Skip to content
Part 10 of 10 in the Series Kaddarata Ce by Fatima Dan Borno

Bayan ya gama ya yi masu test. Har gaban Suhaila ya je ya karɓi takardarta, sannan ya koma ya zauna ya ce kowa ya kawo nasa.

Bayan an fita kowa yana ta zirga zirga amma ita Suhaila ta nemi wuri ta zauna ta yi tagumi kawai tana tariyo yadda abubuwan suke faruwa.

Ji ta yi an cire mata tagumi, ta ɗago fararen idanunta ta dube shi. A Zuciyarta ta ce,

‘Kana da kyau Yaya Farouk. Dole Ummi ta kasa yafe min.’

Abinci ya miƙa mata ya ce,

“Me ya sa baki karya ba kika fito? Da izinin wa kika zo Makaranta?”

 Ta ɗan duƙar da kai ta ce,

“Malamin mu baya son wasa da karatu, zai iya bani Carry Over muddin ban sami Test ɗinsa ba.”

Ya girgiza kai kawai, baya son doguwar magana, ya miƙa mata abincin ya wuce. Har ta daina hango shi bata bar kallon hanyar da ya bi ba.

Ta buɗe abincin za ta ci, ta ji an buge roban, ta ɗago a firgice. Ummi ce da wasu tsagerun ƙawayenta, abin har ya bata tsoro,

“Ummi menene haka? Abinci ne fa kika buge.”

Ummin ta zaro mata idanu,

“An buge ki ɗauki mataki. Banza kawai mayya dangin mayu. Tunda kika yi min ƙwacen miji mun ƙulla kenan.”

Suhaila ta miƙe tana dubanta,

“Dangin mayu? Kina nufin danginki dangin mayu ne? Ummi ubanmu ɗaya da ke dan kin zageni ba zan ji zafinki ba. Ya kamata ki fahimceni bansan lokacin da mijin da zaki aura ya zama mijina…”

 Ji ta yi an ɗauketa da mari, kafin ta dawo hayyacinta Ummi ta ci kwalar rigarta.

 “Ubana ba talaka bane, don haka ubanki daban ubana daban, cin arziƙi ya kawoki gidanmu.”

Farouk ya ƙara so bai ce komai ba, zuciyarsa tana tafarfasa ya sa hannu ya cire hannun Ummi daga jikin Suhaila, ya kamo hannunta kawai suka bar wurin. Suhaila ta dinga shanye kukanta har sai da ya ajiyeta a Office ɗinsa sannan ta fasa kuka tana shessheƙa. Bai ce mata komai ba, ya fice kawai. Ya dawo ya ajiye mata abincin, ya sake ficewa, ta ɗauki abincin saboda yunwa tana cusawa, sai dai cikin ya riga ya cushe da baƙin ciki. Ya sake dawowa yana dubanta, ya kasa ce mata komai har ta fice daga Office ɗin saboda lokacin shigarsu Lecture ya yi.

Har aka gama yi masu karatu bata san me ake cewa ba. Tana fitowa kanta a ƙasa, Ummi ta sake shan gabanta da waya a hannunta tana waya,

“Eh Momi yanzu kuwa zan fasa mata kai inga abinda zai faru.”

 Dutse ta ɗauka hakan yasa Suhaila rintse idanunta domin tasan babu abin da zai iya hana Ummi aiwatar da ƙudirinta. Ji ta yi anriƙe hannun, hakan yasa Suhaila da ta ji shiru buɗe idanunta. Yanayin da ta ga Farouk abin ya firgitata, ba ma ita ba hatta Ummin ta gigice da irin yanayin da ta ga Farouk, cikin wani irin ɓacin rai. Ji kake tas! Tas!! Ya ɗauketa da mari yana huci, ya riƙeta sosai ya juya da ita yana wani irin huci. Suhaila ta durƙusa kawai ta fasa kuka mai cin rai kuka take yi na tausayin kanta, duk irin zumuncinsu yau Ummi ta watsar da komai. Duniyar gaba ɗaya ta yi mata ƙunci. Ji ta yi andafa kanta, hakan yasa ta ɗago. Momi ce hannunta riƙe da wata ‘yar roba, wanda babu komai a ciki sai Acid. Murmushin mugunta kawai take yi.

Tun kafin tasan abin yi, ta ji an buge roban da Momi ke ƙoƙarin watsawa Suhaila,hakan yasa duk suka dubi mai wannan aikin. Ƙawarta ce Sadiya tana riƙe da ƙugu cikin masifa take cewa, “Wannan mata da gani so kike ki cutar da Suhaila, me ta yi maki? Menene a cikin gorar can?”

Sadiya ta yi ƙoƙarin ɗaukar gorar, sai dai tuni Momi ta ɗauke ta ɓace daga wurin. Tana tafe tana waige. A zuciyarta ta tsinewa Sadiya yafi a ƙirga.

Suhaila ta ƙanƙame Sadiya kawai tana aikin kuka, so take ta ga mahaifinta, shi kaɗai take kewa a duniyar nan. A haka Farouk ya dawo ya samesu, bai ce komai ba ya jawo hannunta ya kaita har gun motarsa, ta Shiga shima ya shiga suka bar harabar Makarantar. Har suka iso gida kuka take yi, shi kuma bai ce mata uffan ba. A falo duk suka ja burki, ya dubeta kawai baya son ko kaɗan yana mata magana, sai idan ya zama dole. “Ki daina fita Makarantar nan, zan yi tunanin sauya maki Makaranta.”

Ta miƙe tana ɗan ɗingisawa ta ce,

“Ka yi haƙuri, in dai saboda su Ummi zan bar Makarantar nan sai dai su kasheni. Zafin rabuwa da dangina kaɗai na tabbata ba zai barni kwanciyar hankali ba.”

Tana gama bayaninta ta lallaɓa ta shige ɗakinta. Shi kuma ya fice kawai ya koma Makarantar.

Kamar a cikin magagin barci ta ji ana janta a ƙasa, hakan yasa ta ware idanunta. Anti Laila ce da Jawaheer suke janta kamar suna jan tsumma. Ba su direta a ko ina ba sai falo. Kafin tasan abun yi, Jawaheer ta fara shimfiɗa Mata belt a jiki. Tana cewa,

“Ko ubanki bai isa ya ƙwaceki ba.”

 Suhaila ta riƙe bulalan tana dubanta cike da ɓacin rai,

“Kada ki sake ambatar ubana.”

 Anti ta yi tsalle ta ɗauketa da mari,

“An zagi uban naki ki ɗauki mataki yanzu.”

Suhaila ta duƙar da kanta tana tuna kalaman Abbanta. Tuni hawaye suka zubo mata, ta durƙusa a gaban Anti tana shessheƙa,

“Anti ke kika haifi Farouk, kin isa da shi. Don girman Allah don Allah ki ce masa ya sakeni, ki bashi Umarni in har ya kasance mai yi maki biyayya ki bashi Umarni ya rabu da wacce baku so baku ƙauna. Nima na gaji da irin wannan barazanar.”

Ta rushe da kuka kamar ranta zai fita. Hakan baisa Anti ta ji tausayinta ba, sai ma dubanta da ta yi sheƙeƙe ta ce,

“Mayya dangin mayu. Ni zaki tsara da kalamai? Ki buɗe kunnuwanki da kyau ki ji, muddin na isa da Farouk ina tabbatar maki sai ya sakeki, sai na nuna maki na isa da ɗana.”

Farouk ya shigo yana duban mahaifiyarsa zuciyarsa a jagule. Yana ganin ya dawo da ita gida dan ta sami sassauci, ashe bai sani ba akan ƙaya ya sake ajiyeta. Ya ji dukkan kalamansu, zuciyarsa ta dinga sanar da shi hanya ɗaya ce kawai zai bi komai ya dawo daidai, shi ne ya rabu da Suhaila, idan ba hakan ba babu wata hanya da ta wuce juriya da haƙuri.

Har gaban Anti ya ƙaraso ya durƙusa kawai ba tare da ya iya ce mata komai ba. Ta dube shi duba cikin ido ta ce,

“Yau ina son Ka nuna min ka cika ɗan halas! Ina son ka saki Suhaila saki uku cur! Kuskurewa umarnina daidai yake da tsine maka albarka ka bi duniya. Ina son Ka nunawa wannan tsinanniyar yarinyar bata isa komai ba a cikin gidan nan.”

Farouk ya ɗaga kansa ya dubi mahaifiyarsa, Wata zuciyar tana ingiza shi akan ya saketa kawai shima ya sami hutu. Jawaheer ta ɗauko takarda ta baiwa Anti, ita kuma ta miƙa masa. Jiki babu ƙwari yasa hannu ya karɓa. Da sauri Suhaila ta haye samanta, ta kwaso duk wani abu da zai yi mata amfani idan ta koma gida, ta yi hakanne dan ta kaucewa ganin mijinta yana rubuta mata takarda, duk da ta fi buƙatar takardar amma hakan bai hanata jin gabanta yana faɗiwa da ƙarfi ba. Kafin ya yi rubutun ya ce,

“Anti ba zan iya yin saki uku ba, amma zan bi umarninki in dai hakan zai faranta ranki. Nima na gaji da irin tashin hankalin nan.”

 Anti ta ce,

“Ko nawa ne rubuta mata, nidai ina son intabbatar Suhaila ta tabbata sakakkiya, muddin hakan ya faru bani da wata damuwa ka gama min komai.”

A hankali ya yi rubutu ya naɗe takardar ya miƙa mata. Sai da ta ɗan kafe shi da idanunta masu kyau da haske sannan ta karɓa hannunta yana rawa ta ce,

“Na gode da wannan taimakon da kayi min, tabbas ni ka taimaka ba iyayenka ba. Anti na gode da wannan gudumawa da kika yi min na karɓo min ‘yancina.”

  Ta juya da ƙaramin akwatinta kawai ta fice. Yana ta jiran Anti ta fice amma fir ta ƙi tafiya, ta tsaya kawai tana sa masa albarka, shi dai shiru kawai ya yi yana saurarenta. Sai da ta tabbatar da ta yi nisa sosai sannan ta fice. Shima a ƙaggauce yabi bayanta. Sai dai neman duniyar nan ya yi mata bai ganta ba.

  Ita kuwa Suhaila ta yi nisa a tafiya a ƙasa, ta ji Horn a bayanta, hakan yasa ta ratsa gefe. Kamar ance ta ɗaga kai ta yi ido huɗu da Alhaji Marwan zaune a gaban mota Driver yana jansa. Ya dubeta da mamaki a lokaci guda Driver yaja ya tsaya daidai saitinta.

  “Suhaila ina zaki je haka kike tafe kina kuka? Shiga mota mu tafi.”

  Babu musu ta shiga baya tana ci-gaba da kukanta. Sai da suka yi nisa sannan ya ce,

“Ki yi shiru ki daina kukan, ki gaya min abin da ke faruwa.”

 Bakinta yana kyarma ta ce,

“Su Anti ne suka zo gidan suka tashi hankalina daga ƙarshe bayan nace mata ta sanya shi ya sakeni, saboda abin da suke yi min, ina kwance a ɗaki suka jawoni har ƙasa, shi ne ta ce masa ya sakeni ko ta tsine masa. Shi kuma ya bani takardata.”

  Suhaila tana bayanin zuciyarta tana suya, bata taɓa sanin haka saki yake da ɗaci ba, ta ji abin har cikin kanta. Alhaji Marwan ya dinga jijjiga kansa yana nazarin kalaman Suhaila. Zuciyarsa tana wani irin tafarfasa kamar zata faso  waje. A hankali ya furzar da huci ya ce,

“Ni ɗana na cikina zai saki matarsa ba tare da sanina ba? Ita Lailan ita ta ɗaura masa aure kokuwa? Kai Musa juya kan motar nan muje gidan Karima.”

  Babu musu ya juya kan motar, yana jinjina abin da Farouk ya aikata da wayonsa. (Karima kusan abokiyar wasansa ce wacce suka taso tare. Dattijuwa ce dan ta aurar da ‘ya’yanta dukka, daga ita sai mai aiki a gidanta, sai kuwa jikanta Suwaiba. Duk da ba a damu da kawo mata ziyara ba a dangi amma ta kasance mai son kawowa dangi ziyara shiyasa suka sake shiryawa da Alhaji Marwan. Haka kawai sai ya je gidanta ya zauna su sha hirar zumunci ya taso ya tafi. Itama tana da irin nata rufin asirin.)

   Suna shigowa Hajiya ta karɓe su da farin ciki, tana duban fuskar Suhaila,

“Wacece wannan kamar amaryar Farouk ko dai idanuna ne?”

  Alhaji ya gyaɗa kai idanunsa sun yi jazir,

“Laila ce ta sa Farouk ya saketa ɗazu, a hanya na ganta tana tafe tana kuka. Ni za a ciwa mutunci a garin nan? Ni iyalaina za su nunawa duniya ban isa da su ba? A’a ba dai ni Alhaji Marwan ba.”

Mama Karima ta zaro idanu,

“Lallai Laila ta cika mara hankali da sanin ciwon kanta. Har ta mance tana da ‘ya mace a gabanta?”

 Alhaji Marwan ya sake fusata, ta inda ya shiga ba tanan ya fita ba.

  Mama Karima ta dinga tausarsa har dai ya ɗan sassauto ya dubi Suhaila ya ce,

“Ki zauna anan gidan har zuwa wani lokaci. Kafin nan bani takardar ingani saki nawa ne?”

Ta miƙa masa yana karɓa ya warware ga abin da ya gani,

_Ban san ta yadda ake rubuta saki ga mace ba, da na rabu da ke ko dan samun sassaucin zuciyarki. Ki kama hanya zanzo inɗauke ki da zarar sun tafi. Daga baya zan sanar da mahaifina komai insha Allahu zai sama maki ‘yanci a cikin dangina._

_Watarana sai labari, aurenmu ƙaddara ce daga Allah._

Alhaji Marwan ya saki sassanyar ajiyar zuciya,

“Na tabbata idan har ni na haifi Farouk, idan ni na bashi tarbiyya bana jin zai iya aikata abinda ba tarbiyyata ba ce. Allah ya yi maku albarka. Duk da haka sai na wahalar da shi, dan ya gane mahimmancinki. Ki zauna anan gidan har zuwa lokacin da zan san abin yi.”

 Ya miƙa mata takardar ta karanta. Bata san lokacin da hawayen farin ciki ya zubo mata ba, idan ya saketa ta tabbata Abbanta zai shiga tashin hankalin da ya wuce yadda yake ciki.

  A take Alhaji Marwan ya kira Abbanta, ya gaya masa ya ɗauke Suhaila zai yi wani gyara a cikin gidansa, ko Farouk ya zo nemanta ya ce masa bai san inda take ba. Abba ya amsa masa yana mamakin dalilinsa na yin hakan.

  Haka ya kira Daddy ya ce masa yazo ya same shi anan gidan. Bayan Daddy yazo ne Alhaji ya Zayyane masa komai. Shiru Daddy ya yi daga bisani ya ce,

“Ɗazu Sadiq ya kirani Yana Gaya min Farouk ya zane Ummi saboda tashin hankalin da suka je Makaranta suka sawa Suhaila. Don Allah wasu irin mutane ne muke tare da su marasa tsoron Allah?”

  Duk ɗakin ya sake ɗaukar shiru. Ita kanta Mama Karima sai ta hau su da masifa akan su suka yi sake har hakan ke faruwa. Daga ƙarshe suka bar Suhaila anan suka fice kawai.

  ****

Farouk fa ya fara rasa tunaninsa saboda ruɗewa. Duk inda yake tunanin ganinta ya je babu ita, hatta tashar mota sai da ya je.

  Da yamma lis ya isa gidansu cikin tashin hankali. Alhaji yana zaune yana duba jarida, dukkansu yaƙi yi masu magana, hakan ya ɗaga hankulan mutan gidan.

 Farouk yana zuwa ya fuskanci babu fuska, don haka ya sunkuya a gabansa idanunsa sun kaɗa sun yi ja saboda tashin hankali,

“Alhaji na yi maka laifi, ban kasance ɗa na gari ba, na yi maka kuskuren da zai yi wahala ka yafe min.”

 Alhaji ya ɗan kauda jaridar yana dubansa. A lokaci guda tausayin ɗansa ya karyo zuciyarsa, yana kallon Laila da ‘yarta suna leƙe. Ya girgiza kai kawai ya ce,

“Duk abinda ka aikata rayuwarka ce, a yanzu kai ba yaro bane tunda kana da mata, kasan ciwon kanka.”

  Bai tsaya saurarensa ba ya shige ɗakinsa. Farouk ya zauna ya riƙe kansa yana jin shikenan kashinsa ya bushe muddin ya je gidan iyayen Suhaila aka ce masa bata zo ba. Anti Laila ta ƙara so ta ce masa,

“Ka daina wata damuwa, fushin mahaifinka na kwana biyu na rak! Yana gamawa zaka ga kamar ba ayi komai ba.”

 Farouk ya ɗago yana dubanta cikin damuwa,

“Fushin mahaifina na wuni ɗaya, masifa ce ga rayuwata, zan zama Maraya mara gata muddin mahaifina ya kwana yana fushi da ni. Anti ki taimakeni ki nema min mafita ina tsoron fushin Alhaji.”

  Anan kuma sai duk suka yi tsuru-tsuru. Jikinsa babu ƙwari ya fice kawai zuwa gidan Daddy Idan bata gidan ma zai karɓi adireshin gidan ya tafi.

  Anti Laila ta Shiga ɗaki suka yi tsalle suka tafa da ‘yarta kamar yarinya ƙarama. Wayarta ta zaro ta kira Asiya, ayayin da Jawaheer ta kira Ummi duk suna basu labari. Hajiya Asiya ta ce,

“Nima gani nan juyin duniya ya yi inbar masa gidansa naƙi tafiya. Yanzu baya magana da kowa sai su Faisal, baya cin abinci a gidan. Nikam idan har tsinanniyar nan za ta bar rayuwarmu Wallahi sun daɗe basu yi mana yaji ba. Amma Laila kin burgeni sosai, yanzu sai asan yadda za ayi a kashe auren Ummi ta koma hannun Farouk tunda dama ta ƙi yarda da shi.”

 Laila ta gyaɗa kai,

“Haka za ayi Asiya. Yanzu mu bari mu ga abin da Alhaji zai yi tukun.”

Haka suka kashe wayar suna surƙullensu.

<< Kaddarata Ce 9

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×