FUNTUWA, LOCAL GOVERNMENT KATSINA STATES NIGERIA
“Wato kin mai da ni y’ar iska, nasa ki aiki, inje gidan da nake aiki na dawo, shine baki yi ba ko?, ko arzik’in tashi ma baki yi ba saboda kin raina ni, makira algunguma”, ta idasa maganar tana k’ara shaud’ama wata matashiyar budurwa bulalar dake rik’e a hannunta, data ke jibgar yarinyar, dake k’asa sai uban kuka take tana shure-shure, yarinyar bazata wuce shekara goma sha biyar ba zuwa bakwai.
“Wai baki jin mi nake fad’a ba, shegiya y’ar iska tanbad’d’a mai kunan k’ashi?”
Yarinyar da har yanzu kuka take, harda majina shab’e-shab’e akan fuskar tata, ta kalli uwar ruk’on ta, wacce tunda iyayenta suka rasu, k’anin babanta ya d’auki ruk’onta, ya kawota wajan matarsa Inna Saude. Gasu a gidan haya, kusan d’aki biyar ne zuwa bakwai a gidan. Tunda tazo gidan take fuskartar tsangwama da kyara wajan Inna Saude. Ta tsane ta, yaranta kawai ta sani su uku, Nanah sai Mafida, sai kuma k’aramar su Hauwa. Yaran basu da kunya ko misik’ala zarratin, gashi basu da kintsi, kamar yadda ubansu yake. Kawun nata shima, (Mahaifinsu Hauwan), shima ba wani kintsatstse bane, domin gari-gari suke bi, suna kid’an Duma, na kwarya da kanguna, gida jan gala, da gidan karuwai, da gidan biki, shine sana’arsa. Baya ba Inna Saude duka wasu hak’k’inta, kullum cikin barinta yake da yinwa, ita ce buga can buga nan, domin dai ta ciyar da y’ay’anta. Sai dai Y’ay’an sun mugun raina ta, ita kuma bata da aiki sai d’ura masu ashar na kwashe albarka, da zagi na fitar hankali, shi yasa ga yaran nan, kullum ba kintsi sai k’ara tab’arb’arewa suke a kullum, Mafida kuwa tafi kuwa rashin kunya da iya tantiranci, dan ita, saita kwana biyu bama ta kwana a gidan ba, kuma ba d’an albarkar da zai ce danmi, garama Nanah duk dai itama sai hankalin, amma Mafida ta ce ban waje, domin duk iskancin da iyayenta suke ji, to ta dame su ta shanye, dama can wajan bariki iyayen nasu suka had’u da juna, shi yasa kullum cikin fad’a suke, kamar kaji. To tunda ya kawo, ma Inna Saude d’iyar K’aninsa Maryam, ta bigi k’irji ta ce bata lamunce ba, shi kuma ya ce sai dai tabar masa gida. Wata shewa ta saki tana cewa “ahayee nanaye, ai nida kai Jafaru, sai dai mutuwa, kuma bari kaji, koda ka sake ni, kasan mazan rasa mazan aure ba, ka kalle ni da kyau Jafaru. Kuma yarinya tunda ka ce dole saita zauna tare damu, shikenan kai ka siya mata kwandon wulakanci da wahala, kai ko kunya ma baka ji, d’aki d’aya kwallin kwal muda yara, komi zamuyi sai mun bari yara sunyi bacci tukun, yaran zamanin da sun san komai, kuma kaje ka sake k’aro mana wani nauyin, kai da bama iya ciyar damu kake ba”. Kallonta kawai Jafaru yayi yana yin kwafa ya fice daga d’akin. To tun lokacin Maryam take ganin izaya kala-kala a gidan, ita ce wankau ita ce girki ita share gidan hayar gaba d’aya, ita ce wankin band’aki, kuma duk Inna Saude ce ta yanka mata wannan uban aiki, wankau d’in ma da take yi Inna Sauden ce ke amsowa gidan da take aikatau, idan ta amso saita tulama Maryam su, ta wanke tas kuma bata bata ko asi. To yanzu ma ta bar mata wanki ne, tazo ta tarar da ita, bata yi ba, shine take mata wannan uban dukan na fitar shari’a.
Wani kalar mari Inna Saude ta kaima Maryam, ba shiri ta zabura ta mik’e, jikinta na b’ari ta ce “wallahi Inna Saude, Umma ce ta sani gyara mata wake da zatai k’osan yamma, dashi kuma na gaya mata kin sani aiki amma ta ce ita ba babu ruwanta dole ni ce zanyi mata”. Maryam ta idasa maganar kanta a k’asa.
Kama k’ugu Inna Saude tayi tana jijjiga, tana cewa a zuciyarta “lallai ma Ummar nan, wai ko dan taga gidanta suke zaune ne?, take masu mulkin mallaka haka, kuma ba damar ayi magana ta ce zata kori mutum, da ta san yadda zatai wallahi da sai sun tashi daga gidan hayar nan, domin duk mai kama haya a gidan Umma, idan ka d’ora tukunya to da kasonta a ciki, dole a d’ibar mata, kuma duk dokar data sa dole ne aike binta, saboda wani lokacin basa biyan kud’in hayar kyale su kawai take, suna cin arzik’i, shi yasa ba ubanda ya isa ya tanka mata duk uwar watsin da zatai”.
Can saita dawo da dubunta wajan Maryam dake rakub’e. Ta ce “to munafuka, ai sai ki tashi kiyi wankin yanzu, tunda kin gama ma y’ar mulkin gidan nan aiki, kuma wallahi na baki nan da awa uku ki tabbatar kin gama wankin nan, domin nayi al’k’awari ina dawowa za’a aika masu da kayan wankinsu”.
Shiru Maryam tayi, tana jawo kayan wankin ta fara cikin sauri, tana yi tana share hawaye, ga bayanta dake mata wani shegen rad’ad’i.
SURURE LAGOS NIGERIA
Da sauri Lilaah take sakkowa daga sama, tana kallon Mimi dake zaune akan darning table, suna cin abincin safe, ko kallon inda Lalaah take bata yi ba.
Ta kalli Mimi ta ce “please Mimi key d’in mota zaki ban, ta hawa gaba d’aya gidan nan, driver sai kaini asibiti.and Mimi, I hope we have food to go with?”
Mimi kallon tsaf tayi mata, tana aje k’ofin data kurb’i ruwa a hannunta tukun ta ce “kayan abincin suna a mota ai. I know who you are eating for two days, sometimes it is brought back without eating, Lilaah, I don’t like the shashincin, you know”
Fatar gushin Lilaah ce ta d’an tattare ta d’an tab’e baki, ta ce “No Mimi ai kin san waye nake mawa night.I just want to pass now and come back”
Tana gama fad’a ta wuce da sauri dan bata ma k’aunar Mimin ta sake tsayar da ita, da wani zancan kuma.
Da kallon takaici Mimi ta bita itama, sai kuma ta dawo da kallonta wajan Lalaah ta ce “now you are going to go to the company?”.
“Yeah Mimi yanzu zan wuce, suna so ne idan naje kawai nan take na zana masu irin saffarin ginin da suke so.I will be back for a long time, Mimi, pray for us”
Lalaah ta k’arasa maganar tana tashi ta d’au jakarta, sanye take da abaya y’ar Dubai itama, ruwan k’asa tayi mata mahaukacin kyau, sosai ta haskata sosai, sai key d’in mota dake rik’e a d’ayan hannun nata, sai kuma wasu tagardu dake rik’e a d’ayan inda ta rik’e jakar, kayan sun d’an mata yawa, amma haka ta rik’e su sosai, tana niyar barin darning d’in.
Taji muryar Mimi tana koro mata addu’a, amsawa take cikin jin dad’i, harta dawo tana mata kiss a goshi, sai kuma ta fice da sauri domin ta makara sosai