Skip to content
Part 7 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Fitowar Asma’u daga banɗaki kenan za ta gifta ƙofar ɗakin Zubaidah ta ji an ce.
“Waye a nan?” Muryar Zubaidah ce ta kuma san da ita take ta ce a sanyaye, “Ni ce Anti.”

“Asma’u ce? Zo mana.”

Ta ɗaga labulen ƙofar ɗakin tare da jefa ƙafarta da sallama duk a lokaci guda. Zubaidah na zaune a gefen katifa ta ci uwar kwalliya da alama fita za ta yi. “Ina kwana Anti.” Ba ta damu ta amsa ba ta ce, “Me kika yanke kan maganar jiya?”

Sunkuyar da kai ta yi ƙasa, ta fara jin haushin yadda Zubaidar ta matsa mata kamar cikin a jikinta yake.

“Yanzun nan fita zan yi kuma har gidan Ruky zan biya, mijinta yana abortion, ya iya aiki sosai. Da a ce kina so sai in tuntuɓe shi, Asma’u ki daure a cire miki cikin nan idan ma tsoro kike ji ki daina, ke yanzu ba kya jin kunyar a gan ki da cikin da babu aure?”

Zubaidah ta gyara zama sosai tare da rage sautin muryarta. “Asma’u bari in faɗa miki wani sirrina da ban taɓa faɗawa kowa ba, kin ganni nan sau biyu ana cire min ciki wallahi.”

Asma’u ta ɗaga kai tana kallonta cikin kaɗuwa da jin kalamanta, yayin da ita kuma ta jinjina kai cike da ƙoƙarin tabbatar mata abin da ta faɗa har ƙarƙashin ranta haka yake. Yanzu tsoron Zubaidar ne ya mamaye mata Zuciya so take ta fice ta bar mata ɗakinta, tana kuma jin muddin ta ci gaba da matsa mata kan maganar tana iya tattara nata ya nata ta bar musu gidan gaba ɗaya.

“Ni dai ba na so Anti Zubaida, ki yi haƙuri.”

“Ok shi kenan, ni tashi ki je tunda ba kya jin shawara, ke na ma daina matsawa kaina kan cikinki, tunda ba a jikina yake ba.” Ta kama hanyar ficewa daga ɗakin a ranta tana faɗin “Da dai ya fiye mana daga ni har ke.” Kai ita ba ta ga ma abin da ya sha ma Zubaidar kai da cikin ta ba.

Tun daga wannan ranar ba ta sake yi mata maganar ba, gaba ɗaya ma ta ɗauke mata ƙafa ta watsar da lamuranta, aikin da take saka ta ko aike ma duka ta daina, sai ta wuce ko kallonta ba ta yi ba, bare ta amsa gaisuwarta.

To kuma sai Asma’un ta ji duk gidan ya yi mata ba daɗi, komai ya yi mata zafi, don in ka ɗauke Hajiya dama kaf gidan Zubaidan kaɗai ke nuna mata kulawa.

A wani yammaci ne Asma’u ta samu Zubaidah a ɗaki tana game cikin wayarta. Ba ta amsa sallamar da ta yi mata ba, ta dai ɗago dara-daran idanunta ta kalle ta, sannan ta kawar da kai, ta ci gaba da danna wayarta.

“Anti Zubaidah don Allah ki yi haƙuri.”

A karo na biyu Zubaidah ta sake ɗago kai tana dubanta. “Haƙurin me kuma, me kika yi min da za ki zo kina ban haƙuri? Asma’u ai nice ma zan ba ki haƙuri saboda na takura miki da ƙoƙarin tilasta ki yin abin da ba ki da ra’ayi.”

Duk sai ta ji babu daɗi, ta samu guri ta zauna saman kujera kanta a sunkuye. Zubaidah ta ɗora da faɗin “Asma’u ni fa Allah Ya sani ina tausaya miki ne, a wannan zamanin babu wata ‘ya mace budurwa kamar ki da za ta samu ciki babu aure ta bar shi ba tare da ta cire shege ba, ake zubar da na halak ma idan aka samu wani juyin? Amma ke kin yarda za ki ci gaba da rainon cikinki, ki haihu, ki shayar da ɗan na tsayin shekaru biyu, ki zama Uwa tun baki fara sanin yaya ɗanɗanon rayuwar duniya yake ba. Wannan babban ƙalubale ne ga kyakkyawar matashiyar budurwa kamar ki.

Ni Zubaidah na ƙi jinin in ga yaruwata mace tana rayuwar rashin ‘yanci, na san rayuwarmu da su Ummita tana ba ki sha’awa, a wasu lokutan ki kan ji ina ma ke ce Ummita ko Firdausi ma ba ni ba, to da kin yarda kin bi ni ina miki albishir za ki samu ilimi sosai zama abar alfahari ga kanki da Innarki. Wallahi ina ji a jikina za ki sauya daga yadda kike ɗin nan, ina nufin za ki zama wani abu a rayuwa Asma’u.”


hakka babu a yanzu ba ta da mafarkin da ya wuce ilimi, shi ne babban muradinta a rayuwa, don haka ta yi tsai da ran ta, idan har za ta zama mai ilimi ko yaya ne me zai hana ta bi hanyar da Zubaidah take ƙoƙarin ɗora ta, duk da cewa a can ƙarƙashin Zuciyarta tana da tarin tambayoyin da ba su da amsa kan rayuwar Zubaidah, ya aka yi ta samu ciki har a ka zubar mata, shin ita ma fyaɗen aka mata?

“Kin ga, ni yanzu fitar min daga ɗaki tunda baki yarda da ni ba.” Ta tsinkayi muryar Zubaidah na korarta katsam!

“Na amince Anti Zubaidah, da fatan za ki daina fushi da ni.” Asma’u ta tsinci kanta da furtawa cikin haƙiƙanin amincewa da manufofin Zubaidah na alkhairi a gare ta. Ko dama can ba ta taɓa jin Zubaidah za ta yi wani abu don ta cutar da ita ba.

Zubaidan ta gyara zama cike da jin daɗin fara cimma manufofinta a kanta. Tunda taji wacece Asma’u da ƙaddarar da ta afka mata take son taimaka mata. A gidan duniya ba ta san wani zalunci da za a yi wa ‘ya mace a gurgunta rayuwarta ba kamar fyaɗe, tana son kasancewa ɗaya daga cikin masu yaƙi da laifin.

Asma’u na da kyawun halitta sosai, sai dai yanayin ƙauyanci da gidadancinta ya yi matuqar taka rawa wajen ɓoye kyawun nata, haƙiƙa duk inda ta samu gyara da kula za a ga mace a gurin, bai kamata rayuwarta ta tazgare daga an mata fyaɗe ba, baya ga haka ba ta taɓa ganin abar tausayi kamarta ba, don haka ba ta taɓa jin tana son ta taimaki wani kamar yadda take so ta taimaki Asma’u ba.

“Yanzu yaushe za ki shirya mu je mu ga Dr. K.B?” Ta tambaye ta.

“Duk lokacin da kika sa, ai yanzu wuƙa da nama na hannunki, ni bin umarni ne kawai nawa.” Asma’u ta faɗa cike da ƙarfin hali.

Tsoro ne fal a ƙasan Zuciyarta, ba ta san yaya aikin yake ba amma dai dole ta san ba zai rasa nasa hatsarinsa ba, sai dai ko yaya ita ma tana so ta rabu da cikin da ya zama katanga tsakaninta da rayuwarsu da Inna, sannan tana kan matakin da ba za ta iya tsallake maganar Zubaidah ba bisa la’akari da yadda ta ci burin taimaka mata bil haƙƙi da gaske wajen samun rayuwar ‘yanci.

Ranar da za su tafi Asma’u ta shirya cikin kayan da Zubaidah ta ba ta ta ce ta saka. Sai da kowa a gidan ya fice ya rage sai su biyun kamar yadda ta tsara mata, ko da ta fito tsakar gida Zubaidar na tsaye cikin tsananin ado kai kace matar wani hamshaƙin ce, tana danna ƙaramar wayarta, ƙarar latsa Key pad kawai kake ji. Ta juyo tana dubanta.
“Kin gama shiryawa ne?” Asma’u ta gyaɗa mata kai alamar amsawa daidai lokacin tana ƙoƙarin sanya Silifas ɗinta a ƙofar ɗakin su.

“Haba Asma’u Silifas, ina waɗannan takalman da suka yi min kaɗan na ba ki? Ai za su fi wannan.”

“Wallahi Anti ban iya saka su ba, faɗuwa nake.” Zubaidah ta kwashe mata da dariya, “Kai gaskiya Asma’u da sauranki, to ki wuce ɗakina inda nake ajiye wa ki zaɓi wanda zai miki kuma ba zai kada ki ba ki saka amma dai ba Silifas ba.” Ta miƙa mata ‘ya’yan makullan hannunta.

Asma’u ta buɗe ɗakin ta shiga tana dubawa ga takalman nan reras, ta zaɓi wanda ta san ba zai kayar da ita ba ta ɗauka ta fito ta kulle mata ɗakin, ɗankwali da mayafi ma duk sai da ta sake ɗaura mata.

Suna tsaye a ƙofar gidan da suka sha tafiya cikin adai-daita kafin su zo Zubaidah ta fiddo wayarta ta yi danne-danne sannan sai ta matsa jikin ƙofar ta sa bayan ɗan yatsanta mai zobe ta ƙwanƙwasa. Babu jimawa kuwa ƙofar gidan ta buɗe, wani farin mutum mai ‘yar ƙiba kaɗan ya bayyana a gaban su.

“Amma fa kun yi saurin zuwa, duka minti nawa kika ce min kun fito?” Mutumin ya faɗa yana kallon su ɗaya bayan ɗaya.

“Drop na ɗauko har nan don ba na son tsaye-tsayen nan na kan hanya wallahi.”

Mutumin ya juya ya shige ciki yana faɗin “Bismillah to, ku shigo.” Yadda Zubaidah ta bi umarninsa ita ma ba ta da wani zaɓi da ya wuce bin ta a baya.

Gidan madaidaici ne flat ya tsaru dai-dai misali. Suka sa kai cikin falon, wata farar mace tana zaune hakimce cikin kujera Remote ne a hannunta tana kallon T.V ganin Zubaidah sai fara’arta ta ƙaru, ta taso ta rungume ta cikin murna suka sake zama Zubaidah ta ƙare mata kallo kana ta ce, “Shegiyar duniya kina ciki abinki K.B ya riƙe miki kan maciji kina ta wasa da jelar.”

Matar ta yi dariya ta ce “Ke ba sai ki zauna ba, ina fatan ba wata jakar tsiyar kika sake ƙunsowa mutane ba?” Zubaidah ta kai mata dukan wasa, ta goce tana dariya. K.B kuwa tuni ya bi wata ƙofar ya shige ƙuryar ɗaki ya bar su.

“Wallahi Zuby ki yi wa kanki faɗa, sharholiyar nan ta isa haka, aure yana da daɗi fa.”

Zubaidah ta harare ta. “Umm, su aure manya, ai na ga alama a tare da ke ‘yar duniya.” Suka kwashe da dariya.

“Ina kika samo wannan kuma?” Matar ta faɗa tana duban Asma’u da ke tsaye tana kallon su.

“Yar uwar Hajiya ce daga ƙauye, za mu ga Dr K.B ne.” Ta ba ta amsa.

Daga haka ba su sake bi ta kanta ba suka hautsine da hira irin ta aminan da shaƙu da juna, don haka ta samu guri ta zauna a ƙasa tana sauraren hirarsu kaɗan-kaɗan, yayin da fargaba ta kasa barin zuciyarta. Dr. K.B ya fito daga ƙofar da ya shiga kai tsaye ya nufi ƙofar fita daga falon. Babu jimawa da fitar sa wayar Zubaidah babbar ta sa kiɗa, ta duba sai ta miƙe tsaye tana faɗin. “Bari mu je, zan dawo idan mun gama kafin na wuce School. Taso mu je Asma’u.”

“Shi kenan bari in tashi ni ma in ɗora abinci.” Matar ta faɗa.

Asma’u na biye da Zubaidah suka shiga wata ƙofar daban duk a cikin gidan. Sai ga su a wani madaidaicin ɗaki babu komai a ciki idan ka ɗauke gadajen kwantar da marasa lafiya guda biyu, akwai wata ƙofar daban da za ta sada ka da banɗaki, sannan ta sada ka da Chemist ɗin Dr. K.B wanda ke da ƙofa ta waje. Yana zaune yana jiran su.

A tsaitsaye Zubaidah ta sake gabatar masa da Asma’u a matsayin wadda za a cirewa ciki.

Gaban Asma’u ya faɗi! Har yanzu tana jin kamar za ta aikata wani mummunan abu da ka iya zama babban kuskure a rayuwarta. Zubaidah ta sake yi mata dogon bayani mai cike da kwantar da hankali sannan ta rataya jakarta a kafaɗa, “To ni zan wuce makaranta, nan gidan ƙawata ne Ruƙayya, za ta kula da ke kamar yadda zan kula da ke, ni ma daga na fito daga makaranta ba zan tsaya ko ina ba zan biyo mu wuce gida bayan an gama. To K.B Allah Ya ba da sa’a.”

<< Kaddarar Mutum 6Kaddarar Mutum 8 >>

2 thoughts on “Kaddarar Mutum 7”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×