Skip to content

Kaddarata | Babi Na Uku

Bookmark

No account yet? Register

Adaidai lokacinda muka tattara dukkan nutsuwarmu muna jiran muji abinda mahaifin namu zai fada sai mukaji ya fara maganarsa kamar kaha “uhm mun sameta a raye amma akwai babbar matsala amma zuwa gobe idan yansanda sun gama nasu aikin zamu taho da ita saimusan yadda zamuyi.”

Wannan kalma ta matsala da Abban mu ya ambata ya matukar tayar mana da hankali fiye da yadda muke a baya inata sake-saken wacce irin matsala ce wannan? Haka na kwana da abun araina, kashe gari da misalin karfe goma sha biyu na rana sai ga Abban mu ya shigo gida muna zaune a falo sai gashi yayi sallama ya shigo muka mike a tare nida kanwata Haleema muka nufo inda yake da sauri muna isa kusa dashi Haleema ta kama hannunsa tana murna nikuwa hankalina yana kan kofar shigowa inaso naga shigowar Fatima zarah.

Ganin bata shigo ba yasa nafito daga falon na duba tsakar gida nan ma banganta ba nawuce kaitsaye kofar gida tunani na ko tatsaya ne dauko kaya da niyyar na tayata daukowa nanma dai bangantaba hakan yasa ni nayi saurin komawa cikin gidan ina zuwa sai nace da mahaifin namu “Abba ina Zarah?” Kamar yadda yake kiranta.

Sai ya juyo ya fuskanceni yace mundawo tare amma nabarta a asibiti za,a dubata bari mamanku tadan hada abinci da dan ruwan zafi sai muje asibitin muga likitan cikin kidima nace dashi bari nafara tafiya said ku kataho daga baya.

Haleema dake gefe azaune tayi saurin mikewa tace eh Abba zamu tafi tare da yaya saika biyomu idan ka huta Abban mu yayi murmushi sannan yace kukayi jiran kwana guda ma sai jiran awa daya ne bazaku iya ba kubari dai mutafi tare nima bawani jimawa zanyi ba dan nasan likta zaiso ganina akusa.

Dole muka hakura Abban mu ya gama duk shirin da ya kamata mama tagama abinci da shayi ta zuba mana muka dauka muka tafi asibitin.

Nayi zaton asibitin uncle bala zamuje likitan da yake duba Abban mu kuma abokinsa na yaranta amma sainaga muntafi wani asibitin na daban nayi mamakin hakan har zan tambayi Abban mu amma saina nayi shiru ina jiran naga inda zamuje.

Wani babban asibitin idanu muka je muna shiga kaitsaye muka wuce ofishin babban likitan asibitin muna zuwa kuwa muka shiga gaba dayan mu bayan likitan sungaisa da Abban mu sai yayi masa iso da ya zauna nantake kuwa yazauna a kujerar da ke fuskantar ta likitan suka fuskanci juma muma da muke tsaye abayan Abban mu sai muka gaishe shi bayan ya amsa sai yayi nuni izuwa wata kujera mai gurin zaman mutum biyu dake gefe yace damu mismillah kuzauna acan.

Muna gefe a zaune amma gaba daya hankalina yana kansu inaso naji abinda za,a ce sai naga likitan yafara dacewa akwai abinda yake damunta ba wai matsala ce ta kwayar idon ba akwai wasu jijiyoyi wanda sune maganadisun da yake hada kwayar ido da kwakwalwa harma da kashin dake bayan mutum da zuciyar sa.

Kamar dai yadda wayar A.V take hada da D.V.D ko receiver tayadda T.V zata haska abinda ke cikin receiver to suma kamar haka ne sune suke mika sakon abinda ido yagani izuwa kwakwalwa har tagane abinda tagani wanda a turabce ana kiransu da suna optic nerve.

To sakamakon buguwa da tasmu ta dalilin wannan hadarin wannan jijiyoyin sune wani ya cushe wadannan jijiyoyin wannan sakon baya zuwa ga kwakwalwar shine yasa ganinta ya dauke.

Sai ya mikawa Abban mu wata takarda yace wadannan sune magungunan da zatayi amfani dasu zai taimaka wajen ganin sundawo yadda suke Abban mu yayi masa godiya sannan yakarbi takardar muka wuce kaitsaye izuwa bangaren sayarda magani muka sayi magungunan gaba daya.

Nikuwa tun lokacinda muka zauna a ofishin likitan nan gaba daya hankalina yana kansu har yagama yiwa Abban mu bayani hankalina yayi matukar tashi da naji wai Fatima Zarah bata gani yanzu.

Har mukabar ofishin mukaje muka sayo magungunan nan hankalina baya jikina kawai tafiya nake jikina jinsa nake kamar ba nawaba muna zuwa kofar shiga dakin da take kawai sai na tsaya cak har sunshige sannan suka juyo suka ganni atsaye akofar dakin Abban mu yace dani shigo mana amma ban ko motsa ba sai kawai naga haleema ta matso kusa dani tarike hannuna tajani izuwa cikin dakin.

Muna dakin muka isketa azaune idanunta abude tamkar tana ganinmu har muka karasa inda Fatima zarah take Abban mune yafara magana yace da ita Zarah ya jikin naki.

Maimakon ta bashi amsa sai kawai mukaga ta fashe da wani irin matsanancin kuka tana fadin Abba bana gani bana ganin komai Abba shikenan nazama makauniya Abba wayyo Allah na nashiga uku dama nima mutuwa nayi hatsarin yafimin rayuwa babu ido nazama nauyi akanku.

Abba ne yayi saurin katseta da cewa subhanallah Zarah banyi zaton jin wannan kalaman ba daga gareki amatsayinmi na yarinya mai hankali da ilimi yakamata kisani Allah yana gani kuma yana sane kidauka hakan jarrabawa ce kiyi kokarin cinyeta kuma ma ai lokita ya tabbatar mana da cewa na wani dan lokacine kawai komai zaidawo daidai kawai kedai kidage da shan magninda aka baki idonki zai bude kamar yacca yake ada.

Nikuwa tun sanda naga halinda tashiga tsananin tausayinta ya kamani nakasa rike kaina wasu zafafan hawaye ne suke sauka kan kumatuka na sai kawai nayi sauri nafice nabar dakin nadawo waje na zauna naci gaba da zubarda hawayena sai bayan wani lokaci sannan Abba yafito yace mutafi muka taho mukabar haleema ta kula da ita

Kashe gari kin zuwa asibitin nayi wanda kuma aranar aka sallamosu muna zaune suka dawo Abban mu ne yafara shigowa saiga haleema ta riko hannun Fatima Zarah sun shigo tana yi mata jagora koda na hango su sai kawai na mike tsaye wani sabon hawayen yasake zubowa akan fuska ta.

Ko motsawa banyi ba har sukazo suka wuce suka wuce dakin su nikima kawai nama fice nabar gidan. Saida nayi kusan sati nakasa zuwa ma nahadu da Fatima zarah saboda tsananin tausayi da banma san abinda zance mata ba.

Sai wata rana nadawo gida natarar haleema batanan mama tana kitchen tana girki Fatima zarah ita kadai ce afalon tana zaune kan kujera ina shiga nayi sallama sai ta amsa sai nayi shiru bance komai ba itama shirun tayi danaga haka saina kara matsawa inda take muryata na rawa nace da ita ya jikin naki. Muryarta asanyaye tace dani da sauki kanta akasa ko dagowa batayi ba.

Saina zauna anan kusa da ita nace kinadai shan magungunan nan ko tace eh inasha amma haryanzu dai babu wani sauyi nace da ita ki kwantar da hankalinki dan likita ya tabbatar mana akwai wanda sukeda matsalar da yamafi naki kuma sun warke sunci gaba da rayuwa kamar basuyiba kawai dai kidage da shan magani haka dai nayi ta amfani da kalmomin kwantar da hankali ina rarrashinta hardai naga tafara sakin jikinta.

<< Prev | Next >>

How much do you like this post?

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found this post interesting...

Follow us on social media to see more!

nv-author-image

Umar bin Ally

Graphic designer Fashion designer Songwriter Listener Thinker Singer WriterView Author posts

Share the post on social media.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.