Hayaniyar jama’a sama-sama ta riƙa ji, ga kuma wani irin sanyi da yake busa ta ko ta ina, ta buɗe idanunta a hankali. Ubangiji Shi ke rayawa da kashewa, duk tsananin wahala sai kwana sun ƙare ake mutuwa, ita ma ba ta mutu ba. Yunƙurawa ta yi ta tashi zaune a wahalce, sam ba ta yi mamaki ba da ta ji masassara ta rufe ta.
Ta tuna rabonta da Sallah tun la’asar ɗin jiya, ita da babu sallar da ke shige ta lokacin tana ƙauyensu, a haka tana maƙyarƙyata kanta na juyawa ta tashi tsaye tana laluben gwangwanin alwala.
A daddafe ta ɗaura alwala ta shiga zagayen masallacin nan ta yi Sallah, (abin ka da masallacin kasuwa, ba a sallar asubah). Tana zaune a wajen ba ta tashi ba har gari ya fara wayewa, ta fara ganin komai garau ga mutane sun fara zirga-zirga, tunanin abin da ya wakana jiya ya faɗo mata, ta shafa addu’a ta miƙe da sauri ta fara neman inda rumfar masu abincin nan take, kayanta za ta je ta ɗauka.
Ko da ta iso rumfar sai ta tarar tuni masu abincin sun buɗe har sun hura wuta sun ɗora manyan tukwanen su na sanwa, ta duba sai ta ga kayanta basa nan, ba wasu kayan kirki ba ne fa tsummokaranta ne na sawa.
“Ke! Ke!! Bar wajen nan.” Wata kakkausar murya daga ƙofar shagon ta buga mata tsawa, “Ki bar wajen aka ce.” Kamar ta arce a guje, sai dai ba za ta iya haƙura da kayanta ba, su kaɗai take da su duk duniya, don haka ta kai dubanta ga tafkekiyar matar mai manyan idanu, tunda take ganin mutane masu girman jiki ba ta taɓa ganin mai girman jikinta ba, ta ɗan ɗaga sautin muryarta kaɗan ta ce, “Hajiya kayana zan ɗauka don Allah.”
“A gidan uban wa za ki ɗauki kayanki, wane shegen yace ki ajiye min kaya a nan?” Duk da a tsorace take ta samu sukunin cewa da matar “Ki yi haƙuri don Allah Hajiya.” Matar ta watsa mata harara “Maza gasu can gindin murhu ki je ki ɗauka ki ɓace min a nan.”
Asma’u ta juya wajen murhun, sai yanzu ta lura da kayanta, ta lallaɓa ta isa wajen da su ke, ta ɗauka kenan za ta tafi sai ga wata matar daban ta yi sallama, ko da ta juya sai suka yi ido huɗu da matar nan da ta cika mata kuɗin mota, matar ta ƙare wa Asma’u kallo sosai bisa ga dukkan alamu ta gane ta ta ce, “Yarinya zo mana.”
Asma’u ta matsa kusa da matar, ko ba komai ta taɓa taimakonta, tana da kyakkyawar Zuciya. Matar fara ce tana da bille guda ɗaya a saman kuncinta shekarunta za su doshi arba’in da biyar.
“Me kike a cikin tashar nan har yanzu baki tafi ba? Matar ta tambaye ta. Shiru ta yi kanta duƙe a ƙasa. “Ko baki san inda za ki je ba?” Ta sake tambayarta, wannan mai abincin kuwa tana tsaye tana kallonsu ta matso ta ce “Kin santa ne Hajiya Yaganah? Da alamu cikin tashar nan ta kwana, kuma na ga ba mahaukaciya ba ce.” Hajiya Yaganan ta ce “Wallahi mota ɗaya muka hau da ita jiya tun daga Maƙerawa abar tausayi, shigo daga nan ciki ki zauna yarinya.”
Asma’u ta matsa ta zauna kan wani bencin katako guda ɗaya tal da ke waje, Hajiya Yaganah da matar suka shige cikin shagon inda ake shiga da abinci, bisa ga dukkan alamu su biyun sun san juna sosai, Asma’u ta fara sa ran samun taimakon farko a garin Kano. Tana zaune a wajen tana aikin saƙawa da kwancewa ƙamshin turirin abinci duk ya ruɗa ta, gashi tun jiya babu komai a cikinta face ‘yan hanji, tana jin yadda cikin ke hautsinawa.
Wata budurwa za ta kai sa’arta cikin ‘yammatan jiyan nan ta fito daga cikin shagon, wanda duk shara-shara irin na labulen da aka sa baka iya hangen wanda ke ciki, hannunta ɗauke da wani ƙaton kwando cike da kwanukan zuba abinci ta isa ga wani ƙaton tebur kusa da murhunan abincin ta ɗora a kai.
Bayan budurwar ta buɗe wani mazubi ta ɗebo shinkafa ta zuba cikin faranti, ta sake ƙara taku kaɗan zuwa inda wata tukunyar take ta fara ɗebo jar miyar da ke ta faman ƙamshi tana zubawa kan shinkafar nan har da nama, ta sa cokali, yawun bakin Asma’u tuni ya tsinke, ga tarin mamakinta kuwa sai ta ga budurwar nan ta nufo ta, sannan ta ajiye abincin kusa da ita ta ce, “Gashi ki ci.” Budurwar ta juya ta koma cikin shagon, sai kuma gata ta dawo da ruwa a kofi ta sake ajiye mata.
Wannan duk alfarmar Hajiya Yaganah ce, matar da ta fara taimakonta tunda ta baro ƙauyensu, ba ta tsaya jiran komai ba ta kauda cokalin da ke cikin abincin ta sa hannu ta fara yanka loma, tunda take a rayuwarta ba ta taɓa cin nau’in abinci irin wannan ba, nan da nan kuwa ta tashi da abincin duk yawansa sai a lokacin ta ji ta fara dawowa hayyacinta, ta sha ruwa ta yi hamdala ga Ubangiji.
Asma’u na nan zaune a wurin Hajiya Yaganah da mai abinci suka fito daga shagon, wajenta suka nufo, sannan suka zauna a bencin da take zaune kusa da ita. “Yarinya mene ne sunanki, da alama baki san inda za ki je ba a garin nan, shin ɓacewa kika yi ne?”
Ƙwalla ta cika idanunta taf ta ce, “Ba ɓacewa na yi ba, ban san kowa ba a nan kawai tahowa na yi.”
Hajiya Yaganah da mai abinci suka haɗa ido sannan suka juya suka kalle ta, “Ke ko wace irin matsala ta rabo ki da gida da ƙuruciyarki, kin ko san yadda garin nan yake?”
Fashewa ta yi da kuka. “Wallahi ni ma ba da son raina na taho ba ƙaddara ce ta rabo ni da gida, Innata tana can ban san halin da take ba, gashi har yanzu ban samu wanda ya san Malam Mai Dhala’ilu ba.”
“Wa ne ne kuma Malam Mai Dhala’ilu?” Suka tambaye ta. Ta ce da su, “Abokin mahaifina ne.” Nan ta ba su wani ɓangare na labarinta, dalilin barowarta ƙauyensu.
Sun gamsu sun kuma amince da ita don yarinyar kwata-kwata ba ta da wayewar da za ta iya shirya musu ƙarya saboda ta raɓe su ko ta cuce su, bugu da ƙari sam ma ba ta yi kama da muguwa ba.
Hajiya Yaganah ta sauke ajiyar zuciya, “Tirƙashi! A gaskiya yarinya duk da irin ƙalubalen da kika baro a ƙauyen ku kin yi wauta da kika zo garin nan ba tare da kin san taƙamaiman inda shi Malamin yake ba, Kano na da girman gaske, sannan unguwannin da ke cikinta ba su da iyaka, kin ga kuma shi Malam Yahuzan ke kanki baki san unguwar da yake ba, don haka abun zai miki wahala samunsa.” Ta ɗan yi jim tana tunani kana ta ci gaba, “Sai dai zan miki wani taimako guda ɗaya idan kina so.”
“Ko wane irin taimako ne Hajiya ina so.”
Zan bar ki a gidana ki zauna ki yi rainon cikin ki har ki haife shi, ke na ma yi miki izinin ki zauna iyakar zaman ki, kuma duk lokacin da kika shirya komawa da kaina zan raka ki har wajen mahaifiyarki, ai ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne. Yanzu ki tsaya nan wajen ƙawata Hajiya Balaraba, zan je kasuwa in dawo sai mu tafi da ke, kin ji?”
Asma’u ta jinjina kai cike da gamsuwa kana ta ce, “Shi kenan Hajiya na gode Allah Ya saka da alkhairi.”
Haƙiƙa Asma’u ta ji daɗin wannan albishir, kasancewar ba ta da wata mafita da ta wuce wannan. Hajiyar ta yi musu sallama ta tafi. Ba ta jima da tafiya ba itama Hajiya Balaraba ta wanke ƙafafunta ta damƙa komai gun yaranta ta bar shagon.
Haka nan Asma’u ta ci gaba da zama a wajen har lokacin sallar azahar, ta tashi ta isa wajen budurwar nan da ta kawo mata abinci har da ɗan russunawarta kaɗan ta ce, “Don Allah ki taimaka min ina son inyi Sallah.” Budurwar ta dakatar da tuƙin sakwarar da take ta juyo ta dube ta sannan ta ƙwala kira ga ɗaya daga cikin abokan aikinta.
Bayan ta fito ta umarce ta ta ɗebo mata ruwa a buta, ta nuna mata banɗaki, sannan ta ɗauko darduma ta shimfiɗa mata a cikin shagon.
Bayan ta idar da sallah ta ci gaba da zama a wajen tana jera addu’o’i ga Innarta da ita kanta, sannan Hajiya Yaganah da Hajiya Balaraba da suka ba ta taimakon farko ba tare da sun san ko wace ce ita ba.
Masu sayen abinci ne suka fara shigowa cikin shagon, don haka Asma’u ta taso ta fito waje zuwa wajen zamanta na farko ta zauna.
Da lokacin cin abincin rana ya yi ma haka budurwar nan ta sake zubo mata ta ci ta ƙoshi.
*****
Wuninta guda cur a shagon abincin nan Hajiya Balaraba ba ta dawo ba bare Hajiya Yaganah da ta yi mata alƙawarin dawowa ta tafi da ita gidanta.
Wasa-wasa dare ya yi babu ɗuriyar ko guda daga cikinsu, har lokacin da yaran Hajiya Balaraba suka tattara kaya suka kulle shago za su tafi. Ɗaya daga cikinsu wadda ita ce ta kawo mata abinci karo biyu ta dube ta.
“Ga shi za mu tafi ke kuma har yanzu Hajiya ba su dawo ba, ina ganin ma fa ba za su dawo ba sai gobe, ya za a yi kenan?”
Shiru Asma’u ta yi tana kallon su ta rasa abin da za ta ce musu, ta tuna jiya ma a cikin tashar ta kwana babu kuma abin da ya same ta, don me yau ma hakan zai gagare ta tunda ba ta da inda ya wuce nan ɗin a halin yanzu?
“Babu damuwa ku je kawai Allah Ya bamu alkhairi.” Su duka ukun suka kalli juna a tare, sannan suka ɗan tsaya jim kamar suna tunanin wani abu, sai kuma suka fara takawa a hankali suna ƙoƙarin barin wajen. “Sai da safe.” Suka faɗa a lokaci guda.
Da tafiyar su babu jimawa Asma’u ta miƙe tsaye ta fara taku a hankali zuwa ƙofar shagon inda ta fara kwanciya daren jiya, ta buɗe ledar ta ta kwance ƙullin kayanta ta fiddo zane ɗaya daga cikin zannuwanta ta shimfiɗa ta kwanta.
Har ga Allah ta sa rai da dawowar Hajiya Yaganah ta ɗauke ta ta tafi da ita gidanta kamar yadda ta kwaɗaitar da ita. Sai gashi za ta sake maimaita kwana a cikin tasha, bisa ga dukkan alamu ma Hajiyar ta manta da ita bare alƙawarin da ta yi mata. Da waɗannan tunane-tunanen barci ya ɗauke ta.
Cikin talatainin dare wani zazzafan zazzaɓi ya rufe ta, wato zazzaɓin daren jiya ma ba komai ba ne a kan na yau, domin gaba ɗaya jikinta ya ɗauki rawa sai haƙoranta ke haɗuwa da juna kaf-kaf-kaf! Cikin ƙanƙanin lokaci Asma’u ta fice daga hayyacinta gaba ɗaya.