Skip to content
Part 9 of 9 in the Series Kaddarar So by Fatima Rabiu

Sansanin Yan Ta’adda.

Kwance Fulani take a k’asa cikin ciyayi, sai juyi take k’afarta na mata wani irin rad’ad’i mai shiga kwanya, duk da ta zare k’ayar data shige mata k’afa amma k’afar har yanzu zugi take mata.

Murk’ususun wata mata taji kusa da ita tana shashshakar kuka, ba shiri ta tashi a zabure tana duban matar dake d’an nesa da ita. Kallon ko ina tayi gasu nan an zube su a cikin rana ba abinci ba ruwa, rabonta data ce tasha wani abu tun kamin Inna Wuro ta bata labarin basu ne suka haifeta ba. Yanzun ma yunwa tayi mata mummunan kamu da kyar take had’e miyau, ga k’irjinta data ke ji yana mata zafi, kamar mai shirin kamuwa da cutar kwalsa.

Gabanta ne ya fad’i ganin yadda matar ke kallonta ko kyafta ido babu, kallon matar take itama, ganinta d’auke da k’aton ciki, haihuwa yau ko gobe. Gani tayi suna mugun kama, amma kamar bamai fisgar mutum bace kace nan take ai kamar ta b’ace ko kuma ace ai su iri d’aya ne, a’a kama ce wacce da an gani za’a ce ta jini d’aya ce amma game hankali da tunani.

Fulani bata san sadda ta rarrafo ta nufi matar dake rik’e da cikinta tana zubar da hawaye ba. Wani d’an Ta’adda ne ya kwasama Fulani tsawa da cewa “ke y’ar gidan matsiyata, koma ki zauna inda kika taso, kona fasa kanki da bindiga yanzu”

Ko kallonsa batai ba, domin ita yanzu mutuwar kawai take so, tazo ta d’auke ta ko kuma su su kasheta da kansu, ta gaji, ta gaji da wannan duniyar gaba d’aya.

Rai a b’ace d’an bindigar zai nufi inda Fulani take, da wannan matar, Ogansu ya dakatar dashi ya ce “rabo da ita, da alama yarinyar zatai taurin kai”

shiru yayi sai can ya ce “yo Oga ba sai yanzu ka bani Okay na fasa kanta da bindigar nan ba, yanzun nan lahira tayi bak’o”

“Batta dai ba yanzu ba tukunna”

Fulani duk tana jin miye suke cewa, wasu hawaye ne keta zuba a idonta, ita wallahi da sun kasheta a yanzun da sun kyauta mata ma. Tana isa ga matar ta tallafo kanta suna kallon juna, lokaci d’aya suka ji gabansu ya fad’i. Sharewa Fulani tayi cike da tausayi ta ce “baiwar Allah kema sato ki suka yi ko?, ga ciki koma nak’uda kike yi naga kin rik’e cikin?”

“A’a y’ar uwa ba nak’uda bace, da sauran lokaci, amma ko yanzu zan iya haihuwa saboda tashin hankalin da nake ciki. Ni ba har gida suka je suka sace ni ba, akan hanyata ta zuwa garinmu Katsina, suka tare motar da nake ciki, suka kashe driver na suka taho dani”

“Innallihi wa’inna alaihir raju’on wai su wa’innan mutanan basu da imani ne ko kad’an kashe rai kai jama’a”

Fulani ta fad’a hawaye na mata zuba har yanzu. Matar ta sake damk’e hannun Fulani tana jin k’aunar yarinyar har cikin ranta duk da zasu zo sa’anni da juna, har shekaru sai dai ita zaka iya cewa nan take ta girmeta saboda auran data yi kuma ga ciki sai ya k’ara bud’ata ta koma kamar wata babbar mace.

Ta ce “ya sunanki?”

“Ni sunana Fulani”

“Fulani” ta mai-maita sunan, sai can ta sake cewa “ni kuma Husaina”

Fulani haka kawai data ji sunan ta sake jin wata fad’uwar gaba, had’e da k’ara jin matar a jikinta

“Amma mi yasa kike kuka tunda aka kawo ki jiya, kuma kina rik’e da cikinki?”

Murmushin daya fi kuka ciwo Husaina ta saki tana duban Fulani wacce kamar akwai sauran yarinyata har yanzu dabe sake ta ba, ta ce “hmm Fulani kenan, ya za’ai bazan kuka ba?, ina tuna halin da mijina zai shiga ne da sauran dangina shi yasa kika ga ina kukan nan. Rik’e ciki kuma ina tausayin abunda zan haifa ne a wajan nan, fatana ace sun sake ni kafin na haihu, to amma banga alamun hakan a tare su ba, kamar so suke suga baya na ne, bamu san mi muka tare ma mutanan nan ba, ji nake a jikina kamar bazan sake sa Mijina a idanuwana ba sabo…… Toshe mata baki Fulani tayi tana girgiza mata kai ta ce “ki daina fad’ar haka, ai gara ma ke ni kin ganni nan sai da suka kashe min kowa nawa, shi yasa banga anfanin su sake ni da raina ba ma, su kashe ni kawai na so ace tun can cikin y’an uwana nima sun had’a dani sun kashe, ban san miye hikimar tahowa dani da sukai ba”

Tashi Husaina tayi a zabure tana duban Fulani ta ce “wai kina nufin garinku suka je suka kashe maku kowa, hasbinallahu wa’imar wakil”

Cewar Husaina, bata san sadda ta rungume Fulani suka fashe da kuka a tare ba, kamar wasu wadda suka dad’e da sanin juna.

Wata tsawa aka daka masu wacce tasa ba shiri suka zabura, suna kallon d’an bindigar dake tsaye da bindiga a wajansu. Yana cewa “munafukan banza, idan muka sake ganinku kuna wa’innan maganganun wallahi sai mun kashe ku gaba d’ayanku”

Shuru su Fulani sukai suna k’ank’ame jikinsu waje d’aya.

Wani garin kwaki aka jefo masu cikin wani kwano, ba magi ba gishiri an dai jik’asa sai uban yaji da aka dank’ara mai, sai ruwa guda d’aya da aka jefo masu, su biyu kowa kwano mutum biyu, ga garin bai wuce kayi loma uku dashi ba.

Kamin ka ce mi wasu sun lashe nasu, suna tand’e hannu. Duk rashin dad’insa su kam ba wani ji sukai ba, ruwan ma haka suka d’an kurb’a badan an k’oshi ba.

Fulani ta kalli Husaina ta ce “y’ar uwa ki d’auka kici kawaii kinga ke kina da ciki, bai kamata ki zauna da yinwa ba”. “To ke kuma fa?”

“Ke dai kawai kici ni yanzu bazan iya cin komai ba, garama na bari yunwar ta kashe ni da wa’innan kafuran Allah Ta’ala su kashe ni”

“A’a Fulani ki iya bakinki ki daina cewa haka please, karma suji ki kizo muce tare kawai idan ba haka ba nima ba ci zanyi ba”

Da sauri ta waiga inda Husaina take girgiza kai tayi ta matso tana cewa “shikenan mu ci tare”

Da kanta Fulanin tayi ta ba Husaina abincin a baki, wadda bata lura ba ita Husainar duk rabi ita ta ci sa, loma d’aya kawai Fulani tayi tabar mata sauran tana bata a baki, ko ruwan ma Fulani ba wani sha tayi ba.

Washe gari ma basu samu abinci ba, kusan kwanan su had’u yau kenan a wajan, a yanzu sun gane idan aka basu abinci yau to gobe fa babu maganar cin wani abincin.

Ko a ranar bazai wani wadace ka ba, abinci kamar wadda za’a ba kyanwa shi.

Wata irin kururuwa had’e ihu, su Fulani suka ji. Kai ba shiri suka zabura suna kallon inda ihun ke fitowa. Zare ido Fulani tayi gabanta na wata irin mummunar bugawa.

“Wayyo Allah na shiga uku ku taimaka min zai lalata min rayuwa, wayyo Allah ba wadda zai taimaka min ne?”

Fulani bata san sadda ta ce “Fyushind’o, Innallihi wa’inna alaihir raju’on, su kuma wa’innan harda fyad’e suke ma yara mun shiga uku, nan gaba muma zai iya zuwa kanmu”

Kwata-kwata duk mutanan dake wajan hankalin su yayi mummunan tashi ganin cewa su harda lalata yaran mutane suke, shi yasa kenan suka jido y’an mata, wadda suka kashe masu iyaye ba wadda zai kawo kud’in fassarsu, anfani zasuyi rink’a yi da su kenan?.

Wani kalar kuka Fulani ta saki tana shigewa jikin Husaina sosai kamar wacce zata koma ciki, Husainar ma hawaye take wadda tsabar tashin hankali da firgice har saida taji d’an cikinta ya mata wata irin juyawa, wadda har saida ta d’an saki y’ar k’ara. Ba shiri Fulani ta saketa tana dubanta hankali a tashe tana tab’a cikin tana cewa “Y’ar uwa ko haihuwa ce zakiyi muna cikin wannan tashin hankali?”.

Girgiza mata kai kawai Husaina tayi, amma ita kad’ai tasan azabar da take ji a yanzu.

Ga Fyeshind’o dake kururuwar ihu, ba wadda yayi gangancin nufar inda aka aje Fyeshind’o y’an Ta’addar sun zagaye wajan da Bindigogi ga Ogan nasu wani rusheshe dasu yana niyar kwab’e wando, kai tsabar rashin kunya da rashin imani ma a gaban jama’a a bainar nasi yake shirin keta ma y’ar yarinya haddi.

Fulani ta kasa kallon inda abun ke faruwa, kuka take kawai jikinta na d’aukar wata irin kyarma, daga ita har Husainar hankalinsu a mugun tashe yake, da za’a auna su a wannan lokacin to za’a iya cewa jininsu yayi mugun hau sosai.

Wani tsoho ne wadda shi an dad’e da kawo shi wajan ya tashi yana isa inda Ogan ke shirin keta haddin baiwar Allah, ya d’uke k’asa yana rok’ar suyiwa Allah karsu lalata wannan y’ar k’aramar yarinya.

Wata hanb’ara da sukaima wannan tsoho ya tafi ya bugu da k’asa hancinsa ya fashe, kamin ma ya dawo hayyacinsa kawai suka ji saukar harsashi had’e da k’arar Bindiga. A saitin kansa suka halbesa ko shurawa baiyi ba.

Bakin Fulani bud’e yake kowa dake wajan yayi shuru kamar anyi ruwa an d’auke masu taya Fyeshind’o kuka, suma kukan ya yatsa cak yadda wajan ya d’auki shuru kai ka ce babu halittar dake rayuwa a wajan. Husaina kuwa d’an cikinta ne ya sake motsawa, had’e da naushinta, runtse idonta tayi da mugun sauri tana dafe mararta jikinta ya fara d’aukar kyarma, zufa ta fara keto mata. Ita kam yanzu tasan haihuwa ce tazo mata ba shiri tashin hankali yasa haihuwa zuwa a sadda lokacinta baiyi ba.

Wani d’an Ta’adda ne ya juyo inda suke cike da muryarsa marar dad’in ji ya ce “duk d’an iskan daya k’ara zuwa wajan nan da sunan ya rok’e mu idan muna aiwatar da abu, to zai tafi inda muka aika wannan tsohon”.

Tsoro ne ya k’ara rufe su. Wadda suke kukan ma dole tasa suka toshe bakunansu, hawaye ne kawai kake iya gani na zuba a fuskokinsu.

Fulani hankalinta ya rabo kashi biyu, danta lura wallahi fa Husaina haihuwa ce tazo mata a wannan hali. Kamin su gama dawowa hankalinsu suka ji Fyeshind’o ta kwallara wata gigitacciyar k’ara had’e da cewa ta shiga uku ya kashe ta.

A sadda ya keta mata mutumcinta da rashin tausayi da rashin imani kuma, saboda da mugunta da k’arfi ya shigeta.

A dai-dai lokacin kuma Husaina ta saki wata irin gigitacciyar k’ara had’e da salati a bakinta.

Ba shiri wani daga cikin y’an Ta’addar ya ce “kai kardai waccar matar haihuwa zata mana a wajan nan?, Ai ko kuje ku tsaya inda take tana haihuwa ku amshe abunda ta haifa ku kashe shi, domin baza mu zauna da jariri yana damun mu da kuka ba”

Husaina da Fulani na jin wannan abu hankalisu ya k’ara tashi ainun, Husaina ta damk’e hannun Fulani tana girgiza kai cikin azabar ciwo ta ce “Fulani kiyi min al’k’awarin cewa duk wuya karki bari azzaluman can su kashe abunda na haifa, nabar miki komiye na haifa halak malak Fulani ni nasan mutuwa zanyi, Fulani ki ceci kanki da abunda na haifa dan Allah”

“Innallihi wa’inna alaihir raju’on” kawai Fulani ke iya cewa tana rik’e da hannun Husaina ta tare ko ina, ga y’an Ta’addar da suka zagaye su.

FUNTUWA LOCAL GOVERNMENT KATSINA STATES NIGERIA

“Ke Nana zaki fad’a mana, gidan ubanwa kika samo wannan kud’in, ko sai na mak’ure kin mutu kowa ma huta?, Ashe dama acan Abujar haka kike yi gidan mutane yawon bazan, da tsayawa da samarin banza?, Suke baki wa’innan kud’in ko kuwa?”

Cewar Inna Saude dake zaune a Babban parlon, gidan da take aiki. Da aka aika kiranta yau tazo an dawo mata da d’iyarta Nanah a bisa da bata jin magana ko kad’an, a can Abujar. Shi yasa tajawo Jafaru suka taho tare suna matsifa yarinya zata ja masu salalan tsiya, so take d’an arzik’in da suke ci a yanke masu cinsa.

Kawu Jafaru ne yayi kukan kura ya zafga mata marin daya sa ta wuntsila ta fad’i tana sakin kuka. Ya ce “kin ga y’ar banzar yarinya ana miki magana kina banza da mutane kaga y’ar iskar yarinya, y’ar bak’in ciki, so kike kiyi mana bak’in ciki kenan?”

“Ya isa haka Jafaru”

Cewar Mai gidan,

“Wallahi ranka ya dad’e daka barni na barta kwance dole ta sanar damu gidan ubanwa ta samo kud’in nan”

Kamin ma Jafaru ya rufe baki Inna Saude ta tashi haye ruwan cikin Nanah sai duka take kamar ta samu k’ato.

“Subhanallahi ke Saude miye hakan?”

Cewar Alhaji yana ma Inna Saude tsawa. Dakatawa tayi da dukan nata tana cewa “Alhaji daka rabu dani in kasheta kawai wallahi. Kuma zaki fad’a min gidan uwar da kike samu kud’in nan, ko ki bari idan muka koma gida, insa wuk’a in kashe ki kowa ya huta, ni daga baya an d’aure ni”

Kuka Nanah keyi harda majina tana cewa “wallahi Inna kud’in makaranta ne fa da suke bani nake tarawa suka zama haka”

“Rufe min baki munafuka, kud’in makarantar ne zasu zama haka, algunguma sababbin kud’in bugun Abujar da nake gani yanzu sune kud’in makarantar”

Jannat da ita ce akaba Nanah take zaune wajanta ta ce “ni dai Daddy daka bari munbar ta wajan iyayenta, domin kaga yanzu ma k’arya take gaya ma iyayen nata, mu da ba bata wasu kud’i muke ba, komai muna dashi a gida, idan zata tafi babu abunda bata dafawa domin tafiya dashi har biskit da alawa ina ajewa a gidana domin dai ita da Hana idan zasu school na basu. Na maida ita kamar fa ba y’ar aiki ba kamar y’ar uwata haka na d’auke ta”

Kamin ma Alhaji ya ya ce wani abu karaf Inna Saude ta amshe da cewa “kiyi ma Manzon Allah kuyi hakuri, kun san ka haife d’an yau ne kawai amma baka haifi halinsa ba”

Alhaji ya nisa ya ce “na sani Jannat zaku koma da ita, idan ta sake ni na ce ku dawo masu da d’iyarsu. Abunda yasa na ce haka shine, ba yadda za’ai ku dawo da ita a yanzu tunda kun rik’e ta tun tana y’ar yarinyarta yanzu kuma ta zama budurwa, kune keda alhakin yi mata kayan d’aki, kinga yanzu ba yadda za’ai ku dawo da ita salin alin haka nan kawai, hakan ba adalci bane”

“Daddy shi ai ya ce a gaya masu idan ta tashi auran a gaya masa zaiyi kayan d’akin da komai ba dole sai tana wajanmu zamuyi mata kayan d’aki ba”

“Nasan da hakan, nasan Sageer dama bazai k’i mata komai ba, amma ni na ari bakinsu na ci masu albasa, a bata dama ta biyu idan ta sake ku dawo da ita, ba maganar bada hakuri kuma”

“Ai insha Allahu Alhaji bazata sake ba, shegiyar yarinya kawai”

Cewar Inna Saude dake kallon Nanah tana banka mata harara

Alhaji ya ce “kuyi mata addu’ar shiriya shine kawai ba ku rink’a zaginta haka ba, saboda shi bakin iyaye dandanan yake kama yaro ku kiyaye ma yaranku baki”

“To to to Alhaji insha Allahu”

Cewar Jafaru yana zare ido yana kyaf-kyafta su.

Bayan an sallame su suka taho akan hanya ma sai zagin Nanah suke suna kwashe mata albarka.

A k’ofar gida, Jafaru ya iske Barau Mai Caca. Da zai juyo ya gudu ai ko Barau yayi kukan kura ya cafke sa. Yana zare mai ido ya ce “ka san Allah Jafaru na fika d’anyan kai, ko ka biya ni kud’in sadakin dana biyu, na al’k’awarin da kayi min zaka bani auran d’aya daga cikin y’ay’anka mata, ko nayi ma dukan da zaka kasa tashi. Kaje ka cinye su, ko kuma wallahi na kira maka y’an Sanda su zo su tafi da kai, kuma kasan wallahi har gidan yari sai kayi”

“Dan girman Allah ba sai ta kaimu da haka da kai ba, ai nayi ma al’k’awari zan baka Mafida in….. Wata irin ashar Inna Saude ta lailayo ta dank’ara tana cewa “kutumar Uba, ai wallahi baka isa ba, uban kuturo yayi kad’an bare na makaho, ai na rantse da sarkin da ke busan lumfashi, sai dai idan bana raye, zaka d’au y’ata kaba wannan tanbad’d’an mutunan, ai wallahi sai dai ka d’au d’iyar d’an uwanka Maryam ka basa, amma ba dai cikin Yara na ba wallahi”

A dai-dai lokacin da Maryam ke kawo kai zata fito daga cikin gidan, taji abunda Inna Saude ke fad’i. Gabanta yayi wata irin bugawa, har saida ta dafe k’irjinta tana kallon mutunan da ake son k’ak’uba mata shi yanzu. Miya kai Kawu Jafaru amsar kud’in sadaki a wajan Caca na Y’ay’ansa?, wannan wacce irin rayuwa ce suke haka?. Maryam ke fad’a a zuciyarta wasu hawaye taji suna zub’o mata a kumatu. Tabbas ko zata mutu wallahi bazata auri wannan mutunan ba.

Tunaninta ne ya tsinke jin a abunda Kawu Jafaru ya ce. Wadda yasa ma jinta da ganinta d’aukewa na wucin gadi tsabar tashin hankali da firgice.

ARMAN HARUN’S HOSPITAL LOGAS NIGERIA

Tsaye take tana share hawaye, tunda aka kwantar da Y Aliyu hawayenta suka k’asa tsayawa, gaba d’aya ahalinsu a tashe yake tashin hankalin da suke ciki yasa gaba d’aya komai nasu ya tsaya cakkk. Mimi kuwa canta baro ta d’akin da aka kwantar da Y Aliyun tana sallah tana rok’ar ma d’an nata samun lafiya da addu’ar kare sirikar tata a duk inda take.

K’amshin turaransa yayi mata sallama tun kamin ya iso wajan da take, ta waiga tana masa wani irin kallo mai wuyar fassarawa shima hakane, kallonta yake duk yadda lokaci d’aya ta rame ta fice daga yaccinta. Tunda suka zo asibiti shine ya amshi Y Aliyu. A sadda Lalaah ke mai jawabin abunda ya faru tana kuka, bai san sadda ya rungumeta yana lallashinta ba, a sannan ne kuma ya sanar da ita sirrin dake cikin zuciyarsa, da ya dad’e yana dako a kanta. Ta k’asa gasgata abunda take ji yana fitowa daga bakinsa, ga wata irin fargaba data tuna cewa fa shine Yayarta Lilaah take so kamar ranta. Kawai ta fito daga Office d’in tana rusar kuka kamar wacce akai ma mutuwa.

Har yanzu hawayen sunk’i tsaya mata, koda yazo saitin inda take ya mik’a mata wani kyalle mai taushi da k’amshi ta share hawayen dake zuba mata.

Amsa tayi kawaii can taji muryarsa yana cewa “please muje Office ki zauna ki samu natsuwa”

Bin bayansa kawai tayi kamar wata sakarai.

A dai-dai lokacin kuma Lilaah ta shawo kwana zata nufi Office d’in Arman d’in. Tana gaf bud’e Office d’in taji Bilkees na kwala mata kira. D’an dakatawa tayi da bud’e Office d’in.

A cikin Office d’in kuwa, Arman na k’ara jaddama Lalaah shifa auranta yake sonyi, kuma duk duniya ita ce kad’ai ta tab’a tasiri a zuciyarsa, ita ce kad’ai yake jin wani abu dangane da ita. Ita kuwa kallonsa kawai take hawaye na mata zuba. Tama rasa miye ya kamata ta ce “wai yau ita ce Arman Harun Maleek ke fad’a yana sonta haka?, so bana wasa ba, a yadda take ganin tsantsar sonta a cikin idonsa, anya ba mafarki take ba kuwa?, Arman dai wadda ta sani shahararran likitan nan mai ji da kyau da kud’i da iko kota ina, wai yau shine zaune a gabanta yana mata magiyar ta soshi, ita kam mi zata ce ma Ubangiji. Sai dai abu d’aya ke mugun bata tsoro da damunta, Lilaah fa? miya sa abun zaizo masu a haka?” abunda take cewa kenan a zuciyarta

“Ina ta kiranki tun d’azo wayarki bata shiga lafiya dai?, Kuma naga an kwantar da Y Aliyun ku a nan hospital d’in mi yake faruwa ne Lilaah?”

“Wallahi wai sumewa yayi saboda y’an Ta’addar da suka kira shi suna shaida masa idan aka sake sa Jami’an tsaro a ciki zasu kasheta ne”

“Subhanallahi ah ahh dole Y Aliyu ya suma, masu garkuwa da mutanan nan fa ba imani ne dasu ba”

“Hmm hakane kam”

 Cewar Lilaah ko a jikinta, da kaga yarda take bata amsa zaka san ita abun bai wani dameta ba.

A tare suka nufi Office d’in domin shiga sun tura k’ofar kenan suka ji saukar muryar Arman yana cewa.

<< Kaddarar So 8

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×