yi da yake neman haɗowa har hanjin cikinta su fito waje, daga nan dai Asma’u ba ta sake sanin duniyar da kanta yake ba.