Skip to content
Part 6 of 9 in the Series Kaddarar So by Fatima Rabiu

FUNTUWA LOCAL GOVERNMENT KATSINA STATES NIGERIA

Tsaye take tana dakan surfen wake. Da gudu Inna Saude ta fito daga d’aki, d’an dakatawa tayi tana duban Maryam dake surfe.

“Kan uban nan kayyasa, ke ina kud’i na dana aje a cikin d’aki jiya?, na duba ban gansu ba, kuma ke ce kad’ai kika ga inda na aje su, na rantse da sarkin da ke butsan lumfashi idan baki fiddo min da kud’i na ba, sai nayi miki bugun mutuwa wallahi, inga ubanda zai zo ya kwace ki”

Jikin Maryam ne ya kama rawa, had’e da tashin hankali, wani irin bak’in ciki ne ya cika mata zuciya, wani abu mai d’aci taji ya tokare mata mak’oshinta. Sharrin sata, abunda bata tab’a yi ba, ka aje abunka ta d’auka, koda kwana dubu zaiyi zaka zo ka same shi inda ka gansa, bata tab’a shi ba, bare har ta canza mai waje, ita kanta Inna Sauden ta sani, yau dai rashin mutumcin nata akanta zai k’are kenan?.

Kamin ta dawo cikin tunani taji an tsinka mata mari, fauuuuu. Da mugun sauri ta dafe kuncinta wasu zazzafan hawaye suka b’alle mata.

“Ke kin mai da ni y’ar iska ina magana kinyi banza dani, wato ga banza na magana nayi na gama kin d’auka kenan ba?, nayi abunda zanyi”

“A’a a’a Umma na rantse ban d’aukar miki abu ba, kin sani ban tab’a miki sata ba”

“Dalla rufe min baki munafuka, na sani ko kin canza hali ne, d’an Adam da ba wuyar canza hali yake ba. Wallahi sai kin fiddo min da kud’i na, ko kuma nayi miki dukan da zaki kasa tashi”

Izuwa yanzu kam, Maryam kukan nata har shashshaka take, duk’ewa tayi k’asa tana sake cewa “na rantse ban d’aukar miki kud’i ba, ki sake dubawa dai”

Wani hanb’ari ta kai mata, da k’afa Maryam ta tafi ta bige goshinta. Goshin nata bai sauka ako ina ba sai akan wani dutsen da ake had’a murho, buguwar data yi yasa goshin fitar da jini dandanan ya kunbura. Wani ihu marar sauti Maryam ta fasa, wata irin azaba ce taji ta shigeta.

“Ahh ahh mi zan gani ni Lami?, ke Saude kiji tsoron Allah wallahi, yadda kike azabtar da wagga baiwar Allah”

Juyowa Inna Saude tayi a zafafe tana nuna d’an Lami da shigowarsa gidan kenan ya tarar da abunda Inna Sauden kema Maryam shikam bai iya gani ya kyale

Ta ce “Lami kake ko d’an Lami?, koma dai minene ka fita a harka ta, ka daina shigar min hanci d’an Lamiiiii”

Taja sunan da k’arfi tana nunasa da d’an yatsa.

Wata shawa D’an Lami ya saki yana tab’a hannu had’e da rik’e k’ugu ya ce “ai idan baki daina yima Maryam mugunta ba a cikin gidan nan to wallahi ni kuma bazan daina tanka miki ba a’ato eheee kiji da kyau”

“Maryam d’in K’anwar uwarka ce kota ubanka?, D’an Lami zan karta ma rashin M wallahi”

Zai sake magana sai ga Mafida ta shigo d’auke take da kaya a saman kanta, a roba ce k’atuwa kayan mata ne shak’e da rabor data koma saidawa kwanan nan, gida gida take bi gari-gari take talla gidanjan aure na mata.

Sauke kayan tayi tana duban Inna Saude ta ce “ke Inna kin cika fitana mike faruwa ne?”

“Ubanki ne ke faruwa shegiya y’ar iska, miye ruwanki a ciki?”

“Kinga Inna Saude ki ban amsa, k’ila ma ina da sa hannu a ciki kawai ki gaya min minene”

D’an Lami zaiyi magana, karaf Inna Saude ta dube sa da sauri ta ce “to d’an san a sani, fad’i ba’a tabbaye ka ba, kaga d’an Lami ka daina min haka zan fyato ka kana shigar min hanci fa”

D’an Lami zaiyi magana Mafida ta kyafta mai ido. Shuru yayi domin ya d’au haske.

“Kinga kud’i ne na aje masu yawa, kud’in aikina da aka biya ni na wata, na nema na rasa kuma y’ar iskar yarinyar nan kin ganta ita kad’ai taga inda nake sak’a kud’i na”

“Hmm Inna Saude kenan, ai kin san dai Maryam ba abunda zatai da kud’i ko?, ni ce to na d’auke su na k’ara jari na kayan matan da nake saidawa in….. Kamin ta Idasa maganar ma, kawai sai dai taga Inna Saude a gabanta taci kwalar rigarta ta shak’e mata wuya. Zare ido Inna Saude tayi tana cewa “ai ko uban kuturo yayi kad’an bare na makaho, yau duk gidan ubanda zaki samo kud’i na sai kin bani, idan ba haka ba uhmm wallahi Mafida sai na barki kwance”

D’an fincike cikinta Mafida tayi daga na uwar, kamin ta ce “a’a dakata Inna Saude ai dad’in uban na zuba jari kuma na maida kud’i na, dan haka kinga kud’inki”

Zaro y’ar jakarta Mafida tayi tana k’irga kud’i, ta k’irgo dubu goma ta dank’ama Inna Saude.

Zaro ido Inna Saude tayi tana washe baki ganin iyayen kud’in da Mafidar ke k’irgawa.

Ta ce “kai y’ar albarka ki ce sana’ar da kika fara akwai riba haka sosai, ai ko nima zan zuba jari a ciki. Yanzu dai a bani riba ta tunda da kud’i na akayi sana’ar kuma an samu”

Wani duba Mafida tabi uwar dashi. Sai kuma ta kalli d’an Lami dake kallon Inna Saude cike da mamaki suka had’a baki wajan cewa “to yau Inna Saude mune y’an albarkar, wai yau za’ayi ruwa harda k’ank’ara kuwa”

Sai kuma taga sun had’a hannu sun tab’a a tare, suna sake sakin wata shewar.

Rik’e baki kawai Inna Saude tayi, lallai duk yadda take d’aukar Mafidar tata, ta wuce nan.

SUKUNTUNI, KARAMAR HUKUMAR KANKIA KATSINA STATES NIGERIA

Fulani ba k’aramin tashin hankali tayi ba, ganin yadda garin nasu ya koma. Kota ina kururuwar mutane kake ji, ga k’arar Bindigogi dake tashi a gidajan mutane, kallon ko ina take ganin yadda y’an Bindigar suka zagaye duka ilahirin garin.

Y’an Bindigar tare suke da motoci manya-manya, had’e da Mashina sunfi guda d’ari. Gaba d’aya dukiyoyin mutane sun kwashe sun tasa wasu gaba cikin dokar daji sunyi gaba dasu.

Y’an matan da suka kwasa kuwa zasu kai su goma irin su Fulani.

A k’asa aka tasa k’eyar su Fulani suna tafiya cikin dokar daji ga dare ya tsala. Wasu na kuka da kururuwar rasa iyayensu da sukai. Ita ko Fulani kukan ma izuwa yanzu hawayen sun k’afe babu sai zuciyarta dake mata zugi da rad’ad’i. Abu biyu ne ke mata kai kawo a zuciyarta had’e da tsainin damuwa, na rasa su Inna Wuro data yi, ji take inama da ita suka had’a suka halbe, da itama ta huta da wannan duniyar mai cike da d’unbin abun tsoro da azzalumai da suka zagaye duniyar. Sai kuma na cewa wai su Innar ba sune suka haifeta ba, kai wannan abu na mata ciwo sosai har yanzu ta kasa gasgata abunda ke faruwa da ita.

Halbin bindiga taji, ba shiri sauran y’an matan suka fasa ihu, ganin yadda aka halbe wata, data d’auke wai ita bazata iya tafiya ba ta gaji, ganin zata b’ata masu lokaci suka halbe ta nan take.

Take zuciyar Fulani ta kama wani zullo yanzu mutanan nan kwata-kwata su kashe rai ba’a bakin komai suka d’auke shi ba, Innallihi wa’inna alaihir raju’on, wani sabon tashin hankali ne taji ya rufe ta.

Tafiya yankin azaba, domin kuwa tafiya suke wacce babu tsayawa ko a hutawa, idan ka ce zaka tsaya kuwa, zaka yi a bakin ranka ne. Ga dare gashi Fulani ko arzik’in takalmi bata saba, kai ba ita kad’ai ba bata jin ma gaba d’ayansu sun sa wani takalmi, ai sai da kwanciyar hankali ake iya tuna komai.

Wata irin k’arar azaba Fulani ta saki, jin wani irin rad’ad’in azaba data ji shi daga k’asan k’afarta, har izuwa kwanyarta, Tabbas tasan k’aya ce ta taka, amma tasan ko k’aran hauka ya cijeta bazata tsaya ba. Wata mai suna Fyushind’o dake kusa da ita, ta zaro ido, fuskarta shab’e-shab’e da hawaye ta ce “Fulani ba dai k’aya kika taka ba?, wallahi karki tsaya kashe ki zasuyi kinga kusan mutum biyu suka kashe saboda irin tsayawar nan”

Wani kalar miyau Fulani had’e mai d’aci, ta ci gaba da d’angyashe k’afar tata, bata ce komai ba. Suna tafiya tana runtse idonta saboda ita kad’ai tasan yadda take jin rad’ad’i da k’afar tata ke mata.

Sun shafe daren gaba d’aya suna tafiya, masu raunin cikinsu tuni suke zubewa a kasa, su ko y’an Bindigar basu tsayawa wani b’ata lokaci suke halbe mutum, izuwa yanzu sun kashe mutum ya kai biyar. Har sanyin Asuba ya fara kunnu kai, babu alamar zasu tsaya. Fulani kuwa izuwa yanzu ta galabaita ainun ga tafiya da d’angyashi ga k’ayar dake har yanzu a jikin k’afarta, tana kallon yadda k’afar ke zubar da jini harta d’an yi fushi ta kunbura.

Safiya ce tayi masu, amma ga mamakin Fulani bafa wata alamar zasu tsaya wa’innan mutane, wani kalar dokar daji su Fulani suka tsinci kansu a ciki wadda basu tab’a ganin irinsa ba, ga duhu gashi ko tarin mutum baga ji, babu gida baya babu gida gaba, tsabar dokar dajin ce kawai. Fulani tasan sunyi tafiya mai tsayin gaske wacce ma bazata iya cewa ga adadi nisanta ba, tana da tabbacin sun baro nahiyarsu gaba d’aya sun shigo wata nahiyar kuma, baza suce dai ga inda suke ba, domin ko ina daji ne wadda baza’a iya kiran sa da gari ba.

Wata irin rana mai zafin gaske ake kwanyarawa, ga azabar yunwa data fara nuk’urk’usar wasu daga cikin su, dauriya kawaii suke ga bala’in tsoron su tsaya suyi k’orafi a kashesu, tafiyar kawai suke mai cike da tsananin azaba.

Wani irin sansani, su Fulani suka ga sun iso, mai d’auke da y’an Ta’adda, zagaye da wajan, an kafa wata runfa guda uku, gashi nan harda murhu a wajan, kota ina sune zagaye da wajan wasu a tsaye rik’e da bindigogi, wasu a zaune suna zuk’ar sugari wasu kuma shayi suke sha irin na buzaye, kai da ka kalli idanuwansu zaka shaida lallai babu imani a tare da su.

SURURE LAGOS NIGERIA

“Wallahi Mimi sune suka d’auke ta”

Cewar Aliyu da isowarsa kenan, a garin Logas.

Cike da tsananin tashin hankali ta ce “ka daina fad’ar haka in…. “Mimi ya za’ai bazan fad’i sace ta akai ba?, Mimi kina gani fa Abbie yasa an baza jami’an tsaro a can hanyar katsinar kawai abun tashin hankalinma an tsinci motar da suka tafi da ita tare da gawar drivern, Mimi wallahi sune, Mimi kuma sunk’i koda kiran waya ne su fad’i ko nawa suke so a basu, wallahi Mimi ko dukiyata zata k’are zan basu su sakar min mata”.

Ya idasa maganar tare da fashewa da kuka, kamar mace. Mimi zuwa yanzu ma kukan take itama, dole tasa kawai ta tashi ta haye sama tana hawaye, domin idan ta ce zata cigaba da zama inda Aliyu yake itama kukan zasu had’u suyita yi. Lalaah dake rik’e da Aliyu itama ta d’an kwanta akan k’irjinsa tana sakin wani sassanyan kuka itama. Sai can ta tashi ta ce “Y Aliyu ba kuka ya kamata mu zauna muna yi mata ba, kamata yayi mu tashi muje muyi alwalla muyi sallah, Allah kar ya basu ikon cutar da ita, musa a sauke al’qur’ani mai girma Allah ya bayyana ta”

Share hawayen yayi wasu kuma na sake zubowa, cikin muryar kuka ya ce “Lalaah akan Husaina ni mai rauni ne wallahi, ina matuk’ar tausaya mata ita da abunda ke cikinta, kina gani fa d’auke take da ciki a jikinta, wa’innan mutanan basu da imani fa ko kad’an ina gudun kar suyi mata wani abu, ita da abunda take d’auke dashi”. Wasu hawaye Lalaah ta sake share mai duk da itama hawayen ne ke zuba a cikin idon nata.

Da kyar ta lallab’a shi yayo alwalla, sai da taje tayi sallar tata harta dawo ta iske shi bai ma sallame ba, yana sallar yana kuka, yana kai kukansa wajan Ubangijin sammai da k’assai.

A wajan Mimi ma tana shiga d’akinta, dama bata rabo da alwalla, ita kullum zaka same ta da alwalarta. Kawai ta kabbara salla itama tana hawaye.

Bayan ta gama taji wayarta na tsuwwa. Da sauri ta duba sai taga ashe Abbie ne, da azama ta d’auka kamin ma ta ce wani abu ya ce “na kusa dawowa dole na aje komai na dawo k’asar domin aji da wannan abun, dole a baza jami’an tsaro kota ina dake cikin garin katsinar da wajenta”

“Amma Abbie baka ganin kar ayi hakan, saboda kasan su y’an Ta’addar nan, basa su ana sa masu jami’an tsaro a cikin abun su, ya kamata dai mu bari muga ko zasu kira waya”

“Hmm Mimi kenan tunaninku kenan na Mata amma dole asa Jami’an tsaro a ciki, ai an riga dama ansa sun, domin sune suka binciko inda motar da suka fita take, tare da gawar driver, kinga kuwa duk motsinmu zasu sani, kuma yanzu haka suna kan bincike ne ma”

Girgiza kanta kawaii Mimi tayi, har yanzu Abbie bai san suwaye y’an Bindiga ba, su da suke kamar aljanu idan aka ce yanzu haka sun san da Jami’an tsaron da akasa cikin lamarin ba’a gaddama, yanzu haka sun d’an dakata ne suga iya gudun ruwansu.

Sallama sukai kawaii inda take shaida mai ya tsaya ya idasa abubuwan dake gabansa, zata sa a ci gaba da addu’oi had’e da sauk’e al’qur’ani mai girma, su had’u kuma suyita mata addu’ar Allah ya k’are ta daga duk wani sharrinsu.

Bai wani yadda ba, shi dai yasan dole ne cikin satin ya duro Nigeria.

<< Kaddarar So 5Kaddarar So 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×