Skip to content
Part 4 of 9 in the Series Kaddarar So by Fatima Rabiu

Da gudu ta shigo y’ar k’aramar bukar su, zan birki tayi jin yadda Inna Wuro ke kuka kamar ranta zai fita. Zubewa tayi k’asa tana zare ido k’irjinta na bugawa kamar zai rab’e gida biyu.

Idonta har yanzu Baffanta yake gani kwance cikin jini a tsakar d’akin da alama kukan da Inna Wuro ke yi kamar na mutuwa ne, wata wawar faduwar gaba ce ta rinki Fulani dake zare ido har yanzu tama k’asa magana. Inna Wuro tayi saurin juyowa jin motsi a bayanta, kuka ta sake saki tana cewa “Fulani sun kashe mana Baffanki, ki duba tunda abun nan ya faru suka sassare shi bai k’ara lafiya ba, mi yasa baza su gane mu ba y’an ta’adda bane?, muma kanku masu satar mutanan idan suka samu sace mu suke, mutum nawa aka d’auka a rugar nan, amma mutane sunk’i su barmu mu huta, ki duba fa Baffa bai san hawa ba bai san sauka ba, kawai cikin dare suka shigo suka kamasa da duka, wai ai shine ya sace masu D’an uwa, wayyo Allah ya suke su muyi da rayuwarmu ne?”

A yadda Inna Wuro ke rusa kuka tana dawo da abunda ya wuce na baya zaka san cewa ta fara fita daga yaccinta ne, domin sai surutu take zubawa hawaye na mata kwaranya a idonta. Rushewa da kuka Fulani tayi iya k’arfin kamar ranta zai fita, jikinta har wani jijjiga yake. Tsoro ne ya kama Inna Wuro ganin yadda Fulani ke yi, kamin tayi wani yunk’uri Fulani ta zube a sume. Wata gigitacciyar k’ara had’e da salati Inna Wuro ta ramka, wadda ya zawo hankalin mutane wajansu.

Fitowa Inna Wuro tayi rik’e da Fulani tana kwalama sauran yaranta kira ba k’ak’k’autawa, da gudu samari guda biyu suka shigo cikin gidan. Sai yanzu ne na k’are ma gidan kallo, ashe ginin k’asa ne, sai ka shigo daga cikin gidan zaka iske buka guda biyu, sai d’akuna biyu sai inda suke sanwa dake gefe. Usman ne yayi saurin amsar Fulani gabansa na fad’uwa yana cewa “Inna, ba munce karki bari Fulani taga gawar Baffa ba?, mi yasa kika bari ta gani”. Ya idasa maganar cike da ciwon abunda akaima Mahaifinsu.

“Usmanu, ya za’ai bazata sani ba wadda ko gawar ba’a shirya ba ta shigo da gudu, dama daji taje wai samo masa maganin ciwon k’afarsa da aka bugeta sosai ita duk d’aukarta zata iya samo masa gani, bata san ashe Baffa tafiya zaiyi ya barmu ba”. Inna Wuro ta k’are maganar kuka na sark’eta. Audu dake gefe bai tanka ba, daka kallesa zaka san a zuciye yake, idonsa yayi jawur ba alamar hawaye sai bala’in dake cikinsu na d’aukar fansa tsantsarta.

Juyawa yayi kawai zai fuce waje, Inna Wuro tayi azamar tsayar dashi ta ce “ko kusa ko alama ban lamunce maka d’aukar wani mataki ba, indai akan abunda ya samu Baffanku ne, ku barsu suda Allah, ko suwa ye sukayi hakan”

“Amma Inna, saboda mi?, da kin kyale ni munje nida abokai na mun tada fitina a cikin garin nan, dole a fiddo mana wadda suke wannan aikin”

“Kaima baka ji mi kake cewa bane Audu?, babu dad’in ji, wai fitina miye affanin tada ita to, tunda bamu san su waye sukai mai hakan ba, sanin kanka ne ka sani cikin talatainin dare suka shigo gidan nan, sukai mai wannan ta’asar ku kyale komai ya wuce. Yanzu abunda nake so duka kai Usman shiga da Fulani cikin bukka, kar a watsa mata ruwa har sai ankai Baffah Mlm makwancinsa na gaskiya, idan yaso sai a watsa mata ruwa ta farka, domin suma tayi, bana so ta sake tashi taga gawarsa wani abun ya sake samunta itama”

Inna Wuro ta k’are maganar, har yanzu hawaye ke zuba a idonta, dauriya ce kawai take, domin ji take kamar zata had’iye zuciya ta mutu itama.

Ba yadda Audu yayi iya, haka aka kira mutane aka sallaci Baffa aka mik’asa makwancinsa na gaskiya, sai lokacin Audu ya shige d’aki yana durzar kuka kamar ba gobe. Shi ko Usman sai da Fulani ta farka, tana kuka mai ban tausayi ne ya rungumeta shima ya fashe da kuka.

Inna Wuro dake dubansu ta ce “ya kamata ku daina kukan nan haka nan, addu’a kawaii yake buk’ata”

Fulani ta d’an janye daga jikin Usman ta ce “shikenan yanzu Baffa na, ya tafi bazan sake ganinsa ba kenan?”. Wasu hawaye hawaye Usman ya sake share mata ya ce “ki daina kuka haka nan kinji, baga muba tare da ke kuma zamu ci gaba da kasancewa a tare da ke”.

Wata irin fad’uwar gaba ce haka nan Fulani taji ta sameta lokacin da Usman ke yin maganar, wani irin kallo take binsa dashi, har sai da ya hura mata iska yana mata murmushin yak’e yana sake cewa “ya da wannan kallo haka kamar na baza ki sake gani na bane, muna tare fa”. Da sauri ta lumfashe idonunta gabanta na tsananta fad’uwa, kyakykyawar fuskarta duk tayi ja saboda da kukan data sha, har yanzu wasu hawaye ke sake wanke mata fuska, domin harga Allah fad’uwar gaban da take ji tayi yawa, ga girarta da hagu da take ji tana mata motsi sosai, ga wani irin k’uncin zuciya dake taso mata, duk maganar mutane da su Inna Wuro ke mata na ta kwantar da hankalinta haka nan, amma ina tayi nisan kiwo, ita kad’ai tasan miye take ji a cikin jikinta.

HARUN’S FAMILY HAUSE, LOGAS NIGERIA

“Ai Binta nake gaya miki shegen yaron nan ya dawo, ya kama aikinsa kamar yadda ya saba, inaga fa asirin nan da boka ya bamu bai kamasa ba kwata-kwata nake gaya miki, abun ya fara bani tsoro, yaro sai ka ce aljani komai akai mai baya kamasa dandanan, koya kaman bai wuce na y’an kwanaki abun ya b’aci”.

Haj Shuwa ta fad’a ranta a b’ace, rik’e take da waya a manne a kunnanta. Daga cikin wayar Aminiyarta ta ce “ai ko dole a sake sabon shiri, domin a tarwatsa rayuwarsa, shi d’in mi Aunty Shuwa har da zaki tsaya kina b’ata ranki a banza, kika ma b’atar da wasu kuma suka b’ace duniya bata sake jin d’uriyarsu bare Arman shi a wa, dole ya fad’a tarkonmu karki wani damu idan yasan wata ai bai san wata ba”.

Wata shewa suka saki, sai kuma Haj Shuwa ta sake cewa “amma fa ina ganin kamar y’ar iskar abokiyar zaman can tawa itama fa tana shirin wani abo, domin duk ina ganin take-takenta so take Bilkees ta auri Arman, ita kuma Bilkees bata sonsa, bai cikin wadda take so, so take tayima wata k’awarta kamunsa wai wata mai suna Lilaah, duk ina sane da duk abunda suke k’ullawa”.

“Lallai Bilkees bata da wayo, mutum kamar Arman ka ce wai baka sonsa. Amma Aunty, kina ganin baza mu sake shiri ba, nasa Salma ta dawo gidanku da zama, ko Allah zai sa muma mu had’ata da Arman aure, muci dukiyar, idan yaso daga baya musa ta kashesa, amma ya kike gani”

Wani shiru ya d’an gifta sai can Haj Shuwa ta ce “tabbas kin kawo shawara mai kyau y’ar uwa, ai da duk ni ban kawo hakan ba, kinga ni dama kinga Bobo baida wani aiki saici gashi nan yayi wata shegiyar k’iba, ina so ya zama wani abu amma ya za’ai ya zama yana a haka?”

“Karki damu Aunty, Bobo shine zai gaji dukiyar Alhaji”

“Nasan da wannan amma, ni dukiyar Alhaji Harun nake so, bawai dukiyar Mijina ba, domin Alhaji baida dukiyar Alhaji Harun ko kama k’afarsa baiyi ba, wajan dukiya, kina fa gani duk arzik’insa muke shida yaronsa tilo Arman, da uwarsa Haj Badiyya, ko kishiya fa bata da ita, daga ita sai yaranta su biyu, Arman da Sa’adha. Sai mune y’an cin arzik’i nida kishiyata, wacce aka laluk’a min ita, shi Alhaji Harun baiyi auran ba sai K’aninsa da aka zugasa yayi, shida maida wani abun duniya, ai wallahi duk wadda ya zuga Alhaji ya auro wancan guzumar ban yafe masa ba”.

Haj Shuwa ta k’are maganar idonta jawur.

Binta dake cikin wayar ta ce “ya kamata duk ki manta da wannan abun wadda ya wuce, ki tuna fa, kinyiwa k’awar Haj Badiyya kurciya tabar gidan nan da cikin, mijinki, wadda shekara kusan goma sha takwas kenan babu amo babu labarinta, sai bayan b’acewarta ne aka sa ya auro Haj Zulaihat, harta zo ta haifi Bilkees, itama Haj Zulaihat d’in dakin bada dama da tuni an kawar miki da ita”

“Na tuna da wannan, ni nama shafe babinta ai tuni, ta mutu ita da cikin insha Allahu, sana kuma Haj Zulaihat ita ina da wani babban shiri kuma k’udurin da nake son cikawa da ita. Ita na barta ne a bisa dalili nawa, zaki jisa nan gaba kad’an”

Motsin bud’e k’ofa, Haj Shuwa taji, hakan yasa sukai sallama da Binta, suka tsayar da maganar Salma zata dawo gidan.

Inna Kande ce mai aiki ta turo k’ofar d’akin. A wulakanci Haj Shuwa kuma a tsawace ta ce “Kee kee ya haka, zaki rink’a shigo min d’aki bako sanarwa, bana hanaki shigo min d’aki haka kawai bane?”

Ta k’are maganar a tsawa ce

“Haj kiyi hakuri dama Haj Babba ce ta ce na kira ki abinci za’a fara ci ya kammala a darning table”

Wani dogon tsaki taja, tana cewa “naji gani nan fitowa”

Da sauri Inna Kande ta juya tana rufo k’ofar a hankali kamar wacce ke jin tsoro karda k’ofar ta b’alle.

Sai da ta sha iska, da mula dan kanta tukun ta fito, a yanzu asha wani wanka na fitar hankali ansha ado sai walwali take. Domin Haj Shuwa irin matan nanne wadda kota ina basu so suga an wuce su kota ina, sunfi son suga sune gaba, game da komai.

Kwasss kwasss kwasss. Takun tafiyar Haj Shuwa dake sakkowa daga matakalar bene dake shashinta, ta nufo parlo. K’atoton parlo ne, wadda tsayawa ma fasalta maku shi b’ata baki ne. Gaba d’aya ginin gidan irin na K’asar India ne, irin na masu kud’in cikin K’asar, wadda girmansa da fad’insa, sai wani d’an k’aramin K’auye su zauna a cikinsa, har yayi masu yawa. Kai hatta darning table d’in girmansa ya isa, kalar ruwan zinari ne, gaba d’aya parlon hatta kujeru kuwa, su kansu kujerun sun k’eru iya k’eruwa, kamar na gidan sarauta, haka kalar su take, da tsarinsu, ga wasu mahaukatan labulaye iya ganinka, kai tunda nake ban tab’a ganin irin saffarinsu ba, iya kyale-kyale an zubasa a wanga parlo ga wasu mahaukatan Ac ta k’asa data sama, da suke bada wani mugun k’amshi ko ta ina busowa suke, komai yaji sai wadda ya gani, kai ko fadar shugaban k’asa iya abunda za’a iya zubawa kenan.

Ba wadda bai d’ago ba ya kyalleta sai mutum biyu, My love, da Arman dake zaune a kujera dake kallon juna. Tana kallonsu, sai zuba mata tab’ara yake, amma ba wadda yake fuskantar hakan, sai su biyu ne kad’ai. Ita kuwa Haj Shuwa tunda ta sakko idonta na akansu, wani kalar bak’in ciki ne da hassada ya turnuk’eta. Idonta ne ya kai kan Haj Zulaihat data ciki ta batse, saura kad’an tayi bindiga, Saboda yadda taga Alhaji na bin Haj Shuwa da kallo. Itama tabbas tayi gayun iya gayu, amma sai take ganin na Haj Shuwa yafi nata nesa ba kusa ba, hatta kayan kai da ka kallesu zaka shaida tsadar kayan ba d’aya ba ce da nata, shaid’an ne ya fara zugata, a zuci take cawa “wato Alhaji dama kud’i yake ba Haj Shuwa ita da y’ay’anta, ita kuma yake ware ta da nata Y’ay’an, idan ba shi ba waye zai bata kud’i harta sayi irin wannan kaya haka, gwala-gwale.

Wani farin ciki ne kuma ya kama Haj Shuwa ganin kishiyar tata ta shak’a iya shak’a kuwa, dama haka take so tark’onta ya kama.

Gabad’aya ahalin gidan suna zaune ne akan darning table d’in, sai wasu y’an tsiraru ne da babu, wadda Y’ay’an y’an uwa ne. Arman ne farkon tashi yana ma Mahaifiyarsa kiss gushi, yayi mata sallama tare da iyayensa Maza, yayi Maza ya fice domin ya makara yau wajan aiki.

Yana tashi Haj Zulaihat ta zunguri Bilkees dake kusa da ita, murya k’asa-k’asa ta ce “shashasha, ki tashi ki bisa ku tafi tare mana. Duk ba waje d’aya kuke aiki ba, na ce ki rink’a d’an shige mai yasan da soyayyarki amma kullum ina tufka kina warware wa ko?”

“Haba Momy, kullum fa saina mai-maita miki cewa Bestie na Lilaah ke son Arman, ni kuma zan iya sadaukar mata da komai kin sani”

“Bestien ta ce bura ubata, kinji?. Kiji min shashashar yarinya, wacce bata san inda ke mata ciwo ba, ai da alama Lilar ta fiki hankali, wacce mace ce zata bari irinsu Arman su sub’oce masu. To bari kiji tun wuri ma gara ki fito ki fad’a mata kece keda Arman, ba ita ba, domin ina doran duniya dai ba wacce zan bari ta auri Arman bake ba, dan sai inda k’arfi ne ya k’are”

“Haba Momy kiyi magana a hankali mana sosai, nidai gaskiya bazan iya iyama Lilaah haka ba, dan baki san yadda take sonsa bane in…. Buge mata baki tayi, ba wadda ya lura da su. Sai dai Haj Shuwa tana ankare da duk abunda suke, saboda fad’in darning table d’in kuma nesa suke da kowa, shi yasa ba wadda yake lura da rad’ar da suke yi.

Haj Zulaihat ta sake cewa “zaki tashi ki bisa ko kuwa, sai ranki yayi mummunan b’aci?”

Turo baki Bilkees tayi tana tashi a hankali yadda ba wadda zaiji sai Momyn tata, ta ce “nifa Momy bazan tab’a iya abunda kike fad’a ba, kuma indai Arman ne kin san zuwa yanzu ya tafi, tunda kinfi kowa sanin halinsa, ba jirana zaiyi ba, kuma koda na ce ya tsaya mu tafi tare ba yi zaiyi ba, kin san yadda ya tsani mace wacce take zubar da darajarta ta mace kuwa a wajansa?, to ko Lilaah kullum cikin damuwa take da fama dashi, har yanzu ba wani kulata yake yi ba, nikam bazan iya wannan abun….. Maganar Bilkees ce ta mak’ale ganin wani kallo na takaici da Haj Zulaihat ke binta dashi, ba shiri ta rataya jakarta da d’aukar farar rigarta ta doctor’s ta sagalata a hannunta, tana ciro key d’in motarta ta k’ara gaba. Tana mitar mutum da motarsa amma ace yaje yana k’aramar murya. Ta idasa fad’ar hakan a ranta, dai-dai ta k’araso inda ake ajiye motoci, ta shiga tata, tayi mata key, aka bud’e mata kafcecan k’aton get d’in, wadda masu tsoron wajan zasu kai su biyar, baccin masu tsoron gidan dake shawagi a harabar gidan, kota ina. Harta fice suna d’aga mata hannu masu aiki a harabar gidan, masu ba fulawowi ruwa, tare da masu wankin motocin gidan.

<< Kaddarar So 3Kaddarar So 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×