Shimfida
Shin, wace k'addara ce za ta sa 'yar uwa ta tsani 'yar uwarta ta jini?
Shin, yaya za ka yi a lokacin da kika tsinci kanki a tarkon son wanda 'yar uwarki take so.
Shin, me ya kamata ka yi a lokacin da wanda kake so yake gudunka?
Shin, wace k'addara ce za ta raba kan 'yan uwa?
Shin, Kaddarar So za ta iya sawa d'an Adam ya aikata komai?
SURURE, LAGOS NIGERIA
Shekara ta 1995
"Mimi nahhh?"
Cewar wata matashiyar budurwa dake sakkowa daga kan matakalar bene.
Da gudu ta k'ara su. . .