Skip to content
Part 1 of 2 in the Series Kaddarar Safwan by Khadijah Ishaq

GARDAƊI
Ban yarda wani/wata su juya min littafi ba ko kuma suyi amfani dashi ta hanyar da bata dace ba, ba tare da sani ba, hakan rashin adalci ne.

JINJINA
Jinjina gare ki Sadiya Abdullahi Umar (ohm Teemah) Queen of the writers, ina Miki fatan alkhairi akodayaushe, Muna godiya da gudummawar da kike bamu Dashen Allah Writers’ Association

GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI
Gaisuwa da fatan alkhairi gare ku ƴan uwana da abokan arziƙi, da ƙawayena, base na faɗi suna ba duka ina muku fatan alkhairi.

SADAUKARWA
Na sadaukar da littafi na ga dukkan masoya na, masoyan littafi na, ina muku fatar alheri cikin su harda yayana rabin raina Ibrahim, kana raina bazan manta da kai ba.

*****

Bismillahir Rahmanir Rahim

Kwance ya ke a kan makeken gadon shi, fari ne sosai kuma dogon saurayi kafafuwan shi sanye da takalma, gado ne na alfarma wanda kwanciya a irin wannan se wanda Naira ta zauna mu su sosai d’aki ne had’ad’d’en gaske mai girma sosai kuma ga komai na more rayuwa ya wadatu a d’akin.

Wayan shi da ke can kan drawer ne ta fara ringing tashi ya yi ya zauna, had’e da yin mi’ka, idanun shi a lumshe mi’kewa tsaye yayi domin zuwa ya d’auko wayan tafiya ya ke yana had’a hanya kai da ganin shi kasan baya hayyacin shi, lokacin da ya isa wayan ma ta yanke, wani kiran ne ya sa ke shigowa, wayan ya d’auka hannun shi na rawa da’kyar ya karanta sunan da ke rubuce a jikin BESTY SAFNA d’aukan wayan ya yi ya kara a kunne ya ce “Hello” cikin zazza’kar muryar ta ta ce “Safwan lafiya ba ka zo school ba ga shi har an kusa shiga class?”, cikin canza salon murya don karta ga ne halin da yake ciki yace

“Saf….Nahhh! ba… najin daɗi ne” maganar ya ke kai da ka ji ma kasan a buge ya ke, Daga can Safna ta ce, “Safwan ‘karya za ka yi min?”, “a’a ki yi…” dif..! ta kashe wayar bata ma saurari me ze ce mata ba, yayin Safwan hankalin shi ya yi matukar ta shi da fe kan shi ya yi, sannan kuma ya zube anan bacci ya kwashe shi.

Ahmadu Bello University, Zaria

Can na le’ko muku abun da ke wakana d’aliban ne ke ta sintiri a cikin faffad’ar makarantar ko wa na sabgar gaban shi, wata matashiyar yarinya wanda baza ta gaza shekara sha ba’kwai ba17 na hanga kan wani dakali ita kad’ai da alama ta yi nisa ne cikin tunani fara ce sosai ga ta kyakykyawa ce sosai, kallo d’aya za ka mata kuma kasan bafulatana ce, wata ce wanda itama baza ta gaza shekarunta ba ta nufo wajen da ta ke zaune, zama ta yi tare da dafa kafad’unta tace “Safnah, me ki ke yi ke kad’ai anan ko kina jiran mutumin na ki ne”, wanda aka kira da Safna ta d’ago kai tace “a’a maryam kawai ina hutawa ne kafin mu shiga class, safwan ma na kira shi yace baze zo ba”, “to ai se ki ta so mu shiga class don ga sir Deniel can ma ze shiga”, da sauri su ka mi’ke su ka nufi ajin don idan ya riga ka shiga baza ka shiga ba.

Yana shiga kuma kamar yanda ya saba ya fara lecture don wad’anda su ka zo late kuma se de su ka zauna a waje karatu sosai a kayi, karatun awa1 yayi musu sannan ya bada Assignment yace har wad’anda ba su zo a fad’a musu don shine a matsayinmatsayin C.A d’in su.

Bayan ya fita ne kowa yaci gaba da sabgar gaban shi wa su na karatu wasu kuma surutu, Kamal abokin Safwan ne ya ta so ya zo wajen Safnah ya ce mata “Lafiya Safwan be zo ba?”, kallon shi ta yi tace “baka kira shi ba ne?”, “Ehh”, “to ka kira mana kaji”, juya wa yayi ya koma ya zauna, ita kuwa Safnah tsaki ta ja don ba ta san me yasa bata son kamal d’in nan ba jinin su be had’u ba kwata-kwata.

Yau ‘karfe sha biyu su ka ta shi makarantar Safnah na hango da ‘kawar ta maryam sun jero har zuwa bakin gate d’in makarantar anan ne su ka rabu don yayan Maryam ya zo d’aukan ta, kasancewar ta na Ɗan magaji ne, ita kuma Safnah ta na Samaru gidan su ba nisa sosai da makarantar.

Safnah tahowa ta fara yi don ta samu ko keke napep ne ta shiga zuwa gida ga garin yau rana sosai ake yi. ta dad’e sosai awajen sannan ta samu napep ta wuce gida.

Har bakin dai-dai madaidaicin gidan na su mai keken ya kaita ta ciro kud’in shi ta ba shi, ya wuce yayin da ta shiga gidan na su ɗauke da sallama a bakin ta, Anty na zaune a tsakar gida ta na wa Afrah kitso ta amsa cikin fara’a tare da cewa “Safnah kece da wuri haka” “Ehh anty don ma ban samu abun hawa ba da tuni na dawo”, “to sannu da hanya”, “sannu anty na same ku lafiya?”, “lafiya lau”, ta ce.

Sannan Safnah ta nufi ɗakin ta ta ajiye jakar ta ta fito tayi alwala, kasancewar yanzu kiran sallar ‘karfe d’aya 1:00 ake yi, Bayan ta yi sallar ne ta fito ta zauna gefen anty kan tabarman da ta ke zaune, Anty ne ta kalle ta tace “Safnah ki zubo abinci kici mana”, “to Anty” ta ce sannan ta nufi kicin d’in, tuwon shinkafa ne da miyar d’anyar kubewa, ya ji man shanu, zama ta yi ta fara ci, Afrah ta kalla tace “ke baki san kin girma ba baza ki de na kukan kitso ba ko”, Afrah da a ka kusa gama mata kitso ai kukan ta ‘kara yi don ba ta son magana, dai-dai lokacin sauran yaran su ka shigo tare da sallama sun dawo school su ma, Ibrahim wanda su ke ce wa Khalil shine Babba se Halima, se Ummar, se Fatima, se khadija wanda su ke cewa Afrah ita ce auta, su biyar.

Zuwa su ka yi kamar yadda su saba idan sun dawo makaranta su gaishe da momin su sannan su ka ce “Anty Safnah sannu da gida”, “yawwa sannu” Safna ta ce musu, Khalil ne yace “Anty Safnah ya akayi ki ka riga mu dawowa yau”, murmushi ta yi tace “ehh yau na riga ku”,

Sallah su ka yi sannan Safnah ta zubo mu su abinci ta had’a wa mazan matan ma ta had’a musu sannan ta mi’ke tace “Anty zan je d’aki na yi karatu” “to Safnah Allah ya taimaka”, “Ameen” ta ce sannan ta juya ta nufi d’akin, d’akin ba lefi ya had’u don komai na masu ‘karamin ‘karfi an saka mata, don kawun ta na ji da ita sosai.

Uwar d’akan ta shiga ta kwanta akan gadon tare da bud’e littafin ta Assignment d’in Sir Daniel ta fara yi don tasan shi ba sau’ki, se da ta kusa gamawa da taimakon wayan ta da kuma fahimtar ta.

Aji ye littafin ta yi don wani bacci da ta fara ji kwanciya ta yi duk da ta san Lokacin Islamiyyar su ta kusa.

Baccin awa d’aya1 ta yi Afrah ta shigo tashin ta lokacin su har sun shirya ma, Bayin da ke d’akin ta fad’a ta yo Alwala ta zo ta yi Sallah sannan ta d’auki jakar Islamiyya ta fito, Lokacin ma su Khalil sun fita su na jiran ta a waje, Anty ta gani zaune a tsakar gida tana gyaran wake, tace “Anty mun ta fi” “to Allah ya bada sa’a”, “Ameen Anty”,

Fitowa ta yi ta same su a kofar gidan sannan su ka wuce, kasancewar Islamiyyar ta su a cikin anguwan su ta ke amma da d’an tafiya sosai sauri su ke yi sosai don sunyi late sosai.

Wani d’an zauren gida Safnah ta shiga tare da d’aura nikaf d’in ta, don sun kusa zuwa gidan su Safwan, sannan ta ce su khalil su yi gaba don bata son ya tsaya ɓata mata lokacin.

Kamar yanda ta zata kuwa Safwan na ƙofar gidan su yana zaune cikin taron mutanen shi yana sanye da kayan ‘kwollo ne Blue ne sunyi matu’kar yi mashi kyau sosai ko da ta iso dai-dai wajen su d’uke kai ta yi don karma ya gane ta don shi idan mutum yasa nikaf be cika gane shi, har ta wuce ta fara nisa, Safwan be ma kula ba Wani da suke kiran shi Salman ya ta’bo Safwan yace “Safwan baka ga mutuniyar ta ka ba ne”, kallon shi ya kai inda Salman ke nuna mai, aiko ya gane ita ce mi’kewa yayi da sauri ya bita.

“Safnah! Safnah!! Safnah!!!”

Kamar a mafarki Safnah ta tsinci muryar Safwan na kwala mata kira, abun da ta tsana kuma yasan bata so ne shiyasa, juyowa ta yi ta hango shi can yana tahowa da gudu kallon shi ta tsaya yi har ya ‘karaso nikaf d’in ta d’aga tare da kallon shi tace “to mallam makaho ya da kira haka”, dariya ya yi sosai yace “se ina?” “Inda ka aike ni”, dariya ya ke yi har yanzu ita kuma had’e fuska ta yi, sannan tace “ɗazu me ya naka ka shigowa makaranta”,

“umm!,” rufe ido yayi sannan ya bud’e yace “banjin dad’i ne”, “Haba Safwan ka manta na ce duk abinda za ka fad’a min ka daina min ‘karya” “to momi na ayi hakuri”, dariya ta yi sannan tace “ai idan na haifi kamar ka bazan ganu ba tsabar tsufa ka ganni yarinya ta da ni kace min momi”, “to naji”, “Safwan mubar maganar wasa jiya kaje club ko?” tace, Hannu biyu ya had’a alamar neman gafara yace “kiyi hakuri wallahi kamal ya jani”, “igiya ya saka ya jaka ko me, shima giyar Kamal ya d’ura maka ko?, Safwan ina so ka sani ko badan addinin mu ba don lafiyar ka ma ya kamata ka daina shan giya da sauran su Safwan ga addinin mu ma ya yi hani da hakan kai ka sani fa Safwan”,
“Insha Allah zan yi ‘kokarin dainawa”,

“yafi maka dai, to kasan yau an yi karatu ai ko?”, “na sani har ma naje an koya min kuma na ƙara dubawa a waya”, “Assignment d’in fa?” “Har na gama ma”, Safnah bata yi mamaki ba don Safwan indai ɓangaren karatu ne baya wasa ko kad’an ko be zo ba to se ya koye shi, “to ka ga dama nayi latti ga shi ka ‘kara sani na ‘kara lattin ko!”, ta fad’a tana yin gaba, tare da cemai “se anjima”, “to shikenan”, ta wuce cikin sauri ta nufi makarantar.

Koda ta je su khalil har sun shiga aji an fara karatu, ga kuma wa su wanda su ka yi latti an tara su a waje, ana jiran mallam Ummar ya zo yayi dukan latti, ‘karasawa ta yi inda su ke zube suna da d’an yawa, har ta tsaya a wajen kuma se ta nufi ofis d’in malaman, Mallam Umar d’in ne kawai a ofis d’in yana ta aiki gaishe shi ta yi ya amsa cikin fara’a yace “Head girl kema yau kinyi lattin kenan?”, “ayi hakuri mallam matsala aka samu” “to dama ke nake jira kiyi musu dukan lattin don lebour be zo ba naje ajin ku ma kema baki zo ba, ni kuma ga shi ina ta aiki, ke kuma gashi kin zo latti”, “ayi hakuri mallam”, ta ƙara faɗa “to shikenan kije ki ce wa sauran su tafi aji kawai”

“To mallam mun gode!” ta ce

sannan ta juyo ta nufi wajen da suke, ta ce “kowa ya nufi aji” dad’i su ka ji sosai sannan ita ma ta shiga ajin lokacin har Malama ta fara mu su karatu.

‘Karfe shida 6:00 ake tashin su Islamiyya su na isowa akayi sallar magriba Mazan masallaci su ka tafi tareda Baban su matan kuma sukayi gida.

Basu dawo ba se da akayi Isha’i sannan su ka shigo gidan kamar yanda suka saba a Babban falon Anty su ke had’uwa su ci abincin dare sannan ayi hira kowa se ya wuce ya kwanta.

Part ne mai d’an girma sosai d’akuna uku ne aciki d’aya d’akin su Khalil ne d’ayan kuma uwar d’akan anty, se d’ayan kuma d’akin kawu ne, se kuma a waje akwai d’akuna biyu d’aya nan ne d’akin ba’ki yana kallon na Safnah da su Fatima don anan suma su ke kwana.

Kamar kullum kowa yana zaune a ‘kasa yayin da iyayen na su na zaune akan kujera kowa da filet d’in abincin shi yana ci shinkafa ne da miya yaji nama.
Anty ne ta kalli Afrah tace “Je ki kira Antyn ki ki ce ta zo ta ci abinci” “to mom”, ta ce sannan ta fita zuwa d’akin Antyn na ta.

Ita kuwa Safnah ta na kwance su na waya da Safwan tana ce wa “saura gobe kar kazo makarantar”, Daga can Safwan yace “ai se na riga ki zuwa ma”, “hm zamu gani se na riga ka”, “to Allah ya kaimu” “Ameen”,

“Anty momi na kira” cewar Afrah

“to gani nan, Safwan se da safe anty na kira na” “to se anjima” ya ce sannan ya kashe wayar.

‘Dakin antyn ta shigo d’auke da sallama gurin kawun ta ta nufa ta durkusa ta ce “kawu ina wuni?”, “Lafiya lau Safnah ya karatu?” “Alhamdulillah Kawu!”, “to ana dagewa ko?”, “Ehh sosai ma”, “to Allah ya taimaka”, “Ameen” ta ce sannan ta nufi gurin Anty ta gaishe ta sannan ta d’auki Abincin na ta ta fara ci.

Bayan kowa ya gama ne su ka sha hirar su cike da farin ciki sannan Safnah ta yi musu sedasafe suka nufi d’akin su.

Washegari Safnah Bayan ta tashi sunyi sallah ta fito Kicin ta shiga kamar kullum don kafin Anty ta ta so ta gama mata aiyukan ta tas! ruwa ta fara d’urawa wanda zasu yi wanka nan da nan yayi zafi kasancewa Gas ne, Juyewa ta yi ta nufi d’aki da shi Afrah ta tasa tayi mata, sannan ta ce Fatima ta shiga tayi da ragowar, sannan ta juyo ma halima raguwar, sannan ta mayar ma ta da na flas wanda zata had’a musu Tea da shi ta dawo d’akin lokacin duka sun shirya sun saka Uniform d’in su, Halima ta ce

“Wa je ki d’auko flas a kicin d’in d’aki”

“To anty” ta ce sannan ta nufi d’akin ta d’auko, ta dawo ta bata ruwa ta juye sannan ta mayar da wani sannan ta d’ibo Dankali ta fara ferewa wanda zata soya musu, cikin sauri ta gama ferewa sannan ta daka kayan miya d’an kad’an, ta d’auko kwai ta fasa ta had’a komai na suya sannan ta kira Halima ta ce

“Je ki ta so min su khalil”

cikin sauri ta taso su, ta juye musu ruwan sannan ta mayar da suyar cikin minti 10 ta gama suyan ta zuba akula sannan ta saka ruwan wankan, d’aki ta shiga da kayan ta jere su a dining sannan ta fito ta shiga d’akin ta ta ciro kayan da za ta saka da komai na ta wanda za ta makaranta dashi ta ajiye a gefen gado, ta dawo Kicin d’in ta juye ruwan na ta sannan ta mayar da raguwar shinkafar jiya ta yi ‘kasa da gas d’in, ta je ta yi wankan ta ta sa kaya, lokacin da ta fito ma su Halima har sun ta fi d’akin Momyn su.

Bayan ta shirya tsaf! ne ta fito ita ma ta nufi Kicin ta sauke shinkafar ta mayar da miyar shima ta d’uma sannan ta kashe gas d’in ta fito zuwa d’akin Antyn na ta.

Koda ta shiga kowa na kan dining Anty har ta yi wankan ta, shi ma Kawun na ta yana cikin shirin ofis d’in shi ne dama su ad’akin su ke wankan su sede su fito da shirin su.

Anty har ta had’a musu shayin Ta zuba musu dankalin su na ta ci, ta ‘karaso du’kawa ta yi ta gaishe su sauran yaran ma su ka gaishe ta kawu ne ya ce “Safnah sannu da ‘ko’kari”, murmushi kawai tayi sannan ta zauna wajen zamanta kusa da Khalil Abincin Anty ta mi’ka mata ta fara ci.

Bayan sun gama cin ne su ka fito lokacin mai Napep d’in da yake kai su ya iso, don Daddyn su ma tuni ya wuce Hospital don an kira shi akwai mara su lafiya da yawa shiyasa yana gama kari ya wuce, Safnah jakar ta ta d’auko su ka wuce sai da aka safa sauke Safnah sannan ya ‘karasa da su don ba wani nisa sosai, Safnah cikin makarantar ta nufa don yanzu ‘karfe takwas 8:00, don ma se da rabi zasu shiga class tafiya ta ke yi zuwa cikin makarantar, har ta iso class na su ba wasu mutane a ciki sosai juyawa ta yi can ta hango Safwan zaune da tawagar shi don Safwan akwai mutane sosai, ‘karasowa ta yi har inda su ke zaune, mata ne da maza suna ta hirar su.

“Good morning my friends”, cewar Safnah, Safwan da ke latsa wayar shi jin muryar ta ya d’ago yace “sannu da zuwa ƙawa” kujerar kusa da shi ya nuna mata, zama ta yi tare da gaisawa da sauran mutanen wajen, Sannan su ka cigaba da hirar ta su.

Kamal ne ya kalli Safwan yace “lokaci fa na tafiya bamuje mun karya ba Boss”, sauran ma su kace “haka ne fa”, Kallon Safnah yayi ya ce “muje mu karya ko?” Ba tare da ta kalle shi ba tace “am okay” mi’kewa su kayi wajen su goma sha biyar 15, su ka nufi wani Restaurant da ke kusa da makarantar, Koda su ka shiga kowa zama yayi a kujera ya fad’i abin da za’a kawo mai, shiko Safwan chips kawai ya ce akawo mai bayan sun gama ci ne aka yi musu total d’in kud’in su dubu ashirin da biyar, kud’i ya ciro a aljihinsa da be san nawa ba ne ya mi’ka wa kamal, ‘kar’ba yayi ya biya, raguwan saura dubu sha biyar, ya d’auki dubu biyar, ya bawa saura dubu goma su ka kar’ba su na murna su ka raba, shiyasa su ke son shi don Safwan ba shi da rowa in dai ka ra’be shi za ka ci kud’in shi sosai shiyasa yake da jama’a sosai kuma kowa na shi ne, duk da bawai mai yawan surutu ba ne amma ze zauna da mutane asha hira, Idan ka ga dariyar shi sosai ko surutun shi to shi da Safnah ne, shiyasa kowa ya ke ce wa soyayya su ke yi amma kuma su sun ce ba soyayya su ke ba, kawai ƙawance ne da zumunci da Allah ya ‘kulla a tsakanin su.

Lokacin da su ka shigo 8:29, lokacin ma har mallamin da su ke da shi ya shiga Safnah na zaune su ka shigo, kujerun ajin irin dogayen nan ne, duk guda d’aya mutum biyu su ke zama, Wanda Safnah ke zaune Safwan ya je ya zauna don nan ne wajen shi, Kallon shi ta yi ta ce “se yanzu ku ka dawo?” “Ehh”, kawai ya ce mata, muryar lecturer su ka ji yana cewa, submit your Assignment, Safwan ne ya ta shi ya nufi wajen kamal don jakar shi yana hannun shi, Safnah kuwa se yanzu ta tuna ma da Assignment d’in don ya dad’e, muryar mallam d’in ta ji yana cewa “Duk wanda be yi ba ya fita kuma shine CA d’in ku”, Safnah sosai hankalin ta ya tashi, wa su ne da ba su yi ba su ma su ka fara ba shi hakuri,Ya ce “su fita kawai!” hakan yasa Safnah mi’kewa don fita dai-dai lokacin Safwan ya dawo da takardar Assignment d’in shi yace “Safnah ina zaki?”

“Nabar Assignment d’ina ne a gida gashi ance a fita”, mi’ka mata takardar hannun shi ya yi ta ‘kar’ba sannan ya ce “ki saka suna a wannan ki bada, kije ki zauna kawai”,

“amma Safw…..” “shiiiii!” yatsan shi ya d’aura a baki alamar ta yi mai shiru, juyawa ta yi ta zauna shi kuma Safwan ya fita waje, Safnah ta shi ta yi ta kai nata.
Safwan ko da ya fita sauran sunyi mamakin ganin har da shi be yi ba ya ce mu su ya bar shi a gida ne, Bayan ya gama ‘kar’ba ne ya fito waje, wajen wad’an da ba su yi ba, sosai shi kan shi ya yi mamakin ganin Safwan be yi ba,

“Muhammad!!” Safwan da yasan Lecturer ne kawai ke kiran shi da haka ya taso tare da zuwa wajen shi, ya ce “Muhammad ya akayi ba ka yi ba?”, sunkuyar da kai ya yi yana Murmushi sannan yace “Sir na bar shi a gida ne”, “ok to gobe kazo min da shi” “to, thank sir” ya ce sannan ya nufi aji, su na had’a ido da Safnah Murmushi ya sakar mata ita ma murmushin ta mayar mai sannan ya ‘karaso ya zauna, tace “ya akayi ka shigo kuma?”

dariya yayi ya ce mata, “ke dai kawai kibar maganar ta wuce amma gobe ki zo da na ki ɗin se ki ba ni” “to” ta ce don ganin lecturer ya dawo karatu ya yi musu sannan ya fita yace anjima ze dawo ya basu takardun su.

Oum Ayshat

Ƙaddarar Safwan 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×