Skip to content
Part 1 of 10 in the Series Kaddarata Ce by Fatima Dan Borno

Tafiya take yi, ba ta san inda za ta je ba, fuskarta a cukurkuɗe. Inna ce ta aiketa, amma ba ta son ta je aiken, sakamakon mummunan mafarkin da ta yi. Tana ji a jikinta muddin ta tafi gun aiken wani abu zai iya samunta.

Kafin ta fito sai da ta ɗibi toka ta shafa a fuskarta, hakan bai yi mata ba, har sai da ta ciro ɗankwalinta tasa a cikinta alamun tana da juna biyu. Sauri sauri take yi tana waige. Duniyar ba ta yi mata daɗi.

Ba tare da ta ankare ba ta ji antaka birki da ƙarfi, hakan yasa ta rintse idanunta.

Mutumin ya fito ransa a ɓace ya kama kafaɗunta ya ce,

“Ke! Kina da hankali kuwa? Ko baki kallon titi ne?”

Suhailat ta ware manyan idanunta, a lokacin da hawaye suka sami daman zubowa. Jikinsa ya yi sanyi, a lokaci guda ya ji soyayyar macen da babu marabanta da mahaukaciya ya shige shi.

“Ka yi haƙuri.”

Ta furta tana ƙoƙarin janye hannayensa a kafaɗunta. Shirun da ta ji ne yasa ta ware idanun tana dubansa. Gabanta ya faɗi da ƙarfi. Ba dai abin da take gudu ne zai faru ba?

A hankali ya yi magana, “Sannu ba ki ji ciwo ba? Zo mu je in kai ki gida.”

 Suhaila ta yi saurin goge hawayen tana faɗin,

“Ka bari kawai na gode.”

Da alama yana da kafewa, yadda ya shagala a kallonta yana murmushi,

“Ni kuma na ganki Inaaa…”

 Tsawa ta daka masa jikinta yana kyarma,

“Me kake son cewa? Ko ba ka ga ci…”

Ta kasa ƙarasawa sakamakon shafa cikin tsumman da ta yi, ta ji babu komai. Idanunta ta mayar ƙasa, a lokacin ta yi arba da ɗankwalin ya faɗo ƙasa. Kawai ta fashe da kuka tana cewa,

“Don Allah don Annabi ka fita a rayuwata. Ni mahaukaciya ce, ba kalar macen da za ka iya so bane.”

Ta juya kawai tana kuka. Kai tsaye hanyar gida ta nufa jikinta yana sake riƙidewa. Mashkur bai haƙura ba, ya bi bayanta har ya ga gidan da ta shiga. Ya saki ajiyar zuciya ya wuce gun aikinsa.

 *****

“Assalamu alaikum wai ana Sallama da Suhaila.”

Ras! Gabanta ya faɗi. Ta dubi Abbanta yadda yake dubanta, sannan ta mayar da kallonta agun Inna kishiyar mahaifiyarta. Dukkansu suka yi mata halin ko in kula. Ta miƙe a sanyaye za ta shiga ɗaki, Abban ya kirata yana mazurai,

“Za ki wuce ko sai na sassaɓa maki?”

Tana kuka ta fita. Mamaki ya rufeta, ta dube shi kamar ta yi masa rashin mutunci, sai kuma ta fasa ta ƙaraso kusa da shi, kawai ta fashe da kuka.

“Kayi wa Allah ka rabu da ni. Ƙaddarata ba mai kyau ba ce. Idan ka matsa sai ka yi soyayya da ni, rayuwarka ce za ta shiga cikin hatsari.”

Mashkur ya yi murmushi,

“Kada ki damu da komai. Duk abin da ya sami bawa da sanin Allah. Ni da gaske nake sonki.”

Suhaila ta duƙar da kai, tana tunawa da Mahmud.

Duk yadda ta so ta kauce masa hakan ya gagara, dole ta miƙa kai suka fara soyayya mai tsafta. Babu irin gulmar da ba a kawo masa ba, amma ya toshe kunnansa.

*****

Yau kwana uku kenan, bai zo inda take ba. Gabanta kuwa sai faɗuwa yake yi. Dole ta shirya ta je unguwarsu kasancewar ya nuna mata har gidan iyayensa.

Ta jima tana kallon ƙofar gidan da yake cike da jama’a. Tana nan tsaye ƙafafunta sai rawa suke yi. Da ƙyar ta iya ƙarasowa gaban wani mutum da yake waya ta ce,

“Don Allah Mashkur nake nema.”

Mutumin ya cire wayar a kunne yana dubanta duba na mamaki,

“Wani Mashkur ɗin da yau kwana uku da rasuwarsa?”

Cak! Ta ji numfashinta yana barazanar ɗaukewa, tana ja da baya, a lokaci guda jiri mai ƙarfi ya kwasheta, ta zube ƙasa. Mutumin ya ƙaraso yana Salati. Hakan ya jawo hankulan jama’a aka yi kanta. Tuni ta sume a wurin.

Farfaɗowa ta yi ta ganta a wani ɗaki. Ta ware idanunta tana fatan ace mafarki take yi. Idanunta fes akan hoton Mashkur fuskar nan babu fara’a, hakan yasa ta fasa ƙara tana faɗin,

“Mashkur kada kayi min haka, don Allah kada ka tafi ka barni.”

Wata farar mata da wasu mata suka ƙaraso gareta. Sai kuma suka fasa kuka. Matar tana cewa,

“Mashkur na yafe maka, baka taɓa yi min laifin komai ba. Allah Sarki Mashkur lafiya muka kwanta da shi, ashe a ranar zai tafi ya barmu.”

Suhaila ta ƙurawa sama idanu, idan bata yi ƙarya ba maza biyar kenan suka yi irin mutuwar nan, don kawai sun ce suna sonta. Mahmud sai da ana gobe ɗaurin aurensu ya mutu.

Miƙewa take ƙoƙarin yi tana cewa,

“Idan ni ɗin mai mutunci ce, ya kamata in daina soyayya, ya kamata in haƙura da kowa. Mashkur ka tafi. Ni kuma irin tawa ƙaddarar kenan?”

Mutanen ɗakin sun so su hanata tafiya, amma sai ta tirje akan dole za ta tafi. A wahalce ta iso gidansu, ta faɗa kan shimfiɗarta tana kuka da iya ƙarfinta.

Inna ta shigo tana tambayarta ko lafiya irin wannan kuka? Ido jajir ta ɗago ta ce,”Inna shi ma Mashkur ɗin ya mutu. Inna na shiga uku na lalace.”

Ta sake rushewa da kuka. Inna ta ƙwalalo idanu, a lokaci guda ta ƙwalawa Abba kira ya shigo yana tambayar lafiya? Ta dube shi ta ce,

“Mashkur ya rasu. Shima ya bi bayan sauran.”

Abba ya yi tsaye yana jin tarin damuwa a zuciyarsa. Gabansa ya faɗi da ya tuna da yadda iyayen Mahmud suka so suyi Shari’a da su akan mutuwar Mahmoud.

Bai iya cewa komai ba ya koma ya zauna yana tunanin anya ba zai tura Suhaila gidan Yayansa da ke Abuja ba? Yana tsoron abin da zai iya zuwa ya dawo anan gaba. Tunda ya yi namijin ƙoƙari wajen kaita gun malamai, amsa ɗaya dukkansu suke bashi,

“Lafiyar ‘yarka ƙalau, kuma mijinta yana nan.

Suhaila tana nan kwance kafin wani lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufeta. A hankali take tuna kalamansa na ƙarshe.

‘Ke kika san ko ba zan ga lokacin aurenmu ba?’ Tabbas kalaman da suke faɗa mata iri ɗaya ne, bambancin ba zai wuce yadda kowannensu yake zuba labarinsa ba.

Abba ya zaune ya yi tagumi. Ita kenan ‘yarsa sai kuwa ƙanwarta Hafsat  ita kuma Inna ce ta haife ta bayan mutuwar mahaifiyar Suhaila. Ita kanta Hafsat ɗin ta girma dan ta kammala ƙaramar sakandire ɗinta. Inna ta shigo da gudu tana kiran Abba. A hanya suka ci karo da juna.

“Ka zo Suhaila ta sume.”

Da Suhaila tasan ƙaddarar da suman da ta yi zai jawo mata, da ta hana kanta damuwar da za ta yi sanadin kaita ga suma.

Cikin gaggawa aka fita da ita, Abba ya buɗe tsohuwar motarsa aka sakata a ciki sai babban asibitin Maƙarfi.

Likitan da ya dubata, yasha baƙar wahala kafin ya shawo kan matsalar. Ya fito yana duban Abba cike da damuwa.

“Alhaji me ya firgita Suhaila haka har ta yi irin wannan suman?”

Ba tare da wani nazari ba, Abba ya ce, “Wanda za ta aura ne Allah ya yi masa rasuwa.”

Daga likitan har Nurses ɗin wurin sai da jikinsu ya yi sanyi. Likitan ya koma ya zauna, ya riƙe kansa. Babu abin da idanunsa ke hasko masa kamar fuskar Suhaila. Ya sake lumshe idanunsa yana tunawa da yadda ta ware manyan idanunta akansa, kafin ta sake rufewa. Sosai yake jin wani abu mai kama da so, yana huda sassan jikinsa. Dole ya ware idanunsa ya rubuta magunguna ya miƙawa iyayenta.

Ya kasa jurewa dole ya koma ɗakin da take kwance, ya jawo kujera kawai ya kafeta da idanu. Kamar ance ta buɗe idon, ta ware su dukka akan fuskarsa.

Matashi ne wankan tarwaɗa, ba za ta iya tantance dogo ne ko gajere ba kasancewar yana zaune ne, amma duk da haka bai da alamun gajarta. Irin kallon da yake mata yasa ta sake ware idanunta. A lokacin bugun ƙirjinsa ya tsananta.

“Kina da kyau.”

Ya furta mata, a lokacin da kyawunta ya sake fizgo Shi har ya yi kalaman da bai taɓa jifan wata mace da shi ba.

Sai a lokacin hankali ya shiga jikinta, ba za ta mance abubuwan da suka faru da Sulaiman, Shamsu, Abdulƙadir, Mahmud da kuma Mashkur ba. Don haka ta tashi zaune jikinta yana rawa, hawaye suka wanke mata fuska. Kai tsaye ta fara magana bakinta yana rawa, “Kada ka ce kana sona don Allah. Duk wanda ya ce yana sona mutuwa yake yi. Don Allah ka nisance ni.”

Doctor Adnan ya dubeta Yana murmushi. Gabaɗaya ya ɗauki maganarta a matsayin sumbatu. Don haka ya kama hannunta da ke ɗauke da ƙarin ruwa ya ce, “Kwantar da hankalinki Suhaila. Kin ga baki da lafiya koma ki kwanta.”

Babu musu ta koma ta kwanta. Gaba ɗaya ruɗe take kawai jiran Abbanta take ya zo.

Tare suka shigo da Abba da Inna, Hafsat tana biye da su da kwandon abinci a hannu. Ta ware ido za ta fara magana, idanunta suka sarƙe da na Adnan, ta yi saurin rufe idanun. Dakta ya yi murmushi ya ce,

“Abba tsorona take ji. Yanzu ku zauna da ita zan je gida an kirani hawan jinin mahaifiyata ya tashi zan je in dubata.”

 Abba ya ce,

“Assha! Allah ya bata lafiya. Mun gode da ɗawainiya, Allah ya biyaka.”

 Adnan ya ƙara so har gaban gadon Suhaila ya yi magana a hankali,

“Ina fatan indawo insami kin cinye abincin Umma dukka.”

 Ta yi masa banza kamar ba ta ji me ya ke cewa ba. Yana fita Suhaila ta tashi zaune ta fashe da kuka. Abba ya haɗa rai, “Wai ba za ki daina kukan nan ba?”

 Jikinta yana kyarma tana ajiyar zuciya tana nuna ƙofa,

 “Abb… Wai wai cewa zai yi yana sona. Abba don Allah mu gudu kafin ya dawo.”

 Daga Abba har Inna suka zaro idanu. Babu bata lokaci Abba ya miƙe yana haɗa kaya,

“Ku tashi mu je, wannan bawan Allah mai kirki ba zamu taɓa so wani abu ya same shi shi ba. Ke Hafsat! Maza leka Reception duk nas ɗin da kika gani ki kirawota.”

Hafsat ta fice tana sauri-sauri, domin ita kanta tana shan gori akan Yayarta mayya ce tana cinye samarinta. Suhaila ta sake rushewa da kuka. Abbanta ya fi kowa bata tausayi. Wata nurse ta shigo tana duban su da mamaki,

“Doctor ya ce ku jira shi me ya sa kuka sauya shawara yanzu-yanzu?”

Abba ya ɗago yana zazzare idanu,

“Ki cire mata ƙarin ruwan ku sallame mu mun fasa zaman. Ko ba ki ga ta sami lafiya bane?”

Dole ta cire mata ƙarin ruwa ta ɗauko files ɗinsu ta kaiwa wani Doctor ta yi masa bayani, ya sa hannu aka rubuta masu Sallama.

Abba ya kwashe su a motarsa sai gida.

Haka suka wuni sukuku.

Shi kuwa Adnan bai sami daman dawowa ba saboda jikin mahaifiyarsa ya matsa, sai washegari ake gaya masa yadda aka yi. Hankalinsa ya tashi matuƙa, dole ya ɗauko file ɗin su ya cire address ɗin gidan.

Da misalin ƙarfe takwas na dare, suna zaune a ƙaton tabarman, suna cin tuwo. Tsakar gidan ya wadatu da hasken wutan lantarki. Sallama suka ji cikin muryarsa da bata ɓoyuwa.

Sanye yake da ƙananun kaya, wanda ga dukkan alamu shi ma’abocin son ƙananan kaya ne. Kai tsaye ya ƙaraso tabarman ya cire takalmansa ya hau ya zauna yana duban Abba.

“Abba yaushe ka cire ni daga cikin ‘ya’yanka? Saboda ni kuka bar asibitina?”

Yana maganar kamar zai yi kuka. Suhaila ta kasa ci-gaba da cin tuwon idanunta suka kawo ƙwalla. Abba ya girgiza kai “Ba haka bane Doctor. Ta ji sauƙi ne shiyasa.”

Murmushi ya sakar mata a lokacin da ya kamata tana satan kallonsa, a lokaci guda ɗauki buta ya wanko hannunsa ya tsoma hannun a kwanon tuwon Abba ya fara ci.

“Abba daga yau ni ne babban ɗanka, ita kuma Suhaila da wancan ƙannena.”

 Adnan irin mutanan nan ne ‘yan boko, don haka cikin dabara yasa kowa ya daina ɗari-ɗari da shi. Abba bai ɓoye masa komai ba game da irin matsalar Suhaila. Sai da ya yi shiru sannan ya ce, “Abba a cikin abu uku dole akwai ɗaya, ko wani ke wannan aikin, ko aljanu, ko kuma mayu ne suke bibiyanta. Amma duk da haka kada ku yarda da irin wannan abun. Duk wanda ya mutu lokacinsa ne ya yi. Na yi maka alƙawarin zan tsaya tsayin daka sai na gano ko menene. Fatana ka amince min akan Suhaila.”

Abba ya ji daɗin kalaman Adnan.

 *****

Kwanaki suna zuwa suna wucewa, watanni suna zuwa suna wucewa har zuwa shekara. Adnan ya yi amfani da kaifin hankalinsa ya cusawa kowa a gidan ƙaunarsa. Ita kanta Suhaila har ta mance komai, ta faɗa dumu-dumu cikin sonsa. Yaya take kiransa, shi kuma ya ce ƙanwata. Idan Adnan ya yi kwana ɗaya bai zo ba, hatta Abba sai ya shiga damuwa. Abincin dare kuwa tare da Abba suke ci. Yakan zauna yasha hira da Inna, sannan ya dubi Suhaila ya ce,

“Ƙanwata zo mu je musha namu hirar.”

 Abin da basu sani ba, Adnan ya duƙufa neman dalilin da ya sa samarin Suhaila suke mutuwa.

*****

Tana zaune a tsakar gida tana wanki, ta ji ƙamshin turarensa, hakan yasa ta ɗago cikin mamaki. Suka kafe juna da idanu, kafin ya kai hannu zai tsone idanun ta yi saurin kauda kai,

“Kinsan me ke saurin sanya namiji ya kamu da sonki?”

 Sunkuyar da kan ta yi tana murmushi. Shi ma ya jawo wata kujera ya zauna ya tsoma hannunsa a cikin bokitin.

“Suhaila! Dubeni.”

Ya jima bai kira sunanta ba, tun suna asibiti. Don haka ta ɗago, sai dai ta kasa kallonsa, kamar yadda ya buƙata.

 “Da gaske nake yi maki. Duk rintsi ki kaucewa haɗa ido da kowane namiji, kuskuren yin hakan shi zai sa wasu mazan su yi ta binki su ce suna sonki. Idanunku su ne dafin da har yanzu ba ki gane hakan ba.”

 Sunkuyar da kanta ta kuma yi, tana jinjina maganarsa gaskiya ce, muddin ta haɗa ido da wani sai ya biyota.

“Yanzu bikinmu ya kusa. Hajiya ta ce ta gaji da ganina babu mata. Yaushe kike son mu zama miji da mata? Ko sai kin fara babbar makaranta?”

Suhaila ta ɗago cike da damuwa,

“Don Allah ka daina yi min maganar Auren, nafi son in dinga kallonka a haka. Ka bari mu mutu a haka ba tare da mun yi auren ba.”

Ya yi murmushi yana jin daɗin kalamanta, musamman da yau ba ta yi masa rowar muryarta ba. Sai da ya matse hijabin da ya wanke ya sa a bokitin ɗauraya, ya ɗauki rigar Abba yana ci-gaba da wankewa sannan ya dubeta,

“Nasan abin da kike tsoro. Sai dai tuni na fara gano dalilan faruwar wannan abubuwan. Na yi maki alƙawari gobe Insha Allahu zan zo a gaban Abba zan gaya maku abubuwan da na gano akan rayuwarki. Ka da ki damu mutuƙar ina raye ni zan zama bangonki, ba zan taɓa barin idanun nan su zubar da hawaye ba.”

Suhaila ta tsame hannunta daga wankin ta ce,

“Yaya ka gaya min yanzu ina son ka gaya min.”

Ya girgiza kai yana murmushi.

Ya miƙe yana shanya sauran kayan Abba da ta riga ta wanke, ita kuma tana ƙara baza sauran kayan don su yi saurin bushewa.

A lokacin idanunta suka hasko kan zoben hannunsa,

“Ka bani zoben nan ya yi min kyau.”

Ya dubi zoben, kakarsa ta bashi zoben na magani ne, yana hana duk wani mugun abu isowa gare shi. Yana son Suhaila yana jin daɗi idan ta tambaye shi abu. Don haka ya zare zoben ya miƙa mata,

“Zan kiraki ingaya maki mahimmancin zoben nan. Ki riƙe shi da daraja.”

Kaddarata Ce 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×